18
"Heart" ta Kira cikin wani irin raunanniyar murya. Dagowa yayi yana kallon ta, bakin shi Kam ya rasa Mai zai ce Mata Kuma. Shekara Shidda ai ba wasa ba. Tun yana secondary, bai gama sanin kanshi ba suka hadu da Layusa. Daga zuwa gidan wani friend in shi a Abuja ya ganta, sun zo bikine lokacin suka sauka gidan su Abokin nashi dasu ke da dangantaka.
Ba wani magana suka yi ba rana, illa dai wani series da ya iske su, suna kallo. He loves the series, so Sai ya zauna har aka gama Episode in da suke kallo. Daganan aka hau hiran film in. Ita Kuma dake tasan film in sosai, tare suka yi dan labarin. Ya tashi ya tafi. Sai ma bayan kusan wata biyu yana scrolling a IG ya ganta. Bai wai gane ita ince ba, ta dai yi looking familiar. Bai Mata magana va a lokacin Sai daga baya bayan ya gama ganin irin poems in da take rubutawa. Har da videos, he likes them sosai. Don har comment watarana ya kan mata.
Sai ranar tasa abu a status inta akan love and it darkness.
"Who is the guy? We will love to know him" ya Mata replying.
Fuskan dariya ta tura mishi. Ta sa "No one but if there is, I will love to know him also"
"How can you write to Nobody then? All these messages, it weightness all for nothing. Girl you are kidding me, i swear"
Dariya tayi tayi, daga ranar duk randa tasa love poem Sai ya tura mata "Even this one? 🙄" Ko Kuma "i still can't believe you" dariya take, har tana posting a status inta. "Please help me tell this guy am not dating anyone, he find that hard to believe."
Shima Sai ya tura Mata fuskan dariya. Sai ranar da ya tmbyn ta to meyesa take posting love poems, when she is not in love. As in what motivate ba.
"They are just thoughts and imaginations" tayi replying,
"Then i wish your imaginations came true oneday" da sauri ta tura mai Ameen and thanks. Daga lokacin haka su cigaba da dan gaisawa. Sai ranar da tasa pic ubta a status, Rana ya Kara tabbatarwa akwai inda ya santa. Don haka ya tura Mata "Do you know you look familiar, like I know you somewhere"
Dariya tayi tace "Okay oh, maybe in your thoughts"
"Girl, am serious"
"Then post my pic in your status, maybe some of your buddies can help you remember" ita tsokanan shi take. Shi kuwa posting in yayi. Friend in nashi na ganin shi ya Kira ya fada Mai. "No wonder" yace, don yasan dole akwai inda ya santa.
Mssg ya tura mata asking ko tasan wane wane, sunan friend in kenan. Tana mishi reply ta San shi. Yace okay can you remember so so guy, da kuka yi hiran so so series dashi a Unguwa kaza a Abuja.
Da sauri tace "You are the guy? I thought you weren't serious fa"
"Now you know"
Shikenan daganan suka Fara chatting, ba ma a IG kadai ba har Twitter da Snapchat Sai da suka zama friends. A hankali suka saba sosai, har suka yi exchanging contact suna chatting tanan. Suka dawo kullum Sai sunyi chatting, musamman a series in da suke da interest. Abinda ya Kara keeping friendship in nasu Kuma, she is a poet shi Kuma yana painting. Don tun kafin ya fara University ma, ya fara paintings. A zama da yake shi kadai a gida, he comes to love art sosai. Don ko Nabila ya taba bata one of zanen shi during one of her birthday. Ita ya zana tana boye fuska, lokacin tana jin kunyan. Sai kuma Wanda take ma Anty Salma shagwaba.
She loves that paintings duk tasan tsokanan ta yayi, har yanzu tana nan ajiye dasu a Kaduna.
Abinda yayi keeping alakan shi da Layusa. Yawancin in kowa yayi piece of art in shi, they motivate each other sosai. Har yazo in yayi painting inshi ya tura Mata, Sai ya zamo kaman inspiration ne a gare ta. Na irin poem in da zata rubuta. He paints and she get a poem for it ko Kuma the other way round. Sai ya dawo kaman suna aiki a tare ne. Saboda ko a net suna posting abubuwan juna. Duk fans insu sun sansu as friends. A haka har suka Fara waya, ba irin hiran da basu yi. Daga waya Sai ya gangara Vidoe call. Watarana har 3 hours suke suna magana. Things became even more than friendship, kowa ya gane hakan Amma ba Wanda ya fito ya bayyana ma dan uwanshi. But they felt the tension between them.
Lokacin ya tafi First degree in shi a Cyprus ita Kuma ta tafi Medicine a Sudan. They became so acquainted sosai, har yana tsokanan ta "Saura ayi sabbin guys a Sudan a manta Dani" dariya kawai tayi tace "Wa ma ya sani am about to meet my Mijin aure"
Rudewan shi bai boyu daga gare ta lokacin da yake fadin "Are you planning on getting married anytime soon?"
"Duk lokacin da auren yazo" kawai tace.
Sai bayan an hau an sauko tukunna da kyar ya iya confessing. Bayan wani abokin shi yayi encouraging inshi. Luckily, Yana sanar mata bata tsaya boye boye ba ta bayyana masa itama tana da ra'ayin hakan.
Cikin kankanin lokaci suka gini soyayyan su Mai tsafta. Tare Kuma da planning komai na rayuwan su. The actual plan is lokacin da suka Kai 25 years za suyi auren. Saboda a tunanin shi zuwa wannan lokacin ya riga da yayi settling.
Sai dai rayuwa kana naka ne Allah na nashi. Domin dai da Alama kudurin da suka daukan ma kansu na gaf da rushe warwas a kasan su. Duk da haka baya jin zai iya bari hakan ya faru. Gabadaya kwakwalwar shi ta gama juya, ya girgiza fiye da tunanin mai tunanin ma. Yana jin kawai dole su samu mafita ma kansu, in ba hka ba akwai matsala. Irin matsalan da yake ganin ba ta da karshe kuwa.
"Ya kuka yi dashi?" Ya tambaye ta a kasalance. Don dai ko maganan shi ma bai son yi, ya riga da ya gama kona mishi zuciya baki daya "We talk, he want to help gsky. Ya dai cemin ba zai iya tunkarar mahaifin shi da maganar bane. Irin wadanda magana daya su keyi..."
"Saboda ba rayuwan shi bane?" Wani irin ihu da yayi Sai da ta firgita. Sai faman huci yake tayi, yanayin shi ya tsorata ta, ba zata ce ta taba ganin masoyin nata a haka iya shekara Shiddan da suka yi suna tare.
"Eh? Saboda his life is not involve ko? Meyesa mutane are so selfish ne wai? Meyesa ba zai je yayi building relationship inshi ba yake kokarin tarwatsa na wasu? This is not fair Kuma bazan dauka ba. Komai zai faru Sai dai ya faru..."
"Bilal!" Ta Kira da karfi, dole yasa shi dagowa kallon ta. This is unusual, ya manta rabon da yaji bakin ta ya kira sunan shi.
"Ka tsaya ka saurare ni in gama magana mana. Zuwa yanzu yaci ace ka fahimci cewa rage, anger ko makammancin su ba zai kawo Mana mafita ba" a hankali tayi magana, muryan ta tattare da nauyi mara misaltuwa. Is like Energy inta ya fara kasa akan rigiman nan.
"Love you are giving up?" Ya fada cikin wani irin mawuyacin Hali. Girgiza kanta tayi a hankali "Ko daya Heart, so nake mu bi komai a Sannu. Tunda mun gwada tashin hankalin bai yi working ba. Munyi magana da shi, kaman yanda na gaya mka yace ba zai iya maganan nan da mahaifin shi ba. Amma ya samu mahaifiyar shi, they talk duk da ita ma bata ji dadin zancen ba. Tace she will try ayi wa baban magana. Amma fa in har ma Abbah bane ya janye, to suma ba zasu ce sun fasa ba"
Share wani mugun zufa da ya keto masa yayi. "Ba wani abu mara dadi a wannan labarin. Shin wai love ni meyesa iyayin masu fahimci bane wai?" Da karfi yake magana yana juya kai. Can Kuma ya fara sa hannu shi da karfi yana dukkan kan nashi "Why! Why! Why!"
"Bilal please" ta fada cikin kuka. Yanzu Kam wani sabon kuka ta fashe dashi, abinda tayi ikirarin ta kasa yi baki daya ranar. Sai dai yanzu situation in da Bilal in ke neman sa kanshi ya fi karfin iyawar ta ko Kuma tunanin ta. Gashi tunda aka fara zancen ba wani fahimtar ta yake tsayawa yi ba, balle su yi maganan mafita kaman yanda da suke warware matsalolin su a baya. Tabbas suna da obstacles insu a shekarun da suka deba suna soyayya. Amma har friends inta da nashi mamakin irin nasu soyayyan suke, like tunda suka Fara relationship haduwan su bai Kai sau goma ba ma. Haduwan ma yawanci a Sudan ne lokacin da yake school, in ya dan samu sarari Sai dai Kawai taji shi yazo kusan sau bakwai ya mata haka. Sauran haduwan ne aka yi shi a Abuja, lokacin tazo yin wani abu, shi Kuma yana gari.
Sun gina relationship insu ne cikin gsky da Amana. Da ke shi mutum ne mai tsari da Kuma bin ka'ida domin samun abinda ya dace. To ko soyyayan shi ma hakan ya kasance, shiyasa koman shi ke tafiyan Mai yanda ya kamata. Ko ba don Soyyaya ba, akwai mugun shakuwan da ke tsakanin su da suke jin shi kadai ya isa ya gina musu rayuwan aure Mai kyau. To balle ma suna son junan nasu kaman suyi ya. Sannan wani abun alfaharin nasu shine, soyayyan su is productive. Domin suna taimakon juna ta kowani fanni na rayuwa. Duk success in daya to dole akwai sa hannun dayan a ciki.
Bilal ya riga ya gama tsara rayuwan auren shi zai kasance a yanzu haka. Everything is sort out. Sai dai Kuma ya San in har ba Layusa, hakan ba zai yiwu ba.
"Ki daina kuka Mana" ya fada yana huci sosai.
"Ba ka so in daina in ba" ta amsa still cikin sheshekan kukan take. Ga wasu hawayen ma da ke kokarin Kara ambaliya a fuskan ta.
"Bazan sake ba yi hakuri kinji" shima muryan nashi rawa yake, don yana daf da sakin nashi kukan. Yana jin abinda take ji, haka kuma yana jin kaman ya juya yaga abun mugun mafarki ne kawai ba zahiri ba. Da ko yana jin ba zai Kara yin baccin ba ma a rayuwan shi, balle ya Kai shi ga yin irin wannan mummunar mafarkin.
"God! I just wish all these things will end now" ya fada Yana jin wani zafi na karuwan mishi cikin ranshi. Hakurin dai ya cigaba da bata har saida ya samu ta tsagaita kukan.
"Zan zo Nigeria kwanan nan In Sha Allah. Kafin nan kema kiyi kokari samo Mana solution, in nazo Sai mu cigaba. Nima i will try my best, zan Kira Sisturh, inji shawaran da zata bani Kuma"
"Aikin fa?" Ta ambata tana kallon idanuwan shi.
"Sai da kwanciyar hankali ake. Ni duk wanda ya ban aiki ma na mayar mishi kayan shi. I can't work in this situation by Love, banda karfi ko Energy in yin aikin Wlh. Ke bama aiki ba, cin Abinci, tafiya, bacci ke hatta kallon abu ba Energy in yin shi nake a kwanakin nan ba. In Kinga na samu kwarin guiwan yin abun, to tabbas Yana da dangantaka da cimma burin mu ni kawai"
Dan marairaice murya tayi, yanda ta tabbatar abinda ta fadan zai shige shi "Ehm Ehm Heart Dan Allah Kar muyi haka da Kai Mana. You don't have to play with your health da Kuma aikin ka. Abubuwa biyun nan suna da matukar mahimmanci a gare ka da ni inma bakidaya. Kar ka manta in kace za kiyi wasa da lafiyan, zaka saka kanka a wata irin rayuwa ne Wanda zai zo maka a baibai domin baka Saba da ita ba. Zaka rasa duk wani tunanina naka, Kai hatta maganan da muke da Kai yanzu zai zamo ba mu da daman yin ta. Aiki kuwa heart, kayi tashe da sunan da bai kamata ka tsaye wasa dashi ba. Kai da kanka kake gaya min abun akwai competition sosai, amma dake nakan ya na basu abinda suke so, wannan bai baka matsala. To gaka kuskuren ka kadan kaman dama kake kokarin ba ma wani ya fito ya zamo dakushewar ka, duk da dai kowa rabon sa zai ci. But don't settle for the average, always look for the best kaman yanda ka Saba, na tabbatar hakan ne sirrin cigaban ka kaman yanda mutane suka kasa ganewa" shiru yayi yana sauraron ta har ta Kai aya. Hakan na daga cikin dalilin da yake ji cewa bai iya rayuwan ba tare da Layusa ba. A kullum ya karkace kokari take ta dawo dashi kan hanya. Jinjina Mata yayi, nan da nan murmushin da ya dade bai yi ba Sai gashi ya wanzu akan fuskan shi.
"Hakika duk abinda kaga yana faruwa a rayuwan mu bafa dabaran mu bane ko Kuma cigaban mu. Kawai sa wa raina, Allah ke duba zuciyoyin mu yana bamu abinda muke bukata. So Dan Allah Heart stay healthy for your Self, For your Work, For your Family and" tsayawa tayi tana kallon shi, shima kallon nata yake cike da kauna yana jin kaman ya sata ta zama nashi yanzun nan.
"And for meeee" ta karasa tana sakin wani irin murmushi mai hade da dariya.
"Ina Son my love Ina, l love my Soyayya so much" ya fada yana sakin murmushi, duk kuwa da zafin da yake ji a Zuciyan shi. Shiyasa ya bata sandan girma, domin ita kadai ne zata iya sa shi murmushin a cikin wannan mawuyacin halin.
"Ina son My heart Ina, I love my Zuciya so much" ita ma ta fada, idanun ta cike da kwalla Amma still murmushi take. Hakan ya zama kaman sentence insu, da in dai za suyi magana dole ne Sai sun fade shi" A tare suka sake sakin wani murmushin.
"Allah ya bani ke Love" yanda yayi maganan ya sa mata jin wani kwalla na taruwa a idanun ta. Saurin juyawa tayi don Kar ya gani ya karaya, hannu tasa ta goge hawayen. Sannan ta juyo tana cigaba da murmushin.
Tsaf ya gane kukan tayi amma Sai bai ce komai.
"Allah ya bamu juna Heart" ta fada cikin dan muryan da ke rawa "Yaushe zaka zo Nigeria in?"
"Ina samun Visa zan taho da izinin Allah. Har Kadunan zan zo ai, ko shi wancan i have to meet him" tasan Ibrahim yake magana da yace wancan in, saboda Sam ya tsani maganan shi ballantana ma ya Kira sunan shi.
"Allah ya yardan mana, Ka dai Kwantar da hankalin ka dan Allah. In ba haka ba ko su Mamma ba dadin ganin ka zasu ji ba ai. Ko kana so suyi tunanin am not good to you in suka ga duk ka kare?" Girgiza Kai yayi, ta Kara wani murmushin karfin hali.
"Promise me you will be okay"
"I do" ya amsa Mata. "Bara ba Kira Sisturh" da Kai ta amsa mishi "A gaida min da baby Areef pls"
"Zai ji Maman Areef" murmushi ta mai sosai.
"Okay have some sleep love, kema ban son tunani mai yawa. In kinyi kinsan zan gane" da Kai ta amsa mishi ita ma.
A/N: Don't be confuse guys. This id Bilal's love story. I hope you don't forget that bilal is our brother ko? Have some fun as you share your thoughts on this. 😍😍
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top