CHAPTER 51

Da tsawa tace baka isa ba kamin ta fashe da kuka tana mai fadin ka siyo min gasasshiyar masara. Dariya yayi yace na 'ki din mai hakwaran masara😂

Tace ni ba hakwaran masara bane da ni kuma sai na fadawa umma na abinda kamin. Yace kice bakyason ki ci masara tace toh yi hakuri ka siyo min masaran kaji pleaaase! Yace zanyi tunani.

Jifan sa tayi da gajeran wandonsa dake hannunta. Da sauri ya rufe kofar yana dariya. Yauma kamar kullum ya hadu da wanna receptionist din suka gaggaisa ya bata kudi yace a kula masa da madam duk abinda take so a bata.

.......

Washe gari m. Salis ya fito ya samu jummalo tana ta kokarin dafa dankalin hausa wato sweet potatoes. M.salis yace matar ba gaisuwa ne? Ta sharesa. Dama ya lura tun jiya take sharesa in ba ya zama dole ba bata kulawa shi kuma ya gama nazarin sa bai ma San me yayi ba.

A ransa yace Allah gani gareka nikam na kasa gane Mata kuma inajin har na mutu bazan gane su ba, bansan de ko Dan ita yar kauye bane yasa take caja min kwakwalwa. Gaskiya ne da ake cewa aure sai hakuri kar nayi zuciya naki yi Mata magana abin ya koma gaba.

Matsowa yayi ya dafa kafadan ta yace matar magana fa nake tace Ayya abinka da yar kauye AI ban iya gaisuwa ba. Yace yaushe nace....? Sai kuma ya tuna da tunanin da yayi kila ya subuce masa ya fito ne ta ji me yace.

Yace Ayya uwar gidan salisu baki gane bane fa ni ba haka nake nufi ba... race kuma bana son na gane. Da kofar kitchen din ya jingina yana kallon ta ga yadda hannun braziyar ta suka baiyane yayi magana tace ya zageta gara ya bari in ta huce ya gyara Mata.

Sallaman m. Ahmad yasa m. Salis amsawa yana mai fitowa daga kitchen din tare da mika masa hannu. M. Ahmad yace ya na ganka haka baka shirya ba ? Au na mance ashe angwanci ake sha baza'a je makaranta ba. Abin yayi wa dalibai dadi.

M. Ahmad ya fadi hakan cike da tsokana murmushi m. Salis din yayi m. Ahmad ya kara da amarya ma ganin wanka fa irin wannan shadda haka da kasha ga kamshi da ke tashi. Allah dai ya bada zaman lafiya. M. Salis yace uhm ameen.

Da shike m. Ahmad din babba ne hankali ya fara jika shi hakan yasa ya fahimci akwai matsala. Yace kodai akwai matsala ne? M. Salis yace babu wata matsala yana juyawa Dan ya shiga daki.

Riko hannunsa m. Ahmad yayi yace haba bro bama boye boye AI kuma ba wani Abu da bai dace ka fada.kin na tamabaya ba. Kaga in da matsala ku warware tun da wuri daga tarewa har an fara da uhm? Ni shi yasa banso ka auri yar kauye ba amma ganin kamar tana da tarbiyya yasa na bada gari.

M. Salis zama yayi a hannun kujeran da m m. Ahmad ke zaune yace yaya Mata na da muguwar matsala muma muna da shi amma nasu yafi namu wallahi, ni fa ban ma San me nayi ba amma matar nan ko kallon inda nake batayi kuma ni yanzu na tamabaya ma ace nayi sabon laifi.

M.ahamd yace toh bari in tambaya ma. Shigowqn ta parlourn yasa dukan su biyu kaman masu jin tsoron ta suka gyara zama suma gyara zaman shaddodin da suka saka. Kamar surukar su ce ta shigo shi m. Ahmad kar ta raina shi kuma m.salis kar tace yayi wani abun.

Kallon m. Ahmad tayi tace sannu kamar bai ji ta ba ya dauke kai tabe baki tayi taci gaba da jera abincin da ta dafa. Ba tare da ta kalle su ba tace mijin yar kauye kaje ka shirya ka tafi makaranta kar daliban la yan birni suyi kewan ka.

Bude baki yayi zaiyi magana tace banson ji. Sum sum kamar danta ya tashi yana kallon m. Ahmad irin ka gani ko? M. Ahmad kamar baisan me ke faruwa ba ya tsare yaci gaba da daura idanun sa akan talabijin dukda baya gane me ke wakana a ciki ba ma.

M. Salis kuwa zama yayi a gado ma ya ciro wayar sa a aljihu ya fara buga "mortal combat" a ranshi yana fadin babban yaya na zaiyi maganin ki. Yadda yayi maganar har sanda na murmushi kamar wani yaro irin anci zalin sa ya Kira babban yayansan nan.

M. Ahmad kuwa yadda yaga tana kara hade rai yasa yace ke? Dagowa tayi yace jummai ko? Ta kara cin magani yace zo, sauna ina da magana da ke.

Zuwa tayi ta zauna yace me ya hadaki da Dan uwa na salisu kike ta har hade masa rai ke haka ake wa miji? Sai kuma yace zai kara aure nan zaki bugi kirji kice bai isa ba, me kika rage shi da shi ko?

Kananu tayi da ido yadda fulani ke yi in zasu yi masifa tace eh lalle ma, wato si  wannan mijin nawa kara ya kai maka bayan si ne bashi da gaskiya ko?... hannu m. Ahmad ya daga Mata yace ni ba banbami nace kiyi min ki cika min kunne ba.

Nace me ya miki in bashida gaskiya sai nayi masa magana ba ku tsaya kuna share juna kamar yara ba. Tashi yayi ta tsaya tace kaima sawun kafar nashi zakabi AI ba sai ka fada ba nasan kun girman shi yasa zaku ci zalina. Ta karashe maganan tana bare masa baki.

Jin kukan ta yasa m. Salis fadin Allah ya kara yar banza dama ba cewa take na zageta ba ta hadu da daidai da ita indai bazata daina min abinda take min ba kuka ta dinga yi Dan dole ayi Mata fada saboda ta gyara hali.

Jummalo kuwa cike da turo baki tace yanzu da safen nan  ba cemin yayi yar kauye ba wato irin yana da dalibai wayaiyu ko? M. Ahmad yace shi ya dada miki haka ? Tace da kunnena na ji shi kasa kasa yake magana ya dauka bazan ji ba.

M. Ahmad yace amma AI tun jiya kike kin kulasa tace jiya ne fa da yamma bayan ka sauke sa ina basa labarin garin mu kawai yasa hular sa ya rufe fuskan sa yayi bacci.

M. Ahmad yace ai bayaso yace miki bayason yaji labarin ne jiya ya gaji sosai  shiyasa. Tace ba wani nan kawai de yana nufin ina warin baki ne Dan banayin bayush (brush)  sai asiwaki.

Yace me bayush kuma? Tace kar ka canja zance ni bakina baya wari Allah baki na baya wari ta fada tana bubbuga kafa.

Dafe kai yayi Yace ni nace bakin ki yana wari ne? Ya za'ayi na sani ni da ban taba shinshina ba? Matsowa tayi tana fadin kaji fa.yayin sa take bude baki daidai lokacin m. Salis ya turo masa message.

Zaro wayan sa yayi a aljihu yana shirin bude sakon kawai yaji mutum a jikin sa tana fadin gashi kaima kana kauda kai yayin da tasa hannu take juyo da fuskan sa domin ta kalle sa.

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

Miss untichlobanty 💕

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top