19
Yau Nabila tunda ta fara shiga class in farko da zata yi take jinta wani iri. Ta danganta hakan da period inta da take expecting zai zo a cikin wannan ranar. Shiyasa kawai sukuku ta ke jinta, ba wani sosai ta ke iya daurewa tana participating akan practical in da suke ranar ba. Sai Farida ne ma ke dan taimaka mata, dake su uku ne group daya. Ko Sadeeq ranar ba sosai take iya mishi reply ba. Duba SMS in shi take yi Wanda yake gaya Mata ya kamata yau su hadu, he needs to see her.
Rasa abin ce mishi tayi saboda na farko dai tana tunanin taya zata gaya ma Anty Salma zata fita da Sadeeq. Sannan tasan dole zata sa musu ayan tambaya in ya cika yawan zuwa. Duk ba wannan bama, yau ji yanda take jin kanta ba ta jin tana da energy in da za ta iya haduwa da Sadeeq in. Tasan in dai suka hadu, to tilas Sai ya Mata wani abun da zai yi triggering emotions inta.
"Am not feeling good, I need to rest"
Yana gani sai ga Kiran shi ya shigo, lokacin za su shiga class in makeup kenan don haka bata tsaya picking call in ba. Ta dai tura mishi SMS.
"Bara na fito class, we will talk" daganan ba ta tsaya duba ko yayi mata reply ba kawai ta shiga class in.
Har aka fito aka tashi bata jin dadin jikin ta, Baki daya ranta a jagule take jinta. Har ta shiga gida. Anty Salma na ganin ta tasan ba ta jin dadi saboda ba haka take ba, she is always lively.
"Lafiya Nabila?" Anty Salman ta bukata. Dan yamutsa fuska tayi tace "Anty Salma ban jin dadi ne"
"To fa me ke miki ciwo?" Kara hade ranta tayi, saboda itan ma ba zata ce gashi ba "Kawai raina ne dai bai min dadi"
Kallon ta Anty Salman tayi tana karantar yanayin ta. Ta gane inda aka dosa don haka tace "Sai kije ki yita karatun qur'ani ai, bara in gama da Baban Areef zan zo in same ki" da Kai ta amsa sannan ta wuce. Wanka ta fara yi sannan ta kwanta, ji take zuciyan ta na tashi amma ko kadan ba ta jin yunwa Sai dan banza kwadayi.
Haka taje fridge ta samu su cake, ice cream duk dai kayan sanyi tazo ta baza tana sha ga AC da ta kuri abun ta. Ko da Sadeeq in ya Kira ta kin dauka tayi. Sai Sms in da ta tura mishi akan ba zata iya magana ba. Shi kam har ya rude, ya dauka wani gagarumin ciwo ne ya kwantar da ita. Har ya sanar mata zai zo, tace Aa zuciyan tane kawai ba dadi ba wai wani ciwo bane.
Haka su cigaba da chatting, da alamun kuwa ya taimaka ma zuciyan nata tare da kayan sanyi da ta debo wurin jin sanyi a ranta. Suna cikin magana taji alamun period in yazo da rushing in shi. Dole ta ajiye abinda take yi, taje toilet ta gyara kanta sannan ta dawo suka cigaba da maganan.
A haka Anty Salma ta shigo ta same ta, kasa karasawa cikin dakin tayi Sai da ta kashe AC in sannan ta samu wuri ta zauna. "Kai Anty Salma kinsan yanda Ac in nan ya taimaka min" turo baki tayi.
Dakuwa Anty Salman ta Mata "Kaniyan ki Nabila, lafiyan ki da ranar Allah zaki sa irin wannan sanyi, Kuma miye wannan kike Sha haka?"
"Kai Anty Salma kin fa sanni da son Sanyi ni daman" gyara zama Anty Salman tayi "Ai kuwa lokaci yayi da zaki daina shi?"
"Meyesa to Anty Salma?" Ta fada sounding so curious. Anty Salman taji dadin samun attention inta, don haka ta cigaba "You are on your period?" Da kai Nabilan ta amsa.
"To sanyi da kayan sanyi duk ba naki bane Nabila. Baki San sanyi Yana da illa sosai ga mace ba? Musamman lokacin period" shiru tayi kawai tana sauraron Anty Salman lokacin da ta cigaba da cewa "Nasan Kuma baki ci abinci ba ko?" Nodding kanta tayi.
"To Kar ki sake yarda ki zauna da yunwa daga yau during your period" dan tabe fuska tayi, tace "Anty Salma zuciya na ke tashi wlh, ko marmarin abincin ban yi"
"Zuciyan ki na tashi Sai aka ce Miki kayan sanyin nan ne zai miki magani?" Still tayi kawai tana kallon Anty Salman "Ba fruit ne a gidan nan?"
"Akwai" ta amsa a hankali.
"To bama abinda ya Kai fruit yaye ciwon zuciyan. Ke kinsan ban ajiye kayan nan a gidana, ke dai ke siyo abinki. Kuma basu da wani health benefit a jikin ki. Bance Kar ki Sha ba, but dole kiyi limiting ta'ammali dasu sosai, don banda illa ba abinda yake jawo wa jikin ki. Ke hatta menstrual cramp in nan da kike yi harda karin abubuwan zakin da kike Sha Nabila, bayan haka bata miki jiki zai yi ke hatta Ni'iman da ke jikin ki Sai yayi affecting" dago tayi da sauri tana kallon ta, Sai kuma ta dukar da kanta.
"Eh abinda nake nufi kenan" Anty Salman ta fada ganin yanayin Nabila "ki ajiye kunyan banzan nan ki saurare ni da kyau. Ko kina so kije gidan Sadeeq in naki bai samun gamsuwa da ke ne?" Saki baki tayi tana kallon ta, Sai kuma ta rufe fuskanta ita ala dole taji kunyan zancen "Kai Anty Salma Mana"
"Nabila am serious, tun yanzu ya zaman Miki dole ki San me kike, ki gyara kanki. In ba haka ba kuwa, za ki zo kiyi aure ne abun yazo Yana affecting inki sosai"
"Wai Anty Salma kaman ya?"
"Kaman yanda nake fada miki, in Kuma so kike in miki baro baro to zanyi. Kinga Fruit in nan da kike gani kina rainawa, all these ganyan yaki da kike gani a zube a banza to ba karamin amfani ke gare su. Ga jikin ki, lafiyan ki da Kuma Ni'iman da ke jikin ki a matsayin ki na ya mace. Tun yanzu ya kamata kisan amfanin su, da mahimmanci don haka zan baki Assignment duk wani fruit da vegetable da kika san muna amfani dashi a nan kasan kije kiyi goggling health benefits insu a yau ba Sai gobe ba. All these Garlic, Ginger da kananfari abubuwa ne da dole ya zamanto yana ciki abinda ke shiga cikin ki a kullum. Spices in da kike gani, basu Maggi ba all these curry da sauran abubuwan da kike ganin ana nuko su daga ganye da itatuwa shima dole ki rike shi. In Zaki lura a gida Mamma da olive oil ake Mata abinci, ko coconut oil. Don haka ba wai abubuwa bane kawai da ake amfani dasu in kana neman magani. Aa an Mana sune saboda suna da natural medicine in a jikin su. Amma mu Kuma Sai muka gwammace mu dinga sakawa jikin mu ko cikin mu abubuwan da ake hadawa da chemicals. Kuma shi ke kashe mu, bayan kwana biyu kiji ance ciwon nan ciwon can ko Kuma kiji ma nace cancer, Allah ya kiyaye. Amma in kika rike all these natural abubuwa, to wlh ke kanki Sai kinji canji a jikin ki, all these cramps in da kike fama dashi sai ga ragun Miki sosai. Sannan ke kanki Sai kinsan now you are okay, yanayin ki Sai ya fi Miki dadi. Sannan haka in kinyi aure, in ka rike natural abubuwan nan to In Sha Allah hatta mijin ki Sai ya San ya auri mace. All these abubuwan maganin Mata ba abinda ya Kai fruit, da sauran natural herbs in nan miki maganin Mata. Duk Ni'iman da kike nema akwai cikin shi." Murmushi tayi sosai "Nabila, wani abun dole Sai kinzo aure zan fada Miki. Amma kafin nan, yanzu ya kamata ace kin Fara gyara kanki. Banda zama cikin sanyi, ita mace a kullum so ake a same ta cikin dimi, jikin mace daman da dimi aka San shi. Rufe kafa musamman in Zaki fita, ki guji rashin yawa da takalmi a cikin gida, kina taka tiles haka nan Sai sanyi ya dinga shiga jikin ki, ya jawo Miki wata cutar azo ana wahalan magani. Kinga lalle na gargajiya, za kiyi mamakin yanda nake yawan sawa a na min shi. Maybe za ki dauka dan kwalliya ne amma ba hakan bane Nabila, wani abun don magani ake yin shi, duk da kwalliyan ma yana sawa ayi Kinga benefit biyu kenan. Kinga su Hulba, da habbatus sauda. Duk zan baki oil insu, ki dinga Shan hulban cikin abu mai dumi shi Kuma Habba da Zaitun in ki idar da Sallan Asuba, kina Shan su ko ba kullum ba. Wlh Zaki ji canji a jikin ki, banda magani ma zai zamo Miki kaman wani tsari ne a jikin ki. Hatta shaidanun aljanu da sauran su ba zasu kusanci inda kike ba. Haka Zuma, shima yana da nashi amfanin. Abinda Kuma nake so in gaya miki, shi wannan fruit in ba dole wai hakanan Zaki Sha shi, akwai nau'oin da Zaki sarrafa su kala kala. Akwai komai fa a goggle, YouTube da sita kala kala da Zaki ga irin wa'inanna abubuwan. Ko ni ai kinsan aikina kenan, blogging in nan da Zaki ga ina yi wlh Nabila duk a kansu ne. You can check everything online, ki Kuma yi amfani dashi. A maimakon time da kike batawa a social media kina wani abun. Do something that will help you in life. Ki bar ganin wai saurayin ki na son ki kaman ya cinye ki, wlh in aka yi aure Nabila. Ba wai nace soyayyan zai bace bane, Amma Kuma ba tashi ake ba, hakanan za a ajiye shi a gefe a fuskanci rayuwa. A lokacin Zaki San true colors in mutum, ki karance shi tsaf. Don haka wannan abubuwan da na lissafo Miki in har kina applying in shi to Sai kinji dadin rayuwan auren ki, mijin ki ya zamo ko yaushe so yake ya kasance dake ba wai yana gudun ki ba. Saboda kina gamsar dashi, Yana Kuma samun abinda yake bukata daga gare ki. Ba wai yana neman ki yaji abu Salam ba, to wlh mugun matsala Zaki samu dashi in aka yi haka Nabila. Ba wai sex bane bakidaya rayuwan aure, Amma yana daga cikin jigon da yake tafiyan da auren. Wani Namijin Zaki ga bajin dadin zama da matar shi yake ba, kila ba sonta yake ba. Tana bashi matsala sosai amma saboda ta iya gyara kanta, yana samun gamsuwa a gado Sai kiga ya kasa rabuwa da ita. Sai ma wani mutunci da kima da take karawa a idanun shi." Shiru tayi tana ganin yanda Nabilan ke wani nokewa tace "ki gama noke noken ki ni dai fatana abinda nake fada Miki kawai ya shiga kanki. Ballantana Yan matan yanzu nasan ba abinda Baki sani ba, musamman ke da kika yi makarantar kwana. Ga ki da saurayi dan gayu, dan masu kudi to dole ki tsage damtse kisan me kike yi. Kuma tun yanzu ya kamata ki Fara nuna mishi mahimmanci natural abubuwan nan a maimakon su chocolate da sauran kayan zakin da yake siya Miki. Sai ma kunfi saving kudin ku, in Zaki Sha ya kasance ba ko yaushe ba. Sauran abubuwan in ansa ranar auren ki lectures ne zamu yi na musamman. In ba haka ba da babban matsala Nabila. Yanzu Sai Kuma maganan underwears inki, nasan halin ki Baki da kanzan ta. Amma duk da haka bai baci ba, I will tell you ki dinga zaman towa kina gyara su sosai, banda zama da pant jikake saboda kinsan microbes suna zama a wurin. Musamman fungi da ke son wuri Mai damshi. Ko a wani wuri ne ki zamo kina yawa da tissue inki ko wani karamin towel, in Zaki shiga toilet shiga dashi. In kinyi tsarki, ki goge wurin ya zamo ba wani damshi sannan ki mayar da pant inki, you are saving yourself from infection ne. Sannan duk bayan wani Dan lokaci, ki canja baki daya panties in ki to prevent further complications Nabila. Mafi yawancin abinda ke damun yan matan mu kiwuya ne da son jiki. To duk dole ki ajiye wannan ki fahimci reality, rayuwan mu kenan mu Mata so dole muyi taka tsan tsan. Sai magana shaving, kar ki saban ma kanki zama da gashi a jikin ki koda wasa. Duk Friday, you shave sannan ki dinga shafa Olive oil a wurin, in Sha Ko wani matsalan kaikayi it can help sosai. Ban San ko da Shaving stick kike amfani ba, Amma gsky mutane dayawa sun fi preferring in shi akan Creams, though wasu na jin dadin amfani da cream in. Matsalan wasu na da sensitive skin, so Zaki ga akwai irritation da sauran su. Abinda ya kamata kiyi know your skin, wane yafi Miki aiki. Akwai creams in da suna da kyau sosai, you can try them kiga in ya amshi skin inki. In Kuma kinfi preferring shaver to Shknn. Kar dai ki dinga zama da gashi kawai, kazanta ne ma. Sai ki dinga yawan zufa, a gaban ki Kuma kika yana jawo Miki kaikayi da bushewan gaba. Wlh ba zama kiji dadin jikin naki ba kwata kwata. Sannan abinda yan matan mu ya kamata su gane shine, ba wai sai kinyi aure bane Zaki Fara all these abubuwan, lokacin Zaki gyara kanki. Aa, ba haka bane. To mafiyawan ci abinda suke gani kenan, Kuma suke aikata wa. Hakan babban kuskure ne wlh, wannan aikin iyaye ne su Yakamata su yi guiding mutum. Amma in ba suyi ba, to su matan yanzu Kai a waye yake, ansan komai zamani ya bude Mana Ido dayawa. So Kai da kanka ka zauna ka ma kanka fada, icce tun yana danye a ke tankwara shi. To dole abu Sai kasa shi ya shiga jikin ka sannan za ka iya aika dashi. Don haka dole Sai kin tashi tsaye kin taimaki kanki daga yau Kuma nake so ki Fara kina jina?"
Da Kai ta amsa Mata Sai kuma tace "Nagane Anty Salma In Sha Allahu zanyi"
"Yauwa Ina so in gani a aikace tun daga yanzu. Don haka ki tashi ki neman ma kanki abincin anjima da dare kuma zamu je gida"
Zaro idanun ta, tayi a tsorace "Anty Salma Mamma ta dawo ne?"
Dariya Anty Salman tayi "Ta dawo Mana, Alhaji ne yace a barki ki yi hutu"
"Tare zamu dawo?" Nodding Kai Anty Salman tayi, da sauri ta tashi ta wani rungume ta "Thank you Anty Salma, nagode kinji" dariya tayi, tace ki dai gama muje yanzu.
Ai nan da nan ta hau shiri, bayan taci abincin da ya Sha hadin salads. Sai ci take tana kokarin karawa "forget to tell you, in mace na Period ba a son tayi over feeding. Ke ko yaushe ma overfeeding bai da amfani don haka kici dai dai cikin ki. Drink much water sosai, natural drinks duk kina bukatan su"
"Anty Salma cin abincin ma Sai a hana mutum Dan Allah?"
Girgiza Kai Anty Salman tayi "Bara Zan turo Miki wani wa'azozin Malama juwairiyya, ki sauraro maybe Zaki fi fahimatan me nake nufi"
Ba tace komai ba, ta shirya su ka tafi. A hanya take tura ma Sadeeq ta warware.
Ya ko ji dadi sosai, ya sanar Mata gobe dole ya ganta kawai.
A/N: Oh yeah! This is a promise and i fulfil 😀
Abubuwan da suke kunshe a chaptern nan na dangane da mata da hanyoyin gyaran su is not only for Nabila please. Nasan ba dai na fada muku ba, but this can serve as a remainder. The truth is that tunda Allah ya halicce mu a mata, to fa sai da kikayewa. Rayuwar mu kenan, kuma dole sai mun tashi tsaye. Allah ya bada ikon amfani dashi.
Nagode.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top