12

S💞: "Thank for the warmth of comfort angel, it better than any blanket i've ever used. I feel pleasured. Ina son ki Nabilata" Even though she is still confuse, Sai lokacin taji wani irin murmushi ya bayyana a fuskan ta. Daya daga cikin abinda ya sa take son Sadeeq, he always confess his feeling for her. Ko dayaushe, kokari yake ya gaya Mata Yana son ta. Hakan na sawa, ko tana cikin rudu ta ji hankalin ta ya kwanta.

Tana cikin mota zata koma gida ne daman ya tura Mata mssg in. Ba dai ta Mai reply ba Amma Kuma ba ta da wani tunani a ranta in ba shi in ba. Ya Mata dumu dumu a zuci, Kai hatta numfashin ta, tana jin da kalman sunan shi a ranta yake tafiya. Komai take, shine a ranta. Murmushin ta kayatacce, tunanin shi je ke sawa. Har wani irin kallo na daban ta ke ma mutane, in dai Sadeeq na ranta. Kai hatta yanayin tafiyan ta canjawa yake. Tana tafiya wani lokacin, tana magana ita kadai. It like she is becoming mad in that love. Bakuwan soyayyan da ke samun katon fage Mai kyau a rayuwan ta. Sadeeq ya fara canja ta, domin yanzu koman ta kawai, shine a ciki.

"Ba kiji nane?" Sai lokacin ta dago kanta ashe driver in nata faman Mata magana.

"Au yi Hakuri Dan Allah"

"Lafiya dai ko?" Ya fada yana kallon yanayin ta. Gyade kai kawai tayi, tana kallon shi tunda tasan magana zai Mata.

"Hajiya tace in kai ki gidan Maman Areef. Sun tafi Lagos da Alhaji, Sai zuwa Jibi ko gata zasu dawo" rasa Mai zata yi, tayi. Amma tabbas tana cikin tsan tsan murna da farin ciki.

"To bara na debi kayana a gida" toh yace Mata ta cigaba da driving, tasan Anty Salman ba ta sani ba. So ita ma bata gaya Mata ba, saboda tana son tayi surprising inta.

Zainab dai ta tura ma text, akan tana nan zuwa gidan su Washegari, tayi Missing Zee in kwana biyu ba ta leko ta ba.

Kaman baza ta tura mishi text ba, Sai Kuma taji ba zata iya share shi inba. Don haka, dole ta daure ta mishi sending.

"Mamma is not in town, I will be in Gwarimpa"

Shiga tayi ta debo kayan nata da dan yawa, don tana son in da hali su roki Mamman ta dan barta tayi ko da one week ne. Tana hanya tafiya Gwarimpan ne, taga Sms in shi ya shigo.

S💞: "Such a good new! Can i see you please?" Tasan daman da wuya in bai bukaci hakan ba. Sai dai kuma ba ta fada mishi bane dan yazo, kawai she is use to telling him things, kusan dukkan abinda ke faruwa presently a rayuwan ta, he knows. Ya dai kwace ma Zainab position inta, don da da ita take yawan messages in nan. Yanzu ma su kanyi, Amma ba Kaman da shi in ba.

"Not today" tayi replying back. Shi inma bai yi complaining ba. At least, he got more than enough da zai yi keeping in shi har gaba da goben ma.

Tana sauka a gidan da Baby areef ta Fara cin karo yana jikin Nanny inshi Sai gwaranci yake yi. Ai kuwa Yana ganin ta ya fara yage baki, dake yawan zuwa gidan dasu ke kwana biyu shi da maman shi yasa ya gane ta. Daukan shi tayi tana fadin "Oyoyo baby na" shima har da dariyan shi, irin Wanda ya ke so ta dauke shi, ta karbe shi in nan.

Tana dosa kanta, taci kamshin girki na tashi. To tasan yau Anty Salma an shiga kitchen kenan. A kullum A ake grading inta in dai wurin abinci ne, hakan kuwa yana ba mutane mamaki duba da cewa gidan su cike yake da cooks. Abinda basu gane ba, zaman shiru ya ke sa Salman shiga kitchen in, duk wani cook da za suyi a gidan nan Sai da suka Saba dashi ta yanda ta samu abinda ta dauka gun kowanne, shiyasa ta zama expert dayawa saboda ta tara experience in mutane dayawa. Tunda tayi aure kuwa, Yan uwa da abokanan mijin ta suka fahimce cewa girkin ta bai da na biyu, shikenan ba Sai suka kulla Mata ba. Kullum cikin baki take, tana kitchen tana faman girki. Tun tana mishi complain, yaba fada Mata mutane rahama ne har shi inma abun ya fara fita kanshi. Don haka kawai, in ka ishe su suna ka dan dauke kafa. Sai ya sata dafa abincin Wanda kwata kwata bai da taste, don in aka ba ka fruit ko wani snacks ma dadi zaka ji ka dawo gobe. Har code gare su, in taji yace "The norm" to tasan yana nufin normal abincin da ta iya kenan. Amma in yace Mata "The unique" tasan yana nufin ayi tsiyar kenan, Kuma abincin ko su basa iya ci sai dai su gyara su bayar. Saukin ta ma wai tafiyan su USA, dake nan aikin shi yake.

Hanyan kitchenin ta nufa tana fadin "Ni Kam yau da sa'a nake" tsayawa kallon ta Anty Salman tayi kaman taga abinda ba ta taba expecting ba.

"Ke Kuma daga ina?" Dariya Nabilah "Kaji Anty Salma sai kace Baki San Ina garin ba?"

"Haba Nabila, prison in da kike ai dole ince haka. Lafiya dai ko?" Anty Salma dai da gaske ta dauka wani abu ya faru ne. Don last zuwan ta gidan, da tayi attempting yi ma mamma magana ta bari su taho tare da Nabilan. Tas ta Mata, karshe ma ce Mata tayi ta daina yawan zuwan Mata gida ita hakanan, ba yanda za ayi ta saida akuyar ta, ta Kuma dawo tana ci Mata danga. Hakanan ta dau, danta suka wuce jiki a sanyaye. Yanzu kuwa ai dole tayi mamaki.

"Wai sun je Lagos da Alhaji" Nabilan ta fada, tana kokarin taya Anty Salman bare tafarnuwa.

"Lallai kice Allah ne ya kwato min ke Nabila" dariya su kayi. Sannan suka cigaba da hiran su, suna girkin a tare. Don Nabila ma ba laifi akwai son girki.

Ranar, Sai bayan Isha Sadeeq ya Kira ta. To dake suna ta exchanging Sms. Har Anty Salman Sai da ta gane, saboda yawan taba wayan da take tana wani irin smiling.

"Wai kanwata ko dai siriki aka min ban sani ba?" Cike da kunya ta rufe idon. "Anty Salma ai zan fada Miki"

"Ma Sha Allah, kije abu ya girmama. Yaushe zan ganshi?" Ta bukata.

"Zance ya zo ya gaishe ki" cikin kunyan dai ta Kuma amsawa.

"Eh lallai su Nabila, an girma ya Kama ta brother inki ya San labarin nan gsky" ai da gajin Kiran sunan brother ta bar wurin da gudu. Don Sai taji ma kaman yana wurin ne.

Normal hira suka dinga yi a waya kawai kaman wani Abu bai faru ba. Mostly, labarin yarintar shi yake bata, Sai Kuma University days in shi. Ta riga tasan Fannin Biochemistry yayi first degree in shi. Sai a second degree, kawai yayi professional Masters kan Business. Bayan nan ya Kara karantar English kafin ya dawo Nigeria yin service. Duk karatun nan within Uk yayi su.

"Dad fa ya bani offer in nan finally?" Dan widening eyes inta tayi "Congratulations, ni baka ma taba fada min wani aiki bane ai"

"Porth authority" congratulating in shi kawai tayi, ba kuma wai don tasan abu akan aikin ba

Bayan nan ne ta fito dauke da Areef, ta iske Anty Salman na waya. Don haka kawai sai ta film ta hau kallo tana wasa da Areef. Can Anty Salman ta miko Mata wayan "gashi zaku gaisa" da hannu ta Mata alaman waye. Hararan ta Anty Salman tayi "Zan baki Wanda baki sani bane? Oya collect am" amsan tab in tayi tana kallon screen in dake blank. Mamaki tayi "Hello, who is there? Anty Salman won't tell me" ta fada ganin mutumin bayan shi kawai take gani, Yana faman hada abu a cup. Ta dai kawai gane na miji ne Amma.

"In na juyo ba Zaki gudu ba?" Taso dago muryan, Sai Kuma kanta ya dauke da tunanin waye ke Mata irin maganan nan "Guduwa kuma?" Shiru tayi, Sai ta Kuma cewa "Sai kace dodo?"

"Then bara in gani ko ni dodon ne" yana fadan hakan ya fara juyowa slightly. Widening eyes inta tayi tana son ganin waye ne. Sai da ya gama juyo face in shi baki daya sannan ta gane waye. Da sauri ta rufe fuskan ta da hannayen ta, tana dariya kasa kasa.

"Okay, ni dodon ne kenan?" Ba ta amsa shi ba, Sai ma veil in da tasa ta Kara rufe fuskan nata da kyau.

"Nabila" ya Kira ta, Sai dai ba ta amsa ba Sai noke noken da ta cigaba.

"Won't you grow up wai ke? Kin fa gama secondary school for God sake" ya fada da dan karfi, don shi dariya ma take bashi. Ya dauko yanzu ta girma, za ta daina abinda take mishi, ashe da sauran yarintar.

"Shikenan, Ina ga Sai kin haifan min Jasmine in za ki daina jin kunyan kenan" da sauri ta mike fuskan ta a rufe, ta Mika ma Anty Salma dake ta faman dariya tana gaya ma Areef "Kaga shirmen Small mum inka ko?" Tab in.

"Anty Salma ni dai ki gaya ma brother ya daina cewa zan haifan mishi Jasmine, I have my own Saurayi"

Daga cikin wayan taji yana cewa "Allah mara kunya? Oya come and say it to my face, ashe kunya karya kike yi ma" da gudu ta bar falon tana jin kaman ta nutse. Don ba tayi zaton zai jita ba ma. Anty Salma dai dariya take ta musu.

She can remember yanda abun ya faru. Lokacin tun tana karama in tazo gidan hutu. Suna shiri da brother in sosai, don yawancin lokutta Besty yake ce Mata, ita ma tace mai Besty ba wai don tasan ma'anan bestyn ba. In tazo gidan shi yake bata ta da kayan ciye ciye, lokacin Kuma akwai cousins insu na wurin Alhaji dake zuwa hutu da su Amina ma. So gidan is kind of full, duk da tafiya su ke su barta basa wani dadewa kaman ita.

Ya saban mata da bata gifts duk birthday inta. Da ke December ne, yawanci tana Abujan ko Kuma Bauchi. Ko bata nan, yana ajiye Mata. A certain birthday, lokacin tana JSS1. Ranar wuni tayi ma ba tajin dadi, gashi Mamma ta sa su wani uban aiki saboda tafiyan cleaner in da ke aiki a kitchen. The plan was su fita ko da wani park ne, a dan yi nishadi a siya ko pop corn ne, snacks da drink ayi hotuna. To daman plan in Anty Salma ne, Kuma ita ma she is stuck with work ranar a gidan, ga girki da Mamma tasa tayi ma friends inta da zasu zo. Hakanan suka wuni aiki basu sama fita ba. Brother in Kuma ko bi ta kanta bai yi ba, daman shine ta ke sa ran zai kawo Mata gifts Sai taji shiru ko maganan bai yi. Ita har ga Allah ta gama sa ma ranta shi ma wannan karon ya manta. Ya dai zo ya ganta tana fama da wanke wanke, yace "Besty aiki ake ne haka? Shall i help?" Ba ta San lokacin da ta sakan mishi harara ba. Ji take kaman harda shi ya Kara lalata Mata mood, why will he start something he knows ba zai iya cigabawa ba.

"Worst birthday ever" ta fada tana huro hanci bayan sun gama aikin, gashi she is not feeling okay. Kuma bata son ta kwanta saboda washegari zasu tafi bauchi, yanzu Mamma taga ba ta da lafiya tsaf za ta hana a tafi da ita. Tace ta tsaya taga doctor, tunda su yaran ne kawai daman zasu.

Duk giggling su kayi "Oh gashi gobe zamu tafi bauchi, we will make it up to you someday, maybe" Anty Salma ta fada, Sai taji jikin ta yayi sanyi kawai ta kwanta kan kujera tana tunanin it surely the worst birthday ever.

Nan Anty Salma tayi picking call. Bayan ta gama ta juyo ta kalli Nabila "Nabila please kuje bakin gate ke da Amina. Friend ita Aleena da ta dawo daga Dubai, wai ta bada wani package a kawo min, driver insu ya bawa securities. Go get it for me" squeezing face inta tayi kaman zata yi kuka "Anty Salma fa na gaji Allah"

"Sorry Mana Nabilah please banson scene in nan ya wuce ni ne" Kaman tayi kuka, haka ta tashi suka tafi da Amina. Da ta amso package inma a cikin wani bag ba ta tsaya gani ba ma ta amso ta shigo tana ta hure huren hanci. Taje zata ajiye gaban Anty Salma, tayi saurin dakatar da ita.

"Help me check menene Mana"

"Kai Anty Salma" ta fada kaman za tayi ihu.

Haka dai ta daure tayi bude abun. Gift bag biyu ne, Kuma duk manya manya. Rike daya tayi tana unwrapping ta Mika ma Amina dayan ta bude. Kwallin tab ta gani Sai Kuma medium make up kit.

"Lah Anty Salma you are damn lucky wlh, Leena na son ki, see what she got you" murmushi Salman tayi, Nabila Kuma miko Mata note in tayi "Kinga fa hadda note. Oh no it a poem let me read it"

Da karfi ta Karan ta tana ta murmushi ta. Wishing she is the one, sai da taga anyi mentioning sunan ta sannan ta tsaya.

"Nabeelah!" Ta fada in a surprise tune.

"Kai ni Kuma?" Ta fada tana giggling kanta.

Your besty cares. A ka rubuta a karshe.

Her reaction is priceless, still confuse Sai kallon Anty Salman ta ke tana son ta Mata Karin bayanin. Kin cewa komai tayi, Sai Amina ta turo mata daya note in. Kaman wancan, handwritten a cardboard paper.

Da karfi take karantawa, she can't still believe her eyes. Da sauri ta kalli Anty Salma domin ta tabbatar Mata da abinda ta ke gani. Nodding Kai ta Mata. Jikin ta har shaking yake, tana bude box in da ke wurin Amina. Chocolate box ne varieties kawai. An rubuta Attack your chocolate craving.

"Oh My God! Oh my God! Haaaaa wayyo Kai na" screaming take sosai, tasa hannun ta tayi covering kan hancin ta. Sannan ta Mai dashi kan Kai. Tama rasa Mai zata yi.

Ba tasan sanda ta mike ta buga tsalle ba. Sai Kuma ta duba dayan box in, shi Kam tun a gaban shi tasan donut ne, tunda ga tambarin kamfanin. She loves donut a lot, Kuma wannan is her favorite.

Abun bai Kara girgiza ta ba sai da ta bude sauran gift in taga abinda ke ciki. Tab ne da Kuma make up kit.

A/N: Hmmm 🤔🤔

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top