CHAPTER 8

Ganin yanda marakisiyya ke Dan harhade rai tana sunne kai yasa yace ke uw....ki yana dungure Mata kai yace Dan nace kiyi gaisuwar ne kike hade rai ko kuma Dan na kiraki da sandar rake? Ince ba yau kika soma jin na kiraki da hakan ba? Shegiya ba taimaka miki ma nayi ba? AI sandar rake yana da Dan kauri yo ke duk gakinan ko sandar baki kai auki ba sai kace tsolo ko takand'a.

Daidai lokacin umma ta fito daga toilet jin maganganu tana washe baki dan bata ma hango sailubar ba saboda tana bayan sa kamo hannunsa umma tayi ta zaunar tana fadin yanzu nake ta raya ku a raina nace har 12 ta kusa Baku iso ba fatan dai yarinyar nada nutsuwa ko Dan albarka?

Waigawa yayi yaga sailuba ta Dan dosana mazaunan ta a bakin kujeran dake daki ya dalla Mata wani harara. Sannan ya kalli gefensa ganin ta dauke kai yasa ya bubbuga Mata gefensa. Gumi ne ya karye mata waiyo ya zatayi wai dama haka lud yake ne ? Ita labarin rashin kunyarsa takeji Amman yau ta ganta karara a fili.

Kallon kashe jiki yake Mata Wanda bai yayi wa mutum sai ransa ya baci ko kuma yana cikin rudani. Marairaice masa tayi kamar tayi kuka Dan tasan ba shakka in ta zauna gefensa toh tabbas babu abinda zai hanashi rungume ta ko riketa Wanda bazata iya juran hakan ba saboda kwarjini da umma ta Mata.

Shi kuwa mamakin irin taurinkai da kafewa da sailuba tayi masa Wanda ya ke ganin taki nuna iskancinta ne saboda ta Sami g*ndin zama a wajen umma.

Umma ko bata ma lura da me ke faruwa ba tace ah ah kai lud kaide baka da dama yanzu mai makeup  ka taho da ita saboda ta gyara mahaifiyar ka adan yaba min abin yan matan ? Gaskiya Dan albarka ka fara hankali amma da bakayi wannan dawainiyar ba ai.

Kallon sailuba tayi tace sannu ko yan Mata? Ngozi ne ko chiyoma? Lud ne yayi caraf yace AI ba mai make up bace mom kuma sunanta sailuba. Amma ni Sally nake ce Mata.

Umma da mamaki tace sailuba? Iko sai Allah kasa kasa tayi da murya tace kila arnan arewa ce ko? Wacece ita toh ? Murmushi yayi kamar mutumin arziki yace she is my chick ai mom. Juyowa tayi ya kalli sailuban yace ke bazaki zo ba sai na finciko ki.

Mikewa tayi tana kwarkwasa tazo ta tsuguna a gefensa tace mom ina wuni tana mai dafa cinyarsa da hannunta. Yo dama kawaici take tunda ya dage ko sai ta bada hadin kai komai ya fanjama fanjam!

Kallon da umma ke binta dashi yasa ta tsimewa tayi shiru dama kasada ce irin Tata yasa ta gaishe ta. Kallon hadirin kaji umma ke binsu su biyu shikam ganin ta a gefensa yasa ya kamo hannunta yana mammatsawa. 

Umma tace au au au wato yau kuma a gaba na za'ayi me kankat? Dan albarka Dana fara ce maka Dan albarka saboda wa'azin da naji na daina dukanta la shine zaka badan kasa a ido?

Shine zaka nuna min jarabar ka karara? Yanzun wannan shirgegiyar ina zaka kaita ? Ka duba rusheshiya ta fini auki ma ta dau jajayen kunne sai kace yar yahudawa me zakayi da ita?

Wallahi wagga ko a bazawara AI wani bazai dauke ta ba. Jibeta fa yadda kasan tayi haihuwa uku mutum gaba daya ya kumbura sai kace me hambudar yis da asuba. Gata wata yar dunkurkura da ita sai kace a kwalawa uwarta tabarya.

Dama..... hade rai yayi yace what the f*ck what the f*ck haba mom haba mom gaskiya bakya kyautamin, kinji matsala ta dake. Kinyi karatu but kina Abu kamar tsohuwa you are just 48 years amma in wani yaji ki sai ya dauka kinyi 70. she is my babe fa my girl! my wife! Kawai Dan kinyi aure a 16 years kin haife ni a 18 ba yana nufin kowa sai yayi aure da wuri ba.

Da kike batun wani saikace bazawara wa ya mutu wa ya tashi AI dama na Dade da mayar ta bazawara ta ko my Sally? Bige masa baki tayi tace wa iyazu billah toh na rantse da azim ba a gidan nan ba.

Wallahi baka auren diyar arna shege mai bakin baki ba'a taba yin abin arziki dakai ka fita idona na rufe ta karashe zancen tana bin hannun da yasa ya rungumo sailuban da kallo.

Murmushin karfin hali tayi ta kalli fuskarsa tace hakane mine yayinda takeji kamar ta shako umma hannunta har rawa yake yi. Dayace kare a kunnensa yace zo kawai ya kashe.

Murmushi yayi yace that's my girl shiyasa nake kara kaunarki saboda fadan gaskiyarki.

Umma tace tashi ku fice min kuma kar ma ka tinker mahaifinka da wannan abar.
Yace but mom ni ita tayi min kuma....bai ida magana ba sanadiyyar marakisiyya da ta shigo da sallama kasa kasa. Cikin hade rai yace wow wow wow you much be a fool... ban taba gani wawiya dabba irinki ba wato tunda na Kira sanda kika dauki minti biyu kamin kukazo kallon agogon wayarta tayi tace ko minti 1 fa bankai ba yaya.

Kutmar......ki! Ke zanci......ki fa ina magana kina yi ? Nayi kama da sa'an ki ? I said am I your mate? So yanzu ne kika ga damar zuwa kenan ko? Kila gaba sai mun cika form zamu samu ganin ki hamshakiya.

Rawa jikinta ya soma tana bari tace ka... la yi hakuri ya lud ba da gangan na tsaya ba daddy ne... have shut your mother f*cling mouth young lady...ganinki kawai zazzabi yake samin ni ko muryanki naji sai nayi ciwon kai.

Dago ido tayi ta kallesa yayinda hawaye ke shirin zubo Mata yace daina kallo na da wannan idanun naki munafuka shegiya ramammiyar banza. No wonder Allah yayi ki mutum mutum dabba dabba.

Shessheka kuka ta fara ya Mike da sauri umma ta Mike tace kul karka sake ka tabata amma kamar kara masa karfi tayi ya tunkari marakisiyyar da ta rabe a dungun dakin yadda kasan kadangaren da aka tsoma a ruwa kankara ta wani kame a lungu.

Ta wutar Riga ya cacumo ta ya dagota yace ke Dan uw....ki me aka miki kike kuka ? Wato hada gu zakiyi ko? Toh sannu annamimiya nakasha fandiya.

Kwarfe ta yayi da kafarsa dake sanye da timberland yace ina tsaye kina tsaye ? Girgiza kai tayi good fatan dai baki manta ba ko? Da sauri ta daga kai yace very good you are such a darling.

Ita dai toshe bakinta tayi da hannunta tana kukanta. Wai me tayi ma Dan uwan nata ne a labarin da ummi ta bata tun randa aka haifesa yake Mata zalinci.
Rananda aka haifesa barin gidan yayi sai dare ya dawo an hada ruwan wankan ta akace ya karo ruwa sanyi da shike already an tsunduma ta ciki. Kawai ya dibo na zafi cikin Moda ya juye Mata kuma bawai yaro bane shekarunsa 10 lokacin shiyasa har yau akwai Dan alamun kunar a cinyar ta.

Haka sanda ta soma koyan rarrafe ya daurata akan gado ya fice daga dakin ta fado tayi adungure sallar mage. Har dai tayi wayo ko magana bata shiga tsakanin su daga gansa take buya Dan tasan bakin mugu ne. Wata rana yana zaune a parlour yana assignment batasan yana nan ba ta fito daga ita sai pant abinta zata je kitchen lokacin shekarunta 6 shi kuma 16 kawai taco an kwashe ta Mari sanda ta gware da gini tayi kuli kulin rakiya ta kwalu da gini.
Rarumar ta yayi ya bata double combo din Mari guda biyu wai kawai laifinta shine yana daura ido a kanta yaji gabansa ya mugun faduwa ga tsikar jikinsa da ya tashi. Tun daga ranan ta tsaneshi don da tsoron sa takeji.

Toh abinda yasa yau tsoron da take masa na yarinta ya dawo sabo harda karu shine.....

😂😂😂ALLAH BAZA KUJI DALILIN YAU BA SAI GOBE.

TOH AMMA ME KUKE TUNANIN YASA MARAKISIYYA TA SAKE FARA JIN TSORONSA DARE DAYA?

GASKIYA NAGA ALAMU KWANA BIYUN NAN WASU KO COMMENTS BASA SON YI MIN. TOH AI SHIKENAN ZANYI ZUCIYA ABINA INYI BACCI😁

Nagode Sosai Allah yabar kauna da zumunci love fisabilillah

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

Miss untichlobanty 💕

27th July,2020.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top