Page 37
Haka Nawa Mijin Yake* 🦋
_(Nefarious Hubby)_
Written by *NEESHAR.JAY*
*NEESHARJAY* @wattpad
Page 37
Ganin kallon da yake mata ne yasa ta marairaice idanun ta da suka chanza kala zuwa ja sbd tsabar kukan da tayi jiya da dare ko bacci bata yi ita kanta bata taba sanin tana tsakanin kishin mijinta ba sai a daren jiya sai a jiyan ne ta tabbatar da son da take yiwa Fuad is unconditionally and incomparable, kasa tayi da kanta tana matso kwalla ita kanta bata San daliin zuwan ta kawai tsintar kafafun tayi suna tafiya kuma bata tsaya ko Ina ba sai nan, jin tayi shiru ne yasa shi cewa "idan baki da abin cewa zanje in kwanta bacci nake yi kika tado ni" dago idon ta tayi ta kallesa jin abunda ya fada wato ma haka zai ce mata samun kanta tayi da yin karyar da ita kanta sai da mamaki ya kashe ta "dama zan tambaya ne me zan dafa maku na breakfast?" Mutuwar tsaye yayi yana kallon ta da tsantsar mamaki sae kawae yayi smiling yace "anything you can or feel like doing" kanta kawai ta gyada tana nadamar abunda ta furta ta juya ta tafi, sai da yaga ya shiga part dinta kana ya koma ciki yana jin jina kishi irin na mata.
Afeefah kuwa ganin baya cikin dakin koda ta fito tayi tunanin ko yaje dakin sa ne daya dawo daga duba kofa sae kawai ta zauna daga ita sai towel bakin mirror tana shafa mai, Fuad kuwa wayar ta ya dauka dake parlour ya duba time 9:12am tsaki yayi ya dan kara murya kadan Kamata haura sama. Bedroom din ta ya fara shiga ya hangota tsaye tana duba kayan da zata saka cikin wardrobe, jin motsin bude kofa yasa ta juyo da sauri ganin sa tsaye yana kallonta yasa tayi kasa dakai gaba daya kunya ta rufe ta dan tabe baki yayi ya juya ya koma dakin sa wanka yayi ya shirya cikin wani tissue yard sky blue color sae bakar hular daya saka da wristwatch dinsa na Rolex, ya fito sai baza kamshi yake yi, dakin ta ya leka yaga bata ciki sae kamshin turaren dake tashi lumshe idon sa yayi ya rufe kofar ya sauko kasa.
A dining area ya hangota tana shirya breakfast, guri ya nema ya zauna zaman couch din parlour ya zauna yana duba wayar sa Bayan ta gama ta dago tana kallon sa a hankali ta furta "Masha Allah" Sulaiman ne ya fado mata a rai da sauri ta yakice tunanin sa tana astagfurullah a ranta "ya Fuad ga breakfast din" ba tare da ya dago ba yace "ok".
Sae kusan 3mins after ya mike ya Kara sa dining ya zauna, Tea ta fara hada masa kana ta dora masa toasted bread biyu da kwai a gefe kana itama ta zauna ta hada nata. Shiru gurin har suka gama ya mike ya fice, tattara kayan tayi ta kai kitchen ta dawo ta kwanta a parlour tana mota ita kadai "kawai ayiwa mutum wani gidan sama tsabar wahala ni gsky bazan iya dinga hawa da saukar nan ba idan na sauko to sai dare ko kuwa wani abu amma kam bazan iya ba wlh mutum yayi ta fama da ciwon kafa da baya tun bai tsufa ba mtsw" haka ta karaci mitar ta har ta gaji tayi shiru, daga nan bacci ya fara fisgarta ganin haka yasa ta mike ta shige nan bedroom din kasa ta kwanta abunta sai bacci.
Knocking din kofar data ji ne yasa ta mike tana karanto addu'a dakyar ta mike dan baccin bawai ya ishe ta bane toilet ya shiga ta wanko fuskarta kana ta fito, dankwalin ta ta ware tana rufe jikin ta dashi ta karasa ta bude kofar yan gidan su ta gani tsaye da sauri ta basu hanya tana washe baki Waheedah kam sae dariya take, Bayan sun zauna suka shiga gaisawa ta shiga ta dauko masu ruwa da drinks duk da basu da sanyi ta ajiye, nan fa suka baje hajar firar su sai kusan 12:30 suka dora abincin rana, rice and stew sukayi sai salad da suka hada da zubo Bayan sun gama suka zuba suka ci Fuad kuwa aka zuba masa nasa a kula. Part din mommy suka je can suka shiririce har kusan 4:30 basu yi sallah ba ana ta fira.
Fuad kuwa koda ya fito part din siyama ya fara shiga suhail kawai ya samu a parlourn sai takalma da aka shigo dasu da alamu dai baki tayi, da gudu yaron ya karasa gurin sa shi kuma ya duka ya masa peak a kumatu, dariya yaron yayi yace "Daddy Ina kwana" yace "Lpy suhail Ina mommy?"
Cike da yarinta yace "mommy tayi baki kuma tace kar kowa ya shiga shi yasa tace na tsaya a nan" da mamaki yace "Kai kadai?" Yace "Ehh daddy aunty Faty bata nan" mai aikin su.
Shiru yayi baice komai ba ya juya suka fice da suhail, part din mommy suka shiga gaba dayan su suna a parlour sae wasu baki da akayi Bayan sun gaisa suka masa Fatan alkairi da addu'an zaman lpy, kallon mommy yayi yace "daddy fah?"
Tace "yana sama bai fito ba"
Mike wa yayi yana kallon Afeefah yace "ina Farouk?"
Kanta a kasa bata ji sa ba sai da ya kira sunan ta tace "na'am yaya"
Tsaki yayi yace "ina Farouk?"
"Ya fita shida Adda Hafsah"
Baice komai ba ya haye sama hannun sa sakale dana suhail har suka haura sama, Bayan sun shiga sai da suka zauna a parlour kusan 6mins sai ga daddy ya fito ganin su ya saka ya fadada fuskar sa da murmushi Bayan ya zauna suka gaisa suhail ya tafi gurin sa daddy yace "aa abokina an tashi lpy"
Yace "eh daddyn daddy" ya fada yana dariya daddy yace "toh dan daddy" kallon Fu'ad yayi da tsokana yace "dan daddy Lpy dai?" Dariya sukayi gaba dayan su yace "Lpy daddy Yaushe zaka koma ne?"
Daddy yace "one month break zanyi insha Allah"
Fu'ad yace "Masha Allah zamu dan kwana biyu da kai kenan"
Daddy yace "Ehh toh insha Allah ya maganar office din ya Kamata mu samu lokaci muyi magana idan da akwai abunda company ke bukata sae mu gani"
Yace "haka ne daddy idan muka koma Abuja sai muyi magana dan kasan nan mutane baza su barka ba an jima ba'a hadu ba"
Daddy yace "haka ne Toh Allah ya kaimu"
Yace "Ameen" suka cigaba da magana bai baro gurin daddy ba sai kusan 12 kana ya fita daga gidan.
:::::::::::::🦋 SIYAMA 🦋:::::::::::::
Frnds dinta ne suka zo hakan yasa ta hana kowa shigowa dakin ta dan bata so su ji maganar da suke yi, gaba daya zuwan frnds din nata ya daga mata hankali dan kuwa sai mutuwar shawara suke bata "hmmm wlh kin bani mamaki ai banyi tunanin zaki bari a shigo miki da wata cikin gidan nan ba, hmmm ni kin San meyasa ma ta tun daga Abuja kawae dan na ga reaction dinki na yau ne" suka kwashe da dariya kamar ta fasa musu kuka tace "Haba Haseena ke da ya Kamata ki bani shawara shine kika making fun of me kuma"
Wacca ak kira da Haseena tace "atoh ke din ce duk cika bakin ki a banza ne wlh idan ma idon ki zai bude ya bude dan kishiya ba dadi ne da ita ba barema irin taki gashi yar gida kuma yar dangi ya dakko wlh sai kinyi hakurin wulakancin yan uwan sa"
Waseela tayi caraf tace "wane irin hakuri kuma na rantse duk Shegiya data miki Karki daga mata kafa idan ba haka ba rainaki zasuyi su maida ke kamar bola duk wanda ya dakko sharar sa kanki zai zube ta"
Ummi dake faman danna waya tace "atoh gaya mata dai"
Haka suka dinga bata gurguwar shawara ita kuwa tana kwashe wa tass sai wanda basu fada ba hakan yasa ko shigowar Fu'ad bata ji ba.
:::::::::SULAIMAN::::::::
Sosae auren Afeefah ya haifar masa da ciwo wanda hakan ya saka har hawan jinin sa tashi shi kadae yake dawainiya da ciwon zuciyar sa Atika ma sae data tausaya masa ganin irin halin da yake ciki kamar tayi kuka gashi sunje asibiti har yanzu magana daya ce ya rage damuwa amma inaaaa hajiyan sa da Alh ma sunyi sun gaji sai addu'a kawae amma ai ko menene shi yaja ma kansa duk laifin sa ne.
:::::::::::🦋::::::::::::
Yanzu ma sai dare ya dawo a matukar gajiya dan yawo yayi yau din nan, kamar jiya part din mommy ya fara shiga a sama ya same su ita da daddy Bayan sun gaisa bai jima ba ya fito shida Farouk suna tafiya suna magana sai da yazo shiga part din Siyama ne Farouk ya koma dan dama can ba gurin zuwan sa bane. Da sallama ya shiga a bakin sa Bayan ya tura kofar parlourn, ba kowa har ma ta kashe wutan parlourn sama ya haye direct ya shiga bedroom dinta dan yasan a can ne zai sameta sae dae ga mamakin sa bata ciki bedroom din sa ya shiga wutan dakin a kashe sae dae AC a kunne da bedside lamp hakan ya tabbatar masa da tana dakin bakin gadon ya karasa ya kunna flash din wayar sa dan hasken lamp din bai wadata ba kwance ya gansu ita da suhail suna bacci addu'a ya masu ya shafa masu kana ya fice Bayan ya masu kiss a forehead. Yana fita Siyama ta bude ido tare da watsama kofar harara kamar yana ganin ta gyara kwanciyar ta tayi kawai.
A gajiya ya shiga part din sai dae ba kowa a parlourn kasa sai kamshin turaren dake tashi, lumshe ido yayi kana ya haura sama, a parlour ya sameta zaune tana kallon zee world taci ado cikin lace dinta sai kyalli take fitar wa powder kwai ta shafa sai kwalli da nude lipstick, da kallo ya biya hakan yasa tayi kasa da kanta a hankali tace "sannu da zuwa" "Yauwa" shine kawai amsar sa yana shiga bedroom dinsa, bin Bayan sa tayi tana mita da zuciyar ta "ni ba haka Sulaiman ya saba min ba idan ya dawo" ko da ta shiga ya cire rigar sa yana kokarin cire wando da sauri ta shige bayi ba tare data yarda ta kara kallon sa ba, shi kuwa tabe baki yayi ya fada toilet din tana kokarin fitowa shi kuma zai shigo da sauri ta matsa gefe ya shigo ta fice.
Kayan bacci ta dakko masa ta ajiye a bed Bayan ta fesa masu turare kana ta fice kasa ta sakko ta hada masa abincin da Adda Hadeexa tayi ruwan semonvita daya tuku da kyau sai Muharram kubewa danya data ji kifi, sauran sobon data saka a fridge ta dakko da ruwa da cup ta dora a tray ta haura sama dasu kana ta dawo ta kwashi sauran kayan ta haura tana jin haushin tsarin gidan ta na wannan hawa da saukan.
A parlour ta jera komai kana ta shiga dakin sa, zaune ta same shi yana shafa mai dan tabe baki tayi bata San ya hangota ta cikin mirror ba "zonan" da sauri da dago kana ta karasa cike da tsoron kiran rashin dalili lotion din ya mika mata yace " shafa min a baya" karba tayi a darare ta shafa masa kamar bata so Bayan ta gama yace ta dakko masa kayan sa , bakin gadon taje ta dakko kayan ta dawo, mike wa yayi ya fara karbar wandon ya saka kana yace "toh saka mun rigar" ba musu ta shiga saka masa data gama ya dakko turare ta fesa masa kallon sa tayi sai kawai murmushi ya kwace mata, hade girar sama da kasa yayi dan shi kam bai ga abin dariya ba, hannun sa ta ja suka fice har parlour yana binta kamar soko, Bayan ya zauna ta zauna ta fara saving dinsa abinci duk da baya jin yunwa sai da yaci yasha zobo itama abincin taci Bayan sun gama ta kwashe komai ta maida kitchen koda ta fito a parlour ta same shi yana kai da komowa dariya abun ya bata sai ta gimtse ta nema guri ta zauna tana kallon sa har ya gama kana suka haura sama kashe komai yayi hakan ya tabbatar mata da kwanciya za'ayi kenan duk da taso kallo sae ta hakura Bayan ta shiga ta cire kayan ta ta linke su ta mayar kana ta saka rigar baccin ta doguwa cotton ta haye gado yau ma kamar jiya yah Fuad kam bai daga ma kanwar sa kafa ba.
Kamar yanda kowa ya sani a kwana uku amarcin bazawara mai kishiya yake karewa toh haka ma Afeefah washe garin daga cika kwana na uku Fu'ad ya tara su a parlourn Siyama kasancewar itace babba, guri Afeefah ta samu kasa gurin kafafu Fuad ta zauna Siyama kuwa daya fito ta kashe dauri ture kaga tsiya sae baza kamshi take ta kallesu a wulakance kana ta zauna saman kujera tana daura kafa daya kan daya ta jiya masu keya tana kallon Tv,
Ba wanda ya kulawa cikin su fuad ya kalli Afeefah yace "tashi ki zauna a kujera"
Da sauri Siyama ta jiyo cike da masifa tace "karki kuskura wlh dan ba daga gidan ubanki aka dakko su ba ehe" bata ce mata komai ba tayi kasa da kanta Fuad kuwa a dan tsawace ya kira sunan ta "Siyama" ki shiga hankalin ki" tsaki kawai tayi tana biyar da kanta, shiru yayi na wasu mintuna kana yace "kece babba dan haka bana son fitina kinfi kowa sanin bana son hayaniya dan haka ki rike girman ki" idan bango dake Bayan sa ya amsa masa toh Siyama ta amsa, juya wa kan Afeefah yace "kece karama kiyi respecting dinta sbd she's your elder bana son jin wani abu ya faru" kanta a kasa tace "insha Allah ba abunda zai faru zan mata biyayya iyakar iyawata" wani sanyi yaji cikin ransa ko Ba komai ta nuna yana da muhimmanci a gurinta tunda har ta amsa masa unlike siyama data wulakanta sa. "Ki rike respect dinki dan zai maki amfani a gurin wani ba dai ni ba dan bana bukatar ko ganin wannan jemammiyar fuskar taki talk more of your respect" ta fada tana watsa mata harara. Ba wanda ya kula zancen ta cikin su sai dai wani smiling da Afeefah tayi a cikin ranta tana ayyana kalar sakarcin siyama a fili na nuna rashin biyayya a gaban kishiyar ta lallai da wannan damar zatayi amfani gurin siyen soyayyar fu'ad kuwa. Maganar Fuad ce ta dawo da ita daga tunanin da take yi "Zan kira kwana biyu a part din kowacce a cikin ku hakan ya maku"
Siyama ta mike tana fadin "kanka ake ji dama sbd wannan maganar ne ka wani tado ni mtsw idan ka iyama kayi ta zama a gurinta dama in Banda rashin godiyar Allah irin ta maza kana da mata in banda jaraba meye na karo wata ko kana nufin mace daya bazata ishe ka a kwana biyu bane" wani irin Mari Fuad ya sauke mata mai Lpy a fuska ba ita da aka Mara ba bar Afeefah sai data tsorata tsaki kawai yayi ya fice daga parlourn.
Da sauri Afeefah ta mike tabi Bayan sa tana son masa magana sai dai har ya shige mota hakan yasa ta nufi part dinta tana jinjina girman wannan lamarin, ko sama bata koma ba ta samu guri ta zauna a parlour, wayar ta ta dakko ta shiga message ta fara typing "I never want to stop being your wife. I promise to change the things She did that hurt you and think about your feelings. Don't think about what happened dazun dan bana so ka wahalar mun da zuciyar ka Loml just cheer and move on ur day, I love you so much❤️".
Yana driving ya kunna karatun Qur'ani yana bin kira'ar sbd yanda yake jin zuciyar sa na tafarfasa duk iya zaman sa da Siyama bata taba bata masa rai irin na yau ba tsaki kawai yayi yana sauke ajiyar zuciya yaji alert din message wani tsakin ya kuma yi yana daukar wayar ganin sunan ta akan screen din wayar ya saka shi yin parking gefen titi ya shiga message ya karanta, wani sanyi ne yaji ya lullubesa ya lumshe ido ya kuma budewa akan screen din wayar ya kuma karantawa sai kawai yayi smiling ya mata reply da "thanks Niful hayat".............
*Please kuyi following dina a Wattpad*
#TeamFuad
#TeamAfeefah
#TeamSiyama
*Lioness👑*
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top