7
A hankali ya ke moving jikin shi toward kujeran da take zaune. Dan sunkuyar da Kai yayi, ta yanda yake fuskantan ta da kyau "Na- Bee-larh" dagowa tayi tana kallon shi. A hankali ya Kara furta "Ina son ki" taba saitin zuciyan shi yyi "My heart beats for you Nabee" duk tension in da take ciki, ba ta San lokacin da ta daga idanun ta, ta sakan mishi harara ba.
Dariya yayi sosai, duka dimples in shi suka lotsa sosai. One of the captivating thing, she found in him. Abinda ma ta lura, sanin dimples in na mishi kyau ya sa yake yawan yin murmushi.
Kamo hannun ta yayi, ya bude yatsun ta ya hade wuri daya da nashi. Ba ta janye hannun ba Sai wani irin kallo da ta watso Mai. Ai kuwa Sai ji tayi ya sa dayan hannu ya shafo kan idanun ta. "Cute eyes, wai ke ma kin iya tsiwa ko?"
Ba tace komai ba Sai sa hannu ta da tayi, ta rufe idanuwan ta. Dayan hannun nata kuwa Sai faman wasan ya ke dashi.
"Nazo har zan tafi baki ban komai ba"
"Me kake so in baka?"
"Nice words form you. Yanda zan dinga tuna ki ina tuki, in ta murmushi ni daya"
Kanta dai a kasa yake, ya Kara cewa "Ina jiran ki, am getting late kin kuma san hanya ba kyau"
"Thanks for the visit, it nice seeing you again" more like a whisper, zancen nata ya fito.
"Bara na maida ki gida, kafin a Fara neman ki" Yana fadin haka, ya tayar da motan. A kofan gidan ya tsaya, har ta danna kofan tana fadin "Allah ya kiyaye hanya" ta ji kofan a datse ya ke. Juyowa tayi tana kallon shi, ya daga Mata gira.
"Haka zaki tafi? Ba kice min kina so na ba"
"Ya ilahi!" Ta fada a ranta, ta dai lura ya cika neman rigima. Haka Kuma ya rantse Sai ya bi ta yanda yayi, ya cire ta daga comfort zone inta.
Ta dago tana shirin mishi magiya ya barta, ta wuce Kar tayi dare. Kawai sai gani tayi Yaya Khalipha ya fito waje. Yanayin yanda ta bishi da kallo yasa ya gane akwai wani abun. "Ya dai?"
"Ya Khalipha ne, Yayan Halima. Jiya ya mana warning akan Kar ya sake ya ga wata da saurayi a cikin mu"
"Au ashe ni saurayin kine ko?" Yanda ya fadi zancen ya sata darawa. "Shine Kuma ba za ace ana so na ba?"
Shiru tayi kawai tana murmushi. Gani tayi ya murda handle in kofan shi. "bara na fita na tsaida yayan naku, na sanar mishi na zo wurin ki ina neman izinin shi, tunda ba zaki fada ba" ta dauka wasa take amma Sai taga ya bude kofan yana kokarin bin bayan Yaya Khalipha da ya dan Fara nisa" da sauri ta Fara mishi magiya da ido da hannu, gudun ma Kar tayi magana Khaliphan yaji.
"Oya to tell me kafin naje" ta tsaya tana hesistating taji kawai ya bude baki "Bawa..."
"I love you wlh" ta fada da sauri, dariya ya kwashe da. "Yarinya nasan maganin ki" bude motan tayi cike da kunya ta ruga cikin gida.
Ranar gabadaya dinga tuno yanda Shirin su ya kasance a school take. Daga practicing poems, ranar aka basu wani Assignment in chemistry mai ban wahala. Duk son ta da chemistry, Sai da abun ya gagare ta, duk wanda yazo yaji ita ma ta kasa solving zai ce lallai ba kanta kam. Ba ma suyi zasu hadu ba ranar, kawai ya shiga ajin juniors Kai ma wata yarinya sako, dake shine master on duty ranar kawai ya ganta kanta akan littafi Sai faman cizon biro take, tana neman solution.
"Lafiya kuwa?" Ta ji an fada a kanta, murmushi tayi ganin shine. Don ko lokacin ba su wani Saba sosai ba, ba wani abinda ke shiga tsakanin su a lokacin Wanda ba academics bane.
Tsintar kanta tayi da mishi bayanin assignment in duk da tasan shi English teacher ne, Amma she is hoping for solution ko yaye ne. Amsa yayi ya dan duba, to abinda ba ta sani ba shine first degree in shi kan Biochemistry yayi. Don haka yana amsa ya gane matsalan, cikin sauki ya Mata bayani. Sai taga abun ma ashe sune suke maida shi babba, it so simple ma.
"Daga yanzu ko ba English, if you ever have any problem a wani subject, tell me and I will try to guide you" Yana fadin hakan ya fita, Amma ta ji dadin Assignment in nan sosai. Don baki daya ajin su, ita taje ta musu bayani.
Daganan Kuma, the next abinda ya Kara bringing in su close shine, wani American series. Wani word kawai ta fada, the next thing he said is, "you also watch this series? Oh My God!" Daganan Suka barke da zancen series. A lokacin Kuma an saki wani sabon season ne, gashi Kuma ita tana school shi Kuma currently shi ya ke kallo. Saboda haka duk abinda ya kalla, zai je ya bata labari in details, bai ommiting komai. Sai dai suspense in da yake Kara Mata, kaman yace "Kaza da kaza ya faru Amma ke a ganin ki me Zaki yi at that situation?" Ko Kuma yace "knowing that actor, how kike ganin zai yi reacting a wuri kaza" she rarely guess, saboda series in is not predictable. Sai ta gama guessing inta, ko ta gama fadan yanda zata yi in itace Sai yace "To kinji kinji yanda actor in yayi" then it will be more intriguing.
Next stage in kuwa kananun abubuwan da ya fara kawo Mata. Ba ta mantawa. Kyautan da ya fara shiga tsakanin su, kunun aya ne. Wani hadadden kunun aya da ya Sha kayan kamshi, taji dadin kunun ayan nan. Shi daman ciman shine, kawai ranar ya bata bottle daya. Daga kunun aya, watarana suna magana she accidentally said tana craving kosai. Ai kuwa washegarin ranar taci kosai. Bayan nan abubuwa dayawa ya kawo Mata, musamman na kwadayi, dake shi ma gwanin cin sune.
Kaman yanzu abinda ya ba ma Halima ma, parket in chocolate ne kala kala Kuma duk bana banza.
Ita ta fara Kiran shi da taga dare yayi shiru. Text ya turo mata, yanzu zai shiga gida. He will call her back. Bayan ya kimtsa yayi calling inta back, basu dade suna magana baya suka yi Sallama, Sai dai hiran SMS ya koma.
Sir: "I love you wlh, that sentence i can't never forget"
Fuskan ido a rufe ta tura mishi, wato she is shy. Fuskan dariya ya maida Mata. Sai Kuma ya Kara typing
Sir: "Sarakan kunya, a haka za ayi soyayyan?"
"Bayan kace a koma mutunci kawai"
Sai da yayi dariya shi kadai, yanzu ya san lamarin ta da wasa. Domin dai kure ne kawai yake Mata, bai jin zai iya rabuwa da ita.
Sir: "Scared? Ai to kin ringa da kince kina sona ba Kuma batun komawa"
Rasa abin cewa tayi, Sai shine ya Kara turo mata msg.
Sir: "Ummah tace in turo Dad ina, what do you have to say about it?"
"Kai kaji tsohuwan nan Sai kace itace Mai bada ni"
Bai bata amsa ya Kira ta a waya. Da sauri tayi picking. Bai tsaya sallam ba taji yace "Baki son aure na Nabila?"
"Ni bance ba sir kawai dai..." Sai Kuma tayi dif.
"Kawai miye? Nd banson sir in nan, am no longer your teacher. Call me by name, Sadeeq i prefer it" jin bata amsa shi ba yasa shi Kara fadin "kinji?"
"Eh" ta fada a takaice, tare da fatan zai bar maganan haka. Sai dai a lokacin ya sake fadin "say it, let me hear"
"Ni dai bazan iya fada ba" yanda ta fadi maganan cike da shagwaba ya sa shi sakin wani murmushi Mai cike da shauki. Hakika shi in ya kasance Namiji mai son yaga mace tana shagwaba. "I like it" ya furta a fili.
Ita dai Nabila ta dauka sunan ya ke magana don haka tace "It a nice name, ni dai kawai ya min nauyin fada ne"
"Kaji wannan yarinya fa. Ni Kuma nake fadan naki?" Kaman yana ganin ta, ta tura baki cike da shagwaban ta kara furta "To ai Kai kace. Ni Kuma fa ka girme ni. Duka yayyina maza am not calling their names. Da Yaya Khalipha da brother haka nake ce musu"
"To ni yayan ki ne? Saurayin kine ni, so treat me as one" Ba dai ta amsa shi ba, Kuma taki ta Kira sunan duk kuwa mitan da ya dinga Mata. Daga baya ita ma rigima ta saka, akan ba zata iya Kiran sunan ba.
"Zan Kama ki yarinya, you must say it to my face ma kuwa. Bara na kwanta na gaji wlh" daga yanayin muryan shi kadai, zaka tabbatar da gajiyan nashi. Don haka tace "Allah ya huta gajiya, Sai da safe"
"Okay, I love you" shiru tayi, ta kasa fadin komai.
"Nabila" taji ya Kara Kiran sunan ta. Jin bai ce komai ya sa ta amsa da "Na'am"
"I love you sosai kinji" kaman wani yaro, dake needing reassuring abu haka yayi maganan. Hakan yasa ta murmusawa yayin da take jin sauka da girman abinda ya fada in na ratsa ta, ta ko ina daga sassan jikin ta.
"Baki ce komai ba toh?"
Cikin kankanuwar murya tace "Thank y..."
Ba ta ida ba yace "You don't need to thank me, Gud night dear" kashe wayan yayi.
Bayan nan, ta dade tana kallon wayan. Haka kurum take jin Sam ba ta kyauta ba, tunda har ta fahimci hakan daga sautin muryan shi. Kasa tabuka komai tayi, hatta baccin ta kwanta Amma tunani ta ke zai kwana da fushin ta. Duk yanda ta so kauda tunanin, hakan ya faskara.
"Nabila, it won't kill in kinyi yanda kike so. After all ma ba karya Zaki yi ba ai" wata zuciyar ta ce ta fada Mata. Nan take ta Fara jin in har ba ta aikata yanda zuciyan ke fada Mata ba, to kaman a baza ta samu natsuwa ba. A hankali, kaman ba ta so ta dau wayan ta, ta Fara typing. "Nima i love you sosai my sadeeq" bayan mintunan da ta dauka tana typing, words in da yaci ace ta gama a Yan sakwanni. Sai da ta sake yin wasu mintunan tana kallon mssg in. Kaman Kar ta tura, Sai dai zuciyan ta ya riga da ya rinjaye ta. Kaman dole, ta runtse idanun ta bayan ta Kai hannun ta kan send. Dannawa tayi, sannan ta bude idanun domin tabbatar wa ko sakon ya tafi. Kaman mara gsky Kuma, Sai tayi saurin kashe wayan nata baki daya.
Sadeeq, ya ji dadin ganin mssg in nata sosai a daren. Shi kadai ya dinga kallon screen in wayan shi yana murmushi, Yana Kuma Kara jin soyayyan ta na ratsa shi. Yana son Nabila, domin duk wani irin taku da tsari irin nata, birge shi yake. Bai Kuma ji alamun samun nasara ba, Sai yanzu da ya tabbatar yana gab da cin nasaran. Musamman da yasan yarinyar ta Fara son shi, Kuma ta damu da komai nashi. Sai dai Kuma, ba hakan ya ke bukata ba. Bukata ya ke, ta mishi irin soyayyan da komai zai faru ba zata iya rabuwa dashi ba. Irin soyayyan da damuwan shi ko matsalan shi zai zama nata, ba wai kawai ta damu dashi ba. So yake, taga kaman in ba tare dashi ba to rayuwan ta ma, taga kaman bai da sauran amfani. Yana son ta dauki lamarin shi ba a wasa ba ko Kuma wani abu da zai iya gushewa. Ya dinga ganin hakan a duk wani motsin ta, kalaman ta, idanuwan ta, yanayin ta Kai hatta tafiyan ta. Ta yanda ba wani da namijin da zai iya kawo mishi cikas a game da ita, bama da namiji ba hatta Yan uwan ta.
Ya so ya tura Mata mssg, ko Kuma ya Kira ta. Sai dai bai cika son yawan takura mata ba. Hakan yasa ya kyale ta akan da safe ya Kira ta. Ko da ya Kira in, Sai ji yayi wayan a kashe.
Ita ko Nabila, kunya yasa ta kasa kunna wayan ta ko bayan da ta farka. Sai ma shiryawa da suka yi, suka fita da Halima can federal lowcost gidan wasu Yan uwan su. Hira yayi dadi, basu suka bar gidan ba Sai bayan la'asar. Shi inma Nabilan ce ta matsa. Tasan dole Sadeeq zai neme ta, ga wayan Kuma a kashe yake.
Tana kunnawa, ta Kira shi. Har ya gama ringing bai dauka ba. Za ta kara dialling, Halima ta rike hannun ta. "Ki bari Mana zai Kira ki" ba don taso ba ta hakuran. Halima dai kallon yanayin ta, tayi tace "You love him too much, kaman kina tsoro Kar wani abu ya faru" musawa tayi kawai, ta bar wurin Haliman. Sai dai Kuma a zuciyan ta, tasan hakan ne. Tana tsoron ta mishi wani abu, da zai sa ya Kuma ce mata ya hakura su koma kaman da su dinga mutunci kawai. She likes him sosai, Kuma tana jin dadin kasancewar ta a tare dashi. Musamman irin hiran da yake mata.
Bai kuwa Kira ta back ba. Sai dai bayan magrib ya turo Mata SMS.
S💞: "Nayi fushi Nabila" tana Karanta mssg in, cikin hanzari ta tura mishi.
"Am sorry pls 😔" hade da fuskan tausayi. Bai Mata reply ba, Sai bayan yan mintuna Kiran shi ya shigo. Yana Fara Kara, ta daga hade da yin Sallama.
"Ke bakisan ina da bukatan jin muryan ki kullum ba? Ko bakisan hankalina bai kwanciya in banji ba? Kina son damuwa na ko?" Yanda yake maganan, na kara tabbatar Mata da tabbacin duk wani abinda yake fada in.
Cikin rawar murya tace "kayi Hakuri bazan sake ba" shiru yayi, ta Kara cewa "kaji please?" Muryan nata kaman Mai Shirin kuka, that get to him sosai. Kaman Kar yace Mata bai hakuran ba, ta cigaba da lallashin shi. Amma Kuma bai cika son yana wahalar da zuciyan ta ba, don yana fahimtar yanda take ji.
"Shikenan, Amma Dan Allah Kar ki Kara kinji?" Da sauri tace "In Sha Allah, ka wuni lfy?" Nan ya fara gaya Mata how he feels when her no isn't going through.
"Ji nayi kaman in taho Bauchin Allah, gashi banda numban kowa. I think ko na Ummah ya kamata in samu, Kinga na dinga gaishe ta ma" dariya tayi, sannan tace "Naki wayon, ban yi trusting Ummah ba. Zata iya yin komai ban sani ba"
"Wai ke me kike tsoro? Ta sa ranar auren mu? Ke ba a dadin ki bama, za ki samu yaro dan saurayi, sabon jini ga shi Kuma kyakyawa Bafulatani" cikin wasa yake maganan. Ba yau ya fara Mata irin wasan nan ba. Dan tun a school ya kan gaya Mata "kin San fa irin mu Mata ke so, gani da kyau ga kwarjini. Ko kema Zaki shiga daga ciki ne?" A wancan lokacin, rolling eyes inta take tace "Ina kyaun a nan? Kuma fulanin gani kuke ba Wanda ya Kai ku kyau a kasar nan. To nidai Kam ban ga kyaun ba" hararan ta ya kanyi "Zaki sani yarinya, watarana Zaki maimaita nema" daga haka suke barin zancen, ashe shi tun lokacin ya San abinda ya ke nufi. To itan ma ba wai ba ta sani bane, kin sanin take kawai ta share batun.
A/N: please share your thoughts on Sadiq. How is the story so far?
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top