CHAPTER 52
Zaro wayan sa yayi a aljihu yana shirin bude sakon kawai yaji mutum a jikin sa tana fadin gashi kaima kana kauda kai yayin da tasa hannu take juyo da fuskan sa domin ta kalle sa.
Kamar an jona masa transformer haka ya ji wani gumi ya karyo masa yayinda mutuniyar kuwa ta tsaya kallon sa tana fadin yaya Ahmad kaga na FISA gaskiya ko?
Ganin dai ya tsaya cak yasa itama ta tsaya tana kallonsa yayin da take kyakkayfta ido yar karamar kwakwalwar ta na tunanin ko lafiyan sa? Shi kuwa bai masa tana magana ba kawai Zane fulani ta dake gefen bakin ta yake kalla.
Tace ya Ahmad kaga na fisa gaskiya ba bakina baya wari ko? Bakin sa na rawa in ya bude ya rufe in ya bude ya rufe hakan yasa yace um. Ta cikin daga murya tace kaji ko mijin yar kauye bakina baya wari.
Cire hula m. Ahmad yayi da hannu yana Mata alamar tayi shiru yayin da yake fifita Dan numfashin sa dake dauke masa, bai taba sanin yana da asthma ba sai yau, bayida asthman de amma yaji yadda masu asthma suke ji. Murya na rawa yace Mata jummai,
Kallon sa tayi tana wangale masa baki yace jummai tace iye? Yace kar ki dinga... ya zan miki bayani ne? Kinsan me ake nufi da muharrami? Ta girgiza kai a ranshi yace salisu kana da aiki sai ka sakata makaranta.
Yace toh zan fadawa mijinki ya miki bayani, turo baki tayi tace ah ah ni kai zaka fada min yace mijin ki de ni gida zan tafi. Rike hannunshi tayi tana jijjiga tana Dan tsalle a dabara ya janye hannunsa tare da mikewa domin tafiya Dan yaga alamu ko magana bazai samu daman yi da mijin nata ba in ya tsaya sai ta sa ya sabwa Allah.
Daga samun lafiya sai ta wani zo tana latsa sa dukda ya lura cewa batasan ba daidai takeyi ba. Hakan yasa ya hade rai Tace zan fashe maka da kuka fa ince ma yaya salisu bakason ka koyawa matar sa karatu tsaki yaja yace karki dinga zuwa jikin maza kinji ? Sannan ki dinga rufe jikin ki in kina gaban namiji idan ba haka ba Allah wuta zai saka kj.
Zaro ido tayi tace amma ai mando kanina namiji ne, yace banda kanin ki yana kaiwa nan tayi sauri ya fice saboda yadda gaba daya hannun riganta ya zame Wanda bata damu ta gyara ba ga tsalle da ta tsaya take masa bai taimakawa lamarin ba.
Yana fita ya sauke ajiya zuciya yana jinjina kai yace a ransa yace gidan nan ba gidan zuwana bane har sai matar nan tayi hankali. Amma kuma wani bangare na ransa yayi wasai ko ba komai yanzu yasan ya Sami lafiya.
Bayan ya shiga motan sa har ya five a gidan ne ya Kira m. Salis yace masa ga matar sa nan ya Mata fada shima ya Dana Mata nasiha sannan ya sakata a makaranta bai jira mai m. Salis din zaice ba ya kashe wayar sa.
Jummalo na shigowa daki m. Salis ya Mata murmushi yake tayi masa da sauri ta zaro hijabin ta ta zabga ta nemi waje ta dake. Kallonta yayi yace kin huce ? ni dama ban dau fushi ba kawai naga kana zagi na ne Dan kaga banida wayo banje makaranta ba.
Yace yanzu dai kin hakura ko? Tace eh yace toh ya kika zauna a nesa? Bata kulashi ba tashi yayi ya matso kusa da ita ta matsa ya matso ta matsa har ya tsargu tashi yayi ya shiga ban daki ya shinshina jikin sa yaji dai baya wari ya kalli kansa madubi komai normal.
Batasan ya fito ba sai ki tayi yazo ya rungume ta ta baya yace haba matar salisu fishin ya isa mana. Tsalle tayi ta fita da gudu kamar me aljanu tana fadin kar ka tabani.
Haka suka dinga kewaye gidan wai bazai tabata ba. Shidai yace yaga ta kansa da wannan Mata sai kace annoba?
Har dare ma tace ya jira ta a daki da ta hada abincin sai taje ta kwankwade dakin sa ta sanar dashi sannan ta shige nata. Bayan ya gama ci ne ya shiga dakin ta lokacin tana wanka fitowanta daure da zani gashin hamtanan nan suna fadin excuse me taga mutum yayi tsam Alan gado komawa tayi da sauri tana leko kai tace ya salis me kake nema?
Yace sai ina neman Abu ne zan shigo dakin matata? Tace toh nide ka juya zan hito na sa tufafi ba musu ya juya ta fito tare da zura dogon Riga. Juyowa yayi bayan ta bashi dama yace jumy wai me ya sameki ne? Ni, ni na kasa gane kanki tunda aka miki fada shikenan ko kinada aljanu ne?
Dafe kirji tayi tace Allah ya rabani da segun nan aljani wai, no banida wani aljani me ka gani yace toh AI naga sai gudu na kike yi. Tace ba fa gudun ka nake ba nasiha ne ya amadu yayi min cewa in dinga rufe jikina kuma in daina zuwa kusa da maza sai muharramai na.
Yace toh AI gaskiya ya fada miki nu ma AI muahrramin ki ne. Tace um um ni mando kawai yace min banda shi ku ba muharrami na bane, m. Salis yace ya Ahmad din ne ya fada miki hakan? Tace Itoh hide haka na fashinta(fahimta).
Tana kaiwa nan kuwa ta bude kofa ta tura sa ta Dane gado sai bacci. Zuwa asuba ta rataya kafafu a kallon gadon m. Salis kuwa yana shiga dakin sa ya Kira m. Ahmad yace ka janyo min matsala brother ka ware wani ka daura wani.
M. Ahmad yace me ya faru? M. Salis yace gobe ka dawo kawai Dan Allah gobe ka dawo da sauran rina a kaba. M. Ahmad yace Allah bani zuwan gidan nan.
Salis yace Please brother Ahmad yace ba inda zani fa yana kaiwa nan ya kashe wayar yana sauke ajiyan zuciya. Kiran m. Salis din da ya kara shigowa wayan sa ne ya tsinka masa zuciya har sanda gaban sa ya fadi.
Kin dauka yayi m. Salis ji yake kamar ya mutu ya rasa inda zaisa kansa. Hakan yasa wata dabara ta fado masa ya yanke shawarar TV zai dinga kunna jummalo ta dinga kallon American films hakannan tunda su ba kunya suke da ita ba sai kuma ya sa m. Ahmad yace Mata ta dinga yi ma m. Salis din duk abinda ta gani a film.
Da wannan shawarar yayi bacci kansa na Sara masa saboda ciwon kan da ta basa.
............
Bangaren su lud kuwa yau shopping da yawon shakatawa yakai marakisiyya bayan ya dawo saide kuma ya rasa game kanta Dan kamar mayya batada aiki sai cin masara da naman kaza nace Ayya you don't know what is going on😂
Shida da rabi na yamma a hanya ta musu lokacin gari ya fara duhu taga wani me balangu yadda ta riko hannun lud har sanda gaban sa ya fadi yace menene ya faru cikin murya kamar zata fashe da kuka tace balangu!🥺
Ajiyan zuciya ya sauke yace haba baby yanzu yadda kika sa nayi birki da na daki motan wani fa? Har kin tsinka min zuciya tace toh yi hakuri zaka siya min balsn gun? Yace kina ta kashe min kudi na yaushe yaushe na bude.... sai kuma yayi shiru tace ka bude me?
Riko hannun ta yayi yace kinga boutique dinnan da muka je? Daga kai tayi yace nawa nesting da ya wuce na bude dama surprise naso na miki in mun koma gida yanda daga na fada miki sai ki bani balangu.
Tace au haka fa toh baka siya mana balangu ba ta yaya ni zan baka,yace ba wannan balangun make nufi ba, race toh wanne? Yace kawo kunnenki.
A hankali yayi Mata rada Wanda tsabar girman maganar sanda ta rufe baki tace na shiga uku ni karka koyamin tambada. Da rashin kunya nan ya dinga tsokanan ta suna dariya suka siya balangun suka tafi.
Saide me bayan sun fara ci ne suka lura akwai tsutsa a ciki marakisiyya ce ta gane da yake dukda dubun motan taji tafiyan Abu a hannun ta. Tana haskawa taga tsutsa take ta shararo amai tsikan jikin ta ya fara tashi Allah ya taimaka shna saitin chemist.
Maganin tsutsa ya siya ya bata a take ta sha shima ya sha Dan ya ci guda daya Wanda dakyar ya samu ta tsamma sa a hakan ma tana korafin ya cije ta.
Reverse lud yayi a ba tare da bata lokaci ba sai tungan me balangu. Gefe ya ja shi ya nuna masa yace menene wanna? Saboda shi lud yaso suyi magana asiri a rufe yayi masa nasiha da nuni cewa abin da yake yi zalinci ne.
Sannan yasa shi ya zubda naman yau gaba daya kar ya siyar ya bada wani abun ma saboda ya rage asara. Saboda shi mai laifi in ya tuba sai a taimaka masa wajen gyara kuskuren sa.
Amma me mutumin nan ya rufe ido yace Sam Sam shi ba tsutsa a naman sa shekara 4 hudu kenan yana sana'ar nan ba musu lid ya matso gaban tukuban mutanae da sukayi layi sunzo siya ya dauko wayar sa ya haska wake yace kowa ya matso AI kuwa yana haskawa wata tsutsa na kwana kwana tana lakwashewa jin an haska ta yasa tace hello tare da tsayawa tana kallon mutane😂
Nan fa akayi wa mutumin ca daga karshe yasha duka Dan lud shi gaba yayi abinsa yana shiga motan yaga marakis tana sose sose yace menene? Tace ina da alaji (allergy) ma abin Khan kyami ta fadi hakan bakin ta na rawa.
Fita yayi ya kewaya ta bangaren ta ya bude kofa ya fito da ita gare da wanke aman da ke jikin kayan ta da yake ta tsallake motan su yake hakan yasa hayaniyar da ake na tittinnikan me balangu be dame su ba.
Baya ya bude ya saka ta a ciki shima ya kewayo ya shiga bayan tare sa ware labulen motan sa irin bakin nan na jikin glass sanna ya kunna haske gaba daya fatar ta tayi ja ja wur domin kuwa marakis ta fishi haske.
Kuka ta fara masa tare da kiransa da sunan da take tsokanan sa har yabi bakin ta wato ustazu. Tace ustazuuuu😭 jikina kaikayi ka Sosa min.
Fara Sosa Mata yayi tace mu cire Riga na shiga uku na. Kamin kace me marakis ta dawo daga ita sai lingerie dinga kawai, daga ta janyo kaza sai ta janyo kaza tana sose sose. Lud da yaga abin da gaske ne ya zare belt dinsa ya saka wajen karfe ya Sosa Mata jikin nata har ta bashi tausayi.
Lokacin da abin ya lafa kuwa kwantawa tayi a jikin sa Wanda a yanzu bashida Riga kuma in zaka kashe sa baisan yadda akayi rigan ta bar jikin sa ba saide ya yi karya. Jin kamar tayi bacci yasa tsaya da sosawan.
Kama hannunshi tayi ta gurza alamun yaci gaba da sosawa har dariya taso ta bashi yanda ta larme kamar jaririya. A hankali yace baby? Tace ummm? Yace mu tafi gida ko? Ta girgiza kai hakan yasa yaci gaba da Sosa Mata bayan nata har tayi bacci kamin ya kwantar a hankali ya nufi hanyar gida yana yiwa mai balangu Allah ya isa Dan shi ba haka yaso ba.
Washe gari......
CHAPTER NA GABA ZAI FASHE FA DAN ZAFI NE GARESHI, GA CITTA HARDA KANIMFARI😂
NAJI RUWAN COMMENTS DA VOTES SANNAN AYI SHARING KO KUMA NA FASA YIN ME SWEET.
TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO
Miss untichlobanty 💕
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top