20
Lokacin da su ka isa gidan sun iske Mamma na can side in Alhaji. Saboda haka sai suka zauna kawai abin su suna hdimomin su. Sai da Mamman ta Kira su tace su same ta nan side in nashi sannan su ka wuce.
Areef na hango Alhaji ya fara Mika mishi hannu har da kokarin yin tsalle shi a dole yana son yaje wurin shi. "Kai wannan zakwadin fa Areef" Nabila da ke hannun ta, ta fada tana kokarin Mika ma Alhaji shi.
"Zo nan takwara na kaji, yaro ya San takwaran shi" da sauri ya makale a jikin Alhajin Sai kace wani Wanda za a kwace. Duk dariya su kayi, sannan su ka gaisa ana dan raha.
"Wannan kanin naki dai sai anyi da gaske. Nace an bada yarinya amma Sai roko na yake, ni na rasa me yake nema Kuma. So yake in hana waccan auren Sai kace nine mahaifin ta" Alhaji ke maganan yana kallon Salma. Murmushi tayi domin ita ma dai rigiman da suka gama yi da Bilal in kenan.
"To ko kaine mahaifin ta ai ba a neman cikin nema ko. Haram ne Allah ya hana. Ni na rasa saurin me Bilal yake, duka nawa ma yake" Mamma ta fada ranta a dan bace, daman tunda aka fara maganan ba wai son zancen take ba Sam.
"Aa ni ban ga laifin auren wurin ba. Tunda yaro ya nema ai akwai fa'idan shi nayi hakan. Ba gwara auren ba akan yaje ya fada neman matan banza" Alhaji ya amsa. Ita dai Salma tayi shiru ne kawai. Amma ta San dan uwan ta, abinda duk basu fahimta ba, ba wai auren bane ke shaking in shi. Aa, Layusan ce bai son ya rasa. She understands him shekarun da suka yi suna tare dole rashin shi ya firgita shi.
"Kilan ba alkhairin shi bace Kuma, shiyasa hakan ya faru" Anty Salman ta fada kawai. Alhaji ya amsa da "Tabbas hakane Kam. Ya nemo wata kawai, ko in baida shi mu Sai mu nemo mishi tunda da dai yana son auren, gwara a mishi kawai. Mu rufa ma kanmu asiri" Alhaji ya sake fada.
Anty Salma dai ganin ana Shirin ballo ma kanin ta ruwa yasa tayi saurin bude baki "Alhaji Bilal fa ba wai aure ne yake so ba, daman saboda yarinyar ne sun dade suna tare. Jin an Fara zancen auren ta shiyasa yace a nema mishi itan. Amma tunda hakan bai yiwu ba, Ina ganin kawai a barshi don kanshi zai nemo watan ai, in ya tashi" Hararan ta taga Mamma nayi.
"To Uwar tsari. Laifi ne dan an mishi samo mishi watan? Ko da yake zamanin ma gwara ma kowa ya nemo tashin yafi maka kaima kwanciyar hankali" Salma dai ba tace komai, jin ta hau ta Kuma sauka ita daya dai.
"Allah ya kyauta, na nemi Bilal inji dai. Amma wancan Kam, ki gaya mishi ya hakura ya daina maganan ta. Ya bar yarinya tayi auren ta, don iyayen ma sunce ta tada musu hankali. Allah ya zaba ma kowa mafi alkhairi" duk suka ce Amin.
Sai lokacin Alhaji ya juya ya ga Nabila da ke can gefe tana danne dannen ta, ba ta ma San me suke tattaunawa ba.
"Ni Nabila wani School zata ne?"
Nabilan ta juya. Mamma ce ta bashi amsan yanda su kayi da Abbah. Ba ta ma sani ba ashe ta neme shi akan zancen. "Ni dai gsky nace mishi a bar maganan KASU in nan kawai, wahala kawai za ta Sha. Inma ba ta son wajen ga Universities inmu a nan, ga Nile ga baze gasu Alhikmah duk. Ko Kuma Maryam Abacha na Niger duk ana karatu dai"
"Ke dai kin fi son Private University naga alaman" Alhaji ya fada, tayi nodding kanta "Matsalan strike nake guje mata gsky. Ga sauki gwara kawai a bishi" girgiza Kai yayi "Gskyn ki Kam, kasan mu dai ta zama abinda ta zama. Sai a Fara applying don Ina jin Baze sun bude admission"
Mamma ne ta juya tana kallon Nabila "Kina son baze?" Ta bukata. Nabila kuwa ji tayi kaman ta zuba ihu, gsky tana son komawa gidan su. Tana son zama da mamin ta, duk da dai tasan zasu rabun Amma ba ta son ace ta bar gidan su hakanan. Ga Amina da sauran kannen ta.
"Eh Ina so" ta fada a hankali ba wai don ya Kai har zuciyan ta ba.
"Sai a nema kawai" Alhajin ya fada.
Ita Anty Salma da ke ta gane matsalan kanwar ta ta. Tasan ba zata wani iya taimaka Mata ba, Amma ta lallashe ta sosai. Tace Mata kwana nawa nema, in anyi hutu Sai tace tana son zuwa ganin Mamin ko Alhaji ai zai barta. A haka suka bar zancen duk da dai ba wai tana jin ta samu solution bane.
Sai wurin da suka zo tafiya maran ta ya fara rike Mata. Suna falon Mamma suna kallo, ta Fara Dan murde murde "Nabila lafiya kuwa?" Anty Salma ta tmby.
Citse lebe tayi ta nuna Mata inda ke Mata ciwo. A dan kwana biyun nan, ta lura ko ba period ba ya kan dan rike Mata. Wani lokaci har kafan yana rikewa.
"Me ke damunta?" Mamman ta bukata.
"Cramps ne" Anty Salma ta amsa. Ita dai Nabila kanta a kasa tana jin nauyin abun.
Mamma ce ta juya tana kallon ta, kaman Wacce ta tuno wani abun "Da kika gama school Mamin ku ta Kai ki asibiti an duba ki?" Mamman ta bukata. Slightly, tayi shaking kanta.
"Ai two days nayi kawai na tafi bauchi"
"Okay" ta amsa sai ta juya wurin Salma. "Gobe kuje Clinic wurin Dr Fatima, zan kirata in Mata bayani za a ma Nabila tests da scanning, tuntuni ma ya kamata ayi. Yanzu hka ma cramp in is not normal kila. Ki dai bata Habbatus sauda ta Sha, da Kuma pain reliver kafin goben" Nodding tayi. Tabbas Sai yanzu ma ya fado Mata, Yakamata ace tunda Nabilan ta dawo daga school a Mata tests in infection. Musamman ita da tayi boarding school, anyi sharing toilet da sauran abubuwa. Ba wai sai an tsaya ya nuna kanshi ba sannan a zo ana wahala. Tunda dai yanzu shi Infection ya riga da ya zama ruwan dare, musamman Yan Mata duk ya musu mugun kamu. Sai kaga duk yabi Yana musu wasa da period. Wata Sai tayi watanni bai zo ko Kuma sai ya tafi ya dawo, ko duk bayan two weeks. Wannan duk sign of infection ne. Amma Sai kaga mutane na ignoring irin abubuwan nan. Wata har discharge za ka duk ya hade Mata, shiyasa mace tana da babban aiki a rayuwa. Dole Sai ta natsu ta San miye matsalan ta. Musamman Yan Mata, akwai wanda har ga Allah ba wai ta sani bane.
A hanyan gida Nabila ke ta faman hade rai. Anty Salman tayi banza da ita, Sai Kuma zuwa can da kanta tace ma Anty Salman "Wai ni test in me za a min a asibiti"
"Urinary Tract Infection" da sauri ta gwalalo idanun ta "Anty Salma nikam banda shi, wai fa cramps ne" tsaki taja "Baki da aikin yi Kuma ai. An gaya Miki kowa yake bayyanawa? Ai abub yanayin jiki jiki ne. Wata Abu kadan zai nuna kanshi Amma wata Sai ya gama cinta sosai tukunna, Sai ya nuna sai kiga har kidney ya taba. Don haka infection ba abun wasa bane, dole Sai ana yi ana duba shi ana treatment. Don in ya ma mutum mugun riko to Sai kiga an zo an samu babban matsala. Har fa haihuwa hanawa yake" rufe bakin ta tayi tana jinjina abun, da alamun abun ya girgiza ta sosai jin haka.
"In Kuma Baki son ki samu yara ne Sai in sani"
Da sauri tace "Kai! kowa na fa son yara"
"Yauwa to gara da kika San haka tunda wuri."
Anty Salma barin ta tayi Sai ta gama period suje asibitin. Saboda Dr Fatima ta sanar mata har swab test za a Mata.
Washegari kaman ranar da safe Sadeeq ya zo school in nasu. Tana shiga motan ya ja ya fita daga layin "In nayi latti fa?"
"I just want to see you for some few minutes" da Kai ta amsa shi. Bai yi nisa da location in makarantar ba yayi parking. Ya bude ya fito, sannan ya zagayo ya bude mata ita ma ta fito in. Bayan seat ya bude mata bismillah, ai kuwa ta fito ta shiga. Ya kuwa zagaya ta dayan side in. Ba ta gane manufan yin hakan ba, Sai da taji ya jawo ya hade ta da jikin shi. Wato nan zai fi samun comfort kenan ba Kaman gaban ba. Lamo kuwa tayi a jikin nashi, tana jin yanda tayi missing moments insu a tare.
"Nayi kewan ki" ya mata whispering a kunne. "Beauty" ya fada yana shafo gefen fuskan ta, wasu gashi ne kadan sosai a kwance a wurin, ya lura yana kuma Kara Mata kyau.
"Don't you miss me?" Ya tmby.
"I miss you mana"
"Sosai?" Ya bukata. Tayi nodding kanta "Sosai"
"Then show me" tsayawa tayi tana kallon sa, kaman wata mage take kokarin Kara shigewa jikin shi, shi kuwa dadin hakan ya ke ji. An samu abinda ake so.
"How?" Ta fada kasa kasa.
"Dago kanki in fada Miki" dago kanta tayi tana kallon shi, duk da bata yarda sun hada ido ba "kiss me here" ya fada yana nuna gefen kumatun shi. Kaman Wacce ta tuno wani abun Kuma sai tayi saurin mikewa ta bar jikin nashi.
"Lafiya?" Ya ambata yana kallon ta. Girgiza kan ta tayi kawai tayi. Maganan su da Zainab ne ya fado kwakwalwar ta, duk tana son fada mishi ba kyau ya daina taba ta. Sai Kuma zuciyan ta ke kokarin hana ta haka, ji take kaman zai dauke ta bakauyiya in ta fadi hakan. Da kanshi ya sanar Mata zai koyar da ita duk abinda yake bukata kenan wannan na ciki? A nan Kuma taji wani abu na gaya Mata, miye ma inya taba ta? Ai ba ganewa za ayi ba tunda dai ba wani abun zai mata ba. Ita kanta ba zata yarda da wani abu da zai zarce wannan ba. It just romance, kuma tana karantawa a books in da yake bata. That means irin rayuwan da yake son yayi da matar shi kenan? In dai haka ne she is ready to scarifice for him.
"Oya time na wuce fa" taji ya fada. Sai ta dan kalle shi, ta sunkuyar da kanta. "Shikenan tunda ni zaki ma rowa" ya fada yana kokarin bude kofa, da sauri ta rike hannun shi ya juyo yana kallon ta. Idanun shi dauke da wasu irin shauki, ji yake kaman zai yi hauka a wurin. Don hka still yayi yana kallon ta, runtse idanuwan ta tayi ta dan daga jikin ta, a hankali ta kai bakin ta kan face in nashi. Wani irin peck ta Kai mishi da sauri ta dauke bakin. Murmushi yayi don ta bashi dariya. Dayan cheeks in ya turo shima ta mishi. Zata janye jikin ta ya rike ta sosai. A hankali ya ke Kai hancin shi kan wuyan ta, yana shakan kamshin turaren da tasa, yana jin kanshi ysna Kara birkicewa. Ita kuwa nan jikin ta ya dau rawa, tana jin wani abu na Mata yawa. Ka sa tsaya still tayi tana wani mimike jikin ta. Ga numfashin shi da ke sauka kan wuyan nata Yana Kara birkita ta.
Hakan wani dama ta Kara mishi, nan da nan kuwa ya Kai lips in shi wuri ya fara pecking inta a wurin. Sai wani murmurde wa take, tana jin kaman jikin ta zai bude, she is feeling the effect sosai kaman ta kurma ihu.
Sosai ya hau kissing wuyan yana kara jawo ta jikin shi, yana having feelings in da yake bukata wanda ke Kara rikita rayuwan shi. Dayan side in wuyan ya Kara komawa yana bashi irin effect in da yasa a daya gefen ta. Sannan ya zaunan da ita a jikin shi yana facing bayan ta. Hannu yasa Yana wasa da bayan wuyan ta, tana jin kaman ta kurma ihu. Sai wani faman nishi take tayi, Sai dai me tana jin bakin shi a wuri, zabagen rudewan girgizan da tayi tayi saurin janye jikin ta. Fisgota yayi, ya Kara maida lips in shi bayan neck in nata, yana wani tsotsa kaman zai lashe naman wurin.
Ai bata San Sanda bakin ta ke furta "Wayyo Mami na wayyo, Dan Allah Sadeeq ka kyale ni" dariya yayi, Sai da yaji he is satisfied tukunna ya sake ta.
Da sauri ta gudu jikin kofa, ta jiginar da kanta tana facing kofan. "Nabila" ya Kira sunan ta bata amsa ba. Sai da ya Kara Kira tukunna tace "Ehmm" duk da haka kin dakowa tayi.
"What's the problem?"
A hankali tace "babu"
"To daga naga fuskan ki mana" da kyar ta iya dagowan. Tana kallon shi ya sakan mata wani shegen murmushin, dake saman ma kanshi mugun matsayi a cikin zuciyan ta. Jikin ta duk ya sanyi, don haka ta Kara jnginar da kanta jikin kujera, tana kallon shi kasa kasa.
"How did you like my morning gift?" Shiru tayi ta kasa bashi amsa. Shi kuwa har wani lumshe idanu yayi yace "Such a blissful morning" ba dai tace komai ba. Ya Kara ce Mata "Did i hurt you?" Sau daya ta juya kanta.
"Okay do you like what i did to your body?" Nan Kam kasa amsawa tayi, Sai ma lumshe idanu da ta sake yi. Ya gane har yanzun jikin ta bai gama farfado daga emotions in da yake feeling bane. Don haka kawai sai ya tsaya yana kallon ta, kaman yanda ya Saba, ya shafo idanun ta. Sosai ya ke kallon ta sannan ya ja hancin ta "Beauty in Sadeeq, ina sonki" duk halin da take ciki, dole Sai da fuskan ta ya nuna jin dadin abinda ya fada. Irin murmushin leben nan tayi.
"You are pretty Nabila" ya Kara maimatawa.
"Kaima ai you are handsome sosai" ta fada.
Sai da yayi wani irin Smiling, don shi daman Yana mugun son ace mishi yana da kyau. Ji yake kanshi na wani dakuwa na daban.
"Allah beauty na" da Kai ta amsa shi. Yace "Shikenan beautyn handsome" da sauri ta dago tana kallon shi "Sunan yayi dadi" kamo hannun ta yayi ya fara wasa dasu kaman yanda ya Saba "Allah Beautyn Handsome?" Ya bukata. Ta ko wani lumshe idanu ta bude zu "Allah Handsome" yayi dariya. "Aa su Nabila irin an samu pet name in Kiran saurayi dashi kenan" murmushi tayi cike da kunya, daman ta San shi da dan banzan tsokana tun tana School.
"Yasmeen na gaishe ki"
"Ina amsawa, ita ma kace Ina gaishe ta" ta amsa.
"Toh Shknn zan fada. Yanzu muje na maida ko?" Da kai ta amsa, ta bude kofa ta dawo gaba. Shima ya koma. Hannun nata ya kara rikowa, ta juye tana kallon shi "Yaushe zamu fita?" Dan shiru tayi tana tunani can tace "Anty Salma fa baza ta barni in fita da Kai ba"
"Eh nasani, tell her Zaki gidan kawar ki man. Sai kice Mata zanje dauko ki" shiru tayi can tace "Okay"
A/N: Hope you're all fine? Yeah we are making progress, thank you.
Slm, Ina masu tambayan complete littafin zuciya da gwanin ta? Ga dama fa ta samu. Domin kuwa na kammala daura littafin akan mahanjar Arewabooks. Zaku iya shiga ta application ko kuma web page insu.
Cikin sauki, danna link kai tsaye https://arewabooks.com/book?id=62a1aeddeb4181893a4e8eac
Ayi maza a garzaya domin ganin yanda Zuciya da gwanin nata zasu tasiri.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top