CHAPTER 35

Kallon ta kawai yayi ya girgiza kai kamin ya kamo hannun ta da hannunsa daya yace ko wani lokaci ki kasance cikin farinciki kinji murmushi tayi.

Juya Mata gefen kumatun sa yayi ya nuna Mata da yatsa tace me yace kin gane ai. Make kafada tayi yace please yana turo baki yadda take yi. Peck tayi masa tace toh ya ranka? Yace wasai in fada miki.

Suka fashe da dariya 😂 koda suka isa kallon ta ya yi ya ce muje ko? Fita sukayi hannu sakale da na juna suka shiga lokacin har an fara event nan aka zo aka kwace masa ita akayi gaba da ita haka aka dinga yi Mata congratulations na auren ta yayin da shima hakan ne ta kasance a wajen nasa.

Aminiyar amarya mai suna humaira ce ta hango sa daga masa hannu tayi shima ya daga Mata saboda ya Santa. Karasowa inda yake tayi tace idon ka kenan ango?

Gyara zaman hulansa yayi yace gamunan fa hajiya humaira dama kina duniya? Ta ce ina nan fa cabdi an Dade ba'a hadu ba. Ya ce gaskiya kam. Tace tunda kukayi graduating kuka barmu shikenan sai shamsiya ke fada min kayi aure.

Murmushi ya yi Dan bayaso a ja zance saboda yasan humairan tana son sa a da toh baisan ko ta hakura ba. Wani waiter tayi ma alamu da hannu yazo su ka dauki champagne.

Suna sha take cewa wai ina amaryar taka ne gajiya marakis jiya AI sai hawa da sauka take ko hira bamu samu munyi ba wauwaigawa yayi bai ganta ba yace ban ganta ba Dan muna shigowa badawiyya tazo ta janye ta. Matsowa kusa humaira tayi tace wallahi ka rike matar ka kyam ina fada ma Dan samun irinta sai an tona.

Kaga da ina sonka kuma ina sa ran wata rana zaka so ni. Amma inajin ance ka auri marakis na cire rai baki daya Dan nasan ta fini da komai. Dariya yayi yace toh AI tunda kin hakura shikenan.

.....

Tun sanda aka janye ta take ta raba idanu. Abu kadan sai ta dago kai ta kalli lud dake cikin abokan sa suna dariya sai tayi murmushi.

Wani dagowa da tayi sai taga sun watse da ido taci gaba da neman sa badawiyya ta zungure ta tace madam ayi hakuri nana awa nawa ne zaki sake Jonewa fa.

Hararar ta marakisiyya tayi tace ance miki shi nake nema ne? Dariya badawiyya tayi tace nace miki shi nake nufi ne nima? Kinga kin toni asirin kanki.

Dakuwa marakis din tayi Mata ta na shirin yin magana idonta ya fada kan lud Wanda ke dagawa humaira hannu. Ita dama can humairan bata wani kwanta Mata ba dukda basusan juna sosai ba.

Cigaba da kallon su tayi tana tafarfasa har badawiyya ta lura tace marakis kwantar da hankalinki ba wai soyaiya suke yi ba da dai ta soshi amma yanzu ta hakura.

Love you too din da lud ya fada ranan ne ya fado Mata a kai bata San sanda taje gabanshi ba ta wulla masa samoan dake hannunta tcike da malakar hawaye tace na tsane ka sannan ta fice da gudu.

Mikewa yayi da sauri humaira tace luma!  Kallonta yayi tace in alaina ne muje na fada Mata gaskiya. Girgiza kai yayi yace barshi karki damu kila wani abin aka fada Mata.

Bin ta yayi amma yaga wayam bata nan kiran umma tayi a waya bata dauka ba Dan haka ta nufi can gidan. Koda yaje umman ma bata nan kawai ya zauna hira da daddy yayinda yake ta tsimayin ta kawo karansa amma yaji dif.

Har 10 haman yasa yayi sallama da daddy ya koma hotel room din AI kuwa yana shiga ya ganta a gaban madubi ta buga tagumi. Yace tsumburbura?  Tace jar ka sake Kira na.

Yace wai me aka yi miki ne miye hakan? Tace baka ma San me aka yi min ba ko? Toh wai ni me na maka? Me na maka da zaka dinga bin wasu Mata a waje kana zubar min da mutunci kana nuna ni ban kai ba? Bude baki yayi yace banason jin duk abinda zaka fada.

Baka ji kunyar ido na ba a gaba na kake cewa wata kana sonta ko? Baka San duk chatting din da kakeyi da daddare ina sane ba? Ko ance ma bansan inda kake zuwa da safe ba?

Kamo rigansa tayi tace me kakeso? Nace mame kakeso? Bazaka iya hakuri har mu rabu ba ne ko yaya da zaka je kana bunsuran ci Akan titi? Warce rigansa yayi yace ke marakisiyya ya isa nace miki ya isa haka!

Wani damka yayi Mata idanunsa sukayi kananu yace me kike nufi nace miki me kike nufi? Ke har kin isa ki sakani a gaba kice zaki tuhume ni? Wa ne ke ? Ina ruwanki da abun da nake yi?

Ko da ace ma wata nake bi AI bazai dame ki ba dukda ni bana bi saide a biyoni. Ba yau kika fara gani ko sanin wannan ba. Idan ma ina tare da wata ina ruwanki ? Ince kince baki so na toh miye naki kuma idan wata tace tanaso? Kince ko mai irin halina yace yana sonki kaskantar dake ne toh yanzu kuma me ya faru?

Hannu yasa a aljihu ya zaro wayarsa yayinda ya hankadata ta manny da gini yace da kike cewa ina chatting din dare sai ki duba kiga me nakeyi a waya na. Da wani bakinki harda cewa kinsan ida nake zuwa da safe Qur'ani ake koyamin yanzu nayi rabi izu ta kasa.

Ko ba ke kika ce a dinga kyautata zato ba?yanzu me kika aikata? Turo baki tayi ta rungumeshi tace kayi hakuri sannan ta sakesa.

Wani cida mai karfi tare da tsawa akayi bata San sanda ta dalesa ba tare da nade kafafun ta a kunkumin sa ba. Tsikan jikinsa ne ya tashi amma ya matse yace matsoraciya kawai ni sauka ki fadamin addu'an da akeyi idan anyi tsawa.

Make kafada tayi yace bazan sauko ba yace kul fa. Dariya tayi tace :

"ﺳُﺒْـﺤﺎﻥَ ﺍﻟّﺬﻱ ﻳُﺴَﺒِّـﺢُ ﺍﻟـﺮَّﻋْﺪُ ﺑِﺤَﻤْـﺪِﻩِ، ﻭَﺍﻟﻤﻼﺋِﻜـﺔُ ﻣِﻦْ ﺧﻴـﻔَﺘﻪ"

"Subhanal lazi yusabbihur ra'adu bi hamdihi, wal mala'ikatu min kifatih."

Ake cewa yace Dan sake maimata min mamaita masa tayi yace zaki fadamin ma'anar sa anjima tare da irin mijin da kikace kikeso. Kinyi min alkawari ranan nan amma kika fara shareni wai ashe kishi ne ma.

Tace ni ba kishin da nake yi. Yace toh munji yanzu dai sauka daga jiki na tace oh oh naki din. Pecking lips din yayi yace in baki sauka ba fa.... tace ka fadi duka abinda zaka fada kuma kayi duk abinda zakayi bazaka min wayo ba babu inda zanje.

Daurata yayi a Kan gado yace toh bari kiga ikon Allah yana Jan bargo tace wai dama da gaske kake?.....

washe gari da safe.......

KAR KU MANTA KU SUBURBUDO MIN COMMENTS INSHA ALLAH ANJIMA ZAN KARA UPDATE DAYA SANNAN ZANYI REPLYING DUKA COMMENTS

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

Miss untichlobanty 💕

6th September,2020

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top