CHAPTER 53
Kama hannunshi tayi ta gurza alamun yaci gaba da sosawa har dariya taso ta bashi yanda ta larme kamar jaririya. A hankali yace baby? Tace ummm? Yace mu tafi gida ko? Ta girgiza kai hakan yasa yaci gaba da Sosa Mata bayan nata har tayi bacci kamin ya kwantar a hankali ya nufi hanyar gida yana yiwa mai balangu Allah ya isa Dan shi ba haka yaso ba.
Washe gari m. Salis justin duniya yayi akan m. Ahmad ya taimaka masa yaje ya gyara lamarin m. Ahmad yace babu ruwan sa. Kullum Abu daya ake yi har abin ya fita akan m. Salis ya fawwala wa Allah lamarin sa.
A kwana a tashi rayuwa na tafiya m. Ahmad ya samu sauki sosai likita yace masa daga sun dawo wani sati ma an sallame sa in babu wani matsala. M. Salis kuwa an sallamesa sati biyu ma da suka wuce sai de har yau jummalo ana gidan jiya ta daina saka hijabin amma banda rike hannun bata yarda aje ko ina yau ne ma aka yarda aka masa bye bye hug shi da ya tashi fita film me zafi ya saka Mata dukda bata jin yaren.
Yaga alamu tana daukan lecture ita ba iya aiki zatayi da waya ba, Shiyasa bai batawa kansa lokaci ba ma. M. Ahmad zaune a office dinsa yana tunani shi wace irin kaddara ce dashi komai NASA a bai bai? Yanzu Matar da yake so din ma tana da aure.
Ajiyan zuciya ya sauke yana mai fidda rai akan auren marakisiyya domin taga yadda kwana biyu take farin ciki sosai yasa tana jin dadin zama da lud din. Jummalo ta fado masa baisan sanda ya saki wata mai jegon dariya ba.
Dai dai lokacin yaga computer dinsa tayi haske duba email din yayi yaga letter of promotion ne sanda gaban sa ya tsinke. Karantawa yayi yaga ya samu Karin matsayi ne daga level coordinator zuwa HOD farin ciki kamar me amma kuma tunowa da bazai dinga ganin marakisiyya yasa yayi tunanin kila addu'ar sa ta karbu zai daina ganin baibai shiyasa Allah yasa aka daukesa daga inda zasu na haduwa sosai Dan ya manta ta.
Murmushi yayi yace marakisiyya allah ya albarkace rayuwarki yasa.... fadowa office dinsa da m. Salis yayi babu ko sallama yasa bai karashe addu'ar sa ba.
Rungume sa m. Salis din yayi yana fadin Alhamdulillah bro allah shine abin godiya duba ka gani ya nuno masa laptop dinsa yace yanzunnan nayi receiving letter dinnan rungume juna suka kara yi suna yiwa Allah godiya.
M. Salis yace bro saboda wannan ya kamata yau kazo gida na muci girki ko ya kace? M. Ahmad bayaso dai m. Salis yaga kamar rashin kirjinsa yayi yawa gashi abin farin ciki ya samesu kawai sai yace na yarda amma da shararo ka kirata kace zamuzo tare.
M. Salis yace batada waya AI ko ka mance ne? Shiru kawai m. Ahmad tayi yana nadamar amsa gayyatan da yayi yace toh shikenan matar taka ce sai shiriyan Allah. Shida m. Salis gani yake ya ma m. Ahmad wayo nidai kawai murmusawa nayi.
.........
A hanyan su na tafiya gidan ne m. Salis yace bari ya siyo kayan miya da nama Wanda zasu ajiye Dan kayan miya kudin su ya hau musamman ma albasa.
M. Ahmad yace um mu ina muka San wannan ? Daga company ake kawowa gida mama na ta dafa mana abinci Dan taki na kawo Mata yar aiki wai tana son ta dinga mota jiki kar in tsufa ya kamata ta zauna gaba daya.
Dariya sukayi m. Salis yace gaskiya kam mama batason tsufa ya kamata abin da ta Saba yi kasan Allah da fari da kace min tana shiga gym room dinka tayi exercise ban yar da ba.
Nan suka cigaba da hira har suka iso gidan m. Salis mai gadin makwabta su Wanda kwana biyu shi yaje bude ma musu gate saboda kirkin m. Salis din ne ya bude musu. Toh tunda zama zai ti ta yi a gidan da take gadin Dan masu gidan basu kauro ba, gara yayi aikin lada.
🖤❣🖤
Jummalo tunda m. Ahmad ya fita tace toh yau kuma me ya kunna min ? Anya kiwa ya Ahmad ne yace ya dinga saka min fina finan yahudu yanzu yanzu ana yaki, anjima suhau rungume rungume bari muga na yau kuma me za'ayi a ciki?
Kai ni sunan fin (film) din da ya Samin din ne wahalar fada gare ta wai dilobats(the love birds. BAN SAN KO AKWAI FILM ME SUNAN SA BA DAN BANA KALLO SAI YA KAMA DAN HAKA HADA SUNAN NAYI) sai kace jamusanci.
Matar salisu fa kallo yayi dadi taga an fara kauce hanya da sauri ta rufe ido tare da buga salati ta sauko daga kan kujeran tana gyara zani kasan center table ta shiga tana leke. Can dai ta fara jin wani irin kamar yadda taji sanda ta fada jikin m. Ahmad tana masa hauka.
A lokacin tayi tunanin ko tsoransa yasa taji hakan. Fitowa dai tayi ta nutsu harda tashi ta dauko coke a karamin fridge dinsu da ke parlourn.
Nazari ta fara yi yanzu wai haka zatayi wa mijin ta kawai ta hau tsoran bakin mutum sai kace mayya? (Note: normal film kawai take kalla ba zina ba)
Rufe ido tayi tana gwadawa a jikin Goran ta kawai sai ta tuntsire da dariya abin ya Mata sugar, tace kai gaskiya bazan iya yi idona biyu ba saide in ido na a rufe.
Hakan yasa ta tashi ta shiga daki ta dauko bakin Dan kwali ta ajiye a gefen ta. Duk abin da akayi sai tayi imagining tace kai ahe mu yan kauye an barmu a baya, shehu shiyasa naga duk yan garin mu cewa suke aure suke so.
Allah sarki ni jummalo an barni a duhu, toh wa zai fada min ni da ko kasance ba'ayi da ni. Da saide Bello na.... shiru tayi ji a karo na farko da tayi tunanin Bello bata ji komai a ranta ba kawai tace Allah ya ji kan ka.
Ta shi tayi tunowa da yau bata ji motsin msndo ba kar yazo ya kalls ba da ita ba hakan yasa ta sa pause kamar yadda m. Salis ya koya Mata. Tace la ai kuwa sun tsaya sun dena motsi.
Fita tayi zuwa dakin mando ta samu ya shanya baki sai bacci tace kai yaron ba ba dai asara ba sai ya yini yana basshi kamar gawa.
Komawa tayi taci gaba da kallon ta tsalle ta daka tace ase I lo yu (I love you) din da nikeji saratu na fada a cikin salurar ta ahe turanci ne, she masoyi ake fada wa. Ko menene ma'a nar sa? Zan tambayi ya salisu in ya dawo.
Can sai ta jiyo shigowar mota lekawa tayi taga m. Salis yana kokarin shigowa hannun ta har rawa yake ta daure idon ta bayan ta tsaya inda ta tabbatar in ta tsaya kofa bazai hambare ta ba.
Su m. Ahmad kuwa har zasu shigo ya tuna da kayan miyan da ke booth mikewa m. Ahmad mukulli yayi yace bro kayi gaba bari nasa su tumatirin nan a deep freezer dake baya na shinfida albasan nan a kasa sai na shigo.
Kar fa ka fada Mata surprise din, m. Ahmad yace ni na isa na shiga sabgata Mata da miji ? Allah ma yasa bata parlourn karban mukullin gidan yayi yayin da m. Salis ya juya tare da komawa.
Mukulli m. Ahmad yasa ya bude yaji an daka tsalle an fada jikin sa ana fadin baby oyo oyo kamin yace wani Abu ta hade bakinsu.
A cikin makokoron sa yake jin bugu zuciyan sa yayin da ya saki mukullin da ke hannun sa yayi mutuwar tsaye saide kash jummalo bata zo da sauki ba, caraf ta riko harshen sa.....
Saide haka kawai take mamakin yadda taji banbancin jilin mijin nata kamar ya Dan kara tsayi sannan kuma haka kawai taji tana so ta zauna a haka har ta mutu, wannan ne yasa ta fara tunanin ko ta fara son m. Salis din ne?
Murmushi ta tayi a wannan yanayin tana kara narkewa a jikin m. Ahmad din Wanda Allah sarki bata San shi bane. Hannun hagun tasa ta lankayo wuyan sa yayi da tayi anfani ta da hannun daman ta tasa cikin rigan shi.
Wani numfashi m. Ahmad yaja Dan shi gaba daya ya daina tunani ma da kwakwalwar sa kawai ya tsaya ne kamar gunki.
Ba abinda ke tada masa tsikan jikin sa kamar turaren da ta fesa, a yau ne ya yarda babu sarki sai Allah, a yau ne ya yarda akwai yanayin da Dan Adam ke shiga ya kasa aikata komai da jikin ya ma kasa banbanci fari da baki, ya kasa banbanci me ya faru da shi, me kuma ke faruwa da shi.
(Toh toh toh ga m. Salis nan zuwa Dan! Dan!! Dan!!! WASA NAKE HAR KUN WANI DAFE KIRJI KUNA ZAZZARE IDO😂)
sakan masa baki tayi tace I lob yu sannan ta fara kai hannun ta wajen maransa. Flash din wuta ya gani a idonsa hakan ya baisan dalilin da yasa ya dura Mata yawun sa Dan ta sake sa ba saide kashe da alamu bai yi aiki ba Dan ji yayi tace kara min.
Yasan in yayi kokarin yin tsawa ma maganar a rada zata fito hakan yasa ya yanke hukunci kawai ya since Mata idanu kila Allah ya kawo masa agaji.
Mugun nauyi hannunsa ya masa ji yake ko biro bazai iya rikewa ba amma a haka ya ja gyalen nata Wanda hakan yasa idan sa fadawa kan kirjinta da mugun sauri ya rufe ido daidai lokacin hawaye suka sauko mai kuma shima baisan na menene ba.
Mutuniyar ma tana ganin sa tasha jinin jikin ta. A second daya tana kyafta ido yakai sau 10. Baki na bari tace yyyyy...yya...ya ah..Ahmad? Bude ido yayi suna hada ido wani Abu ya soke ta.
A zuciyar sa addu'a daya yake iya yi Wanda banda ita ba abinda ya tuna
"أعوذ بكلمات الله التامة من شر ما خلق"
"a'uzu bi kalmatil lahi tammatin min sharri ma kala'ka"
MU HADE A CHAPTER NA GABA IN AKAYI RUWAN COMMENTS DA VOTES NAYI UPDATE DA WURI NAJI SHIRU KUMA KUJI SHIRU😁
TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO
Miss untichlobanty 💕
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top