CHAPTER 49
Da sallamar su suka shigo BILKISU kawar maman Dan musa ne tayi musu iso kamin ta shiga ciki ta sanar da su jummalo. Fitowa sukayi da ita suka zauna m. Ahmad ne ya fara magana da innalhamdu lillah. Gaban ta ne ya fadi da ras.
Nasiha da duk wani Abu da ma'aurata ke bukata m. Ahmad yayi musu kamin ya Mike yana me kallon agogon dake sakale a hannun sa Wanda gashi ke kwance yace toh saida safin ku Allah ya bada zaman lafiya.
Maman Dan Musa ya kalla yace auntyn mu ga abincin ku a Kan dining table. Ita dai ta amsa da toh ne bawai Dan ta gane ko ta san menene dining table din ba.
Bayan ya fita ne su bilkisun suka nemi wajen kwanciyan su. Ango da amarya ma suka nufi nasu daki kamar yadda m. Salis yayi tunani. Domin da ya nufi hanyar daki ya dauka jummalon ta biyo shi.
Ha'a ya shiga daki ya juyo yaga wayam, sai yayi tunanin ko Wanda suka kawota wayaiyu be sun Dan yi Mata bayani ita kuma ta fahimta a baibai ta tafi dauko plate. Murmushi yayi yace a cici abin da ke ranta kenan.
Wasa wasa minti har 8 amma mutuniyar ku bata iso ba. Tashi yayi ya fita bayan ya ajiye hulansa da babban Riga gaban madubi, amma me? Sai ya ganta zaune inda ya barta.
Gefen ta yaje yana tunanin toh ko bacci ne ya kwasheta tun kamin sanda m. Ahmad me musu nasiha? Amma yana kiran sunan ta ta amsa da na'am. Yace na dauka bacci kike yi AI naga baki shigo ciki ba.
Tace ka fadi min ne ?ni da hiska ta ke cikin tsumma ta ina zan gani?yace gyale de ko? Tace koma wanne ne mu tahi saida safe sai yaga ta kama hanyar dakin da su ummu musa suke.
Yace ina kuma zaki? Tace bacci nikeji. Yace AI ga hanyar dakin mu. Tace dakin mu? Au haka fa ahe in anyi aure daki daya ake kwana. Mancewa nayi imin uziri.
Murmushi kawai yayi a ransa yana fadin AI tun ba yau ba nayi miki uziri. Bayan sun shiga daki sukayi sallah tare da cin duk abinda zasu ci. Banso my zurfafa dominn ko jummalo Sam nuna wa tayi bata San inda m. Salis ya nufa ba domin ita Sam banda rike hannu toh ko anyi aure ba abinda aka halatta sauran iskanci ne.
Ita kuma bata shirya mai garin su yasa ayi Mata bulala ayirin (20)ba kamar yadda sukeyi bisa dukan garin su ba wai bin Shari'a ba. Abinda bata sani ba shima m. Salis din bawai wani tsiyar zai Mata ba Dan ba narkewa ya gama yi ba yana dai son ya dinga rabarta ne Dan ya Saba.
Abin haushin ma ashe al'ada takeyi ta dinga basa ciwon kai Dan sanda akayi kusan minti 30 ana Abu daya. Daga karshe ya bata hakuri ya hau kujera yayi kwanciyar sa yana shawara shin ya fadawa m. Ahmad ko kuwa ya zama namiji kuma mai gida ya dinga samar wa kansa maslaha?
A haka har bacci yayi awon gaba da shi dukda ko yana jin jummalo dake watsa amaro tana juye juyen ta a Kan gado.
Washe gari ko da ya tashi ya samu tayi wargaje wargaje a kan gado gashi duk tayi staining wajen hakan yasa bai tashe ta sallah ba ya fice yana tunanin wato da ta fada masa tana al'ada gara ta nuna bata San komai ba.
Bayan ya dawo daga sallah ya dauko paper zai Mata rubutu akan kar su dafa komai dafe kai yayi tunowa da bata iya rubutu ba ma yace kai ina da aiki fa. Haka ya fice yana mai mika daganan ajiyan gidan sa hannun Allah.
Kar kamin ya dawo a kone masa ita😂. Bai ma yi nisa ba ya hango motan m. Ahmad hakan yasa shima ya juya suka dawo gidan tare.
Gaisawa sukayi m. Ahmad yace ango ango ango mijin amarya an tashi lafiya? Murmushi m.salis din ya yi yace Alhamdulillah! yana mai yiwa m.ahmad din iso zuwa cikin gidan.
M.ahmad yace wai ya naga da sanyi safiya ka fito ? M.salis yace wallahi abin Karin kumallo zan Nemo nasan yan kauye da tashin safiya. m.Ahmad gashi har mama ta hada muku kaga kun huta ma kenan saide ba nauyi fa shayi da bread ne sai kwai but tace karfe tara zan kawo muku gwaten wake.
Cikin fara'a m. Salis yace gaskiya muna godiya bari ma na bika Muje nayi Mata godi......kamin ya rufe bakinsa sai ga mutuniyar wato jummalo ta fito tana sose sose. Ba tare da ta kallesu ba tace wai ina zaka da sanyi sahiyan nan?
M.salis yace gidan mu zani,wuce su tayi zuwa kofar da zai kaita farfajiyan gidan tana leke leke. M. Ahmad yace ke wai baki iya gaida mutane bane? Kin fito ba Dankwali a kanki bayan sarai kinji muryar da ba ta mijin ki ba?
Har ya karashe zancensa bata juyo ba saide ta dena leke leken da takeyi fuskarta yayi ja a take. Tabbas tasan ba mijin ta bane kadai a gidan amma bata dauka m.ahmad bane.
Juyowa tayi tana kumbure kumbure tace barka da sahiya. Da gudu tazo ta rike hannun m. Salis cikin shashancin tace wai nikam so kake ka kahe mu ne? Ni banga rijiya ko tuka tuka a gidan nan ba da mi zamuyi wanka? Jiya ma da badan akwai ruwa cikin bokataye ba da hikenan bazamuyi alwala ba.
Shi kuma ruwan da ke cikin randar bahida yawa bai wuce Kofi daya ba. Kuma nasan duk hyawarar wannan yayan naka ne ko hiya wata(pure /sachet water) ai ka kawo mu hya.
M. Salis da tsikar jikin sa ke tashi tunda ta rikoshi yace muje kitchen in nuna miki. A Kitchen din ya nuna Mata bottle water da yadda ake budewa. Ya nuna Mata fridge da aikin sa.
Fitowa sukayi ya nuna Mata yadda ake aiki da su famfo Dan bai yi kama da normal famfo ba da yake akwai su control din shower amma yadda ake kunnan famfo kawai ya nuna Mata.
Dan abubuwa masu muhimmanci duk ya nuna Mata sannan yace shikenan an yafe min? Tace sosai ma kuwa ni na tahi yin wanka domin tsafta gareni. Tana kaiwa nan ta saki hannunshi ta shige daki yayinda m. Ahmad dake zaune yana kallon ikon Allah ya saki murmushin da bai ma San yayi ba yana tabe baki.
Koda m.salis ya karaso wajen sa m. Ahmad yace gaskiya kana da kokari ba kadan ba kuma kana da hakuri. M.salis yace toh ya aka iya zata gane AI komai Dan lokaci ne. Haka suka fita suna hira su m.Ahmad bai tambayi m. Salis yadda ma ta kaya a daren jiya ba Dan yasan ansar tunda yaga jikin ta.
TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO
Miss untichlobanty 💕
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top