13
Hannun ta tasa a kan heart inta tana jin yanda gaban ta ke bugawa, she is so schocked. Like gabadaya ta gama cire rai ne.
"My heart is exploding, Brother, my best i can't believe you did this to me! Wayyo, am sorry nayi ignoring inka dazu sorry please kaji, I can even be the mother of your Jasmine, if you ask me in dai zaka hakura" ta fada loudly, tana fidda numfashi Mai karfi, tsabagen irin mugun girgizan da tayi. He got her Apple tab and make up kit. Abinda ta dade tana buri kenan ta samu for years, make up kit. Tana son make up, kullum za ka ganta gaban mirror ta shafa wannan, ta shafa wancan tana kallon kanta tana dariya. For the tab, it just a suprise gift saboda idea in shi bai taba zuwa Mata ba. Sai dai instant love da taji tana ma abun.
"Is it enough suprise for you?"
"Oh yes yes it is" ta fada tana hugging Anty Salma da ta Mata question in. Tsayuwa dai gagaran ta yayi ranar, dole ta koma tayi squatting tana kallon kayan tana blushing. Ko Kuma kawai ta tashi ta hau rawa.
Unknow to her, tuntuni Video ya sa a mishi. Daya daga cikin cousin in nasu. Sai da aka gama sannan Asim, wanda ya gama vidoe in yace "I know brother will love to see this" juyawa tayi, Sai lokacin ta ankara yana daukan tane.
Da sauri ta biyo shi zata kwace camera in, da yayi wani tsalle ta bayan kujera ya bar dakin. Bin shi tayi tana "Asim please Dan Allah Mana" tasan haukan da tayi, ba zata so ya gani ba. Sai dai Ina ana kaiwa wurin dakin brothern, ya fito yana tmbyn menene kawai ya gansu.
Suna hada ido, ta juya da gudu cike da kunyan ganin shi. Don tun ma bai kalli video in ba, taji tana jin kunyan shi. Gashi tana kitchen yazo ya gama Mata magana, tayi banza da shi Sai ma hararan da tayi ta mishi ya tafi ya kyale ta. Ita ba ma wannan ba, the most embarassing about that Jasmine thing. Yana yawan fadan sunan da zai Kira first born in shi Jasmine ne, because he loves the flower.
So each time ya fadi haka, Sai ta tmby shi "BB wa zai zama mother in Jasmine in to?"
Wani irin blushing yake Sai yayi muttering "I will find her soon" she calls him BB watarana wato Brother da Besty kenan. Akwai lokacin da ta taba tmbyn shi same question da yayi magana kan Jasmine, tace "BB har yanzu ba ka samo Mum in Jasmine in ba wai?"
"Will you be?" Ya fada. Blushing ta danyi a kunyace, Sai Kuma ta tabe baki. The thing is, tana da deep crush akan shi lokacin da take yarinya. Shi yasa duk lokacin da yayi maganan babyn da zai haifa Jasmine, Sai abun yayi bothering inta. So making that statement, is like ta tona asirin zuciyan tane.
Washegari kafin su tafi bauchi yazo ya same ta a dinning. Ba ta San zai shigo ba, da guduwa zata yi. Tana ganin shi tayi kasa da kanta don kar ya ganta. Shi kuwa yana ganin ta ya gane discomfort Inta. Har zai juya sai ya fasa kawai ya nufe ta, ba tasan ya karaso wurin ta ba ma. Sai dai Kawai taga mutum tsugunne a gaban ta. Da sauri ta rufe fuskan ta da tafin hannun ta.
"Mummyn Jasmine" ya fada in a hushed tone. Tab! Kokarin Fara guduwa tayi, yayi saurin cafko hannu ta "Haba Mummyn Jasmine Kar ki min haka Mana, I want to see your lovely face" habawa ji tayi kaman ta nutse, gashi duk an dau dariya. Ita ko ta juya ta kasa facing inshi, duk yanda yaso ta juyo ki tayi ta rufe idon ta gam. Hakanan ya kyale ta, tun lokacin Kuma ba ta Kara yarda sun hada inuwa daya ba. A haka Besty ya zama history, tun da bama ta yarda su zauna gudaya. Ya tsokane ta har ya daina, tana ganin shi take guduwa daga wurin. Shi dariya ma take bashi, yana ganin har yanzu da sauran tane shiyasa.
Washegari bayan ta shirya, Anty Salma ta sauke ta a school in. "In an tashi driver zai zo ya dauke ki" make kafada tayi tace "No Anty Salma, bana fada Miki zanje gidana su Zee ba. Zata aiko a zo a dauke ni"
"Okay, see you later" Jan motan tayi ta wuce. Nabila tsintar kanta tayi da kallon wurin da Sadeeq yayi parking jiya. A hankali abun ke dawo Mata, ji take kaman yanzu abun ke faruwa. Ta Kai mintuna a wurin tana kallon gun, har Sai da Farida, Wacce su ke Classes duka biyu tare tazo ta ganta. Taba ta tayi "Nabila lafiya kuwa? Kaman tun jiya wani abu na damun ki ko?" Murmushin karfin hali Nabilan ta mata "Bakomai fa Farida" Nodding kawai tayi tace "Zo muje to" ta fadi hakan ne don tasan ba suyi sabon da Nabilan zata fada Mata damuwan ta ba. Ita kanta Nabilan ta gane ta kyale ta ne kawai.
Unlike her Fareeda ita da kanta tayi enrolling a Skincare class in. Tace Mata ita tana ganin suna tafiya tare ne, because dole ai Sai ka gyara jikin ka tukunna za ka tsaya karawa da kwalliya.
Ba laifi ranar ta maida hankali a classes in. Tun kafin a tashi, Zee ta iso daukan ta.
"Girl you drive?" Nabila ke maganan ganin kawar ta zaune a driver seat. "Oya hop in" Zee in ta fada tana smiling. Shiga motan tayi "I just hope we are safe"
Sai da suka tsaya ordering pizza da ice cream sannan suka wuce. Zee in na encouraging inta akan tace a kai ta Sudan, it will be more fun. Nabila dai shiru tayi kawai tana tunanin ta inda zata Fara gaya ma Zee plans inta. Kwata kwata yanzu ba barin Nigeria a cikin agendan ta, yanda take ji ko Mamman za ta iya challenging akan haka. Ballantana ko jiya da suka yi magana da Sadeeq Sai da ya fada mata yanason yaje Kaduna ya gaida Abbah. In yaso daga baya yaje wurin Mamma.
"Wai Ina ta magana kinyi shiri, ko Sudan in bai Miki bane? You want somewhere better ko, irin su UAE, USA ko UK. Good"
"Jumping into conclusion zee"
"No am just getting into your head" Zainab in ta musa. Nabila ba taja musun ba sanin ba lallai ta yarda ba.
Can tace "Kingane i have another plan"
"Akan me? Aure?" Da tsokana Zee tayi maganan, sanin kawarta ta na tare da Sadeeq. Sai dai tayi mamakin yanda Nabilan ta jinjina kanta.
"What? Are you kidding?" Girgiza Kai Nabilan tayi "Am not Zainab"
"Amma hakan bai daga cikin plan inki. So why the sudden change? Shiya canja Miki ra'ayi ko?"
"Ba maganan canja ra'ayi bane Zainab" dan jim tayi, ganin yanda kawar nata ta zuba Mata na mujiyan tasan cewa tana jiran more explanation ne. "Ina son Sadeeq"
"Don't let him ruin your life Nabila" A marairaice Zainab ta ke maganan. Ji take kaman she needs to save her friend ko wani hali kuwa.
"I need to marry him ne Zainab" da sauri Zainab ta juyo tana fuskan tan ta sosai. Bata ce komai ba ganin sun iso gidan su. Sai da ta shiga suka fito, suka karasa ciki, feeling the tension between them. Har Zainab in ta Kai ta, ta gaida mahaifiyar ta. Tukunna suka wuce dakin ta.
Da ke Azahar yayi, Sallah su ka hau Shirin yi. Bayan sun gama su kayi lunch all in silent. Tana cikin scooping ice cream in gaban ta, taji zee ce "I don't Understand you need to. Dole ne? Why is that a necessity?"
"Yana so na Zainab, sosai" ta amsa. Still ganin kawar nata is not convince yasa ta cigaba da offering more explanation. "He recently get a job, ba zai rasa in da zai ajiye ni ba. He is capable of getting married Kuma shi Namiji ne Zainab, he needs a lady"
"And so?" Zainab in ta fada cikin ihu, da alamun zancen ba karamin soya Mata zuciya yake ba. "Na fahimci he is ready to settle, kefa? You have a life ahead Nabila, lafiyan ki kuwa?"
"Stop being dramatic Zainab, Mata nawa ke aure bayan sun gama Secondary. Ba a kaina za a Fara ba haka Kuma ba nice ta karshe ba. Sadeeq needs me, he wants me and i have to be with him. Kigane mana Dan Allah" da hawaye mala mala a idanun ta, ta karasa zancen. Abun ya dade yana Mata ciwo, yanda Zainab ba ta fahimtar ta kan lamarin shi. She is her best friend, she have to understand. Sai dai can kasan zuciyan ta, tasan ba wai abinda kadai ya sata hawayen ba. Kawai, she is trying to protect herself ne kawai.
"Nasani Nabila, I can see it from his eyes. He needs you but he needs your body more" Tayi seconds tana kallon Zainab in, maganan da ta fada yana shiga kanta da kyau. A hankali Kuma tana bashi ma'ana. Can Kuma tayi saurin runtse idanuwan ta, tana girgiza Kai.
"Aa Aa Aa Zainab Wlh ba haka bane. Na yarda he love my body Amma shin hakan ba abu bane wanda ke faruwa? In Namiji naka son ka daman komai na jikin ka is intriguing to him ai. It normal, I read novels. I know more than you do"
Juya Kai Zainab tayi cike da takaici. Lokacin ta yarda kawar ta, ta riga da tayi nisa. Da gaske shawaran da ta daukan ma kanta at this young age shine kadai mafita. Komai za ta fada ma Nabila akan Sadeeq yanzu ba ta jin zata yarda da ita.
Nodding Kai Zainab in tayi. "Kina addu'a kuwa?"
"Ina yi"
"To Shknn, Allah ya zaba Mana abinda yafi zama alkhairi" daga haka zancen nasu ya wuce, su ka hau wani hiran.
Sai can Sadeeq in ya turo mata message akan tana ina, ya fito daga interview. Fada mishi tayi tana gidan su Zainab, ya sa ta turo mishi location.
Lokacin Kuma call in Anty Salma ya shigo. Zata sa a zo a dauke ta.
"No Anty Salma zai maido ni"
"Wa?" Anty Salma ta fada "So kike Mamma ta kashe ni"
"Ina zata ganki Anty Salma. Sadeeq ne zai maido ni, Sai yazo ku gaisa daganan."
"To Shknn, daman ina son ganin shi ai"
Sadeeq in bai dade ba ya iso. Zee ta raka ta har wurin motan. Ya fito suka gaisa da Zainab, ita dai ba wani sakan mishi fuska tayi ba. Duk kuwa da ya dan jata da hira a wasa. "Bara naje ko, zan amso ma Mama Sako a can gidan" Zainab in ta fada tana kokarin bin hanya.
"Bara mu sauke ki mana" da so tayi ta ki, duk da kuwa wurin bakin hanya ne. Amma ba ta son kin da take ma alakan nasu ya zama obvious. Hakan ya sa kawai ta shiga motan.
Yana Fara tukin, ya juyo yana kallon Nabila da ke gaba. Hannun ta na tadan gefen shi. Kamo hannun yayi ya hade da nashi, kaman yanda abin yanzu ya zame mishi normal. Ta juyo ta kalle shi, ya daga mata gira. Ta so ta kwace don ganin Zainab, Amma Kuma ba ta son ta kunyan ta shi gaban ta. Haka suka sauke Zainab in, ko godiya ba ta tsaya mishi ba ta fita daga motan, tayi banging door in.
"She seem strange" ya fada. Saurin Kare ta Nabila tayi "Bata jin dadi ne, Kuma bata son fitan aka sa ta dole" haka dai aka bar zancen.
Ba gida suka tafi direct ba. Da ke she is not familiar da titin Abuja ba ta gane ba. Sai da taga tafiyan yayi nisa tukunna. "Ina zamu wai"
"Motsa jiki" ya amsa yana kashe Mata Ido daya.
"Kai Anty Salma zata yi fada fa Allah" ta fada a marairaice, muryan ta ma kaman Mai shirin kuka.
"Kar ki damu zan fada Mata muna tare. Bakince zamu je in gaishe ta ba?" Da Kai ta amsa shi yace "Good, baki da matsala ba dadewa zan yi ba. Am use to doing it ne, in banyi ba bazan ji dadin jiki na ba" daganan ba ta Kara cewa komai ba. Sai shi dake ta faman Mata bayanin aikin da ya samu. Ta ji dadin da cikin Abuja aikin yake.
"Yaushe zanje Kadunan wai?" Ya bukata, tana lura dashi inma yana bukatan ayi auren ne kawai. Abinda ta riga ta sawa kanta shine mafita a gare su.
"Bara nayi magana da Anty Salma tukunna, Sai ta gaya ma Mami"
"Okay" ya amsa. A bakin wani dan madaidaicin gida yayi parking. Ta juyo tana kallon shi.
"Muje kiga gida na Mana. Recently aka gama Gina shi" ya mata bayani.
"A nan gym in yake?" Ta tmby a dan tsorace.
"Nan ma zamu je direct ai" Hannu ta ya kamo ganin ta tsaya still, ya jata zuwa cikin gidan. Tun daga waje tasan gidan zai hadu, Sai dai yanzu da ta shiga abun yafi karfin tunanin ta. Gidan da ta ma kallon madaidaici, ta gane ya karfin a Kira shi haka. Tun daga tsarin architecture in gidan, zaka san ba abun banza a cikin shi.
"In zagaya dake ne" da sauri ta make kafada, dariya ta bashi. "Okay, ai ba matsala muje Gym in."
Hannu su a rike suka is wurin, dake dan ta baya kadan. Duhu ne sosai a wurin, Sai da yayi saurin kunna haske tukunna. Ta gefe tana iya hango wurin su basketball da sauran su. Sai ta gefe ne kayan gyming in suke. Kallo daya ta ma wurin tasan da wuya in akwai abinda babu.
"Kujera ya nuna Mata, ta zauna a Kai. Sai gashi ya shiga wani dan karamin daki. Bai dade ba ya fito da kayan gyming in a jikin shi. Wando three quarter Sai shirt, daya dan Kama shi. Da ta ganshi Sai da taji wani iri saboda bata taba ganin shi a hakan ba. Kai ita bata ma San yana da wani Kira mai kyau ba na jiki Sai a ranar. Ga shaidan gyming in ya bayyana a jikin shi.
"If you want to change, zaki samu size inji ciki" kulle ido tayi ta bude, silently ta dan motsa kanta. Hakan yasa ya gane she don't want to do it ne. Bai matsa mata ba, da hannu ya Mata alaman yana zuwa. Bai jima in ba ya dawo da bottles in ruwa a hannun shi. Sai Kuma orange juice guda biyu. Da can in chocolate guda biyu.
"Kin taba Shan dark chocolate?" Girgiza kanta tayi.
"Oya have one" amsa daya daga cikin can in tayi ta Kai Baki. Da farko da ta Kai bakin ta wani irin suprise look ta bashi. Musamman da ta lura jira yake yaga reaction inta. Sai da ta chocolate in, ya fara melting a bakin ta. Wani irin daci taji ya ziyarce bakin nata guda daya.
"What the hell?" Kusan ihu tayi, tana wani irin tabe baki. Da sauri ta tashi, cikin grass carpet in da ta hango taje ta fara dashi.
"Worst chocolate i ever tasted. Daman shine dark chocolate in? Terrible!" Mita take tana cigaba da kokarin zubar da duk wani taste in chocolate in. Shi dai yana gefe Sai murmushi yake.
A/N: Hello to y'all. Are you guys enjoying the book? Mu cigaba ko a dakata? What do you guys feel about Zainab?
Nagode.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top