CHAPTER 33


*Not edited*

Turo baki tayi ta daura hannunsa a cikin ta tace yunwa nake ji mai gida. Yace yanzu zan Nemo abin ci uwar gida . Suka tun tsire da dariya a tare.

Bye bye yayi Mata tare da juyawa sannan ya tafi da guduma murmushi dauke a fuskar sa.
Receptionist da ke hada kayan ta tace barka da sake fitowa yallabai Luma ganin bai kula ta ba yasa tace yallabai lafiya kake zuba murmushi haka?

Kode madam ne? Sosa kai yayi yace kai kede kin fiya gulma hannu yasa a aljihu ya danka Mata 2k har kasa taje tace godiya nake Alhaji luma Allah ya barka da aunty amarya ya tsokale idon makiya.

Cike da fara'a yace ameen na gode  da addu'a ni zan fita. Tace toh sai mun ganka oga. Ficewa yayi abinsa domin ya siyo wa marakis dinsa nama.

A daki kuwa komawa ciki marakisiyya tayi tana girgiza kai tare da mamakin yadda lud ya canja cikin kankanin lokaci.

Wayan ta ne yayi ringing ganin sunan mansura yasa ta dauka ba tare da bata lokaci ba. Mansura tace hello amar su ta ango. Tsaki marakisiyya tayi tace nifa matsala ta da ke kenan wallahi wai kawai sai mutum ya kara wayan sa a kunne sai ki wani ranbatsa masa hello ko yar sallamar nan baza kiyi ba?

Mansura tace afwan amarya tsabar dadin naji muryarki yasa ma na mance toh assalam alaiki ya kike ya ogan naki? Marakis tace uhmm wa'alaiki assalam oga na kalau yake ya ma tafi siyo min gas meat ne. Ta fadi hakan cike da tsokana.

Mansura tace Allah shegiya kice abin yazo ashe ma ba sai na karo ba AI dama nake cewa Wanda na baki kwana 3 zaiyi gara mu karo ko na wata amma naga bashi da anfani ma.

Marakis tace ke uwaki kaji min yar iska ai Wanda kika banin nan ma kwana biyu zai min kinsan ni ba irin sauran mutane bace ai dole na sha dayawa idan ba haka ba za'a Sami matsala amma yanzu kinga ko taba ni yayi ina iya rike kaina.

Mansura tace toh AI shikenan ni miye nawa tunda dai kin bani kudin ba ruwa na in kinga dama kisha in kinga dama kar ki sha amma in ta nine wallahi gara kar ki sha toh ke da mijin ki me zaki wani takura kanki kawai in yazo miki ki mika kai.

Marakis tace ke ni ina mamaki ma in fada miki bai ma nuna yana wani bukata ba kodai da gaske yake matan NASA ne dai ragwaye? Mansura tace ko kuma yana neman wasu a waje ba kin dai San halin. Ki fa dage ki dawo da hankalin mijin ki kanki ehe.

Wani Abu ne taji ya soki zuciyar ta amma ta danne tace ke mansy baby bari nayi wanka zamuyi maga na anjima. Nan suka yi sallama cilli da wayan marakis tayi tace Dan iska har na fara tausaya masa no wonder naga bai wani damu ba ashe de ashe de.

Ya kamata nasan me nake yi Dan wallahi kar na bari ya kawo min raini ya taba wasu kaji a waje sannan ya dawo nima yace zai mukurshe tunda ni dama bawai shirin kare rayuwa ta nake dashi ba.

Gararin ma ya kwaso ma infection ya jona min ala kakai. Nasan zaman da zamuyi ma. Haka ta dinga tafka da warware har ya dawo da fara'arsa yace my tsumburbura ga naman ki fa kinga har yogurt ma na siyo miki.

In bude miki? Girgiza kai tayi yace tashi muyi kallo toh kinga ba'ason mara lafiya ya dinga yawan kwanciya tashi kinji. Shirun da ya ji tayi yasa yace wai menene? Ko jikin ne? Ya kai hannunsa I zuwa goshin ta tare da tabawa Dan matsawa tayi hakan yasa ya rabu da ita kawai ya ajiye Mata a gefe yace ki ci kar ya huce.

A kujera ya zauna ya ci nasa abin sa yana kallon TV har wajen takwas tana kwance bayan ya gama kallon wrestling ya Mike ya shiga ban daki yayi wanka ya fice abinsa ya tafi gym.

Bayan ya dawo still juaya kwanciya kawai tayi amma ko kallon inda laidan yake bata yi ba. Zuwa yayi ya zauna a gefen ta yace tsumburbura wai me aka miki ne? Tace kamar ya me aka min babu aka min mana kawai na gaji ne.

Dariya yayi yace ji bakin ta toh me kikayi ma da zaki gaji? Ko de kinaso ne. Tabe baki tayi tace ni me zanyi da shi ba wani abinda nake so ka kyaleni Dan Allah.

Yace bazan kyaleki ba har sai kinci abinci tace na koshi. Daura hannu yayi acikin ta yace kamar yaya kin koshi bayan dazu dazun nan kika dinga marairaicewa kina ce min yunwa kike ji kode bakin ne yazo yasa kike samun wannan sauyin yanayin?

Girgiza kai tayi tace ba ko daya tare da sauke hannunsa daga maranta jin ya fara Dan mammatsawa. Kamo hannunta yayi ya finciko ta ta zauna. Ya ce please na yi miki wani Abu ne kinsan ba mutun ci bane dani ko Dan kinga ina lallaba li saboda umma shine zakiyi min taurin kai?

Tace ni Dan Allah ka barni nace maka bana jin yunwa in da inaji da zanci AI. Cikin ta ne yayi kara kurrr! Saboda dama tun dazu take hadiye yawu Dan yadda kamshin ke dukan hancin ta.

Dariya ke son kama lud amma ya tsare yana kallon tare da daga gira alamun shi kuma karan na menene? Tace ciki na ne kawai ya rude tare da bashi baya wani sautin ne ya kara fita Wanda da kaji kasan ba shakka yunwa ce.

Dariya ya fara yi Mata yace madam dalla tashi ki ci abinci ba wai ki tsaya kina yi min fulako ba. Cike da borin kunya ta janyo AI kuwa ta cinye komai tas ta shanye yana kallon ta yayinda yaci gaba da press up dinsa.

.......

Haka zama yaji gaba ba shiri kuma ba fada sannan duk sanda lud ya fita gaban marakisiyya faduwa yake a haka har sukayi kwana hudu. Yau da la'asar marakis na zaune tana chatting yayinda take sanar da mansura cewa ta karo Mata maganin kuma ta siyo da yawa wannan karan.

Bata tura ba sanadin lud da ya shigo. Sannu da dawowa tace ya gyada Mata kai sanadin wayar da yake yi.

Ruwa ta dauko ta kawo masa tana ganin yadda yake ta wani fara'a kamin yace kar ki damu duk abinda kike so zan siya miki ai. Shiru yayi can yace kede bari har na jiyo dadin sa tun daga nan in fada miki.

Shiru yayi yayinda ta ajiye ruwan tana ji kamar ta falla masa Mari. Can yace yauwa good girl Dina miss you too sai kinzo mu wuni muna yawo abin mu. Bye sanna ya kashe wayar.

Kallon yadda marakisiyya tayi abasa wa  tawalla yayi yace yace wai madam me matsalar ki kullum fuska a murtuke sai kace shaniya kinsan Allah in na murtuke nawa zaki sani ne.

Murmushi tayi tace ba komai kawai de yau dinne nake ji nan wani iri. Tana kaiwa nan ta bashi waje sanadin wani Kira da ya shigo wayar ta.

KAR A MANTA ANTAYO DA COMMENTS FA. VOTES DIN NAN MA PLS AYI SHI.

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

Miss untichlobanty 💕

4th September,2020.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top