16
Cikin sadakarwa ta cewa Zee "Nagode zee, I will try inga na kiyaye" tana fadan hakan ne bayan Kuma har a zuciyan ta, tasan cewa ba lallai ta iya ba. Ita dai tasan ba zata fara attempting wani abu ba, amma in har ya Mata. Her body can't deny him. Ji take kaman they belong together tun can daman, everything feel connected.
"Promise ba zaki Kara bari ya taba ki ba" Zainab in ta fada with full hope. Sai da jikin Nabila yayi sanyi, karya ba ya cikin tsarin rayuwan ta. Ba Kuma taso ta ma Zainab Sai dai yanzu ya Kama mata dole. Tana son Zainab, domin ita kadai ce zata iya gaya mata gskynan to herself. Da sauran kawayen tane, they will tell her it happen, ai wayewan kenan. Duk ba lallai ya kasance su in sunayi ba. Amma haka aka dauki abun.
A daya bangaren Kuma Sadeeq mean the world to her, tana son shi irin Soyayya da take jin she is ready to fight the world for him. Ba zata iya rabuwa dashi ba haka Kuma duk abun farin cikin shi kaman wajibin tane.
A hankali ta kalli zee in, lumshe idanuwan ta tayi ta bude. Alamun ta yarda kenan, bata yi amfani da bakin ta bane saboda tana tsoron zai iya fallasa sirrin zuciyan ta. Idanuwan ma kasa tayi dasu, feeling so guilty.
Kafin Magrib zee ta wuce, don haka ta koma ita kadai tana mai cigaba da tunane tunanen ta.
Ranar ba su hadu da Sadeeq ba, Sai doguwan wayan da su kayi. Yana fada Mata how he miss her, she also miss him too. Kuma yanzu freely take fada mishi hakan, bayan so akwai shakuwa. A hankali she is being more free with him. Kaman ya na nuna Mata hanyoyi da zata iya mai sharing kawai da ke ranta ne. Because he tells her everything, ko da doubt ne ke damun shi akan ta. Labarin first day in shi a office ya bata, suka yi ta dan murmushin su.
"Banji dadi ba yau ban ganki ba" ya fada yana dan Hamma.
"Sleepy sleepy you are, Je ka kwanta akwai gobe" wani hamman ya Kara yi
"Lokacin bacci na bai yi ba. Babe, gsky an wahalar miki dani dayawa, dole naji bacci" dan kwantar da kan shi yyi kan pillow in da ke gaban shi. Idanun shi sun kada, da gaske baccin dai ke son tafiyan Mata dashi.
"Mu dau mataki kenan?" Ta ambata, ya gyade Kai "Eh Mana, ban gaji da kallon ki bane. Gobe dole nazo ganin ki kafin na wuce office"
"To wai In na koma gidan Mamma yaza ayi" wani hamman ya sake yi "I will sneak you out mana. Ke in fa ban ganki ba I realize za a samu matsala nema"
Ta lura ya fara fita daga cikin hankalin shi, duk magana daya Sai yayi hamma. Ko kuma ya kulle idon Sai yayi saurin budewa. Ita dai Sai kallon shi take tana dariya. "You better sleep, ni dai i can't decide not to go tunda Mamma bata nan"
"Dole kije na ganki, Sai da safe dear, Ina son ki kinji" wani irin smiling ta saki kaman she is about to cry "To ya zanyi duk da you look horrible when you say this, I still love you like this. Oya go and sleep" da sauri ta kashe wayan, don tasan magana zai sake yi. Tayi ta dariyan ta, ita daya har tayi bacci.
Da sauri ta gama shiryawa, Sai da ta bude wayan ta, ta mishi sending well wishes message sannan ta shiga motan. Tayi mamakin da bai mata reply tunda tasan zai je aiki, so he is awake. Ko bayan nan ma, shi ma bai baccin safe bane. Yawancin abubuwan shi da safe yake yi, ya kance yafi albarka.
Tana sauka daga mota taga an Mata wani haske. Tana juyawa taga motan shi, kallon motan ta Kara yi, ya kuwa tabbatar shi inne. She thought wasa yake yi da yace jiya Sai ya ganta kafin ya tafi office. Hakanan ta lallaba wurin motan nashi, ta bude ta shiga.
"What did you eat for breakfast?" Ya bukata. Kallon cikin ta tayi, ta dan taba shi "Na Sha tea, Sai anjima zan siya snacks a nan inci" ta fada tana nuna mishi wani canteen.
"Zama da yunwa ko Nabila? Kina so ki dinga rama kenan, shiyasa kullum gaki nan kawai ba kya kiba abun ki"
"Kana son kiba ne?" Yanda tayi maganan Sai da ta bashi dariya. "Ni ke nake so ba kiba ko rama ba" Sai lokacin taji relief hadda dan yage hakoran ta.
Juyawa yayi ya Kai hannun shi baya, basket taga ya ciro babba har sai da ta taya shi ya ajiye a tsakanin su. "Kina cin bread ko?" Kallon shi tayi, irin she want to say waye bai cin bread in nan.
Plate ya fiddo, ya ajiye Mata. Sandwich ne kusan guda bakwai yasa a plate in nata. Sai Kuma fried egg da wani toast bread a gefe.
"Wa zai ci wannan?" Da dan tsoro ta fada. Ya tabe baki "Mai magana ko kici ko na saki ci dole" yanda taga he mean it ne yasa taji kawai tana so taga ya zai sa ta dolen, she is in with the fun. Don haka ta make kafada ta juya.
"Okay oh" ya fada yana gyara hannun rigan shi. Rike plate in yayi da matso kusa da ita, da sauri ya riko hannun ta ya sa karfin shi ya juyo da ita suna fuskantan juna. Folding lips inta tayi dan neman magana. Ai kuwa Sai ji tayi ya Kai hannun shi saitin baki yana yawa dashi a hankali, kaman Susan kadangare ya ke Mata a wurin. Sai da ya bari jikin ta ya fara sanyi irin yanda yake so sannan ya tura finger inshi cikin bakin. Ai kuwa ya budu, dayan hannun shi ya dau sandwich in ya tura da karfi. Ba ta da wani solution dole ta Fara tauna, dake abun ya mata dadi. Daganan silently ya dinga bata a Baki kusan biyar taci tace "Am okay please Mana"
"No ki Kara dai" girgiza Kai tayi tana kallon cikinta. "Na koshi wlh, baka ji yanda nake jina ba"
"Kin dai kulle cikin ki kawai" hannun shi ya Kai kan cikin, ya wani shafo. Sai da ta dan daka daga kujeran ta tsabagen yanda taji "Na yarda kin koshi, Sai tea"
"Kadan Amma" kadan in ya zuba mata, shima a baki ya bata. The tea is special, don Sai da ta tmby shi ingredients yace sirri ne.
"Zan wuce office, Anything for your guy?" Kallon shi ta danyi kaman tana so ya barta ta wuce. Sai can tayi saurin kamo hannun shi, pecking in shi tayi a tafin hannu. Kafin shock ya gama sakin shi ta bude motan ta fita. Ya dade yana kallon hannun yana grinning kafin ya ja motan shi ya bar wurin.
Sai wurin 4:30 pm yake tashi daga office, hakan yasa basu yi wani magana ba ranar. Sai text inta da yake replying in ya dan samu time.
Bayan Sallan la'asar ta gama karance karance ta, ta fito parlor wurin Anty Salma. Samun ta tayi tana waya da MacBook. Tasan dai bai wuce brother, tunda dashi ne suke yawan video call. Wuri ta samu ta zauna, tana kallon movie in da Anty Salman tasa, Wanda ke kallou parlor kawai, tunda ita dai attention inta na kan wayan.
"Nabila zo kiga budurwan yayan ki" Anty Salma ta fada. Curiosity ya sa ta matsowa ba tare da la'akari da waya ake dashi ba. Sai da ta tura kanta tukunna, ta hango shi yana nuna ma Anty Salma zanen da yayi na fuskan yarinyar. Although, painting in da yayi ne ya cika screen in, but she can still see his eyes.
Dan jan baya tayi da sauri "Kai Anty Salma"
"Nabila baki da dama, kedai akwai shiriri ta Allah" dan turo baki tayi. Tana jin brother in yaja tsaki "ke dai kin zama bagidajiya Allah" Hade rai tayi ta Kara cunno bakin gaba, ita ala dole tayi fushi ya ce Mata bagidajiya. Ba tasani ba ashe Anty Salma ta matso da screen in wurin fuskan ta. Kawai jin dariyan Brother in tayi "Wlh baki yi kyau. Na tausaya ma Wanda zai kwashe ki Nabila"
Hade rai ta Kara yi ta dauke kanta daga screen in. "Anty Salma kice mishi wlh na fi wannan budurwar tashi kyau. Kuma Sadeeq ina ma ya fishi kyau, Kuma ba kwasa na zai yi ba tunda yana..." Ganin yanda Anty Salma ta saki baki tana kallon ta ne ya sa ta saurin yin shiru. Sai lokacin ta gane da kunya ta dinga maganan Sadeeq gaban Anty Salma. Amma maimakon tayi shiru, Sai ma rufe fuskan idanunwan da tayi ta cigaba da cewa "And tell him Jasmine inma ba kyau zata yi ba wlh, in dai wannan zai aura"
"Toh fah, to Kai kaji sakon ka ba Sai na maimai ta ba ko?" Dariya yayi sosai yace "Wai Nabilan haka ta zama parrot ne?"
Tabe baki Anty Salma tayi "Nima haka na ganta. All thanks to Sadeeq in, duk shi yaja Mana ma"
Zaro idanu brothern yayi "Wai Sisturh are you serious? Wannan yar har Saurayi gare ta? To ni duka duka Nabilan nawa take nema? I think ko 18 bata cika ba Ina?" Tana jin su a gefe ta wani hada rai. Ita ta tsani a kirata karaman nan, shikenan Kuma mutum ba zai girma ba? In an San shi a karamin Shi Kuma haka ake dawwama? Kowa ma ai progressing yake in life. Ta najin kunya brother, shiyasa ba ta bashi amsa ba. Amma wlh da Yaya Khalipha ne, ko kashe ta zai yi Sai ta amsa shi, shi inma ta gane cin zalin su da yake ne, ke bata courage in gaya mishi magana son ranta.
"Am serious Bilal, ina jin ma ai Nabila aura Mata Sadeeq in nan kawai za ayi a huta. Kafin ta jawo Mana wani abun, she is always talking about him. Ya canja ta, ko kunyan da kasani tana dashi ma raguwa yake yi"
Shi dai Bilal bai daina mamaki ba, shi Kam Mai xai yi da yar 18 years ma bare Kuma Wacce bata cika ba. Wasu mazan akwai daukan ma kansu aiki, a ganin shi kenan. "To wai Amma tsaya Sisturh, nawa yake da har kike maganan aure ma tukun. Ina ga shi ma yaron ne?"
Dariya tayi, ganin har yanzu kanin nata ya kasa gasgata abun "Bilal he is my mate fa, munyi new horizon da shi. Kaga ko 26 ai he is due for marriage, ballantana ma he already settled. Maybe ita Kuma kaddaran ta kenan aure da wuri, Sha we are praying for the better thing" tabe baki yayi yace "Hmm ehm, akwai kallo Kam a wannan gidan. Amma sisturh wannan ma ai child abuse ne wlh. Ya girme ta dayawa"
Salma Kam dariya ma ta bashi ganin how he sounds and looks serious. "Just 10 years. Bilal ana yi Sosai ma, ko dan Kai you are dating your mate ne?"
Rolling eyes in shi yayi "she is better for me Sisturh, ni banson auren wanda na girma gsky. Gara Wanda Zamanin daya, komai dai dai. And layusa is perfect ai"
Dariya tayi tace "Perfect for you ba kaman yanda Sadeeq in Nabila is perfect for him. Yanzu dai Zan fadawa Alhajin ko, in yaso duk abinda muka yi i will tell you. In matar ka ce zaka aure ta Bilal"
Cije lebe yayi yace "My only wife Sisturh, Ina son ta sosai. And she loves me ita ma, kawai dai matsalan da ban bi shawaran ta bane since. But now ki tayani addu'a, everything will be alright" Da confidence in shi yake magana, kana ganin yanayin shi kaga Wanda ke dulmiye cikin Soyayya. Wanda so ya gama mallake zuciyan shi, sannan ya ajiye mishi dafin shi a ciki.
"Allah yasa Bilal, addu'a Kam muna yi Kuma zamu cigaba In Sha Allah. But don't forget Mamma is not in support" rolling eyes in shi ya kara yi. "Ai hka ta ma Baban Areef, Amma ba gashi yanzu ya zama history ba?" Kai kawai ta gyade, ba ta son gaya mishi wannan is a different case scenario tasa yayi losing hope inshi. In dai ba alkhairi bane ai ba zai yiwu ba In Sha Allah, in Kuma shine suna fatan yiwuwan hakan. Tunda yarinyar ita kanta tana burge ta, Kuma akwai hankali gaskiya.
"Bara inje Sisturh akwai aikin da zan karasa gobe zan yi submitting. Ki cewa Nabila ta kwantar da hankalin ta, ita kadai za ta haifan min Jasmine. In ba ita ba Jasmine" dariya kawai Salma tayi, ballantana ma da ta tabbatar Nabilan taji. Pretending take hankalin ta na kan movie Amma tana jin komai da suka tattauna.
"To Uwar Jasmine ai kinji sakon ki ko, ko ince mishi za ki hada shi da Sadeeq" nodding Kai tayi, Sai Kuma ta boye kanta akan cinyan ta tana dariya kasa kasa.
Sai da Anty Salma ta kashe wayan, sannan ta juyo tana kallon ta. "Anty Salma wai wacece waccan in?"
"Layusah, Girlfriend in Brothern ki. They have been together kusan shekara shidda kenan, Yana so ya aure ta yanzu Yana son su Alhaji suje mishi tambaya"
Kwalalo idanu tayi tace "Lah, shine ni kuma Brother ke ce min ban isa aure ba? Bayan Sadeeq inma ya girma shi" dariya Anty Salma ta sake yi. Nabilan ta Kara cewa "Kuma Anty Salma ni wasa nake ma Brother, that lady is pretty sosai. Their Jasmine will be beautiful Allah"
"Toh Shknn zan fada mishi ba Sai ya hakura ba kenan" da Kai ta amsa Mata. Can Kuma ta Kara juyowa "Anty Salma ni wai brother har yanzu yana Canada ne? Wai me ya keyi a can ne ni? Har fa na manta kamannin shi da kyau Allah"
Hararan ta Anty Salman tayi "Sai kace tsayawa kike ku gaisa. Ke uwar kunya abinda ya faru tun kina JS1." Dan marairaice fuska tayi kawai.
"Tun yaushe ya bar Canada ma, ai an kwana biyu gsky" dan zaro idanuwa tayi, guiltily tace "Ina yake to yanzu, why is he not in Nigeria"
"Because Yana aiki a Saudia" Anty Salman ta amsa.
"Lah brother ke Saudia? Kice yanzun ya zama ustaz ma kenan" Anty Salma dai dariya tayi, daganan suka canja akalar hiran tasu.
"Na Kira Mami kan batun Sadeeq" da sauri ta gyara zaman ta, ta juya tana kallon Anty Salman da kyau. "Me tace Miki to?"
"Ashe Amina ma an bada ita? You didn't tell me"
"Lah Anty Salma mantawa nayi Allah"
"Okay, tace zata yi magana da Abbah. Yaje ya ganshi, in yaso daganan Sai ayi bincike. If they're satisfied then Sai a bukaci ya tura iyayen sa. Yanzu dai tace in sunyi maganan. Abban ya fada Mata ranar da zai same shi, she will tell me"
Nodding kanta tayi alaman ta gamsu. "Amma fa" Anty Salman ta fada da dan karfi. Juyowa Nabilan ta Kara yi tana kallon ta, don har ta tsora ta ma "Tace gsky Sai kin Fara School ko da one year ne ki gama inma za ayi auren. Kuma Abbah in Sadeeq in yaje ya ganshi, shi zai samu Mamma suyi magana. Ya ji yanda za ayi" Shiru tayi kawai, Amma jikinta yayi sanyi. Gani take ba lallai Sadeeq ya yarda har Sai ta gama One year ba tukunna ayi batun auren sun yanda ya kagun nan.
A/N: Not much to say today. Hope you are all fine? So tell me do you like Brother Bilal?
Happy reading.
Nagode.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top