CHAPTER 33

A bangaren su luba kuwa kwantar da ita yayi a kujeran baya ya fara bata hura Mata iska ganin da karfi ta shaki numfashi ta soma ja da karfi da alamu tana bukata.

Ajiyar zuciya ya sauke yace sannu baby na sannu kinji? Me ta sameki nasan de ba haurowan da mukayi bane ko shine? Girgiza kai tayi tace numfashi nane ya kage. Dama satinnan bana iya zama wajen da babu iska ko an kunna ac sai nabar window a bude.

Yace subhanallah shine baki fada min ba? Toh muje asubiti ko? Kai ta daga Dan ita ma tanaso tasan matsalar ko an taba Mata wani abun ne a ciki. Amma karfa su jiyo wata masifar gara ma su fara yawon in ma mutuwa ce daga baya ta mutu Dan bazata yadda ta mutu bata ci abinci ba.

Dariya aliyu yayi yace hajiya ta ina jinki fa. Ba a tunani kike wannan maganar ba dariya tayi tace kaga kaifi na? Yace karma ki damu babu wani batun mutuwa.

Park suka tafi sukayi ra wasanni da ciye ciye sun mance shaf da sunada wata matsala ganin yamma yayi yasa yace muje asubitin nan sai na mayar dake gida. Turo baki tayi tace amma uncle dole ne sai naje gidan? Nifa Allah bana son komawa ni dakai nakeson zama... saboda kafi min su Kaine ka nuna min gsky tun ina karama kuma ka soni su kuwa banda......

Da sauri ya toshe Mata baki yace kul luba wadannan fa iyayenki ne koda ni bai zama dole na musu biyaiya ba ke wajibi ne kuma kuskure kowa yana yinta nima nayi har sau biyu ban tsawatar miki da wuri ba na barki kina nema ki tsoma kaina a ruwa sannan na kuma yadda aka boye auren mu Wanda na tabbata kaunar da nake miki ne ya janyo min yin wannan sukacin saide har yau abinda na kasa ganewa shine yadda akayi na fara son yarinya...

Ji yayi ta rungumesa tana kuka tace uncle maimata. Yace me? Tace abinda ka fada dazu da gaske kana kaunata? Murmushi yayi yace sosai kuwa luba ban gano hakan ba sai randa baki kwana a kirji na ba kika kwana a wani waje ranan da aka kashe mana jinin mu kuma ake ma soyaiyar mu barazana. Kuskure na na uku shine da ban taba fada miki ina kaunarki ba.

Lubabatu...ni Aliyu bala bakabe ina matukar sonki kuma kaunar ki ya ratsa jinina saide inaso ki sani.... San kara aure.... da sauri ta zabura saboda yadda gabanta ya fadi... shi kuwa ko a jikinshi yace inde har Allah zai halittu min wata Wanda tayi daidai da ke zan aura amma in bani watan ki ke daya ce a duniya toh dake zan zauna.

Ajiya zuciya ta sauke tana duka kirjinsa cikin wasa tace har ka bani tsoro wallahi kamar hanji na zai zazzago. Dariya yayi yace Allah uwar yayana harda hawaye ya fadi haka yana goge Mata hawayen.

Tafiya sukayi suna isa asibitin yakaita wajen likitanta bayan sun gaisa yace likita dama batun matata ne tace tunda wannan abin ya faru bata fane meke Mata dadi ba takanji ciwon mara, sannan bata iya zama a inda babu iska. Luba tace kuma ni daya sai inji inason nayi kuka sannan wani lokacin haka kawai ana cikin zama sai na fara bacci.

Dan murmusawa aliyu yayi saboda ya tuna yadda takeyi ne sanda taje da ciki bai sani ba kawai ita daya sai tahau bacci. Akwai ranan da ta shiga ban daki bayan sun raya sunna tace zatayi fitsari kamin nan shi ya cire bedsheet shiru shiru bata gama ba yace zan shigo ba shiru dama kullum yakan tsokaneta tare zasuyi wankan amma sai ta dage bazai shigo bayin ba.
Yana budewa yaga ta baje akan shadda tana baccinta harda yawun bacci.

Har ya gama tunanin sa luba tanata Jerowa likita abinda takeji ita dai dr murmushi kawai takeyi sanda taga abin ba karau bane tace toh naji daga nan AI ko baki min bayani ba nasan me ke damunki.

Kallon aliyu tayi tace ka tuna lokacin da na sanar dakai matarka ta rasa cikinta? Yace sosai kuwa likita har haushi kika bani saboda yadda kike wannan murmushin taki Dan dariya tayi tace toh fa baro baro haka zaka fada min? Toh shikenan yanzu ko zan birge ka.

Abinda baka sani ba matar ka tana dauke da cikin yan 4 ne.... zaro ido aliyu yayi yace ban gane ba Dana yara 4 na rasa ? wallahi ladidi kin shiga uku. Tace tsaya mana lokacin da kishiyar ta ta jefeta guda daya ne ya fita sauran yaransu uku suna nan kuma yanzu haka watan su uku harda kwanaki idan kunaso zamu iya yi muku ultra sound da pregnancy scan domon kuga hotansu.

Abinda yasa na boye muku kuwa shine idan kun sani zakuyi ta ritita cikin Wanda zai janyo a sake kai masa wani farmaki sai nayi shiru sai ya Dan kara kwari amma nayi mamaki da baka gane ba domin ko yanzu ka taba zakaji taurin su.

Yace tabbas sanda take da cikin jikina ya bani dukda ban tabbatar ba kuma wannan ne karo na farko da aka dauki cikina. Bayan kin sanar damu cewa babu cikin na lura cikin ya Dan taso ma amma sai nayi tunanin ko kibar da tayi ne ya kawo Mata tumbi ashe de.

Rungume luba yayi yana zura hannu cikin riganta ya shafa cikin ita kam kuka ma take sharara masa don farin ciki ta kasa cewa komai har sanda tasa likitan yin kuka. Tace toh muje a dauka mana hotan likita waiyo dadi Allah na.... a tare sukace Alhamdulillah suna mikewa domin a nuna musu jariran su.

LUBA

ALIYU

LADIDI

A gida kuwa yan sanda sune gidan uncle abba sukayi musu tambaya dama yanzu ummi a gidan suke yini sai dare suke komawa gida asuba tana yi su sake  dawowa.

Bayan an gama musu ne aka nemi ganin luba domin ayi Mata tambaya akaji wayam an neme ta sama ko kasa babu ita babu labarin ta. Anan ne aunty maryam tace ba shakka fita tayi ta tafi wajen yaron nan. Nace kaji aunty maryam da karfin hali shekara 3 fa kika basa.

Su luba ko tun a mota sukace tunda akwai ciki yanzu kam dole a barsu inma wabi auren ne a sake daurawa babu me rabasu ko anki ko anso.

Aliyu ne yace ta zauna a mota ya bude Mata window yayi locking yace zai shiga ya fara magana dasu kar a kawo ma yaransa lahani komi rintsi kar ta fito. Da murmushin sa ya shiga hannunsa dauke da hoton yaran su. Yana shiga yaji shar aunty maryam ta kwasheshi da Mari.... ummi ta dada masa wani uncle ABBA ya bada biyu lafiyaiyu daddy ma ya sauke mai yan sandan ne suka rikesu da sauri sukace ya haka? Ya zaku sashi a gaba da duka babu dalili.

Suna hada ido da Dan sandan yace nazifi ? Inspector yace malam Ali? Dama wai duk wannan zancen kai ake nufi? Musabaha sukayi su uncle abba sukayi sakoko ummi harda rike haba. Zama sukayi uncle ABBA yace inspector ya naga kaji sanyi haka ? Kamashi fa zakuyi muma nan zamu kai karar sa yayi zina da yar mu yana Mata karyan ya AURETA harda dirka Mata ciki.

Inspector yace tabbas nasan malam Ali shekaru biyar kenan da suka wuce shine ya ceci diyata da matata ba'a keta musu haddi ba domin lokacin an harbeni bana hayyaci na ma.
Daddy yace mutum na iya canjawa wancan alin da wannan da banbanci.

Aunty maryam tace ita wancan hamshakiya gwamma uwar matar Zamu samu ganinta ko sai mun yanki ticket mun cika form?  Wayansa ya dauko ya Kira dayan layinsa Wanda ya bari a mota Dan kar a gane ya bata waya yace ta shigo amma tayi a hankali don Allah yaransa.

Tana zuwa bakin kofar da sauri ya taro ta yana sannu sannu ko baby? Ina ke miki zafi? Tafiyar nan da kikayi bai miki wani illa ba ko? Ummi ta fashe da kuka tace kaji shi ko inspector ance masa cikin ma ya zube amma bai yarda ba wallahi bashida kunya ko kadan.

Kallonta inspector nazifi yayi yace wannan yarinyar AI nasanta karde kuce min ita ce lubabatu? Tabbas randa kayi min taimako wannan yarinya kuma tare lokacin bazata wuce shekaru 14 ba ko? Aliyu yace girman jikina shekarunta 11 a lokacin. Yauwa inspector AI na fada ma nace lokacin shekarar mu daya aure washe garin Ranan sanda nazo Dubai a hospital ka tuna har ka bani shawarwarin rayuwa amma Dana koma bayan kwana 5 ban same ku ba?

Shiru inspector yayi yace gaskiya kayi hakuri malam aliyu nasan de munyi maganganu amma gsky bazan iya tuna me mukace ba. Yace ka gani ko? Kowa zai tuna komai amma da anzo batun aurena da uwar 'ya'ya na toh lokacin ne aka manta ko ace min be faru ba ma. Me kuke nufi da ni ne? Duba kalli ku gani Allah ya albarkace mu da yara har uku ya fada yana nuna musu hotan.

Dafe kirji aunty maryam tayi tace tace ke suwaiba(ummi) mun banu mun lalace ya kuma dirka Mata wani. Hayaiyakowa tayi zata cafko luba da ta makale a jikin aliyu. Ya aiko Mata wani kallo batasan sanda ta koma ta zauna ba tana huci. Dauke kai tayi tace inspector ko zan iya sanin dalilin zuwanku?

Dagowa inspector yayi yace munzo ne muyi arresting dinka......

😳😳😳WAIYO KIRJINA HAR WANI FAFAT YAKE YI... YANZU KARDE TAFIYA ZA'AYI DASHI ABAR LUBA A HANNUN SU AUNTY MARYAM?!

GASKIYA DOLE NAYI WANI ABU BAZAN ZAUNA INA GANI A BARAR MANA DA TRIPLETS DINMU BA DAYAN MA YAYI ALLAH YA TSARE NA GABA!

AYI COMMENT KO NA KUMA ZUBAR DA BIYU DAN NAGA KWANA BIYU BACCI KUKEYI BAKWASON YIN COMMENT KUMA DE KUNSAN NA IYA YAJIN AIKI😎

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

Miss untichlobanty 💕

10 July,2020.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top