CHAPTER 4
DAN ALLAH KARKU MANTA DA FOLLOWING DINA SECOND BIYAR KACAL ZAI DAUKA.
Finciko ta yayi har sanda tayi Tuntube yace zo nan Dan......ki DAGA MOTAR UBAN WA KIKA SAUKO? Warce hannunta tayi tace sakeni kazamin banza kawai toh daga gidan ubanka na taho idan ba iskanci da neman magana ba na taba tuhumar rayuwanka?
Falla Mata wani wawan Mari yayi Wanda yasa gyalen abayanta faduwa Yace okay nagane wato dama can kema yar hannu ce zuwa kike ana tsokale ki shine zaki wani fake kamar na Allah kullum kina cikin sa manyan riguna Lamar buhu kuma farare sai kace likkafani. Yana kaiwa nan ya zuke kara daya na sigari a zuka daya sannan ya hura Mata yana kara sakwa sakwa da belt din wandonsa Wanda ya sake bawa bakin gajeran wandonsa baiyana.
Yatsine fuska tayi tana tari ga hawaye idonta yayi jaa kamar wata mayyar kura tace Allah ya isa na banza mugu dakiki mara lissafi lud wato da ka saki matarka bai isheka ba shine ni kakeso ka kassara ni da hayakin nan kakeso ka rabani da kyan fuskanna ko? Toh ka kasheni ka huta mana. Yace with pleasure ma kuwa shakota zaiyi ta hango motan daddynsu da sauri ta dauki gyalenta tasa saboda akwai driver dinsa Wanda yake ba muharramin ta ba ta ruga da gudu kamar mahaukaciya.
Tun kamin ya fito a motar ta fada jikinsa tana masa kuka tana nuna lud ba karamin tsorata yayi ba ganin shafin hannu kwance a fuskarta a wani zabura ya fito rike da hannunta har cogen dake kafarta yana neman kadata yazo gaban lud ya tsaya. Ido cikin ido yake kallonsa har lud din yaji wani iri ya kauda nasa yace dad Allah ko me tace ma karya take zagi na tahau yi shiyasa na... na mareta.
Mu hadu a parlour na shine kawai abinda dad ya fada masa tare da shigewa ciki sanda ya Dan dauki lokaci Dan bai taba ganin ran mahaifin nasu ya baci haka ba hasali ma idan umma tana fada daddy ke kare masa.
Ciki ya nufa yana zazzare ido Dan ba wasu addu'an arziki ya iya ba balle yayi ta. Idan yayi ma babu anfanin yinta domin bakin masu halin sa baya cikin bakin Wanda Allah ke Ansar addu'an su.
Bude kofan yayi yana fadi excuse amma kamin ya ida zancen yaji ras! Dafewa yayi ya kalli Wanda ta mareshi yana fadin momm.... kamin ya karashe yaji an dad'o masa wani sanda yaja numfashi take idonshi suka canja kala jijiyar kanshi da wuyansa suka Mike domin kuwa ko tsawa daddyn sa bai taba masa ba.
Tas! tas!! Yaji kananun hannuwanta sun falla masa Mari ai sai yayi kukan kura ya shakota. Fincikesa mommy ke kokarin yi amma ya rufe ido yana makure wuyar yar uwan tasa har ya dangana da garu.
Umma kuwa ganin yaki sakin wuyan yasa ya ta kama karamar yatsansa Zara murde jin zafi yasa ya hankade ba tare da ya kalle ta ba. Faduwa tayi ta bige kafanta da center table Karan da ta Dan saka ma baisa ya bar marakisiyya ba sanda daddy yace kai lud sake yarinyar nan ko in tsine maka!
Ai yadda kasan walkiya haka ya saketa hula daddy ya cire yana huci yace kalli mahaifiyar ka! Sai lokacin ya lura da umma da gudu ya tsuguna gabanta yana fadin mummy kiyi hakuri wallahi bansan na tureki ba ma gaba daya raina ya baci ne ya za'ayi yarinyar nan ta mareni?
Marakisiyya dake zaune daba a kasa ido zuru zuru tana tari tace wallahi...ni... ni ba yarinya bace tunda ko yau akayi min aure sai in haifi da mai katan kan da yafi naka. Daddy yace toh Dan..... ki fito da miji tunda auren kikeso wai ku yarannan wasu irin mayu ne yaya haka ne? Jarabar tayi yawa tasowa yayi ya kamo matarsa ya zaunar a kujera yana fadin hajiya sannu kinji sannu yana shafa bayanta kamar yadda ake wa yara.
Wani kallo ya watsa ma lud yace tunba kai ba munafukin yaro kawai toh bari kaji daga yau anyi an gama ince soyaiyar da nake nuna ma yasa kake abinda kakeso? Dan kaga kai daya ne namiji ko? Toh na Sami labarin abinda kayi dazu yanzu kai bakaji kunya ba cikin gidanka akwai Mata biyu da basu fita idda ba shine zaka saki wannan su zama uku? Kasa da wata uku kayi aure 3?
Kawai saide kayi aure da ka biya bukatarta sai ka saka ka dawo gidannan da zama toh an gama wannan! Komawa gidanka zakayi ka duba cikinsu wacce ta maka ka miyar da ita dakinta. Karka dauka bansan me kakeyi ba. Zaka aureus ka saka su kuma idonsa ya bude sai ka koma kana binsu ko? Toh AI an kare wannan.
A zabure lud ke kallon dad dinsa yace daddy ni kayi min hakuri amma babu wacce nakeso a cikin su suma sun sani kwadayi ne ya kawosu ba komai ba wallahi. Dad yace kai ka sani ko ka fito min da Mata nan da jibi ko na nemi duk wacce tamin asa muku Rana cikin kankanin lokaci ayi auren kuma babu saki.
Rungumo kafar daddyn NASA yayi ya kwantar da kansa a cinyarsa yace daddy AI duk laifin mommy ne take cewa sai na sakesu. Tace ba dole ba AI karka ga laifi na ni nan nasan me nakeji yo duk yaran nan da kake aura ko wacce yadda kasan kaza haka take komawa kafa duk a bankare shine zaka wani ce min ni nake sawa ka sakesu.
Ni wannan jaraba taka ba kanta toh ko mahaifinka... sa sauri daddy ya toshe Mata baki Dan zuwa yanzu bacin rai yana neman yasa ta Saki layi. Itama fahimtar haka yasa tayi shiru tare da kama hannun mijin nata ta sauke daga bakinta.
Bandakin parlour ya shige suka ga ya fito fuska da hannu a jike. Shelve wato ma'adanan takaddu ya nufa yana neme neme yakai minti 10 kamin ya dauko MUWADDA IMAM MALIK ya zo ya zauna kamar mutumin arziki.
Yace umma menene wannan? Cike da mamaki tace littafin imam Malik ne. Jinjina kai yayi yace masa Allah toh Allah yayi masa rahama dan ya kyauta ya rubuta mana alkur'ani ya kyauta ba kadan ba gsky.
Dukda yanayin da ake ciki hakan bai hana marakisiyya fashewa da dariya ba tace oh Ilimi manya ga mutumin dake ce min ya fini ilimi amma ko MUWADDA na babban malamin fiqhu da hadith imam Malik bn Anas na karni 711-795 bai sani sani ba toh wannan littafin dake hannunka hadisai guda 1720 ne a cikin ta sai ka koma ka dauko Qur'anin.
Tsaki yayi yace ban lura bane ina sauri ya Mike tare da komawa gaban shelve din ya laluma ya laluma ya dauko SUNAN IBN MAJAH zai dawo tace ba sai ka iso ba bashi bane. Sosa kai yayi Yace kai inajin ya kamata na soma saka glass fa.
Ita dai tagumi tayi tana murmushin mugunta yayinda nadama ya lalube dad umma kuwa takaici ke damunta kamar ta makure lud ta kashe ace mutum ko al Qur'an baisan kamar sa ba?
Shi kuwa dauko wa yake marakisiyya na mayar dashi sanda ya dauko MUSNAD BN AHMAD na imam Ahmad bn hambal tace bashi bane SUNAN ABU DAWOOD ya dauko SUNAN ALSUGHRA tace bashi bane ya dauko daya daga cikin ALMUSTADRAK ALA ASSAHIHAIN.
Yace finally gashinan gidan nan akwai son Allah tayi dariya harda rike ciki saboda haka suke volume biyar ne tace babban malamin bashi bane fa wannan littafin al hakim al naisha puri ne.
Ya dauko SUNAN AL-DARIMI(addarimi) ta girgiza kai tace wannan na Abu Abdullah bn abdurrahman al darimi ne sai yama daina daukowa kawai nuna Mata yake da yatsa ya nuna Mata daya daga cikin KUTUBU SITTA, ta tsaya kallonsa Wanda ke nuna mai bashi bane gyara zanzaron wandonsa yayi ya tsaya akan kafa daya Dan ya fara gajiya ya nuna Mata FATAHUL BARI,RIYADUSSALIHIN,SAHIH MUSLIM,JAMI'ATI TIRMUDHI,MINHAJ TALIMIN, RISALA tace kai na gaji don Allah kai kaje ban garen hadisai da fiqh kayi kekam kuma dai nayi imani da Allah bakasan ko daya ba kuma bakada ko daya.
Yace toh dalla in zaki fadawa mutane wannene ki fada wasu takardun dake nan ko ma'ana babu. Tace kul ka iya bakinka karka barota da karfi kodan banyi mamaki ba Dan nasan da wadannan gara tandin shisha a wajenka. Toh a can sama littafin dake hannun damanka zaka na farko sannan akwai wani a layin kasa ma amma yanzu dauko wancan din. Fatan kanada tsarki ko? Yace Dan u**rki ba akan idonki nayi alwala ba?
Marakisiyya tace uwata kuma UWARKA ba?
TOH FA KAI JAMA'A ANA WATA GA WATA ABIN YADAU ZAFI BA KANTA.
KAI AMMA I AM DISAPPOINTED IN LUD YABAN KUNYA DAYAWA WALLAHI TOH WAI YA ZA'A KAYA NE KUMA ME YASA LUD KE NEMAN ALQUR'AN?
INA JIRAN COMMENTS DINKU TARE DA VOTES DINKU.
TAKUCE KARAMARSU BABBARSU KARAMARSU BABBARSU WATO
Miss untichlobanty 💕
23rd July,2020.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top