CHAPTER 44
M. Ahmad yace kai salis karfa kaje ka fara so na daga neman magani in ba haka ba heart break ne ajalin ka yana kaiwa nan ya kwanta abin sa.
Da sauri m. Salis din ya bisa gadon yana fadin brother tsaya mana nifa ba irin wannan nake nufi ba ina nufin irin kaunar da uwa ke wa danta ne fa. Ya fadi hakan yana jijjiga hannun m. Ahmad din.
Murmushi m. Ahmad din yayi yace za ma kayi bayani ne wuce ka kwanta mutum har yana da iyali ga gemu amma bai girma ba. Rungume hannun m. Ahmad din yayi a kirjin sa yace inde a gaban yayana ne toh ko yaye ni ba ayi ba suka kyalkyale da dariya.
Karo na farko da m. Salis din yaga fara'a m. Ahmad din sosai ba wai murmushi ba. Zare hannun sa m. Ahmad din yayi yana dariya tare da fadin kai sake ni kamin mabruka ko suhaila ta ke ta kaini police station.
M. Salis yace yanzu kuma da matata za'a dinga kafa min hujja? M. Ahmad yace zancen kakeso ni sake min hannu bacci nake ji.
.....
Jummalo kuwa nasiha maman dan musa tayi ta Mata tayin sa take fada Mata yanzu kam dole ta girma ta dena shiririta.
Sannan suka yanke shawarar yadda zasu fara gyaran jiki da kuma inda zasu Nemo kayan daki. Jummalo tace ni banison ayi min wani gyaran jiki. Umman musa tace AI tunda kinyi aure gyara jiki ba ranan dainawa.
AI shiririta ne irin na Mata ayi gyaran jiki ma amarya dafa nan baza'a sake ba sai ta haihu ko za'ayi Mata kishiya. In anyi sa'a ne a samu masu kara yi sanda suka bushi iska.
Wasu gani suke daga sunyi haihuwa 1,2,3 toh shikenan sunyi expire. Wallahi kin cuci kanki. Toshe kunne jummalo tayi tace na ji, na ji, na ji har nayi shekara 50 San dinga gyaran jiki.
Ni bacci nake ji ma saida safe tayi sauri ta rufe kanta da bargo ummu Dan musa tace kanki ake ji. Yar kaniyar yarinya. Da gaban innar taki ne ai yanzu kina can kina wanki kamar jaka.
Tasan cewa gaskiya ne hakan yasa tayi kwanciyar ta kamar me bacci bayan taji alamun ummu Dan musan ta fita ne. Ta tashi ta zauna tare da hade kai da guiwa.
Tunowa ta yi da lokacin da mahaifiyar ta ke da rai tana halin jinyana ajali lokacin tama da shekaru 4 ne a duniya.
Wanda alokacin inna bata fito da halin ta karara ba amma kuma a hakan take AI ka ta yin kiwi yayin da ake barin mahaifiyar nata ba ci ba sha ko kallon inda dakin ta yake ba'ayi sai ranan litinin da juma'a.
Lokacin ne ake gyara Mata daki da jiki saboda kawu musa yana kawo Mata ziyara. Toh a ranan da mahaifiyar ta rasu ne da kwana daya kawu musa yace a bashi jummalo.
Nan fa inna ta rufe ido ta yaga masa rigan mutun ci ta nuna ko duniya zata nade bazata bada ba. Kai ka dauka Dan tamason yarinyar ne saboda yadda take zakewa AI yar mijin ta ne wa ya mutu wa ya tashi.
Rikici yaya rikici har sanda aka je wajen mai gari anan ne yace toh shikenan ita ta rike yarinyar amma in an tashi aurar da ita kawu musa ne zai bada ga Wanda yaso.
Taso tayi jayaiya amma aka danneta Dan dole ta hakura.
Ita kuwa jummalo haka zata fito bata ma San yadda zatayi da sanayen ba.
Wani matashi mai suna Bello shi ke taimaka Mata ya hada da nasa sunayen yayi kiwon suna hira tare in ta tashi tafiya sai ya bata nata.
A kwana a tashi har jummalo ta fara sonsa ba tare da ta sani ba haka dai shima ta kasan ce a nashi barin har dai takai ga ya fada Mata watanni 8 da suka wuce kenan.
Shida Bello ganin mutane dayawa na neman auren ta yasa ya fada Mata dukda cewa inna na yi mata sharri da kazafi iri iri wani lokacin har cewa Dan mai gari tayi AI jummalo maiya ce.
Amma da shike bellon Hasan wacece jummalon hakan yasa ya fada Mata sakon zuciyar sa. Bayan ya sanar da iyayen sa ne suka amince aka je wajen inna sai cewa tayi AI jummalo mai farar kafa ce.
Mahaifin sa basu yarda ba saboda sum San halin innan sarai AI kuwa bayan sati daya innan tasa bakin maciji ya tsare sa har lahira Wanda akan idon mahaifiyar sa hakan ya faru.
Take itama zuciyan ta ya buga domin kuwa da daya tilo gare ta kuma gashi akan idonta maciji ya sare sa.
Kuka kam jummalo ta yi shi nan inna ke cika baki tana fadin ba na fada ba anki a saurare ni gashinan daga cewa zai aure ta ya rasa rayuwar sa.
Baban Bello bai yadda da zancen innan ba domin kuwa bellon yana bashi labarin duk katobarar da ake kullawa a garin hakan yasa kawai ya kwashi kayansa ya fantsama duniya yana mai yin Allah ya isa indai har kashe masa Dan sa akayi da gangan.
Nan fa duk masu son jummala kowa yaja da baya su karatun ma da ke samu lokaci zuwa lokaci ana tayawa kafa ya dauke musu sai dag bayan nan ne kamar wata 3 da suka wuce suka samu samarin.
Saide kash basusan samarin ba aure ya kawo su ba kawai sunzo ne ayi ashararancin Wanda suke nunawa su karatun AI hakan wayewa ne. AI hakan yan birni ke yi.
Su kuma da shike sha aka tafi ne biski ne a cikin kwakwalwar su sai suka bada hadin kai har ma suna ganin sunfi jummalo yin sa'an miji saide kash basusan me ke kasa ba.
Face majina jummalon tayi a karo na 6 saga fara tunanin ta yayin da tace Allah ya ji kan ka Bello na Allah yayi maka Rahma.
A haka har bacci ya kwashe ta a zaune tana rike da hotan Bello wanda ya bata ne sanda ya fara zuwa birni ya dauki hotan har ma yayi Mata alkawari zasuyi hoto tare in sunyi aure.
..........
Washe gari da safe kuwa mutanen ku oga lud da marakisiyya an shirya. Zai fita yace toh baby ni zan wuce, a jinyace tace kaga ni banason kace min tsumburbura na kawai.
Kumatun ta yaja yace Allah my tsumburbura kice sunan yana miki sugar toh ai shikenansai na da wo. Ko shirya zamu je mu gaida su umma ko? Tace toh babu damuwa.
Bayan ya fita da minti kamar 30 haka marakisiyya na kwance taji anyi knocking tace kai yayi saurin dawowa ma ko an fasa karatun ne oho.
Bude kofar tayi taga ba kowa hakan yasa ta leka akace surprise! Da karfi har sanda zuciyan ta ya tsinke mansura ne da beeba hannun su rike da flower.
Mika Mata sukayi suna kallon cikin ta beeba tace ya haka? Mansura tace me kika gani. Beeba tace naga kin murmure amma ba tumbi. Mansura tace beeba ya kike Abu kamar kinzo daga primary kin taba ganin inda karamin ciki ya nuna ne?
Mika Mata flower din sukayi tace ke ni ku rike abun ku bana wani son kwaikwayon malam bafuren nan na banza da wif gashi duk sun lalata mana rayuwa kowa yana kokari ya kwaikwayi rayuwar su ne.
Sabon Allah kamar cin gyada a daba a bu ne ami saukin yi , in kuma an jarabce mu sunfi kowa katan bakin yin korafi da zage zage. A dinga daurewa Wanda bashida laifi laifin. Allah de ya kyauta.
Mansura tace kuma fa mutuniyar magana ki dutse Allah ya yafe mana na baya ya kuma tsare mu daga aikata na gaba. Beeba tace wannan haka yake ke kinsan gara ke ma kina neman tsari daga ba gaba amma mutane in anyi magana ki lura fadi suke "uhmm toh Allah ya yafe mana wato zasu maimata kenan "
Marakisiyya tace ni ba wannan ba mansura akwai wani jarida da nake so ki sayar min fa. Beeba tace wato dam yar zagaye kuke yi min?
AYI HAKURI NAYI LATTIN UPDATE NA RUBUTA YA GOGE KUMA WALLAHI ALLAH NA MANTA MA ME NA RUBUTA AMMA DOLE NA CIKA ALKAWARI DAN HAKA GASHINAN NA BAKU.
AFWAN, TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO
Miss untichlobanty 💕
20th September,2020.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top