CHAPTER 36

KAMIN KU FARA KARATU DAN ALLAH GA WANI ABU DA ZAMUYI.

KIYI TAGGING MUTANE BIYAR A COMMENT SECTION NI KUMA ZAN BAKI KYAUTAN CHAPTER DAYA. DUK WACCE TAYI HAKA ZAN BATA.

AYI KARATU LAFIYA

Tace ka fadi duka abinda zaka fada kuma kayi duk abinda zakayi bazaka min wayo ba babu inda zanje.

Daurata yayi a Kan gado yace toh bari kiga ikon Allah yana Jan bargo tace wai dama da gaske kake?.....

washe gari da safe lid ne ya fara tashi saboda hasken rana da ya dale masa ido   agogon hannunsa da ya ajiye a Kan side drawer ya janyo ya duba yaga 12:08 na rana.

Komawa tayi ya kwanta tare da sauke ajiyan zuciya Dan basuyi bacci ba sai da suka yi asuba Wanda shi ya fara yi ya dawo ya kwanta kamin marakis tayi hakan yasa basu hadu ba.

Dan ko da yace zai taimaka Mata da hannu kawai ta masa alamun bata so hakan yasa ya kasa gane shin farin ciki take ko bakin ciki amma yanzu ganin ta kwance jikin shi ya tabbatar masa da cewa bata jin haushin sa.

Rufe idonsa yayi dukda bayi da niyan komawa bacci haka zalika bayida niyar tashi.  Wajen bayan minti Goma marakis ta fara juyi kadan ya bude idonsa a ransa yace toh an fara kenan.

Da sauri ta tashi tazauna a tsorace saboda mafarkin da tayi ta ganta a bandaki tana shirin tsulawa.

Wani mugun yawu ta hadiye har sanda lud ya ji karan sa amma baice Mata komai ba abinsa ya ci gaba da kallonta.

A hankali ta laluma kasa bata ji jika ba hakan yasa ta sauke ajiyan zuciya tashi tayi ta shiga toilet din. Yayin da lud kuwa yana nazar tar ne yaga yanayin nata Dan abin da ya Mata bai tsammaci zata iya mikewa ba amma ta bashi mamaki yanzun Dan bai ganta a tsaye ba da asuban.

Kallonta yayi yaga tafiyan ta bai canja ba amma tana Dan yin gogo in tana tafiya. Bayankamar minto biyar ta fito da alamu har brush tayi kallonsa yaga tayi hakan yasa ya rufe idonsa baki daya Dan dama lumshe su ya yi.

Zuwa tayi ta zauna a side bed drower na bangaren sa bayan ta matsar da agogon sa. Da fari da yaga ta dago hannu tsakaninshi da Allah ya tsammaci duka zata kai masa ta tashe sa amma kawai sai yaga tasa hannu a suman dake kansa.

Jingina tayi da ginin yayinda take nazarin shin batayi kuskure ba da ta bada kai yanzu? Tunda bawai ya gama shiryawa bane karfa aje a Sami matsala ta haifi da lud kuma ya koma tasha Abu ya kwabe Mata.

Toh idan kuma ya sauke kai ne Dan kawai ya samu wannan abin kuma yanzu ya samu sai su koma gidan jiya kenan.

Wani Abu ne yace Mata toh ke me kike damun kanki ? Na farko de ba wai zunubi kikayi ba. Mijin ki ne kuma kema AI sauki zaki samawa kanki atleast ba zaki kashe kudin siyan magani kina wahalar da kanki ba.

Wani bangare na zuciyar ta ya sake ce Mata toh yanzu in lud ya tashi ya shusshuka Mata rashin mutunci ya zatayi? Tun kamin wannan ya faru bari ta taimaki kanta koda na karshe ne.

Da dayan hannunta tasa yatsa tana shafa hancin sa kamin ta saki murmushi matsowa tayi da fuskar ta kusa da nashi saura kiris.... kawai taga yayi murmushi.

Bude baki da hanci da ido tayi tace kan kut... dama idon ka biyu. Da gira ya Mata sigina yace ya kika fa sa?  Juyawa tayi da sauri ta kalli gefe tace me na fasa ? Dama wannan zan goge ma.

Taba bakin nasa yayi yace me zaki goge min? Tace uhm miya na gani au ina nufin shayi. Kai wai shayi custard ne. Wata bazawarar dariya yayi yace toh AI banci komai ba ma yanzu na tashi ko ruwa bansha ba.

Tace oh ina jin ido na ne bai gani ba. Tashi ya yi ya zauna tare da sauko da kafansa kasa yace kin tashi lafiya ? Daga kai ta yi yace toh kalleni mana ko dodo na zama? Ko daga jiya kuma har kin tsorata kin sare ne?

Turo baki tayi cike da in ina tace ni nace ma banason na kalleka ne? Kawai wuya na ke ciwo in na kalli gefen. Yace okay.

Mikewa ya yi ya kewayo ta inda fuskanta yake da sauri ta juya yace ha'a ba kince yana ciwo ba? Tace yanzu nan ne yake min. Kewaya wa yayi ya koma dayan gefen ta juya. 
Zama yayi abinshi yace toh hado mana Shayi ko hannun ma yana ciwo?

Da sauri ta bar gefensa taje ta hada shayin kawowa tayi ta ajiye da sauri ya riko hannunta. Janye wa tayi ya matse ta a jikin sa tare da kamo habar ta.

Kallon kasa tayi yace kikace ba kin kallona kike ba tace ni ka barni. Murmushi yayi ya lashi saman hancin ta yace ko de kin fara soyaiya ne?

Da sauri ta Mike tace wa ? Ni? Allah ya kiyaye bana sonka cabdi! Mikewa yayi yana kewaya ta yayinda yake Sosa gemunsa irin alamun tunanin nan 🤔 yace hmm toh ni yaushe nace kina so na?

Cewa fa nayi ko kin fara soyaiya ne? Tace toh na ji ni dai yanzu zo muje ki bani shayin nasha. Tace sai kace wani yaro? Wuce muje kamin na maka tsimagiya. Ta fadi hakan tana kara hade rai irin da ya bata wa mahaifiyar sa rai dinnan.

Kai kofin shayin tayi kusa da bakinsa ya kurba ya fesar tare da sake yar siririyar kara alamun shayin ya kona sa. Da sauri ta ajiye ta kalleshi tace ya kona ka ne?

Murmushi yayi yace iye ashe kin samu da ni? Tace kan bala'i dama wai da gangan kayi shine yanzu zaka sakani goge goge? Tace ni ban damu da kai ba kawai tausayin ka naji kar harshen ka ya Kona baka gama koyan al Qur'an ka koyi ma'anar sa ba.

Kasan kai din zaka yi kyau in ka zama malami. Yace da gaske? Tace oho ban sanin ba. Dauki shayin ka kasha kamin nayi fushi wallahi.

Tashi tayi domin ta gyara wajen sai hura hanci take ita a dole ranta ya baci. Shi kuwa maganar da ta fada masa yasa ya tuno da lokacin da sailuba ta taba ce masa sweetheart da kai malami ne kyau zakayi irin gemun nan da ka ajiye.

Wani kallo ya aika Mata wanda tana gani tasan zasu hau su sauko ne yace ke wace irin yar shegiya ce? Dan kin gama rainani ki dube ni da kyau saboda ki zubar min da aji shine zaki wani ce da ni malami zanyi kyau?

Falla Mata Mari ya yi yace Dan u.....ki nine zan zama malamin?nace nine.. nine zan zama malamin? Shegiya kawai na miki kama da Dan kauye? Toh bari kiji ko da wasa in na zama malami sai naci uw.......ki.

Ajiyan zuciya ya ajiye a ranshi yace hmm yanzu kuwa tunda marakis ta fadi haka indai Allah ya yarje min sai na zama malami.

Iskan da ya ji an hura masa a fuska yasa yace na'am tace wani tashar la tafi kuma ni ka kawo min abinci yunwa nake ji. Yace muyi order din take away?

Ta Dan turo baki kamin tace toh kayi yace yauwa mai sona cike da tsokana hade gira tayi tace ni wai yaushe nace ina son ka? Dan Allah ni tashi ka saka rigan ka.

Yace I see da tun da wuri kice jikina yana saki a wani yanayi toh dauko min t shirt din da ya miki.

Daukowa tayi tana juyowa taga mutum a bayanta. Janyota jikin sa yayi yace tun dazu ana cewa ba'a so na sai hura hanci ake amma bakin ki ya kasa dena murmushi.

Tace ba murmushi nake ba duk bayan wata bibbiyu nake yin ciwon baki sai aga kamar ina murmushi. Yace iko sai Allah kowa da yaji zancen nan yasan da gyara a zancen naki. Kinga duk sauran jikin ki sun iya karya har bakin ki amma gashi nan dai lips dinki sun kasa yi. Ko shin Dan suna yi ma nawa biyaiya ne🤔?

Bai tsammata ba ya ji tace zo nan nayi maganin ka tare hade.....su

A SUBURBUDO MIN COMMENTS FA EHE

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

Miss untichlobanty 💕

7th September,2020.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top