End
Haka Nawa Mijin Yake* 🦋
_(Nefarious Hubby)_
Written by *NEESHAR.JAY*
*NEESHARJAY* @wattpad
Page 40
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya abubuwa da yawa sun sauya ciki kuwa harda samun dai dai tuwa tsakanin Afeefah da Siyama duk da ba wani magana suke ba hakan kuwa ba karamin kwantar da hankalin Fuad yayi ba.
Bayan wata 6
Lokaci baya jiran mutum sai dai kai ka jirasa, gaba dayansu suna kebbi sunzo sallah babba gdan duk ya harmutse da hayaniyar yan kawo lefen Faty kaya Masha Allah sae son barka anyi komai cikin mutunta juna, Bayan yan kawo lafe sun tafi gdan ya rage hayaniya yara suna ta wasan su, jin kamshin abincin da aka shigo dashi ne part din Hajja ya hautsina cikin Afeefah da gudu ta shige toilet din parlour sai kowa ya bita da ido, jin kakin aman da take yi ne ya saka Adda Maryam bin bayanta gaba daya ta galabaita sae amai take kamar zata fito da kayan cikinta da taimakon Adda Maryam ta gyara Bayan ta gama aman suka fito wadan ke parlourn we jera mata Sannu suke yi Adda Hadeexa ce tace "dama baki da Lpy?"
Girgiza kanta tayi tace "aa wlh Adda warin abincin nan ne ya haye min kai" dariya tayi tace "a lallai Toh Allah ya raba Lpy"
Adda Maryam tace "dama ni Ina ganinta nasan wlh ciki ne da ita dan gaba daya ta sauya" zaro ido waje Afeefah tayi tace "ciki kuma?" Dariya suka kwashe da ita da sauri ta mike sai daki Adda Maryam tabi bayanta tace "dama baki San kina da cikin bane" cike da kunya tace. "Ehh Adda" "ta shi mijin naki ya sani" tace "aa".
Wayar ta Adda Maryam ta karba ta dannawa Fuad kira ring biyu ya dauka jin muryar bata Afeefah bace ya saka shi gaida ta duk da bai San ko waye ba sai data gaya masa "Congratulations kanin mu your wife is pregnant sae dae bamu San ko wata nawa bane idan kazo sai kuje asibiti".
Da sauri ya mike yan fadin "what Adda Maryam da gaske kike yi kuwa" dariya tayi tace "Allah da gaske Kai dai sai ka zo" daga haka ta kashe wayar.
Mommy dake zaune tana kallon sa tace "Lpy dai ko naga kanata zabga murmushi ko aljannah aka kiraka aka gaya ma an maka albishir da ita" dariya yayi yace "aa mommy Bari dai Ina zuwa" bai tsaya jiran me zata ce ba ya fice daga gdan bai tsaya ko Ina ba sai gdan su Afeefah. Kiran wayarta yayi Bayan yayi picking yace "fito muje Ina waje" tace "toh" kamar zatayi kuka dan ba yanzu taso komawa ba, haka ta masu sallama ta tafi Adda Maryam na mata dariya, a waje yayi parking motar dan haka tana shiga yayi reverse sae da suka fara hanya tace "ina wuni" "Lpy ya gajiya" "alhmdllh" Ba wanda ya kuma cewa kala cikin su ita ta jinginar da kanta a seat din motar shi kuma hankalin sa na kan driving din da yake yi.
Asibiti ya nufa Kai tsaye, Bayan sun isa ya dan taba ta dan har ya fara bacci ganin yayi parking ya sakata kallon sa sai kuma taga asibiti suke kallon tuhuma ta Bisho dashi kawai ya Basra ya bude motar ya fice, dole itama ta fito ya rufe motar tareda zagayawa gefen ta ya kama hannun ta, marairace masa tayi tace "nifa Lpy na qalau Allah kuwa" bai kulata ba har suka je office din dr Saudat, cikin sakin fuska suka gaisa ta basu guri suka zauna nan Fu'ad ya gaya mata abunda ya kawo sa da mamaki Afeefah ke binsa da kallo har ya kai karshe.
Tambayoyi dr Saudat ta dan yima Afeefah kana ta kira wata nurse aka deba jininta dan ayi test. Tashin farko result ya nuna ciki ne a jikinta na wata biyu da sati daya. Hamdala ya shiga yiwa ubangiji da nuna tsantsar godiyar sa da Allah yayi masa badan yafi kowa ba ba kuma dan shi din wani ne ba harda kyauta yayi wa dr, ita kuwa Afeefah kunya ce ta kamata sai kasa tayi da kanta tana smiling, wai yau itace ake farin ciki dan ta samu ciki farin cikin ma daga mijinta Sulaiman ne ya fado mata arai lumshe ido tayi tana shafa cikin ta cikin wani irin yanayi. Hanunta ya kama suka fice daga office din Bayan sunyi wa dr Saudat sallama, Kai tsaye gida suka wuce cike da farin ciki baiyi Parking ko Ina ba sai part din mommy, ganin yanda suka shigo fuskar sa dauke da fara'a ita kuma Affeha kanta a kasa sai abun ya bata mamaki, su Waheedah ma dake zaune da kallo suka bisu guri ya samu ya zauna a kujera Afeefah kuma ta rakube jikin kujera kanta kasa ta gaida mommy ta amsa "ni dai kun daure mun Kai wannan annashuwa haka da nake gani zaman fuskar ku haka" mommy ta fada.
Smiling Fuad yayi yace "mommy albishirin ki"
Tace "goro"
Dariya yayi yace "to meye ladan da za'a bani idan na fada"
Dariya tayi tace "Kai bana son shashanci idan zaka fada ka fada ka barni da zullumi"
"Dariya yayi yace "aa nikam sai kin gaya min abunda zaki bani"
Tace "toh naji dan anace"
Yace "Yauwa dama Ba komai bane uhmmm.....uhmmmmm meye ma? Toh na manta kuma"
Dakuwa mommy ta masa tace "ungo nan kanin baban ka Basheer ni zaka mayar kakar ka kuma yau zaka fada ko sai na maka duka a nan gurin"
Dariya yayi yace "Haba mommy da dana Kice zaki dake ne"
Tace "wannan kuma damuwar ka ce ehem Ina jinka"
"Ba wani abu bane dama yarki ce ta kusa kawo maki jika shine kawai"
Farin ciki Mara misaltuwa ne ya mamaye mommy sae godiya takewa ubangiji, Waheedah kuma a 360 ta dira ta kanainaye Afeefah tsawar da fu'ad ya saka mata ce ta saka ta natsuwa, mommy da kanta ta mike ta rungume Afeefah a jikinta tana mata fatan sauka Lpy, sun jima a part din mammy kana da aka kira sallah suka mike Afeefah ta fice part din su Fuad kuma suka fice masjid.
Bayan ya dawo sai da ya fara leka part din Siyama, Bayan sun gaisa ne ya zauna ta kawo masa ruwa ya karba yasha yana tambayar ta Suhail. Tace "yana gidan su mommy" baice komai ba ya mike zai fice sai kuma ya dawo "kina bukatar wani abune".
Tace "aa" yace "Yauwa dama Afeefah ce..." sai Kuma yayi shiru haka kawai ya tsinci kansa da jin kunyar gaya mata samun cikin sa Afeefah tayi sai yake ganin kamar bai kyauta mata ba. Kallon sa tayi tace "meya same ta"
Da kyar ya samu ya gaya mata wani irin muguwa faduwa gabanta yayi Amma sai ta dake tace "Allah ya inganta" a kunya ce yace "Ameen" kana ya fice. Zama tayi a gurin dabas tana jin wani zafi na taso mata daga kasan zuciyar ta badan tayiwa Mama alkawarin ta zubar da makaman yakinta ba da ba abunda zai hana ta zubar da wannan cikin, bata ankara ba taji hawaye na zubo mata a kumatu lallai lokaci yayi da zata gyaran zaman ya da mijin ta lokaci yayi daya Kamata ta gyara rayuwar gdan ta. Sai kusan 11 ta mike ta koma daki a wannan daren sai bacci barawo ne ya sace ta.
A gurguje...................!
Haka rayuwa ta cigaba da gudana zaman Siyama da Afeefah a hankali ya fara canzawa wanda hakan ba karamin dadi yayiwa Fuad da mommy ba danshi daddy bai San wainar da ake toyawa ba.
A dayan bangaren kuma sosae take samun tattali da kulawa ga cikinta har ya fara fitowa hakan yasa mommy mai da Ammi gurin ta.
____________
Sulaiman
____________
Ta bangaren sulaiman kuwa abubuwa sun dai daita sai godiyar ubangiji shi da Ateeka sunyi adopting orphan daga gdan marayu tare da alkawarin zasu rike sa kamar su suka haifesa.
________✨
Rayuwa mai juyawa yanda Allah yaso lokaci mai gudu yana maida abu tarihi kamar ba'ayi ba, cikin Afeefah kam wata 8 yanzu gashi sai hidimar biki suke ba kama hannun yaro basu tsammanin bikin Waheedah zai taso yanzu ba sai gashi dangin mijinta a shirye suka zo hakan yasa daddyn yace gwanda kawai a hade da Faty da ya ukasha ayi gaba daya hakan yasa gaba daya abubuwa suka kacame masu sai hidima ake harda Siyama aka hade abun sai son barka. Ka idar Abba ce ranar juma'a yake aurar da ya'yan sa haka ma gasu Waheedah bayan sallahr juma'a duban mutane suka shaida auren Waheedah da angonta Abdul'azeez sae Faty da mujaheed, Bayan an gama aka je aka dauro na ukasha da matar sa Hafsa.
_________✨
Nakuda ce ta taso mata gadan gadan gashi ba kowa part dinta sai ita kadai wayarta na daki ko takawa baza ta iya ba ballanta na ta dakko kamar daga sama sai ga Siyama ganin halin da Afeefah ke ciki yasa ta fita part din mommy da gudu sai gashi sun dawo tare taimaka mata sukayi aka sakata a mota sai asibiti a hanya ne mommy ta kira Fu'ad ta shaida masa halin da ake ciki.
Not less than an hour ta haifo katon jaririn ta mai kama da ubansa, murna gurin wannan ahali ba'a magana anyiwa suhaib kani. Siyama dake ta kokari tun dazu saboda warin asibitin daya addabeta ta mike da gudu saboda aman daya taho mata ba shiri, sai da ta amayar da komai na ciknta kana mommy ta taimaka mata, da Fu'ad ya tambayi meke damun ta tace ba komai kawai warin asibitin ne ke tada mata zuciya kin yarda yayi sai da ya saka dr ya duba masa ita, gwajin farko ya tabbatar da ciki ne da ita na sati 6 da kwana biyu. Wannan labari ba karamin kara da dada zuciyar su yayi ba, ganin ba abunda ke damun baby da maman shi aka sallame su suka koma gda. Kafin kace me labarin haihuwar Afeefah ya gama karade dangi gaba daya nan yan barka suka fara zuwa tururu.
Bayan sati yaro yaci sunan sa Sadam.
______BAYAN WASU SHEKARU_______
Yara ne su biyar ke Ta wasa a babban parlourn gdan sai ihu suke kamar zasu tada gdan dattijuwar mace dake hakimce cikin shiga ta alfarma Ta dune su tace "Kai suhaib kaji kunya kaine babba Amma kana biye masu kuna wasan banza oya kuzo ku tafi gurin iyayen ku ni na gaji"
Karamar cikin su ta kwala kara tana fadin "oyoyo adda waheee" da gudu yaran suka tafi sukayi hugging dinta suhaib ya karba babyn dake hannunta suka kara so cikin parlourn.
Mommy dake washe baki tace "lale mara ba da autar mommy lale" dariya tayi tace "hala dai auta bata gdan ne mommy shi yasa batayi korafi ba" dariya tayi tace "Ehh tana skl" gaisawa sukayi da mommy "Ina ita Ammin taku ne ko kin zuwa kuma tayi"
"Aa mommy tana part din mamin su muna shigowa ya tafi da gudu tayi tunani gaba daya yaran suna can".
"Allah sarki ya babanta Toh"
"Suna lpy yace idan tayi hutu zaizo da kasan ki kuma bashi aronta"
"Allah sarki Sulaiman toh Ba komai".
Shigowar Siyama Afeefah da Ammine yasa yaran zuwa da gudu suka rungume yar uwar su, nan fa hayaniya Ta kara cika parlourn, Bayan sakkowar juma'a sai ga Fu'ad da Faruk da matar sun shigo abun sai ya kara yiwa mommy dadi sai kallon zuri'arta take cike da shauki. Bayan sun gaisa masu aiki suka shirya masu abinci a nan parlour aka baje ana ci cike da barkwanci.
ALHAMDULILLAH!
Anan na kawo karshen wannan labarin abunda nayi kuskure a ciki Allah ya yafe min ya kuma sa ku amfana da abunda na rubuta.
Ina matukar godiya da nuna jin dadi na da kuka bama wannan littafin lokaci kuka karanta shi.
Mu hadu daku acikin sabon book Dina _*IBN FARHOON_* Amma fa na kudi ne.
Allah ya yafe mana gaba daya.
Lioness 👑
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top