CHAPTER 31
Yace mami ki dai yi nazari shiru tayi can ta dago wani hope ne yazo masa kawai sai ta girgiza kai. Take ya ji nauyi a zuciyar sa tare da sauke ajiyan zuciya tace amma dai akwai wani allura da akace za'ayi maka sanda na haifeka.
Gyara zama yayi yace ko an sanar dake allura ta mecece? Tace ah ah gaskiya ni ba'a sanar min da komai ba. Domin ni a tunani na ko allurar kara lafiya ce da ake yi. Kasan lokacin ba kowa ke yarda yaje asibiti ba ma.
Nide da shike baba na Dan boko ne shiyasa ko a lokacin ma aka kaini saboda tun a lokacin kamar yadda ka sani mun rabu da mahaifin ka.
Mikewa m..salis yayi zai fita m. Ahmad ya rike hannunshi yace ka zauna mana. AI ba komai Dan kaji kar ka damu.
Murmushi m. Salis din yayi yace bari dai na Baku fili zaku fi sake wa. Murmushi kawai m. Ahmad din ya mayar masa kamin ya maida hankalin sa ga mahaifiyar ta sa.
Bayan m. Salis ya basu guri ne tace nikam Ahmad na tambaye ka mana. Ya ce ina jin ki ummi na ! Ta ce fatan dai baka karya min alkawarin da kayi ba dai ko? Yace wanne kenan ummi Dan alkawarin dake tsakanina da ke ai yawa garesu.
Tace wannan yaron nake magana naga kamar jiya a gidan nan ya kwana kuma naga kun Jone sosai Wanda nasan ko abokai ba ka da shi balle har kayi amini.
Murmushi kawai ya yi yace karki damu ban karya miki alkawari ba kuma banida niyan karyawa kawai de jinin mu ya hadu ne tun da yanzu kuma rayuwa ta kawo mu wuri guda.
Tace toh AI shikensn Allah dai ya tsare ya ce ameen ummi kyakkyawa. Dariya tayi tace kai de baka rabuwa da tsokana ta ko sai kace wani kakar ka? Murmushi yayi ya Mike yace AI gaskiya nake fadi ummi kina da kyau ne.
Tace toh a dai nemomin yar kyakkyawan sirika nima naga yan jikoki na yace karki Sami damuwa tashi yayi ya shige daki yayinda taci gaba da cin apple din ta.
......
Umma zaune a gefen daddy tana yi masa tausa tace oh Alhaji naga fa ka wani Mike tsam da kai daga ganin yaran nan ko? Dama jinyar ashe ba ta gaskiya bace so kake anyita hada maka shayi kawai ko? Taba kanta yayi yana Dan dariya yace toh in Mata ta tayi ta hada min shayi AI ba laifi bane ko laifi ne?
Tace ah ah saide ma nayi ta kwashe lada nayi maka dubara. Yace a ina kikayi min dabara ? AI tare muke kwasa saboda alkalimatud daiyiba sadakah, toh kin gani kina min aiki ina yi miki kalamai da d'ada' mash zaki cakwai cakwai kuma kinga hakan na karanta miki kinga lada biyu kenan.
Tace oh kaide wannan mijin nawa ba dai wayo ba wato abin hakane ko? toh AI kuwa nima zan koyi kalaman nan kaga shikenan ina maka aiki ina kalamai sai na fiki lada? Yace AI ni ina ciyar dake kinga nima ina da nawa tace uhm kaida kake kwace abincinka a gado.
Dariya yayi yace lallai matar nan AI da kin fadi kanki tsaye baki tsaya kina kwana kwana ba. Zo toh ki ga wani Abu toh.
.......
Sai bayan magrib marakisiyya ta bude ido tare taga mutumin anyi Dane Dane an wani kan kame ta kamar ance zata gudu.
Shiru tayi tana nazarin m. Ahmad da yadda ya kwantar Mata karya duk Dan kar ya aure ta toh gashi yanzu Allah ya kakaba Mata wannan mutumin oga lud bata ma San inda zata saka shi ba.
Ganin yadda ya hada fuska yana baccin ya lafta Mata kansa a cikin ta yasa ta tuna da wani lokaci tun tana secondary school lokacin da suka rubuta junior WAEC ta shigo parlour da gudu tana ihun ta bada labari wa umma.
A parlour ta tarar da shi ya hakimce kwance a kujera ya daura hannu akan goshi idonsa rufe karasowa kusa da shi tayi dukda tana tsoron kar ya shuka Mata rashin mutunci irin Wanda ya Saba shuka mata.
Riko kramin yatsan hannunsa Wanda ke cike da zobuna tayi a hankali a kunnensa tace ya lud yau na gama rubuta junior WAEC yanzu nima zan zama yar SS 1 jin shiru bai kulata ba yasa ta saki wani Dan iskan murmushi da kaga idon ta kasan tsiya zatayi.
Daukan remote tayi ta kashe ball din da yake kallo da gudu ta haura sama tayi cilli da jakan ta tun akan Benin kamin ta shiga daki nan ma akayi wulli da hijab dama sandal tun a parlour aka yi cilli da shi.
Sai gata kamar ana hankado ta ta sauko da wani yar jaka karama a hannun ta. Budewa tayi ta dauko powder ta shafa masa a fuskar nan yayi fari fat. Ta dauko Jan baki ta shafa harda yi masa wani gira daya ta kalli gabas daya ta kalli yamma.
Su barbada kumatu aka shafa masa kamin ta ce yauwa. Since ribbon din kanta tayi ta daura masa a gashin sa ta tsakiyar kai yayi da tayi masa kitso guda biyu da robali.
Ita duk a tunaninta bacci yake yi yayin da shi ko luf yayi yana jinta sanda ya bari ta karkare tsaf ta Sami wuri ta zauna tayi wani mahaukaciya kwalliyar ta kundai San adon yan da.
Yana kallon ta da ido daya bayan ta gama ta haura sama ta ajiye ta dauko camera din daddy ta sauko tazo ta saita ya dinga yin wasu mahaukata pose dinta ta sauke hannun nasa harda su ja masa kumatu.
Ganin yanda ya turbune fuska ne yaki dariya yasa tace Allah kasa ya yi mafarkin abinda zaisa yayi murmushi ni kam ban taba ganin murmushin sa ba tunda aka haife ni.
Ita sawa tayi ranta kamar irin yaro Dan shekara 1 ne a gaban ta hakan yasa tayi masa peck a kumatu taje ta saita camera ta dawo. Daga hannu tayi kamar wata shashasha tace Allah ka taimaka min yaya na ko murmushi yayi a baccin nan ya Allah ka Dan tausayawa yar marakisiyyan nan.
Ace yayi mafarkin wani tsoho ya taho kiki kiki a keken sa kawai yayi ar Kabo ya hantsila cikin kwalbati.
Ga mamakinta sai taga yayi murmushi AI kuwa camera yayi kicif ya dauka.
Cikin jin dadi ta Mike ta dauki camera zata haura sama kawai taji ance KE ZO NAN DAN UB....KI!
TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO
Miss untichlobanty 💕
1st September,2020.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top