15
*KISHIYAR ƘABILAH 15.*
BY SURAYYAHMS.
Yola:
Wajajen karfe 4pm na yamma su Ahmed suka kammala shiryawansu izuwa gidan Alhaj Aliyu mijin kakar adiaha.
Already brother kazim Aremu daga can u.s haryay magana da wani Abokinshi mai kudi dan siyasa ne honourable sabo, nan da nan aka musu arranging motoci guda uku na kece raini da zasu je gaisuwar dashi, black colour lexus guda biyu da DBX jeep, dukan su suna zuba kyalli aka dire musu agaban hotels din snn aka hadasu da official drivers.
Dukan su manyan kaya suka saka, dan uwan mahaifinsu mai suna uncle bakre da brother hamzat sun sako shadda ubansu mai gare da hulunansu masu shegen tsada wanda daga ganin su za kasan cewa shigar tasu ta barazana ce kawai da suka shirya musu dan suja girma wa familynsu sosai, brother hamzat dimeji yasaka golden colour shikuma uncle bakre ya saka wata royal blue getzner, Banji ya saka black half jumfa bugun kamfani, Ahmed kuma ya saka full fitted jumparsa sky blue colour mai wani irin kyau da sheqi dukansu sun sako hulunan da sukai matukar dacewa da kayansun sosai.
Fadin irin kyan da sukayi dukansu acikin shigar tasu bazai iya misaltuwa ba,banda qamshin turare masu dadi babu abunda yake bibiyarsu dan a kallo daya kamasu zaka iya sanin cewa tabbas suna dashi snn sun kece raini.
Already sun siyo duk wata tsarabar gaisuwar su ta aure na alfarma wanda zasu kai gidan alhaj aliyun domin Adiaha,brother kazim ya riga ya gaya musu cewa yana son ayi komine a lokaci guda batare da bata lokaci ba,yace idan har mutanen Adiaha basuda wata matsala har kudin sadaki ya tanadar su bayar sabida baison ayita memeta jeka ka dawo tsakanin Abuja da yola.
Tun safe Adiaha take cikin zullumin abunda zatayi kafin su Ahmed suxo danko kayan da zata sakanma ya zama mata damuwa dan data gudu agarinsu batazo da kayanta ba sai wanda yake jikinta. Tay girki kala kala ta aje dan al'adarsu ne su bada abinci awajen neman aure. Komi tay ta shirya snn tay wanka tay kwalliya Karshe wani tsohon Abaya mai kyau hjy hajarat ta dauko ta bata akanda tasaka kafin suje sumata siyayya washe gari. Shekarun su yaja sosai yanzu ba wani neman kudin sukeyi sosai ba, iya dan abunda suka tarar ne suketa lallabawa ahankli sai temakon da yayan alhaj aliyun suke kawo musu.
Wajajen karfe biyar saura motocinsu Ahmed suka bayyana acikin harabar gidan alhaj Aliyu inda aka musu iso izuwa cikin babban falonsa ta alfarma.
sallama sukayi daga waje sai akazo aka shigo dasu ciki, nan suka tarda shi a falonsa tare da manyan yayansa maza su biyu, da kuma limamin da ya musuluntar da Adiaha da wani dan uwansa malam shehu.
Tunda su Ahmed suka shigo ciki Sai satar kallonsu awajen akeyi sabida yanayin shigarsu ta kece raini da wayewa.
Cike da girmamawa
Da karrawa akayi yar gaishe gaishe snn aka fara tattauna dalilin daya tarasu.
Tunda manya suka shiga tattauna zancen auren Ahmed baice uffan ba dan tunda ya rusuna kanshi ƙasa babu abunda yake tunani sai komawarsa gidan dan sosai ya gaji da batun auren nan. Iya abunda yaji awajen shine da akace musu ai Adiaha ta riga ta musulunta snn harma ta amshi sabuwar sunanta na musulunci wato REEMA BASSEY
Sunan REEMA suna ne mai kyau na larabci,duk dama wasu yararruka suna amfani dashi da wata ma'ana daban,a harshen larabci sunan REEMA yana nufin "white gazelle" or "a Good and polite at heart person"...
Sosai sunan ya dace da Adiaha dan ita yarinyace mai kyawun hali da saukakken zuciya mai taushi.
Saida akayi kabbara snn Ahmed ya daga kai shima yay dan murmushi jin kowa na mata murna, yanajin su uncle hamzat da uncle bakre suka karkare maganan nasu acikin mutuntawa.
An yarje an amince za'a bawa Ahmed auren Adiaha,saidai ko da aka kawo zancen saka rana sai dukansu suka fara yin baya baya da zancen hidiman biki musmmn ma da aka ga kamar su Ahmed din suna da shi sosai
Alhj aliyu bai boye musu komi gameda abunda ake ciki da iyayen Adiaha ba sabida inma wata hidimar biki ne zata tashi susan dacewa Adiaha fa bata da kowa ata fannin iyaye bare ace zasu mata wani hidiman aure.
Bayan ya musu bayanin hakan ne uncle hamzat yy magana cikin katse musu hanzarinsu shi yace musu subar zancen dukkan wani hidiman biki da kayan gara su zasu mata komi tunda basu rasa ba. Atakaice dai mata kawai suke so.
Jin hakan yasa Kowa yy hamdala aka sanya musu albarka, Anan aka yanke sadaki Aka ce musu su kawo ko dubu hamsin ma yayi,nan Uncle hamzat suka ciro kudi suka bada dubu dari biyu da hamsin. Snn suka ce musu sunason adaura auren ne ranar Asaba dats nan da kwana uku..nan aka tsaida magana.
Ata cikin gidan kuwa
Sosai Adiaha ta matsu dan tana mugun son taga Ahmed ido da ido yau sosai, dan sosai tay kewarshi aranta kwana biyun nan da basa tare, tana son ta fada masa abubuwa dayawa aciki harda damuwarta dale damunta aranta na rabuwa da iyayenta.
She want him to atleast hold her and comfort her abit sabida haryanzu abin bai dena damunta aranta ba.
Saidai koda aka kammala shirya komi Ahmed din ne yafara matsa wa yayansa akan su tafi kawai shiya gaji.
Alhaj aliyu ne ya matsa akan lallai su tsaya suci abincin da aka shirya domin su, musmmn ma ganin irin kayan tsaraba na Alfarma da suka kawo na auren Adiaha. Duk wasu abubuwanda yake wajen brother kaxim da bro hamzar ne sukayi shi shibaima san komi akai ba dan sosai yayunsan suke sakaltashi tun yana dan karami.
Da kyar Ahmed ya daure ya shiga cikin gidan suka gaishe da hjya hajarat a falonta wanda yawanci ma banji ne yake amsata dan Ahmed kam ya dawo musu tamkar amarya kmr wanda baison yay magana a cikinsu sosai,hjy hjara ta lura da shi yaron bakaramin jamusu aji yakeso yay ba, yanayin sa da kasaita, da kuma kamiya musammn ma dayaga jikin Adiahar na rawa akansa duk ta zautu da alaman tana sone su kebe sugaisa suka dai.
Koda ta gaishe sa acikin mutanen ma bai wani sake mata fuskansa sosai saidai kawai yay mata murmushi, batun zanca addininta saiyace mata "congrats" daganan baisake kulata awajen sosai ba sai sama sama in ana hirar lamariin tasu.
Badon banji yana ta saka su dariya yanajan su a hira ba da tuniwani zaice ko hala auren dole za'ayi ma Ahmed da yarinyar danko ruwan da adiaha ta kawo musu awajen shi baisha ba abun duk saiya dame hajy hajara ganin inda Ahmed yake dan babbasar da komi.
Bayan tafiyarsu ne hjya hajara ta dinga yima Adiaha surutayya akan behaviours din Ahmed.
Takaici kamar zai kashe tsohuwar ganin yadda Adiaha take ta murnan kayan tsarabar gaisuwar
Da suka lodo suka kawo.
A tunaninta soyayya ne yasaka aka kawo mata kayan tsaraba na Alfarma.Ga goro, ga buhunan abinci,manja, gishiri,doya,kudin katoton rago, banda kananan carton carton na wasu abubuwan.
Suna zama zasu ci abinci grand ma ta kasa hkr Cike da masifafen mita Tace Adiaha kina bani kunya fa, am actually ashame of u today.. Dolene ma yaron nn yana hura mana hanci ni banga laifinsu dasuce su zasuyi komi ba saboda kin nuna masu we are nothing,memakon ki kare martaban familynki ure here getting excited kinzo nan kinata murna akan abun duniya bakiga yadda yaron nan yake daukar kansa agabanmu tamkar wani sarki ba...
Why is he behaving like temakonmu zaiyi, mune zamu bashi mata amma
Shine yake mata fadi da jan aji ? See oo My grandoter, ki bude idonki dan Bai kamata ace Duk wann wahalar da kikayi akansa kwana biyun nn ace ko minti biyar bazai samu dominki ba, Atleast ai yasan halin da kika shiga ciki na rikici da iyayenki akansa but im deeply suprise all he has to say to u is congrat, Kai kai..nide wann abu baimin ba. He is such a jerk.
Adiaha ta bata rai sosai tace grand ma wai sau nawa zan gayamaki ne haka fa Ahmed yake, shi bamai son magana sosai ba idan kin fahimce shi sosai zakigane cewa he is a good man.
Hjy hajara batace komi ta nade hannu cikin mamaki tanata kallon yadda maganan yy ma Adiaha zafi tanata hargagin fushi.
Nan ta fara kare Ahmed akan dukkan korafin da kakartan tay, harda ce mata ai yanajin kunyan yayunsa ne shisa bai sake jiki da ita ba, snn dan yace mata congrt akan zanca addini ai dama badan shi ta sauya ba.
Babu ta yadda zaka kushe Ahmed agaban Adiaha batare da kawo maka wani dalilin da zai kare shi ba. Sai cewa take ai tausayin halin da take ciki da iyayenta tare soyayyar dayake mata ne yasaka familynsa suka ce zasu mata komi na hidiman auren and she is happy nd grateful for that.
Adiaha ta dauka duk wasu kalmomin nata datake kare Ahmed dashi agaban grandma masu ma'ana ne saidai batasan da cewa Maganganun datake furtawan yanayiwa kakarta ciwo aranta bana wasa ba.
Aranta cewa take Adiaha is blind and desperate about this guy. Batasan da cewa mutuncinta take sayarwa ba. She wont have value to them musmn ma indan sunajin kansu a matsayin cewa sune sukayi komi na aure.
Ta rasa abunda zata ce mata kawai ta fasa cin abincin ta tashi cikin fushi ta koma dakinta tabarta awajen ita kadai tana ta bawa kanta dalilai akan Ahmed na cewa lallai yana sonta ne sosai shiyasa zai aureta
Jin abun yafara dan damunta saita tura masa sakon tex a sabon layin sa and she foolishly told him cewa grand ma dinta is not really pleased with him, ganin hakan ne yasaka ya daure ya kirata suka fara gaisawa.
Rabon shi da kiranta awaya tun ranar da suka rabu a calabar dan yace mata bayason tana kirarsa koyaushe musmmn ma indan tana tare da familynta.
suna kammala gaisuwar Yy kmr bai karanta tex din sosai ba, sai Yace mata ta memeta masa meyene grand ma dintan take cewa akansa..
Tafara gaya masa duk abunda kakarta ta fada da irin bayanin da itama tay mata akanshi.
Ahmed ya daure fuskan sa sosai cikin yanayin basarwa da bata rai yace "Toh shikenan naji,.zan gayawa yayunq sai azo ayi magana a tsaida batun auren tunda grand ma dinki tace bata aminta da halina ba.
Adiaha ta kwalo ido waje tace "Ahmed meyasa zakace haka? Da Bai amsa ta ba sai jikinta yay mugun sanyi dan Sam batay tsammanin jin hakan daga gareshi ba.
Tuni yanayinta ya canza cos its seem he is gaslighting her now sabida yasan babu yadda ta iya dashi, Cike da bugun zuciya da damuwa Adiaha tace Ahmed pls ni ba hakan nake nufi ba, kay hakuri karkakai maganan gaba,grand ma is just being worried about me sabida yadda taga na rabu da iyayena duka akanka.
Cikin yanayin hade ransa Yace " okay, yanzu kenan laifina ne da iyayenki suka rabu da rayuwarki Ko dama akaina ne kika zanca addini? Zatai magana cikin katseta da shakurarren murya yace "silent,ya isa haka.
"kar ke ko kakarki ku fara tunanin daura min wani laifi akan wani abu daya shafi rayuwaki dana iyayenki sabida ni aurenki kawai nace zanyi Amma bance ki canza Addini ko ki bijirewa iyayenki akaina ba...ya lumshe ido jin tafara kuka tanamai neman tafara bashi hkri, ya kuma bata ransa muryansa kasa kasa cikin shan qamshi sosai yace ..'look ni ba hkuri nake so daga gareki ba, i' m quite disapointed in u ryt now, kukan ki bazai nuna komi min ba, nifa bangane miki ba, shin aurena zakiyi dan Allah ko dan in bauta miki dake da kakarki? Wn ai duk laifinki ne, dan inba kece kika nunawa kakarki cewa ure blaming me for ur personal issures a mind dinki ba da hala bazata fara dora bururakarta akaina ba.
"Me kakarki takeso?dan nazo gidanta shikenan sai In lashe kafarki ko in goyaki a baya na? Da nace zan aurekin is dat not enough for u ppl? why wud ur grand ma expect me to take all the burden of ur pain...nine na dauke ki daga gaban iyayenki ne ko nine nace ki rabu dasu?
Cikin tashin hankli Adiaha tace Ahmed pls listen bahaka bane kasaurareni mana
Tashi zaune yay cikin katseta tare da nuna mata bacin ransa a fili, Adiaha tafara kuka sosai ganin ya dau abunda da zafi sosai ,ransa a harzuke yace bana da lkcin wnn rigimar, yau alhamis ne, kije yanzu ki gaya mata cewa inhar bata aminta dani ba toh suy gaggawar fada ma yayuna kawai mubar garin nan yau yau,as for kudin sadaki da duk wani abunda muka kawo gidanta karsuji tsoron kin fadin mana komi mu bamu damu da wani abun duniya da muka kawo muku ba,ina son kusani cewa auren nan fa ba dole bane akaina, ko akace muku babu mata ne da suka fiki a duniya?ya kyabe bakinsa cikin yanayin basarwa, muryansa a kasa kasa yace "Ohh pls, she can marry you off to wanda hanklinta ya kwanta akai for all i care, amma dai bazan dauki laifin da banawa in dorawa kaina ba,and no one shud think of controlling my life, akanme?mace zan aura ko rai zaku ban?..
Cikin shesshkar kuka Adiaha tace Ahmed ka dau magann nan da zafi mesa zaka fadi haka
Yace Da zafi mana, daga na bada sadaki yau ko kwana daya baiyi ba sai afara tunanin juyamin tsarin rayuwata?ni ba karen mata ba, in a al'adanku maza suna bautawa mata mu bamu yi, our women are expected to be very peaceful nd respectful...
nide na fada maki, Better do sumting about it koni na fadawa yayuna da kaina..u can't insult my family..snn bana wasa da martaban iyayena ko acikin mafarki, idan har kunada matsala dani then we wll call this weding off and leave.
Yana fadin hakan ya katse wayarsa Adiaha tay rigib ta sulale kasa ta dinga rabza kuka tana cewa hello hello Ahmed pls listen, ba haka bane, sai shiru, ji tay tsoro da fargaba mai tsanani yana neman dabaibayeta.
Kukan datakeyi anan yajawo hanklin kakarta izuwa dakin hankli tashe ta yo kanta tana tambayarta ko lpya? Cike da bori ta haura mata tana cewa duk laifinki ne Ahmed yaji haushi yana fushi dani..grand ma why wud u complain about him dat way, gashi ai yace ina disrespecting familynshi, yace babu ruwanshi, wai idan kina da matsala dashi zai fasa aurena kinema min wani..
Hjy hajara ta rike kirjinta dataji ya dau zafi sai ta rasa baqincikin Adiaha kona ahmed din zata fara dubawa.
Tace Reema kina hauka ne Meyasa zaki je ki gaya masa maganan da mukayi dake anan gidan tsakanina dake? Na fada ne dan in wayar miki dakai why wud u tell him ashe bakida wani sirrin kanki komi aka gaya a gidanku sai kigawa Ahmed?
Tana kukan tace oho..
Nide kisan yadda xakiyi Ahmed ya dena fushin nan dani sabida duk kece kika jawo min,ai gashi nan yanata cewa wai zai fadawa brother dinsa cewa zamu fara controling din rayuwarshi dan ya kawo sadaki na..
Grand ma what if he call off the weding? I wll kill myself, wallai bazan iya rayuwa babu Ahmed ba.
Hjy hajara batace komi ba tsaban bacin rai jikinta sai rawa rawa yakeyi shikadansa sosai, a mugun fusace ta dauki wayar Adiaha ta dinga kirar layin Ahmed waidan ya dquka ta gaggaya masa bakaken maganganu masu zafi ta huce takaicinta amma sai bai dauka ba.
Suna cikin hakan saiga Alhj Aliyu ya shigo dakin, ganin yanayin su yasaka ya fara neman karin bayani, hjy hajara hartana kunfan baki da hawayen takaici tafara maida masa maganganu,
Tace "Alhaji kafa nemo yayun yaron nan, kace musu suzo yau yau su tattara abun duniyansu an fasa auren..sudin wa? Sudin banza.."Me Ahmd din nan ya taka? meyake ji dashi da har zai gaya min baqar maganan dayaga dama akan dan zai aure jikata? Akwai maza dubu wanda suka fishi kyau da kudi,shi ba komi bane agaban wasu mazan wllh, shashasha dashi ma wanda baisan halacci ba, wani irin wahala ne yarinyar nan batasha akansa ba har shine yau zaixo yana dagawa mutane kafada da jijiyar wuya dan anfadi masa gaskiya? Ai gaskiyan kenan baidamu da halinda Yarinyar nan take ciki ba, gani yake kmr sadakan kobo za'a bashi sam baiya kallon mutane da daraja katon bayarben banza.
Anan ne adiaha ta gane cewa ashe kakarta neman Ahmed take donta ci mutuncin awaya amma badon ta bashi hakuri ba.
Anan ma suka fara wani sabuwar cece kucen ran hjy hajara ya baci sosai alhaj aliyu kuwa yanata lura da zallan kalaman tsagwaron rashin kunyar da Adiahar ta kara fandarewa da shi.
Alhaj aliyu daya fahimce komi yajawo matarsa gefe suka bar dakin ya dinga rarrashinta har saida zuciyarta yay sanyi sann yafara gaya mata cewa hikiman daya ne zai iya budewa Adiaha ido ta gane cewa shayi ma ruwa ne, wann hikiman shine su kyaleta ta aure Ahmed din,yace mata nan da bada jimawa ba ita dakanta zata dawo bayan ta shiga hanklinta ayayin da duniya ya gama koya mata wayo.
Da kyar hjy hajara ta Amince da wann shawaran dan taso ace kawai afasa auren kodq mutuwa Adiahar zatayi, Abun nada matukar ciwo kana kallon jininka zai fada acikin halaka boro boro amma ka kasayin komi akai.
Saida ta nutsar da zuciyanta sosai snn ta iya danne komi aranta tay hakuri snn ta daura niyyar bin shawarar da mijintan ya bata akan Adiaha.
Ata fannin Ahmed kuwa tunda ya kammala waya da Adiahq bai sake kallon inda wayar take ba, duk tulon miscals dinsu da suka masa shi baisan sunyi ba, wajen hotel din da suka kama yaje ya samu abokinshi Banji yana zaune nan yafara gaya masa situation din, yace masa ai kakar Adiaha tana son ta dora masa laifin komi shiyafara tunanin fasa auren ma sabida baison rainin hankli.
Banji ya sha mamakin jin hakan, musmmn yadda Ahmed ya fayyace masa maganan da sigar cewa sunason suyi controlling dinsa with emotional blackmail dan ace ai tunda sabida shine Adiaha ta bar iyayenta da addininta dolene ya bauta mata sai yadda sukayi dashi.
Ran banji sai ya baci sosai dayaji hakan, suka ta bambami sunata kushe halin irinna matan da suka kasance yaren kakar Adiaha dake ita inyamura ce,.
Saidai Duk da hakan Banji baiyi fushi sosai da Adiaha ba, yay tunani mai kyau akanta dan yasan abun da tay ma abokinshin da wuya sosai.
Yace ma Ahmed yay hakuri yaji tausayin yarinyar sabida tana sonshi sosai..
Ayanzu ma basai an fada masa cewa Adiaha tana mutuwar kaunarsa ba, banji yace bakowace mace bace zata bar komi nata tazo domin namiji kai hatta kafayat dasuka dade suna tare baya zaton zata masa irin wnn sadaukarwan da Adiaha tay masa.
Abokinshi Banji ne ya dinga lankwasashi da dalilai kafin nan zucyarsa tay sanyi har ya rusuna yabar zancen, suka fara wani hirar na daban.
Tambayarsa yakeyi yadda zaiyi da kafayat bayan ya aure Adiaha
Ahmed Yace bai sani ba.
Amma yasan bazai bawa kowa hakuri dan bai aure ta ba, yace "rayuwar shi ce, dan haka yana da ikon da zai canza ra'ayin sa akan duk wacce yaga dama witout owing them any explanation.
Banji baice komi ba duk dama yasan akwai kura agaba.
Washe gari ranar juma'a hjy khadijatu ta idar da sallah kenan ta turawa kafayat tex message mai cike da nuna kulawa tanamai tambayarta ya jikinta kuma yaushe zata dawo, ko tazo ta daukota ne sabida gobe ne za'ay walima na komawa sabon gida and she wants her to be deir tunda a matsayin ƴarsu suke daukanta.
She care soo much about kafayat dan tunda akace mata batajin dadin jikinta kusan kowani lkci suka hadu da mijinta saita tambayeshi ko yay waya da ita amma ko wani lokci amsar dayane dukansu basu samu damun magana da ita ba
Gara gara ma shi dayake yakan samo musu bayani awajen mahafyarta.
Kafayat na zaune a bakin gadonta ta farka a barci kenan zata shiga wanka
Taji shigowar sako,jikin ta duk a muce yake dan kwana biyun nan tunanin Ahmed ne kawai yake fado mata acikin ranta musammn ma da Alfah yace babu aure a tsakaninsu.
Maganan ya shige jikinta da kwakwalrta sosai harma fiyeda yadda itakanta take zato.
Duk zuciyarta a hatsale yake da damuwa Tana kammala karanta tex din hjy khadijatu memakon taji sanyi aranta sai taji fushi da damuwa mai yawa ya hautsina mata jiki, agefe ta jefar da wayar tare da jan wata doguwar tsaki dan inhar akace Maganan Alfah ya zamo gaskiya to babu shakka an cuceta.
Jin kanta takeyi very frustrated with her life har yau haushin kowa da komi takeji aranta.
Wanka tay ta fito ta sanya english wear riga da skirt blue colour ta baza kitson attacemnt dinta ya sauko har gadon baya yana shan iska, nan ta sauko kasa izuwa falon kawar mahafinyar tata, ko ina yay shiru acikin gidan da alaman ita kadaice tasamu har sun kammala karyawan su sun fita. Ido ta daga ta sake kallon agogo ganin karfe bakwai da rabi saura na safiya
Mamaki takesha aranta dan tasansu da baccin asara, sai tarasa miyene mai matukar muhimmancin haka har da zai fitar dasu da sassafen nan. Wani zuciyar yace mata hala harkan business dinsu ne yasaka sukayi sammako
Nan ta zauna tafara hada tea makanta dan saiyaune tafara jin dama dama ajikinta, cikin nitsuwa tasha tea din da two slice of bread, ta dade azaune awajen ganin basu dawo ba har wajen karfe goma na safiya hakan yasaka taje kitchen tafara fere doya ta tafasashi yay laushi ta hau daka sakwara.
They have varieties of soups a fridge cikin kankanin lokci ta hada komi abunta hadi da cewa batada gwuyar aiki arayuwarta, bayan ta kammala komi ta fito dashi falo tanakan ci batare da sanninta ba awajen wani irin baccin bazata ya kwasheta.
Ata wani bangaren kuwa
Hjy fatihat da kawarta hjy rakiya sune agaban goddes sunata kallon ta acikin wani kwarya.
Wani ruwa goddes ta miƙawa hjy fatihat tace ta zubashi akan setin inda zucyar Kafayat yake daga cikin kwaryan.
Babu musu ta amshe goran ruwan goddess tana fada mata wasu kalmomi da yarensu itama tana nanatawa ahankli ta juye ruwan akan kirjin kafayat duka tana kammalawa sai gq wani irin yawun bacci mai yawa ya fara fita daga bakin kafayat yana zubowa acikin kwaryan
Bayan ya taru sai kafaya din ta bace musu a kwaryan bat.
Dariya goddes ta bushe musu dashi alaman aiki ya kammala, kafin nan ta daga kwaryan can sama tare da yawun kafayat din, tana saukarwa ta saka hannu aciki tq dauko wani garin magani a cikin kwaryan da ya bayyana dakansa,nan ta miƙa musu tace su bawa kafayat garin da shine zasu cimma burinsu acikin sauki.
Zuciyarsu fari tasss suka bar wajen goddesss suka dawo gidan suka samu kafayat tanakan bacci tuwonta haryay sanyi sosai.
Saida suka kammala tattaunawarsu snn hjy fatihat tace duk da sun karbo maganin daukar fansa amma batason tay ma yarta komi na dole arayuwarta, dan haka kafin suy amfani da maganan sai tay magana ta fahimta wa kafayat.
Hakan kuwa akayi kafayat ta farka a daburce ganin kan kirjinta ya gama jikewa da ruwan da batasan daga ina yafito ba
Ganin ta daburce sosai saisuka hau lallabata sunace mata wai Ac ne ta mance bata kunna ba da kuma damuwar auren Ahmed damilare data saka Aranta
Nan Suka zauna kamar mutanen kirki suka fara lallashinta sunata bata shawara kamar iyayena na gari, hjy fatihat ta nuna mata cewa ita dai harga Allah bawai bata son Ahmed bane, kawai bata son yarta ta aure namijin da baisan darajarta bane kwata kwata,tacewa kafayat inda ace Ahmed yana sonta kamr yadda take sonshi da sosai zata goyamusu baya, amma duk wata uwa bazata so taga yarta tana bautawa soyayyar namiji ba a sune sukesonkan ma ya ka kare bare ace kaine kake sonsu.
Duk suka taru suka kashe ma kafayat jiki ta hanyar nuna mata cewa duk abunda sukeyi dan suna son cigaban rayuwarta ne.
Cikin salon yaudara Hjy rakiya tace mata ai itace ta matsa wa hjy fatihat akan suje sunyi bincike da kyau akan batun aurenta da Ahmed, kuma sunji cewa maganan Alfah gaskiya ne, amma suna son su kara gwadawa. Nan ne suka fito da garin maganin suka bawa kafayat
Hjy fatihat ta hade rai salon yaudara irinta nuna bada son ranta take hakan ba saidan farin cikin yarta duk dama aranta manufarta dabanne wanda kafayat din bata fahimce wayonsu ba.
Sam basa son kafayat taga laifinsu akan komi
Su sun riga sun mince da Alfah dan bai taɓa fadin musu karya ba, babban damuwarsu ayanzu shine yadda zasu dau mummunan fansa akan famlyn bello jimada batare da kafayat ta san nufinsu ba.
Suna damka mata garin maganin suka hau yi mata bayani dalla dalla
Anty rakiya tace mata sau uku ake so tay amfani dashi akan mutanen da suke fada aji agidan su Ahmed..
Kafayat tace hjy khadijatu ne da alhaj bello da kuma anty mojushola
Sukace mata sam, koda zasu amince da sauran amma dole ne ta bar zancen hjy khadija agefe sabida itama babban munafukace itace take juyawa Ahmed kansa akanta.
Hjy fatihat tace, Alhaj bello jimada, da anty mojushola da anty ramatou sune zatay targeting dinsu da maganin.
Sann a abinci ko abunsha zata sakawa kowannensu ta dai tabbata sun shanye magananin sau uku uku.
Cike da salon yaudara Hjy rakiya tace mata wnn maganin ne zai saka kowa acikinsu ya yi iya abunda suke so akan Ahmed..
Tunda aka fadi hakan kafayat sai taji kamr andawo da haskene cikin zuciyarta, take taji wani irin farinciki mai yawa ya mamayeta, tay musu godiya tare da basu tabbacin zatayi abunda suke so din.
Bayan nan ta shirya komawa Abuja and she was planning to surprse them kowa saida ta siya masa cookies mai dadi da tsada, na anty moju da anty ramoutu duk saida ta barbada maganin aciki she also bought a very good strwberry wine too wanda akayishi da crisp of fermented strwberry fruits.
Shikuma alhaj jimada acikin wani park din dabino mai dankon nan ta barbada mashi snn ta kama hanya ta dawo Abuja.
Da fara'arta ta shigo gidan kowa na murnan ganinta, hjy khadijatu tana kallo ta raba musu tsaraba dukansu itace kawai bata bata komi ba.
Hakan bai dameta ba duk dama tanashan mamakin yadda kafayat din ta saka su agaba saida suka cinye tsarabar data basu.
evryone is happy, atleast she is back and healthy, da yamma ranar friday din itace taje tay musu girki agidan su anty moju
Tun anan ta badawa sun anty moju magani acikin miyarsu suka ci abinci.
Sann ta debo abincin a cooler ta kawo ma Alhaj bello har gida acikin sashen sa takai masa inda shikadaine zaici, tare da fruits wine din tay masa serving komi tazauna gefensa tanata zuba mashi tadi tare da nuna godiyanta akan kulawar da suka nuna akanta shida matarsa.
She said she make the food speacially for him harda drink din ma...
Tass tass ta saka shi yacinye tana ta masa murmushin da bai gane kansa ba,aranta lissafi take, ance sau uku, so ta bashi acikin dabino, ta bashi a wine, da kuma dinner, ta gama dashi kenan saura su anty mojushola, tasan gobe asabar ne ana rububin waliman komawa sabon gida hala bazata samu daman bashi maganin ba shiyasa ta gwammaci ta gama dashi ayau ta huta makanta.
Yaji dadin hirar data zo tana tayashi cos kafayat is very kind and sweet, sosai yake sha'awar ta ma dansa Ahmed koda zai shiga hanklinsa ya nitsu ya aureta cos aganinsa babu namjin mai lpyar bazaiso mace kamr kafayat ba, ta mallake komi da mata ke nema, ta iya magana tana da respect, gata da iya zama da mutane snn ta iya abinci.
Shigowar hjy khadijatu ne yasa hirar tasu ta katse, hjy khdja tana shan mamakin kafayat wai har taje can gidan su anty moju tay girki amma bata gaya mata ba bare ta kasa da ita. Batace komi ba kafayat din ta fara kame kame tana murmushi tace mata karta damu mai aiki zata girka mata spaghetti jolof dan shine takejin sha'awar ci yau ba tuwo ba. Acikin raha suka kare maganan duk dama jikin kafayat yabata cewa hjy khadijatu hala zatace ko tana fushi da ita ne.
Ita kuwa hjy khadijatu aciki kawai ta bar zancen bata nuna a fuskanta ba, tasan dolene dai akwai abunda kafayat tasaka aranta game da ita akan Ahmed. Fatar ta shine Allah ya bayyana mata gaskiyar lamarin dan wata rana tasani cewa bata mata bakinciki akan lamarinta da Ahmed.
Hirar Ahmed din suka farayi da mijinta dake duk sun bari aransu akan cewa Ahmed yana calabar ne yana aikine
Suna kan hirar su mai dadi sai ga kirar brother kazim ta video call ya shigo, da murnansu suka dauki kirar suka fara gaisawa dashi cike da nuna masa soyayya shikuma yanamai basu girmamawa sosai
Yaji mamakin ganinsu atare duk dama bukatarsa kenan ya samesu atare dan gobe ne yake son aje a daura auren Ahmed acan yola.
Baice musu komi ba tukun,iya Hirar waliman komawarsu sabon gida na gobe suka fara masa cike da nuna farincikinsu agareshi..
Hajy khadijatu take ce musu cousin din Ahmed yasra hussain zata zo yin karatunta abuja zata zauna agabanta gida zai karayin dadi with young young ones around them sunata dariya sosai.
A siyasance brother kazim ya fara shigo musu da maganan dan uwansa Ahmed,ya tanbayesu ya suke ciki da batun shirin aurar dashi?duk sun sha mamaki da sukaji cewa Ahmed damilare yana comunicating sosai da dan uwansa bayan su insuka nemeshi basa samunshi koda awaya ne.
sun fara tattaunawa akansa kenan suna kawo masa complain na yadda Ahmed yake musu taurin kai akan batun tsaida matar aurensa sai ga kafayat ta shigo wajen da plate din spaghetti dataje ta dafawa hjy khadijatu, suna jin sallamar ta suka katse maganan sukayi shiru har ta iso,tana zuwa ta ajiye wa hjy khdjatu abincin agabanta cikin girmamawa tanamai saka mata albarka, jiki na rawa ta tsuguna har kasa ta fara gaishe da brother kazim, ya amsa mata ba yabo ba fallasa tanata masa murmushi mai fadi ganin ko sake mata fuskansa baiyi ba, aranta kuwa so take yace wani abu mai dadi akanta dan tasan ko shima yana son ta ma ahmed kmr sauran family members, dake tun abakin kofa tajishi yana dan ambatar sunan Ahmed dinta duk ta dauka zancen auren ta da Ahmed din zasuyi.
Da murmushi tay masa sallama bai wani kulata sosai ba, Bayan nan ta fice a dakin domin ta basu waje, tana fita taje ta laɓe abakin kofa nan tasaka kunnenta tanajiyo maganansu daga waje.
jim kadan sai ji tayi brother kazim yana tuhumarsu akan dalilin dazai saka subar ta tana zama acikin gidansu da sunan tana jiran Ahmed ya aureta dan bata da kunya.
Kafayat tanajin yadda brother kazim ya fito fili ya kukkushe zaman datake musu agida yace musu sam babu mutunci aciki.
Shiru suka masa dan kaf din sun nan tausayin kafayat din sukeji aransu shiyasa suke bata wann gatan sosai.
Brother kazim yace sam baiji dadi ba, acewar sa mutuncin yarinya budurwa shine ta zauna agaban iyayenta namiji zaije gidansu ya nemo aurenta bawai itace zatazo har gidansu tazauna da sunan tana jiran shi dan ya aure ta ba.
Ran kafayat ta bai wani baci ba da korafin brother kazim ba sabida tasan gaskiya ya fada mutane dayawa ma sunsha gaya mata cewa she is making her self too cheap and desperate akan Ahmed msmmb datake zama agidan su akan dan ya aureta.
Haka kawai taji kmr korafin brother kazim din ya shige jikinta da mind dinta, jikintan asanyaye ta bar wajen ta tafi tabar wajen batare da taji karshen bayaninsan ba.
Kayanta ta deba ajaka ta bar gidan acikin daren ta koma gidan iyayenta da niyyar washe gari zataje nasarawa taje ta fada ma mum dinta abunda brother kazim ya fada.
Surayyahms chat *08060712446*
*Wanda ba su yi saving number ta ba su yi sai su mini magana ni ma zan saving ta su* 👍🏻
Reply with "saved" is enough😍
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top