¢нαρтєя 1

بسم الله الرحمن الرحيم

*ᴀ ɢɪғᴛ ᴛᴏ ᴡᴀʟᴇᴇᴅᴀʀʜ*🦋

Matashiyar bururwace zaune a cafeteria sae faman tsaki takeyi ita kadae Kara kallon wrist watch dinda ke daure akan tsintsiyar hannunta tayi cikin honey voice dinta tace"oh Allah it's too late" ta fada tana dafe kanta.

Wayarta da kuma dauka kirar iPhone 11 pro max zatayi dailling number kenan Kira ya shigo dauka tayi tana ya mutsa fuska"Waleedarh Kun gama class dinne?"

Dayan ban garen Waleedarh tace"yes am done kina Ina yanzu?"

Yarinyar tace"cafeteria plss kiyi sauri I have alot to do"

Waleedarh tace"ok I will catch up with you soon"

Batafi 15mins ba sae ga Waleedarh ta iso gurin zama tayi tana"washh Allah lecturer din nan bae da M wlh"

*Nasmarh* tace"hmm do u need something or we should just go?"

Waleedarh tace"no I can't eat anything now"

Tace"ok mu tafi"

Mikewa sukayi suka tafi. Fara tafiya sukayi waleedah ta riko hannu Nasma tace "wai me yasa fateemarh bata zo skl ba yau I guess something is wrong with her"

Tabe baki Nasma tayi irin she don't care din nan tace "oho" taxi suka samu Bayan ya tsaya suka shiga ya kaisu apartment dinsu,
    A matukar gajiya waleedah ta tura kofar Bayan ta bude kofar da key kokarin cire vail din da tayi rolling kanta dashi ta fara tana fadin "Nasma I think idan muka huta plss muje mu duba Fateemarh"
  Ba tare da ta bama zancen mahimmacin ba tace "alright"

_____________________________
Najeeb POV
______________________________


Cikin takun sa na takama da Izza yake tafiya sai dai duk da haka bazai hana ka gane a gajiya yake ba da sauri guard dinsa ya bude masa main door din gidan ya shiga, sanyin AC daya hadu dana turaren wuta ne suka kara bada gudummuwar saukar masa da kasala a jiki lumshe ido yayi yana budewa akan Najwah dake zaune tana game a tab dinta.
  Sallama yayi ciki ciki kamar wanda akayi wa dole, da sauri ta dago kanta bawai dan taji sallamar sa bane sai dai kamshin perfume dinsa daya sanar da ita presence dinsa gurin.

"Yah sannu da zuwa"

Ko kallon ta baiba ya haye sama abunsa yana ji PA dinsa ya mika mata briefcase dinsa, yana shiga daki ya cire necktie din da ke wuyansa tare da fara kokarin cire kayan sa. Toilet ya shiga in not less than 30mins yayi taking shower dinsa ya fito, bacci ne cike da idonsa har wani lumshewa suke dakyar ya samu ya shirya cikin kayan baccin sa cotton ya haye gado.

Mami kuwa ganin har karfe 9:24pm bai shigo gda bane yasa ta fito daga dakin ta ganin Najwah ita kadai a parlour yasa ta tambaye ya ko Najeeb ya shigo gdan turo baki tayi cike da shagwaba tace "Ehh mami yana daki"

Girgiza kai kawai tayi tana nifar dakinsa ta rasa kwana biyu meke damun tilon dan nata gaba daya ya kuma birkicewa, tura kofar tayi ta shiga ganin baya parlour yasa ta shiga bedroom dinsa. Hango sa tayi kwance saman katon Turkish bed dinsa ya rufe tun daga kansa har kafarsa da duvet yasa ta lumshe ido tana karasawa ciki ta rage masa sanyin AC din ta masa addu'a ta fice.

Bata samu Najwah a parlour ba hakan yasa ta wuce part din Abu kawai.

___________________
*Nasma POV*
____________________

Tsaki tayi na karo babu adadi tana kara gyara zaman vail dinta "waleedah wlh I will go and leave you"

Tsaki itama waleedah tayi tace "matsala na dake  kenan wlh c'mon let go"  da yake the same building ne but different apartment sai kawai suka taka a kafa, suna zuwa suka danna  doorbell ba jimawa aka bude masu frnd din Fateemarh me Aneesah da suke zama apartment daya da Fateemarh smiling tayi ganin su Waleedah ne ta basu hanya suka shiga ciki gaisawa suka fara yi da waleedah Nasma kuma ta shige ciki abunta tabe baki Aneesah tayi tace "kina fama da wannan yarinyar wlh sai uban girman kai mtsw"

Dariya waleedah tayi tace "Wlh kuwa bata da Ego kawai dai kin San kowa da yanayin sa Nasma bata son hayaniya ne"   Aneesah bata kuma cewa komai ba suka shiga ciki Fateemarh na zaune tana yatsine fuska alamar dai bata jin dadi. Dariya waleedah ta shiga yi babu kakkautawa duk da zafin ciwon da Fateemarh keji bai hana ta zabga ma waleedah harara ba da kyar ta hadiye dariyar tace "hey what's wrong with you naga kina wani cin magani"

Kamar zatayi kuka tace "menstrual cramps ne ke damuna" ta karasa fada tana hawaye ba waleedah kadae ba har Nasma sae da tayi dariya kamar kuwa jira fateemarh keyi sai kuka dakyar suka rarrasheta suka zauna zaman fira har dare kana suka koma...........



*Lioness👑*

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top