6
Halima ta sa ta gaya ma Umman za suyi bako. Hararan ta Umma tayi tana fadin "Kai kaji min yarinyar nan, ni kakar kice da Zaki kawo min saurayin ki? Harda zuwa ba ko kunya wai Umma za a zo gaishe ki" hade rai Halima tayi.
"In kin kwantar da hankalin ki jikar taki ce zata kawo shi bani ba" murmushi Umman ta Fara "Au to kice bakon wannan ja'irar yarinyar ne. Amma ke tsaya me ya hada ki da yan nan garin kina garin gwamna fisabillahi. Ni fa ban son matsiyata gaskiya"
Dariya ma abun ya so ya basu. "To Umma ba ma dan nan garin in bane. Daga Kano zai zo, shiyasa aka gaya miki domin a shirya tarban shi" Halima ce ta sake bayanin, nan da nan kuwa fara'an Umman ya karu.
"Ah to Ma Sha Allah, ince dai iyayen naki basu sani ba? Don na fi so ni in Fara ganin shi, in tantance shi tukunna" Nabila dai tabe baki tayi. Tana jin Umman na kiran babah akan azo a hada ma bako kayan tarba.
"Ai Sai gobe zai zo" tana fadin haka, ta dau gyalen ta suka yi saurin yin waje. Wurin Friend inta da suka gama school tare, Rukayya. Suna fita suka ci karo da Yaya Khalipha, da sauri su ka juya cikin gidan a tare. Ai kuwa a hanya suka hadu da Anty za ta fita Unguwa. Nan fa su ka fara rokon ta akan tace tare zasu fita, saboda Kar ya hana su.
Ai kuwa Yana hango su ya mike yana gaida Antyn. "Anty Unguwa Zaki je ne? Muje in sauke ki mana" a tare suka kalli juna, Sai Kuma su kayi saurin basarwa. Hakanan su ka shiga motan ba da son ransu ba, gashi gidan da Anty zata kwata kwata ba hanyan inda suka dosa bane. Don wahala hakanan suka tsaya, ya sauke su sannan, bayan ya wuce suka lallaba zuwa inda zasu.
Ranar da Abakar in zai zo, tun da safe ba ta iya komawa bacci ba ma. Tsabagen tension da bata San na menene bane, ba wai ranar za ta Fara ganin shi ba. Sai dai tasan Kuma ba ta taba zama dashi a matsayin wanda wani alaka ta so ke tsakanin su ba. Gabadaya Sai ta ke jin kaman ba Sir in da ta sani bane zai zo wurin ta.
Ko bayan sun gama karyawa, Wanda abincin ma ba wani maida hankali tayi taci ba. Sai kaiwa da komowa take duk ta kasa natsuwa. Umma dai zuba Mata idanu tayi, Sai da ta ga abun ba na kare bane tace "Oh ni ya' su. Yaran bana Sam ba kunya, yanzu ke saurayin kike ma rawan jiki tsakanin ki da Allah? Ni Kam wannan wani irin tarbiyya ne wai ma'u ta baki?" Nabila ba ta tanka ta ba, fama ma ta ke da abinda ya dame ta ita. Halima kanta, dariya kawarta ta take bata.
"Ke relax mana Nabila, lafiyan ki kuwa? Sai kace in yazo cinye ki zai yi wai? Dan Allah kwantar da hankalin ki. Ba fa yau Zaki Fara ganin shi ba, all these nervousness" da kyar ta iya kakalo murmushi. "Ni ma bansan meya sameni ba Halima, i can't be calm" dariya Haliman ta kara yi "Ni ko zan so in ga wannan mai sa'an haka"
Karfe biyun rana ya iso, da ke a ranar zai wuce Jalingo. Nabila Kam kasa zuwa shigo dashi tayi, Sai Halima ce da wani kanin ta su kaje su ka shigo dashi har falon Umman.
Da fara'an shi ya dan durkusa kasa yana gaida Umman. Ta amsa tana kallon shi, da gangan Halima taki matsawa domin ta ga reaction in Umman kawai.
"Mun same ku lfy kaka?"
"Ina fa lfy dan bature? Ina nan ina fama da ciwon baya da kafa, ga ba daman mutum yayi magana yanzu sa ce wai tsufa ne. Na ga dai su inma zasu tsufan, ko ba haka ba dan bature?" Murmushi yayi sosai "Hakane Kam Umna"
"To Kai ko dan bature, tsakanin ka da Allah ina jika ta, ta samo ka ne wai? Anya ma ba niyyan dauke ta kake dashi ba? Gama yanzu naji ance garkuwa da mutane shine sana'an da ke ta..." Dariyan Halima ne ya katse Mata maganan ta. Duk su ka juya suna kallon ta.
"Wlh ba ni bace abun dariya, Kakar ki Innah ita ce abun dariya Amma bani ba" saurin wucewa Halima tayi, don tasan don Ummah ta sille ta gaban shi, ba wani abu bane.
A daki ta same ta tayi jugum tana kallon kayan da ta fiddo zata sa. "Nabila miye haka? Ya fa iso fa" da sauri ta mike tsaye. Simple Abaya ce daman ta fiddo zata saka. Kallon Haliman tayi tace "To yanzu fita zan yi kuma gaban Ummah?"
Hararan ta Halima tayi "To wai ba kakar ki bace? Kinsan dai Ummah ba lallai ta baku wuri ba ko?"
"Aa gsky nikam ba zan iya zuwa ba, in sun gama ai zai Kira ni ma" dole dai Haliman ita kadai ta koma falo, ko da ta fita ta iske baba duk ta cika mishi gaba da abinci da na sha iri iri, kusan duk su biyu suka hada shi ita da Nabilan. Ta same shi hankali kwance, Sai hira su ke da Ummah Yana ta kwasan gara abin shi, shi abubuwan Umman ma kaman nishadi kawai yake sa shi.
"Amma dai fa ba wani daukan lokaci za ayi ba. Tunda an riga an San juna, da iyayen ka sun zo kawai ma sai a daura ba Sai an tsaya wani wahala ba wlh. Ni daman ban cika son bidi'an nan ba. Gwara ayi auren kawai, a wuce wurin" Zaro idanu Halima tayi, ba tasan Sanda tace.
"Ummah daman kinsan shine?"
"Wani sani Kuma bayan wannan Hali dubu ai gashi mun zanta dashi. Kuma ni gsky ya kwanta min don haka dole Usman ya bi zabi na" juyawa tayi wurin Abakar in ta cigaba da fadin "Ka ganta nan ita ma yar uwar tace. Duk da bani na haifi baban ta ba, Amma dai duk dangi dayane. Don haka in kana da wani Dan uwa ko abokin da ka yarda dashi, itama kawai a taimaka Mata, Sai ayi tare kaga an Kara zumunci"
Da sauri Halima ta juya tana kwallawa Nabila Kira. Shi dai Abakar dariya kawai yake yi, domin tsohuwar na tuno mishi da kakar shi Iya, kusan irin mitan ta kenan.
"Ko ki fito yanzun nan ko Kuma Ummah ta miki sakiyar da ba ruwa" nan fa Halima ta kwashi duk abinda taji Ummah na fada ta gayawa Nabilah. Ai bata ma tsaya wani tunani ba ta debi takalma ta yi falon tana fadin "Ummah dan girman Allah ki rufa min asiri"
Daga Umman har Abakar in juyowa su kayi suna kallon ta. "Asirin mai za a rufa Miki?" Ya bukata, yana kallon ta. Saurin sunkuyar da kanta tayi kasa cike da kunya. Sai lokacin ta gane abinda ta aikata.
"Gwara dai ka tmby ta ai, ke kuwa duniya wani asirin ki ne kike son a rufe?" Cike da kunya ta fara takawa tana niyyan tafiya daki.
"Ke miye haka Kuma? Ki dawo ni ban son gulma da munafunci. Tunda kin futo ku menene na komawan. Ni bara ma in tashi, lazimi zan yi" ba ta tsaya jiran komai ba Kuma ta dau hijab inta da carbi ta nufi daki.
Ajiyan zuciya Nabila ta saki, ganin da gaske tafiyan tayi. "Ummah case ba" Halima ta fada tana girgiza Kai.
"But she is fun to be with, tana da dadin hira" ya fada yana kallon su biyun.
Wani irin "Hmmmm!" Suka ja a tare.
Bayan tafiyan Halima ya dan juyo yana kallon ta. Gaishe shi tayi hade da tmbyn hanya.
"Alhmdlh" ya amsa. Dago idanuwan shi yayi da kyau ya zuba mata, Abayan da ke jikin ta dark blue ne da aka yi mishi ado da golden. Duk da ita ba wata Fara bace sosai Amma Kuma kayan ya amshe ta sosai.
"I've been wondering, yanda za kiyi looking ba a cikin Uniform ba" kanta a kasa, Sai blushing take tace "Ai duk abu daya ne"
"Incomparable! Nabila kin ganki kuwa? Superb!"
"Thanks" ta fada a takaice. Tana ji ya Kira sunan ta, ba ta amsa ba don ta San magana ya ke son yi.
"Dago ki kalle ni mana" Slowly, ta dago idanuwan ta, Sai dai idanun ta na fadawa cikin nashi, taga irin kallon da yake aika Mata. Da sauri ta dauke nata idanun gefe, ta runtse su.
"To fah! Kice abun Babba ne. Come on mana nine fa, ko kin manta duk hiran da muke zama muna yi ada? Muna sharing ideas, you weren't acting like this. So why the sudden change?" Kaman ba zata yi magana ba tace.
"To ai da, da yanzu ba daya bane" dariya ya danyi yace "To miye bambancin?" Shiru tayi bata bashi amsa. Ya sake cewa "To wanne yafi dadi?"
Ba ta tsaya tunanin amsan da ke bakin ta ba tace "Wancan mana" ko kadan ba ta kawo wani abu a ranta ba.
Shi kuwa gogan daman tarko yayi niyyan mata "To a dawo?" Da sauri ta bude ido tana kallon shi, kalaman nashi ba karamin girgiza ta yayi ba. Tsoro kiri kiri ya bayyana a idanun ta.
"Ehmm? Ko ya kika gani?" Kasa magana tayi, she can't believe shi ke gaya Mata wannan maganan Kuma a gidan kakannin ta. Yana nufin a share duk wani batun soyayyan da ya Mata kenan su koma mutuncin da suke ada? Tab, to tayi ya da zuciyan ta? Da ya fara saman ma kanshi gurbi a ciki. Wani irin dimi taji yana hada mata daga can cikin jikin ta. Missed up emotions, sun taru sun hade duk a wuri daya. Ko yanayin fuskan ta, ya kasa boye halin dimautan da take ciki.
"Kinga ni fa Shawara na kawo Kawai. Tunda naga you aren't comfortable with my confession. Ni fa ban son takura miki kwata kwata. Ban son abun ya zama Kaman forcing inki nake, saboda kina ganin mutunci na ko Kuma jin nauyi na" ba ta katse shi ba har Sai da ya gama sannan ta dan kalle shi.
"Ni fa bance ba" ta karasa zancen tana dan dukar da kanta kasa. Boyayyen murmushi yayi "Baki ce me ba Nabeelarh?"
Shiru tayi bata amsa mishi, yayin da ta ke jin zuciyan ta na wani irin tafasa. Dan dago kanta ta sake yi sai dai idanuwan ta Kam a lumshe suke, yayin da zuciyan ta ke kara tafarfasa. Ba ta ankara ba Sai ji tayi ana hura Mata iska akan fuska, da hanzari ta bude idon. Ashe ya matso daf da ita, har tana iya jiyo numfashin shi. Wannan kusancin, baki daya nan da nan ya maido mata da close contact in da su kayi having a kwanakin baya, ranar graduation inta. Moment in da har yanzu ta ke feeling a cikin jikin ta, even though har yanzu ba ta gama processing in shi ya samu wurin zama ba, Sai dai ta San abu ne wanda ba ta jin zai iya gushewa a kwakwalwar ta.
Dan ja baya yayi, ya mike daga kasan baki daya ya koma kan kujera ya zauna. Agogon hannun shi ya duba "Garinmu da nisa, ya kamata in Kama hanya."
"Okay" ta furta a hankali.
"Ke kika min girki?" Ya bukata
"Ni da Halima muka yi"
"Good, haka za ki dinga min su masu dadi in mun yi aure" Kunya taji sosai har da dan dukar da kanta.
"Yan matana kenan sarakan kunya. Bara na ma Ummah Sallama ko?" Da sauri ta mike ta shiga dakin Ummah. Ba su dade ba suka fito tare.
"Bature har zaka wuce? To Sai yaushe Kuma?" Ummah ke tmbyn tana washe baki. Dariya yayi yace "Sai dai in Zan dawo Kuma" wasu kudade ya ciro ya dan ajiye a gefen ta. "To Ummah bara na Kama hanya"
"Ah to har da dawainiya? To angode angon Nabee" bata fuska tayi tana kallon Umman.
"Ke nifa ban son iyayi, miye kike kallona kina bata fuska Kuma?" Lokacin Halima ta fito, tana kunshe dariyan ta.
"To ai Sai kuje ku raka shi ko? Allah ya kiyaye hanya, kaji bawan Allah" haka suka fita daga falon nata suna biye dashi a baya.
Sai dai ya je wurin motan shi, ya bude. Wani leda ya dauko mai kyau ya Mika ma Halima "To Hali dubu, an gode da tarba Mai kyau. Allah ya bar zumunci" dariya tayi tace "Ummah ta ko ya maka kenan? Shikenan mun gode, Allah ya kiyaye hanya" ta fadi hakane, dan ta dago shi yana son magana da Nabilan ne. Don haka ta juya ita kadai ta koma, Nabilan har za ta bita. Irin kallon da ya taga yana mata yasa ta tsaya.
Bude motan yayi ya shiga, sannan ya bude dayan side in da hannun shi. "Bismillah" tilas ta zagayo, tana tunanin me Kuma ya ke so ya sanar mata haka.
Tana shiga, taji ya sa key ya tada motan. A tsorace ta juyo tana kallon shi. Gashin giran shi ya daga yana cigaba da murmushi. "Matsoraciya kawai, ba sace ki zanyi ba. Ina so muyi magana ne, Amma ban son mu tsaya a bakin gidan ku, ko na tsaya in?" Da sauri ta girgiza kanta.
Sun dan yi nesa da gidan kadan yayi parking. Daga kafafuwan shi yayi kaman wani wanda ya ke kan couch ya nannade su, kafin ya juyo yana kallon ta, kallo sosai ya ke bin ta dashi cike da shauki da dimbin so a cikin idanun shi. Kasa hada ido dashi tayi, dole tayi lowering gaze inta Amma ina, tagumi ma yayi yana kallon ta. Da alamun hakan wani nishadi ya ke sa shi.
"Bayan dawowa na daga UK ba, ba yanda Dad ina bai yi ba, in dinga zuwa Company insu ina ganin yanda aikin su ke gudana. To ni Kuma sai naki, saboda banda interest kwata kwata akan family business inmu, kaman yanda sauran yan uwana su ke da" Kai tsaye kawai ya fara bata labarin. Hakan ya sa ta maida attention inta kanshi baki daya, tun can daman labari na daya daga cikin dalilin dayasa shakuwan nasu ya Kai haka.
"Saboda haka yayi fushin da ban taba tsammani ba. Lokacin NYSC, ya tabbatar min da ba zanyi shi a garin Abuja ba. Ya min hakane saboda yana ganin kaman bazan iya jure rayuwan wani gari a Nigeria ba bayan Abuja da Lagos. Don haka ya sauke min su daga cikin garuruwan da zan yi Service. Ban so hakan ba, amma banda wani zabi. Ina da hanyan da zan bi in samu canjin Sai dai am afraid, in ban bi abinda yace ba again, zai hana ni aikin da na dade ina nema. Na dade da sanin ya amso min offer in, so kawai yake ya gani zan bi abinda yake so ko zan cigaba da mishi taurin Kai. Hakanan na hada kayana na taho garin Kano, a camp mu ka hadu da mansur. Kuma shi ya bani shawaran in zo mu nemi private School kawai, shi ya min hanyan samun makarantar ku, a lokacin duk ba wai son koyarwan nake ba. But now, i have never made a perfect decision than this, Nabila saboda ke ina appreciating hukuncin da mahaifina ya min." Shiru yayi yana kallon yanayin fuskan nata.
A/N: Okay, am sorry please. Am a bit busy today that i almost forget you guys. Anyway, here it is.
Any thing to say about malam Abakar? Just share your thoughts about him please. Nabeela should go ahead and fall for him or not? Any red flags about him?
Okay, let me ask this. If you meet a guy like Sadiq, will you fall for him or will you run for your life? State why please.
Yeah, please do share the book, we need more readers to make the journey more sweet.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top