Page 29
*Haka Nawa Mijin Yake* 🦋
_(Nefarious Hubby)_
Written by *NEESHAR.JAY*
*NEESHARJAY* @wattpad
Page 29
*Aslm Alkm sisters masu karanta book din nan ta wattpad Ina bai baki hakuri sbd koda nayi posting basa gani wattpad dina ya samu matsala and am still working on it so plss da wannan handle din zaki iya cigaba da samun littafin nan dama wanda zanyi nan gaba ga handle din nan *neesharjay* wannan shine sabon handle dina ku nuna min kauna ta hanyar following, liking da kuma commenting plsss. Also wadan da basu fara ba kuma suna so su karanta to ku duba ta wannan handle din *neeshejay* a nan zaku samu farkon sa da kuma sauran littafan dana rubuta a baya nagode*
............... ................. ................ ................
Jikin Sulaiman Kam alhmdllh ya farfaɗo sai dai kariyar ce har yanzu da bata warke ba da ɗan sauran ciwon da sukayi rauni sosai, abinda yafi ɗaga hankalin sa dana mutanen gidan su kuwa shine da Dr ya shaida masu ya samu matsala a spinal cord Dan haka ba zai ƙara haihuwa ba wannan zance ya ɗa ga hankalin sa sosai sai kuka yake yana Allah na tuba ya Allah ka yafe min innalillahi wa'inna ilahirin raji'iun" zama mama tayi kusa dashi cikin kulawa ta soma magana "ka godewa Allah da bai ɗauki ranka ba wannan yana nufin babbar damar da ka samu dan ka nema yafiyar sa lallai Allah ya na na ma masu hali irin naka ishara yanzu da kake son haihuwar sai ya kwace abunsa tunda daga farko baka amsa hannu bibbiyu ba Sulaiman haihuwa babbar kyauta ce shi yasa kaga ko wane bawa yana addu'ar Allah ya azurta shi da ƴaƴa wasu da yawa suna can suna nema ido rufe amma ina sai kai da Allah ya Bama dama kayi watsi da ita, Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama yace ku hayayyafa dan nayi alfahari daki ranar alkiyama dan haka yanzu wannan ba lokacin kuka bane kawai ka dage da addu'a ka kuma ɗauka wannan ce ƙaddarar ka ba yanda za'ayi ka canza ta Allah ya maka albarka"
A hankali ya amsa da "Ameen mama Nagode"
Atika kuwa gaba daya ta rame ta jeme kamar ba ita ba damuwa ta mata yawa dame zata ji da jinyar Sulaiman ko da gorin rashin haihuwa da ake mata duk inda ta zauna ta ga yara.
Zaune suke kan baranda a gaban dakin da sulaiman ke kwance ba su kadai bane a kwai wasu masu jinya suma yarinya ce ta rarrafo zuwa gurin Atika ta saka hannu zata dauke ta sai taga ta jawo jobar dake kusa da ita gaba daya ruwan suka leme kasa harda jiƙa masu carpet yayi din gurin kan yarinyar Atika tayi tare da kwada mata harara. Maman yarinyar ta zo ta ɗauki abunta ta faɗin "daga kawai ta zuwa bar da ruwa sai ki dun gure Mata kai iya haka ake yi ya kodan baki san zafin haihuwa ba ne" wannan kalma tayi matukar ɓata ran Atika kawai ta saka kuka mama ta fara rarrashin ta dakyar tayi shiru.
.............*
Zaune take da ɗakin mommy kasancewar gaba ɗaya ƴan gidan sun tafi school sai Faruk da bashi da morning lecture kuma ya fita ya dawo mommy kuma tana sallah ne, shigowa yayi dakin bakin sa dauke da sallama can ciki karaf idon sa suka masa mugun gani da sauri Afeefah ta sauke rigar ta ƙasa tana janye Ammi da take shayarwa duk kunyar duniya yau ta gama lullube ta ji take kamar ƙasa ta buɗe kawai ta shige abinda take gudu kenan dama tun farko.
Shi kuwa Wani yarrrrr yaji tun daga yatsan ƙafar sa har cikin kansa da sauri ya dauke kansa ya kuma tamke fuska kana ya zauna kan sofa yana jiran mommy ta idar da sallah mike wa tayi ta saɓa Ammi zata fice tace "yah Ina kwana" kawar da kansa yayi yace "lpy" har ta kai kofa yaga Ammi na masa dariya tana miƙo hannu smiling yayi mata yace "kawo ta" ba musu ta miƙa masa ita tana kallon yanda take washe masa baki ita har mamakin sabon da sukayi take tana miƙa masa ta juya ta fice abunta.
Bayan mommy ta idar suka gaisa tace "Ni kam wai ina siyama kwana biyu bata shigo min ba" yana kallon fuskar Ammi data daga hannu tana taɓa fuskar sa yace "bata jin daɗi ne shi yasa and kuma yaran ki basa shiga gurin ta" taɓe baki mommy tayi tace "toh Allah ya bata Lpy zancen shiga gurin ta kuma ai halinta ne yaja mata idan ta gyara zasu gyara suma" bai ce komai ba ya cigaba da wasa da Ammi zuwa xan ya mike yace "mommy Ni zan fita ina da meeting 11" ajiye Ammi kan bed yayi tace"toh Allah ya kiyaye ya taimaka" yace "Ameen mommy" ya fice abunsa.
Bayan wata 5
Alhmdllh jikin Sulaiman yayi sauki dan yanzu ma ya ɗan fara taka ƙafar sa a hankali kuma jikin sa ya fara murmurewa sai dai tarin damuwa da kewar Afeefah da ƴar sa ne suka masa yawa ba wanda yake don gani yanzu kamar Ammi jin son yarinyar da mahaifiyar ta yake har cikin ransa sai dai kash sun masa nisa.
A kullum dasu yake kwana kuma yake tashi ya ɗauki alwashin idan yaji sauƙi zai je gare su koda Afeefah zata ji tausayin sa ta yafe masa ta dawo su cigaba da zama yayi alƙawarin zai kula da ita kuma bazai ƙara cuta mata ba.
Ni Ko nace hmmm zata yarda kuwa?.
.............. ............... ................
Siyama ta fito cikin shirinta hannun ta rike dana Suhail daya dawo daga gidansu daga gani fita zasu yi dan sun ɗau wanka ba kaɗan ba, party ɗin mommy suka shiga Afeefah na zaune tana chatting Ammi kuma tana zaune ƙasa tana wasa abunta kallo ɗaya tayi ma Afeefah ta ɗauke kai Suhail kuma daya ga Ammi yazo da gudu gurin ta yana "kasa mommy babu" tsawa ta daka masa bashi ba har Ammi sai da taji tsoro nan take ta fara kuka mommy jin haniya ya yasa ta fito tana tambayar Lpy?
Afeefah bata ce komai ba ta ɗauki Ammi ta fara rarrashin ta siyama kuma tsaki kawai tayi ta kalli mommy tace "dama zamu fita ne mommy" tace "to sai kun dawo" kama hannun Suhail tayi suka fice.
Bayan sati biyu
Mommy ta kira Fu'ad bedroom ɗin ta bayan sun gaisa in a serious note mommy ta fara magana "Fu'ad dama alfarma nake ne ma a gurin ka" da mamaki yake kallon kafin ya furta kalmar"alfarma" tace "ƙwarai kuwa alfarma" yace "haba mommy umarni kawai zaki bani ai"
Girgiza kai tayi tace "bazan maka umarni ba dan zaka iya saɓawa wanda hakan kuma zai ɓata min tai shi yasa nace alfarma"
Yace "toh mommy ki faɗi ko wace iri ce"
Ɗago da idon ta tayi tace "Fu'ad Ni na haife kan dan haka na fika sanin abinda yafi dacewa da kai ina so ne ka auri ƴar uwarka Afeefah"
Da sauri ya ɗago yana kallon ta with shock girgiza kai tayi tace "shi yasa nace bazan maka umarni ba Fu'ad Afeefah marainiya ce ta taso ba uwa ita kaɗai tasan how much she feel Fu'ad tana da zurfin ciki bata iya sharing damuwar ta da kowa ciki kuwa har da ni duk da iya bakin ƙoƙari na da nayi."
Numfashi ta sauke ta cigaba "waheedah ta gaya min kullum da dare sai tayi kuka bayan kowa ya ƙwanta bacci nayi tambayar duniya har na gaji amsa ɗaya take bani ba abinda ke damun ta Fu'ad ina sonsa Afeefah kamar yanda nake son ka Ina kuma tausaya mata matuƙa bayan rashin uwa ga zawarci mijinta na farko ya cutar da ita ya bar mata wani tabo da bazata iya manta wa dashi ba a ƙarancin shekarun ta bai kamata ace tana going through all this ba Fu'ad"
Ta ƙara sa magana hawaye na zubo mata da sauri ya matso kusa da ita yace "mommy you're crying unbelievable" share mata hawayen yayi tace
"Dole nayi kuka Fu'ad mamanta is the only sister I have ita kaɗai nake da and mum taso ne kamar ƴan biyu ba wanda ke bari wani abu ya samu ɗan uwansa har ta koma ga Allah kaima shida ne da irin son da muke ma junan mu Fu'ad dan Allah ka auri Afeefah insha Allah zata kawo ma haske cikin rayuwar ka data yaran ka"
Shiru yayi can yace "don't worry mommy insha Allah I will help" race "Toh ka zauna dai kayi tunani"
Hmmmmmm
Me Fu'ad yake nufi da he will help?
Shin ya amince zai aure ta ne ko kuwa?
Wane yanayi Afeefah zata tsinci kanta idan aka gaya mata wannan al'amari?
Wane hali siyama zata shiga? Zata bari ayi auren ko kuwa?
#TeamFu'ad
#TeamAfeefah
Vote
Comment
Share
*Lioness👑*
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top