Page 35

Haka Nawa Mijin Yake* 🦋
         _(Nefarious Hubby)_

          Written by *NEESHAR.JAY*

          *NEESHARJAY* @wattpad

Page 35

Kanta a kasa Abba ya kuma cewa "kinyi shiru Afeefah bana so a kara komawa gidan jiya duk da Ina kyauta ta zaton fu'ad bazai wulakantaki ba amma nafi so naji daga bakin ki"
"Ehh" Abba shine abunda tace ta gudu, dariya yayi yana girgiza kai Yah Ashir yace "hmmm wannan yarinyar halinta sai ita wlh"
Abba yace "haka rayuwar ta take duk cikin ku nafi jin tausayin Afeefah bawai dan mahaifiyarta ta rasu ba sai dan yanayin rayuwar ta" yah Ashir dariy kawai yayi suka cigaba da firar su.

Afeefah kuwa daki ta wuce abunta tana jin zuciyarta na tsalle kamar zata fito kwanciya tayi a gado tana maida numfashi kamar wacca tayi gudu, har aka kira sallah la'asar tana kwance a gurin kamar ruwa sai kusan kasa 4 ta tashi dakyar ta shiga bayi.

...............Fu'ad🤍

Bayan mommy ta gaya masa yanda suka yi da iyayen Afeefah yace zai tura nasa magabata a saka rana, mommy tace "toh duk yanda kayi.....toh amma ka kira ita Afeefah kunyi magana?"
Girgiza kansa yayi yace "aa"

Tace "toh ka kirata, fu'ad baza ka gane bane rayuwar Afeefah daban taje ni ban taba ganin yarinya mai saukin Kai da sanyi kamar ta ba duk sanyin mahaifiyarta bata kai Afeefah ba tana da biyayya bata da taurin Kai na tabbata ko yanzu ba sonka take ba amma tayi biyayya zata aure ka dan Allah ko Bayan raina fu'ad Karka cutar da Afeefah dan bazan taba yafe maka ba" da sauri ya dago yana kallonta ganin har da hawaye a fuskarta kusa da ita ya koma ya zauna tare da rike hannunta yana share mata hawaye "Haba mommy na miki alkawari bazan taba wulankanta jinina ba ko da aure bai hada ni d Afeefah ba bazan wulakanta ta ba" bata ce masa komai ba haka ya cigaba da mata alkawari kala kala har lokacin sallah yayi suka mike.

.....Bayan kwana biyu.....

Shirin biki aka fara ba kama hannun yaro sai kace auren budurwa, komai sabo Abba ya siya mata tun daga kan spoon har gado da kujeri a gdan su na birnin kebbi aka zuba mata Turkish chairs da royal dan two parlour ne daya a kasa sai na sama 4 bedrooms duka ba wanda ba'a zuba ma gado na alfarma ba dakinta aka saka milk sai dakin miji white dayan bedroom din ma white sai daki daya dake kasa aka saka marron. Kitchen daga gefe sai dining da study room dinsu a gefe.  A Abuja kuma 3 bedrooms  amma guda daya kawai ya saka kaya dan fu'ad yace shi zai gyara dakin sa dana yaran sa. Sai parlour da aka zuba mata couch dinta masu kyau Royal blue.
Abba ya taka rawar gani sosae a wannan bikin ya zubama yar sa kaya na gani na fada sbd yana da hope din nanne gdan ta har ta koma ga Allah.

A bangaren amarya kuwa sosae su mommy da aunt ke guaranta dan biki saura sati daya yanzu, gaba daya Afeefah ta chanza kamar ba ita ba sai wani sheki take yi. Ba abunda take tunani yanzu sama da yanda zata fara zama da fu'ad ita da ko doguwar magana ba hada su take ba gaisuwa kawai ke hada su, toh amma yanzu gashi kaddara zata hada su aure abunda koda mafarki bata taba tunani ba kai koda wani ya gaya mata a gaba zata auri Fuad baza ta yarda. Gauron numfashi ta sauke tana jin jina wannan lamari na ubangiji lallai ba abunda Allah baya iya yawa fatan ta kawai Allah ya bata ikon cinye wannan jarabawar ba tare da ta nuna gajiyarwa ta ko ta saba masa ta ko Wace hanya. Lallai akwai aiki jaaaa a gaban ta tayi zaman gdan mai mata tasan halin waccan amma wacca zata tarar fa tun bata San da zancen auren su ba ta fara nuna mata kyara inaga sun zauna Inuwa daya. Abunda ta sani kawai zata je tayi zaman ibadah bawai dan mijin na sonta ba ko tana son shi amma zata yi kokari ta sauke duk wani nauyi daya rataya a yunwa ba tare da gajiyawa ko kosawa ba.

               ........Fu'ad......

Hankalin sa kwance yake abubuwan sa kamar ba ango ba, matsalar sa da siyama kuma yanzu ya dai na damuwa yama fita iskarta ga wani aiki daya taso masa a office baya dawowa sai dare amma duk da haka yana bama dan sa lokacin sa haka ma mommy kafin ta wuce kebbi yana shiga gurin ta kullum idan ya dawo idan suka gama fira ya sunkuto suhail su dawo sometimes kuma idan yan mutunci na kan siyama zata zauna a parlour tayi ta cika tana batsewa ko magana bata masa a dole ita fushi take dashi zai mata kishiya gaba daya yanzu ta fita hayyacin ta duk ta sakawa kanta damuwa ga yan gefe dake zugata shi yasa kullum take tsiro da sabon rashin mutun ci son ranta.

A gurguje...........🏃🏻‍♀️

A week later...

Rana bata karya sai dai uwar diya taji kunya kamar yanda hausawa suka ce, yau ta kama Friday kuma yau ne dubban mutane suka shaida daurin auren Fua'ad Muhammad Yelwa da Afeefatu Mahmoud Bagudo Bayan sallahr juma'a a nan central mosque, sosae Daurin auren ya tara mutane da yawa sai fatan alkairi ake masu. Ango sae kamshi da maiko yake zubawa fuskar sa shimfide da yalwataccen murmushi wanda kallo daya zakayi ka gane daga cikin zuciyarsa yake fitowa.

A lokacin da aka daura aure Afeefah na zaune bakin gado tasha ado cikin atampha super dinkin riga da zani daya karbi jikinta ga lallen da akayi mata ja da baki daya kara haska fatar hannunta kananun kitson da akayi mata ya sauka har baya, ba wata kwalliya aka chaba mata ba nude makeup data samu damar kwanta sosae a fuskar ta aka zana mata tayi kyau Masha Allah. Mutane cike da gida Ammi kam tunda aka shiryata bata kuma sakata a ido ba wasu daga cikin frnds dinta ma duk sun zo sun cika daki sai hayaniya suke yi.
   Sakon daya shigo wayar ta ne ya saka ta dakko wayar tana dubawa  ko a mafarki bazata taba mantawa da mai wannan numbern ba sosae jikin ta yayi sanyi lokacin da ta fara karanta sakon kamar haka "Aslm alkm malama Afeefah Ina mai matukar farin cikin taya ki murnar auren ki Allah ubangiji ya bada zaman lpy da zuri'a dayyaba ki cigaba da hakuri kamar yanda na sanki dashi ada sannan ki ninka biyyar da kikamin sau dubu kibi mijinki sau da kafa Ina miki fatan alkairi bissalam. 
          Sulaiman"

Shiru tayi Bayan ta gama karanta sakon haka kawai take ji kamar bata kyauta masa ba da kyar ta samu ta yakice tunanin abun a ranta, bata ajiye waya ba wani sakon ya kuma shigowa yah Fu'ad kamar yanda ta masa saving number ta gani rassss gabanta ya fadi da kyar ta samu ta tattaro natsuwarta ta bude message din rubutun da baifi layi uku ba ta fara karantawa "you're now mine and u will continue to be forever insha Allah Happy married life mrs Fu'ad yelwa" murmushi ne ya kubce mata sosae ta dinga juya abunda ta karanta cikin ranta haka kawai ta samu kanta da jin farin ciki Mara misaltuwa.

Da yamma aka kuma shiryata cikin lace mai kyau da daukar ido a nan cikin gda aka gabatar da walima data kayatar sosae Bayan an gama mutane suka watse aka bar yan Kai amarya.
  Wanka ya kuma yi har da na tsarki dan yanzu period dinta ya dauke dama tana ta tunanin yanda zata je gdan a haka, Bayan ta fito ta saka Atampha super England sai katon mayafi data daura tundaga kanta part din Abba aunty ta kaita yayi mata huduba kana duk sukayi nasu aka wuce da ita bawar Allah Afeefah harda kukan ta😝 .

Part din mommy aka fara shiga da ita bayan ta mata nasiha aka wuce da ita part dinta sai sama, kow sai yaba kyaun gdan yake yi itakam bata ma jinsu dan ta tafi duniyar tunani zaman da akayi da ita ne y dawo da ita ganin har 9 tadan gota ne yasa suka tafi suka barta ita kadae ba yanda batayi ba akan Faty ta zauna amma taki haka suk barta har kusan goma b wanda ya shigo kishingida tayi bata San lokacin da bacci ya dauke ta ba.

Fu'ad kuwa bai dawo ba sae 10:23pm part din mommy ya fara shiga bai jima ba ya wuce part din Siyama a tsaye ya sameta tana ta safa da marwa.........



#TeamAfeefah
#TeamFu'ad
#TeamSiyama


*Lioness👑*

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top