CHAPTER 36
Alkali yace ke kuma wacece kuma me hadinki da wannan Shari'an? Shigowa kotun tayi tace nice ladidi matar aliyu wadda ake ikirarin mijina yayi min fyade.
Toh wannan maganar ba haka take ba mijina yayi min abinda yafi FYADE abinda ya ninnika FYADE abinda ba ko wace mace akewa ba.
Miji na bai taba kyautata min ba kyautatawa ba halin mijina bane baya kyautata ma matansa.
In akace shi mutumin kirki ne an cuceshi.
Alkali yace ke mu ba gasar iya magana mukeyi anan ba in kinada abin fada toh in babu kuma kada ki batawa shari'a lokacinta.
Ajiyar zuciya tayi tace kamar yadda na fada baiyi min FYADE ba laifi na ne nice na hada tsimi na ajiye a fridge shi kuma yasha lokacin da ya dawo gida ďan ya dauka juice ne kuma batason ya tasheni a bacci. Kallonta aliyu yayi ya saki baki jin yadda ta feso karya amma de yayi tsit baice kala ba.
Tace kuma kamar yadda nace ba mutumin kirki kadai bane mijina mutumin arziki ne ga dattako da iya nuna so da kauna Dan albarka abin alfahari na... kamar yadda nace bai taba kyautata mana ba bauta mana yakeyi ni da aunty lubabatu.
Aunty maryam haba kawai ta rike luba dake zaune a kasa tana kuka ma kamewa tayi. Toh kode asibitin da taje ya taba Mata kwakwalwa ne.
Lauya hindatu tace look mrs ladidi idan har akwai Wanda yake tursasa ki ki fadi wannan magana ne toh ki fada ma kotu kada kiji tsoro.
Ladidi tace babu me tursasa ni babu abinda mijina yamin rashin fahimta ce kawai ya faru da mahaifiya ta kuma de shekaru bai wani ja ba bare nace tsufa ce.
Alkali yace toh ya batun lubabatu da akace zina suke? Tace haba mai Shari'a? Wace Mata ce zata bari ana zina a gidan ta tayi shiru? Billahil azim ba zina suke ba matarsa ce.
Lauya hindatu tace amma ko kina da bayanin abinda ya samu hakorin ki? Tace AI wai hakwara na ? Ranan da suka kawo mana kyakkyawan news ne tsabar jin dadi aljanu na suka tashi to a garin su rike nine ma na yaushe mana jaririn mu kuma anan ne na dinga gwara baki na.
Tsumu tsumu lauya tayi wato de ta fadi or what? Alkali ne yace ikon Allah... duba da jawabin da muka saurara daga bakin ladidi kotu tayi wulli da wannan case sannan duk wani laifi da ake tuhumar aliyu da aikatawa ta wanke shi. Malam aliyu Allah ya bada zaman lafiya ya kuma raya yan uku yana kaiwa nan ya buga gudumarsa yace court!
A bakin kotu kowa jiki a sanyaye yayinda aliyu ke nazarin wani munafurci ladidi ta tsiro dashi luba ko ganin zuciya take Mata ladidi ta riko hannun luba tace sister wai da gaske yaran mu basu zube ba? Wani tsalle luba ta daka a tsorace Dan ita ba haushi ladidi ke bata ba ganin ta banziya take Mata.
Makalewa tayi ajikin aliyu ladidi tazo da yar sandan ta tace yaya aliyu ina wuni murya a sanyaye yace lafiya ladidi daga nan baice kala ba ta riko hannunsa suka fara tafiya a hankali su uku kowa da tunaninsa ladidi ba abinda ke Mata yawo a zuciya sai nadamar abinda tayi.
Aliyu ko tausayi ta bashi da tana so da matasa an dauresa a zuwarnan nata amma ta tattare duka laifi ta bashi. Yan jarida da gulma nan sukayi musu ca da tambaya babu Wanda ya kulasu luba ya cicciba yasa a mota ya karbi sandan ladidi ya jingina a gefe itama ya dauketa ya sata a gefen luba kawai sai suka ga ya fara kuka.
Kewayo wa yayi ta bangaren luba yace fito baby a hankali ta fito ya shiga tsakiya ya miko Mata hannu alamun tazo. Shigowa tayi ya kwantar da ita a jikinshi ya kwantar da ladidi ma dukda cewa yana jin haushinta amma yana sonta.
Driver yace ina zamuje Alhaji karami? Yace gidana... suna isa suka shiga parlour sake zama yayi a doguwar kujera suka zauna a gefensa kawai sukaga ya dafe goshi ya fara musu kuka kamar yaro. Babu abinda yake tunawa sai yadda ya dinga dukan ladidi kamr bashida imani da yadda suka sha wahala.
Rungume shi sukayi dukansu biyu suna tayashi kukan.😭😭😭 Sallama su aunty maryam baisa sun daina ba aunty maryam ke fadin jama'ar Allah ya haka ya zaku mayar damu wasu sususu? Um? Haba aliyu kai haka ake ya zaka dasu a gaba kun wani makale juna kuna kuka?
Ummi tace toh lubabatu hamshakiya AI sai ki matsa a jikin Mata da miji ko ? Kara fashewa da kuka tayi. Wai ni me kikemin haka ne bazaku barni na huta rayuwa ba? Toh wallahi ko zaman zina muke saide muci gaba in na haihu a daura sabon aure Dan idan tafiya dani kukazo yi bazan biku ba.
Daddy ne zai dauketa da Mari ladidi ta shiga. A take ciwonta ya fame suka fara sallallami itakam murmushi tayi tace karku damu hukunci na nake karba.
Zama aunty maryam tayi tare da ajiyan zuciya tayi musu abin tausayi tace don Allah ko zamu samu bayanin abinda ke faruwa? Hawaye ladidi ta goge tace tabbas na kasance me kaunar mijina saide ya kasance me bukata amma dukda haka bai dameni ba.
Innayo yar uwata itace ta fara nuna min dole na tashi na tsaya idan ba haka toh tabbas luba zata kwace min shi kishi ya rufe min ido na biye Mata toh sai ta bani sharadi. Idan dai inaso ta hadani da wani boka mai aiki da iyawa sai na soma zina.
Salati su aunty maryam suka rafka... sukace ladidi ga shirka ga zina ? Tace na nuna Mata kamar na soma zinan amma babu wani zina Dana soma yi domin inason mijina kuma jarumi na shi daya ma ya isheni.
Koda ta kaini akayi mana aikin akace za'a saka luba ta tsaneshi bazata soshi ba ko kadan. Inata jin dadi har akyi min rasuwar nan kace min tafiya zakayi idan baka je zaka samu karayar arziki toh sai naje ayi mana aiki kar mu rasa dukiya 'ya'yan my me zasu ci? Anan boka ke sanar min babu wata tafiya kawai kana tare da luba ne abin ya kona min rai sosai.
Anan innayo ta bada shawarar a mantar daku komai naji tsoron hakan domin nasan girman aure amma sai naji na kasa bijire ma abinda tace.
Toh tun daga lokacin muka mance komai harda ni kuwa sai dazu ina bandaki boka ya baco min. Ina ganinsa naji tabbas na sandan kuma a take na tuna komai.
Boka yace ladidi nasan kina mamakin mai ya kawoni kuma nasan kin tuna komai ban taba yin aiki da nake ta nadama da Dana sani irin naku ba saboda aure na lalata nasa ake yi musu ganin mazinata. Ladidi ki sani ke kanki duk abinda kike yi cousin dinki ladiyo ce tasa na tsafe ki saboda tana son mijinki. Shi yasa ko me ta fada baki yin musu. Ki sani bakida laifi ko kadan a abinda ya faru domin kema ba a haiyacin ki kike ba.
Ladidi ni kaina wannan aiki da nake dole ce ta sani domin tunda mahaifi na ya rasu kawu na ya kaini wajen wani malami wai makarantar allo karyace babu wani malami matsafi ne haka na koyi tsafi sai wata 10 da suka wuce na fahimci tsafin da nake ma shirka ce Dan yana kota mana addinine tare da murde wash abubuwan ya koya mana tsafi mu Wanda muka iya yace mu waliyai ne kuma baya bari mu nemi fatawa wajen kowa.
Cire gashin dake kansa yayi ya wanke fuskarsa wallahi da na lallashi ashe ma matashi ko yaya aliyu bai kai ba. Anan ya dukusa ya bani hakuri yace ya cire jarabar da yasa ma aliyu domin dama innayo ce tace yace bazai iya ba Dan sanda taje wajena da fari kamin ta kaini.
Yace min amma bazai iya tunatar daku ba sai akan sharadi daya sine zaku tuna. Idan har na tona asiri da baki na kowa zai tuna amma dole rayuka guda biyu zasu salwanta idan ko ban fada ba bazaku taba tunawa ba kuma bazaku yarda ba. Aunty maryam tace gara fa da kika gane bamu yarda da taysuniyar nan ba.
Ladidi tace zaku tuna karku damu yanzu mu jira zuwansa Dan yace idan na fada jikinsa zai yi masa Saba toh zaizo ya warware sai ya tuba ya kuma nemi Ilimi sadidan me kyau ba wadda akayi Mata mix me cuwa cuwa ba.
Kamin ta rufe baki ya baco kamar ba boka ba so handsome dashi ya durkusa ya gaishe su. Aliyu ya kada cewa komai luba kuwa gyangyadi ma take Dan she can't come and kill herself.
Yace zan tuna muku kuma ladidi ta bada rayuwa daya wato na innayo yanzu na biyu ne bamu samu ba.
Ladidi tace a dauki tawa a na biyun mana a zabure bokan yace Sam bazan iya ba ladidi kinsan irin s..... take yayi shiru kamin yace adai nemi wani. Luba tace indai za'a dena mana ganin mun tana yin zina toh why not a dauki baby daya a ciki na? Aliyu ya bige Mata baki yace ke shashasha rufe mana baki.
Shiru tayi tace toh ni gaskiya kar a sake cewa nayi zina. Yace toh ni bari na dauki duk wadda naga dama yana fadin haka ya rufe ido aiko kowa ya Mike mai kai masa damka nati me girgiza kai nayi ladidi tasa hannu zata bude idon nasa kawai sai ga gawa.......
😳😳 KAWAI ME NA SHIGA UKU! ALIYU YA DAUKA KO LUBA? LADIDI? AUNTY MARYAM? UMMI KO DADDY? KODE UNCLE ABBA NE? KO WATA FAN DINA YA DAUKA NE MA? WAIYO ALLAH 🥺😭
TOH KARDE KU MANTA KUYI VOTING TARE DA COMMENTING SANNAN KU TAYANI SHARING. NAGODE DA KAUNA TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO....
Miss untichlobanty 💕
14th July,2020.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top