8

"Su kyau manja, ka jira a yabe ka Mana" ta amsa.

"No, gwara inyi appreciating abinda Allah ya bani. Now tell me, meye sa kike tsoron Ummah ta Kai maganan mu wurin su Abbah" dan jim tayi sannan tace.

"No kawai Ina so in Fara school ne, Abbah Yana son makaranta sosai" dariya yayi yace "Ni dai banyi Kama da Wanda zai hana ki School ba ai ko? Kuma numban Ummah, ko ba a ban ba nasan yanda zan yi in samu" dariya tayi, sun dade suna waya kafin su kayi Sallama. Daganan hiran ya gangara messages, sun dade suna yi. Sai wani irin murmushi take yi na daban, wani lokacin ma ba wai maganan soyyaya yake Mata ba. Aa, kawai hiran ne da suka Saba yi, Sai dai a ciki yana dan jefo words in da zai nuna Mata, mahimmancin ta a gareshi. Wannan inma, ba sabo bane saboda yanzu ta gane tun da yana amfani dasu.

Kaman in ta fadi wani abu Sai yace "keh bari Mana, Kar ki sa in kasa bacci" ko Kuma "kina so na kasa tashi daga inda nake ko?" Ko "Na kasa cin abinci, duk na fara ramewa ma kuma ke kika ja" ire iren maganganun dai dayawa.

A duk lokacin da suke magana, tsintar kanta take a wani yanayi na daban, Wanda take ji cikin kwanciyar hankali da annashuwa. Sai dai duk da haka, ta kanji sautin bugun zuciyan ta na karuwa. Mostly, daga yanayin yanda yake Mata magana. Komin shi na da irin effect in da yake samarwa a jikin ta. One minute za taji kaman tana tsoro the next taji farin ciki ya Mata yawa, ta rasa inda zata sa kanta. In ko basa magana, ta kan kasance ne cikin tunanin previous conversation insu. Haka nan ita kadai Sai ta tsinci kanta, tana murmushi, ko dariya ma wani lokacin. Ko Kuma ta runtse idanuwan ta, tana tuno wani abu da ya fada Mata. Wani lokaci, har tsalle take Sai tayi Sai ta gane abinda tayi. Ko kuma tana cikin tafiya, ta sa gudu duk da ita kadai. Kama wata mai aljannu. Nan ko duk love effect ne ke haka da ita. Without her realizing, a hankali duk wani kankantan takun shi, da salon shi na kara ruruta girman soyyan shi a cikin zuciyan ta. Ita kanta ba wai ta kan gane hakan bane, all she knows is that, he matters a lot to her. Dan ita kanta yanzu, ta riga tayi sabo da magana dashi ta yanayin da bata iya jure lokaci mai tsawo ba tayi magana dashi ba. Ko bai nema ta ba, zata neme shi. A kullum kwanan duniya, shakuwa Mai girma ke kara shiga tsakanin su.

Shi inma ya gane, kullum da irin progress in da ake samu. Saboda wani time, da gangan zai ki kiranta, don dai kawai yayi testing inta. Tabbas, yasan zata Kira. Kawai, yanayin lokacin da take dauka ka fin ta kiran, ya ke aunawa yaga iya cigaban da aka samu.

Kwanan shi biyar a Taraba ya juyo. Sai a safiyyar ranar Kuma ya ke gaya Mata zai biyo ya ganta kafin ya koma Kano. Sosai taji dadin hakan, Sai dai Kuma sabuwan tension in da hakan ke nufi. Aminiyar ta Zainab ce ma ta Kira ta ranar, ta dan kauda Mata tension in. Har lokacin ba wai ta gaya ma Zainab in abinda ke faruwa tsakanin ta da Abakar Sadiq in tayi ba. Hira ce dai suke yi kawai na school suna dariya. Nan Zainab in ke fada mata ta Kira ta, ta gaya mata an saman Mata admission in karatu a Sudan ne, dan daman tana da burin karantar pharmacy. Abun ya zo Mata as surprise ita ma, kwata kwata ba ta San ana Shirin fitar da ita karatu ba. Nabila kuwa, taji Mata dadi sosai, Sai taji kaman ma ta Kira Abbah ta gaya mishi tana son zuwa can in itama, tunda ya riga da ya bata daman zaban ko ina take so.

"To Sadeeq infa? Kiyi ya dashi?" Zuciyar ta ya tunatar da ita. Sai Kuma lokacin ta gane, a yanzu duk wani decision da zata yi dole zai yi involving in shi a ciki. Yanzu haka da yake maganan ganin Abbah, ta ina zata fara zuwa Sudan karatu? Da wannan thought in ta share maganan Sudan, suka cigaba da hiran su da Zainab.

Maganan Mubarka ma suke yi, da kw suna da kusa da Zainab in a cikin Abuja, so sukan hadu. "Ai baki San me Mubarak ya ce min ba" gyara zama Nabila tayi, tace "Ina sauraron ki" tasan tsaf halin Mubarak, yanzu haka wani shiriritar ya fada, at least tunanin ta kenan dai.

"Kinsan zai tafi China karatun Engineering ai"

"Haka ya fada min" Nabilan ta amsa, dake Mubarak in ya kan dan kirata bayan kwana bi biyu. Sun dai fi chatting a WhatsApp, Sai Kuma comments akan post in juna a su Twitter da IG.

"Yauwa, wai ya fada ma mamin su akan yana dawowa a nema mishi aiki Yana da wacce zai aura. Don dai shi da gaske yake, sonki yake tsakani da Allah." Dariya su kayi dukkan su. Nan Zainab in ke tmbyn ta Malma Abakar.

Shiru tayi tana tunanin mai zata fada ma kawarta ta. Tasan ko tayi karya, dole ta gano ta daga baya. Tunda dole komai zai fito fili, ba ta son tana boye ma Zainab abu. Sai dai Kuma tasan she is not in support of the relationship shi, da kaman Khadija ne, yanzu haka tasan yazo bauchi wurin ta. Kuma da Zainab in zata San khadijan ta riga ta sani, ai kuwa da da kyar su Kara magana kwana kusa.

"Kinyi shiri ko ba kwa magana ne?" Ta sake tmby.

"Muna yi. Ya ma zo..." Har ta Fara fada Kuma sai tayi shiru.

"Ina yazo?" Zainab in tayi saurin tmby.

"Kawai fa ya biyo ya gaida Umma ne, da zai je garin su kinsan dan taraba..."

"Ko dai yazo wurin ki?" Zainab in ta katse ta, dake bata da gsky tsit tayi.

"Har abun naku ya Kai nan Nabila, shine ko in sani ko? Da nice uwar surutu tuni zan sanar dake komai"

Da sauri Nabilan tace "Aa wlh zee ba haka bane. Kawai dai nasan ba kya son shine" tasan halin kayan ta, shiyasa tayi sauri explaining. In Summary ta Mata bayanin abinda ke tsakanin su.

"Yaushe Zaki zo Abuja wai?" Tmbyn da Zainab ta Mata kenan bayan ta gama fada Mata, hakan ya Kara tabbatar Mata zee in is not interested a maganan Sadeeq in.

"Sai na koma KD tukunna, zan zo kafin Anty Salma ta koma" daganan Sallama su kayi.

Wannan zuwan nashi brief ne, domin ko abinci sai da Ummah ta matsa mai sannan yaci.

"Ince dai kama iyayen nake magana ko?" Murmushi yayi, yana kokarin ganin reaction in Nabila da ke pretending hankalin ta na kan TV.

"Kar ka wani ce zaka biye Mata. Su ai iyayen su boko ya lashe zuciyan, sun Kuma daura su suma akan akidan. Yanzu mu da ba muyi bokon ba me ya faru ba? Ba ma muma muka kawo su duniyan ba? Yanzu Allah na tuba har a dinga wani fifita bokon nasaran akan Sunan Rasulu, zamani dai yazo Mana da bala'i wlh" Nabila da Halima Kam ba Wanda ya tanka ta, daman sun saba share batun ta. Sadeeq inne yace "Aa Ummah bokon da amfanin shi ai, kawai dai daya bai hana daya ne"

"Kai Kuma kaji ka da wani batu. Au na manta ashe kaima baturen ne ai. Yanzu Kai tsakanin ka da Allah Sai ka bar matar ka ta sunnah na fita da sunan karatun nasara? Ko da yake ma ni Kuma miye nawa? Ka dai turo iyayen naka kawai, a daura nima yanzu Zan Kira baban nata. Shi zancen aure ai ba a wasa da lamarin shi"

da sauri Nabila ta juyo tana kallon ta, ranta a hade ita ma Umman haden ran tayi. "Yarinya kya ji dashi dai, aure ne dai Sai anyi shi. Ana neman Miki hanyan Aljanna kina kaucewa"

"Ummah ni wai me na tsare Miki ne? Sai kace a wurin ki nake zaune Zaki dinga min haka Sai kace an gaji Dani. To ni wlh ma gidan mu ma zan koma" tana fadin hakan ta mike fuuu tayi hanya daki kaman wata guguwa.

Taba baki Umman tayi "Kya ji dashi yarinya, ba abinda zan fasa nidai" dauko wayan ta tayi tana kokarin mikawa Sadeeq in wai ya lalubo Mata numban Abbah, gwara ayi ta, ta Kare. Kawai sai gani tayi Halima ta wafce wayan, tayi hanyan waje da gudu.

"Ke Hali dubu miye haka? Gsky dai bature hali dubu tayi asara wlh. Bakin ciki fa ta nuna ma yar uwarta kiri kiri, kodan saboda ba ni na haifi uban ta bane oho? Kodan ma me akayi da jikin innah. Daman ni na dauke ta mutum, ashe ashe zata nuna min iyaka ta. Kiri kiri ta fa nuna ma jikata bakin ciki, wannan ai mugunta ne da hassada" Sadeeq lallashin ta kawai yake, ga dariyan da ke cin shi ganin Umman ta Fara tara kwalla.

Ba a dade ba sai ga Nabila ta fito rike da trolley inta da Kuma handbag, kaman dai yanda tazo. Ko kallon Ummah ba tayi ta yi hanyan waje.

"To ke Kuma Ina Zaki? Ina ce zance ya Kare, tunda dai Hali dubu ta gudu min da wayan. Ta min halin sata, kiri kiri ta nuna Miki bakin ciki fa Nabee. Gsky Hali dubu ba mutuniyar arziki bace, don haka ki fita daga sha'anin ta Nabee, domin zata Kai ki ta baro ne kawai."

"Ni Ummah ba wani maganan Halimatu ba, ni kawai kar ki Kira Abbah. Ki bari zan fada mishi da kaina" murmushi Umman tayi.

"To ai shikenan. Banda abinki ba ai na gaya miki Hali dubu ta gudu da wayan, tayi halin bera. Kuma tunda zaki fada mishi in ai hakan ma zai fi kawai. Ba ruwana ma ni, yanzu dai ki maida akwatin ko" Shi dai Sadeeq yana daga gefe Yana ganin drama. Ta je ta ajiye jakan ta dawo. Lokacin Kuma Sadeeq in ya tashi tafiya, don sauri yake.

Yau ma Sai da ya Kara ma Umman wani kyauta. Nabila ta fita raka shi, suka hadu da Halima a soro tana danna wayan Umman.

Tana ganin su ta mike tsaye "har ka fito?"

"Haka kika iya rest?" Ya fada yana dan darawa. Ita ma dariyan tayi "Yau ai na San Baba Sai yayi awa kusan uku a na karanto mishi girman laifin da na aikata"

"Ah to bake Mai yar uwa ba" ya amsa, Nabilah dai murmushi kawai take. Sallama su kayi da Haliman, yau ba ta biyo su wajen ba, su biyu su ka fita.

"Nan da two weeks Zamu yi POP" ya fada yana folding hannun shi bayan ya jingina jikin mota yana kallon ta.

"Allah ya sa albarka" tace.

"Yaushe Zaki zo?" Da sauri tace "Ina?" Dariya yayi ganin reaction inta. "Kano Mana, ko ba Zaki zo wurina ba?"

Sunkuyar da Kai tayi "Rufa min asiri"

"Asirin ki rufe, to yaushe Zaki Abuja? Ko su ba za aje musu hutu bane?"

"Zani Mana, dana gama na nan"

"Zamu hadu a can ai" da yace haka sai da taji wani dan faduwan gaba, dalili kuwa tasan gidan Mamma zata. Ta Kuma San ba zata yi tolerating kawo saurayi ba ko da wasa. Ta dai San kila Sai taje wurin Anty Salma ta ke da daman nan.

"Zan tafi, me zan samu da zai dinga tuna min da ke" ya fada yana kallon ta, Sai dai ba irin kallon da is normal bane. Kallon da ta gane yanzu Yana Mata in yana niyyan sa ta wani abu ne.

"Ba muna waya ba" ta amsa, tana dan kallon shi ta gefen ido.

"Not only your voice my Beela" shiru yayi, yana kallon ta don San gane reaction inta. Idanuwan shi yayi kaman wani Mai jin bacci, nan ko tsabagen soyayya ne dake diban shi. Da akwai yanda zai yi ya maida Nabila jikin shi yanzu da yayi, Yana jin kaman duk wani numfashin sa, hade yake tafiya da bukatan ta a kusa dashi.

"Can you get in the car?" Kallon motan yayi sannan ya kalle ta. Tsoro yanayin shi ya bata, saboda gani tayi yanayin shi ya mata shige dana ranar graduation In su. That moment da yake kallon ta, kafin ya hade lips inta da nashi. Tana jin kaman inta shiga ba abinda zai hana wannan yanayin Kara faruwa. Ba abinda kuwa ta ke tsoro kaman yanda ta ke jin ba za ta iya hana shi ba, in har yayi attempting yi in.

Shi inma yanayin ta ya karanta ya bar zancen. Hannun shi yasa ya kamo hannuwan ta, duka guda biyun. Yana kallon ta cikin idanu, kafin ta sauke nata a kasa. "Me yasa baki iya hada ido dani wai?" Cikin kasala ya fadi maganan. To itan ma baki daya jikin ta, na amsa contact in hannun da ke tsakanin su. Wani irin abu ta ke ji kaman Yana Mata yawo a cikin jini.

"Ban so eye contact" ta amsa

"Saboda yana karantar da ke abubuwan da suka fi karfin kwakwalwar ki ko?" Ba ta amsa shi ba, saboda kusan hakan ne. Duk lokacin da yayi kokarin hade idanuwan su wuri daya, Sai taji wani abu na daban na zagaye ta, haka Kuma ta kanji kaman kanta ba zai iya dauka ba. Sannan ta Kuma jin kafafun ta, kaman ba zai iya rike ta ba, kaman zata silale kasa ta koma ruwa, kaman yanda kallon da take samu daga gare shi ke sata ji. Tana jin Kam ba wani sauran tunani Mai kyau a tattare da ita. Ta kanji kaman shi kadai ne, abinda ya rage Mata Mai kyau a rayuwan ta. Ita da kanta, ta kanyi mamakin yanda soyayyan shi ke sa Mata jin kaman zuciyan ta a cike take, ba Kuma ta bukatan wani abu a cikin ta still Kuma a wannan lokacin Sai ta na jin wani irin zafi da radadi na ratsa zuciyan. Hakan na birkita ta, ta rasa menene zuciyan nata ke bukata haka.

Yanzu haka ba ta San dalili ba, Amma Sai take jin tana so ta yi kuka, ko abubuwan zasu ragu Mata. To abun daure kan shine, ita ba wai tashin hankali bane ya Mata yawa. Shin daman in abun farin ciki yayi ma mutum yawa Yana sa shi jin haka ne? She is feeling hopeless, abubuwan duk sun taru sun Mata yawa har suna neman su fi karfin daukan ta.

Kara kamo hannuwan nata yayi sosai, ya daura a kan kirjin shi, ya musu wani irin runguma Mai kyau. Tilas ta dago idanun ta, tana kallon shi. Duka contact in da suka yi sharing bai fi na Yan sakwanni ba Amma ji tayi kaman zata malale a wurin.

"Kar ki damu, you will get use to everything. But you will always be safe with me, kinji" da Kai ta amsa mishi, sannan ta dan runtse idon. A hankali ya saki hannun. Bude motan shi yayi, ya dauko leda biyu.

"Wannan ki ba Halima tsaraban tane" ya fada yana Mika mata ledan. Sai dayan Kuma yace "old edition of my favorite novel. Tun ina secondary na karanta, shine na kawo miki."

A/N: Please COMMENT, share your thoughts. You are not motivating me, honestly.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top