CHAPTER 3
DAN ALLAH KARKU MANTA DA FOLLOWING DINA SECOND BIYAR KACAL ZAI DAUKA.
In ya kalli kofa sai ya sake kallon wajen yana nuna kofa da yatsa yama rasa abincewa ganin tsayuwa ba zai fisheshi ba yasa ya fita yana nazari wai ko kwakwalwar sa ta Sami matsala ne Dan shi dama can yasan tunaninsa baibai ne cikin aljabi yace in ba kuskure nake ba sha'awa ke damun marakisiyya toh amma nawa ko me?
Kai Ahmad bakada hankali ! Toh amma me yayi zafi da iyayenta bazasuyi Mata aure ba abinta? Tunda karatun ma shekara daya ya rage ta karashe a gidan miji mana me yasa suke kokarin kashe yarsu da hannunsu? Ba tabbata dai ba mijin aure ta rasa ba.
Shiga motan nasa yayi, ms marina zata shiga yace miss madeena ina kuma zaki shiga tace ciki mana raka ku zanyi yace no mun gode ga jakarki yana kaiwa nan yaja motarsa ya nufi asibitin makaranta.
Suna zuwa kuwa aka tabbatar masa da zargin sa Jim yayi yace toh yanzu ya za'ayi kenan dr? Likitan tace mun duba student information dinta batada aure amma sir idan kasan family dinta ka sanar dasu a gaggauta yi Mata aure Dan mace ce mai tsananin bukata fiye da tunanin ka. Ga maganinnan ta dinga sha duk sanda taji akwai matsala idan yayi tsauri ta hanzarta zuwa asibiti!
Godiya yayi Mata sannan ya fita ya tafi aji domin gabatar da lecture kamar yadda yayi alkwari domin shugaba na gari baya karya doka. Mutane suna renews suna dauka wai ai latti ba komai bane.
Ya kai me wannan dabi'a Wallahi in baka sani ba ka sani.. in ka sani kara sani duk kudin da kaci alhalin bakayi aikinsa ba kaci haram! Kayi yarjeje niya da mutum ko gwamnati zakayi masa aiki na awa 8 a wata banda ranakun hutu toh ko minti daya in ka yaye bakayi aikin ba kuma babu dalili tohku zauna ku dauki percentage ko naira 5 ce karka rainata ka mota masa kace bakayi aikin wannan lokaci ba.
Ko kuma Wanda a wajen aiki zasu dauko waya suna chatting a WhatsApp ko suna tweeting da Instagramming a lokacin aiki kun cuci shugabanku koda babu aiki wajibi ne a kanku karku shiga lokacin da akace na aiki ne.
In kun gama mu zauna kuyi lazimi ko kuma muhara ta karuwa da abokan aiki yafi muku sauki ku mayar da kudin da bakuyi aikinsa ba da kuci sa ranan akiyama Allah yasa a kona duk wani tsiro daya fito a jikinka saboda kaci wannan kudin.
Kaiconka ! asarar ka! ranan da Dan uwanka zai shaki kwalarka ya kaika gaban Allah yace ka zalunceshi asara ta kare ma kuma babu ruwan mala'iku. La ya'asunallah! basu sabawa Allah kamaka zasuyi su tittinnike la su jijjibge ka kuma sun jibgi banza. Suyi ma Abu sankan d'arira babu ruwansu.....
Tunda ya shigo aka fara kananun maganganu aata ta dangwali kawarta tace ke kareema kin lura cewa yau ne rana na farko da malam Ahmad yasa farin kaya ? Tace na lura fa kuma wallahi yayi masa kyau sosai laraba tace kareema kenan, baki dauko ba. Gyara zama jameela tayi tace toh bani insha mana ta wajena!
Laraba tace jiya akan idona naga malam Ahmad yana labe yana sauraran maganganun karuwar nan marakisiyya kinsan bata taba yin shiga babu fari a ciki ba duk yadda za'ayi sai dai tayi zallar fari ko ta hada da wani kala toh ina shagon da suke lokacin da take cewa dama yasa farin kaya saiko gashi yasa. Kareema tacd toh sun Ganshi ne?
Laraba tace bar yan tasha ni ina nasan musu ? Shine yau zasu nuna mana karshen fitsara suma wani makalkale juna wai gware sukayi. Abinda bata sani ba kuwa shine duk abinda take rada ma kareema a kunnen malam Ahmad.
Baice musu kala ba ya gama koyarwarsa ya fice abinsa direct sickbay ya koma ya samu har ta farfado ana nuna Mata yadda zatayi aiki da maganinta tana ganinsa tayi sauri ta dauke kai.
Ji take kamar a nitsa ta cikin katifa saboda kunya. Fili likitan ta basu itako tana ganin haka ta kwanta luf ta rufe ido. Murmushi yayi yace rakisiyya menene kuma na rufe ido? Ya jikin naki?
Shiru tayi ya tabe baki yana murmushi yace kinga ni babu abinda zance miki amma dai ki gaggauta sanar da iyayenki matsalark karki cucu kanki kinji da sauri ta juyo zata ce toh kai ka aureni mana.
Sai ta tuna ta rufe bakinta tare da sauke kai yace me kikeson cewa? Tace umm dama so nake nace kayi hakuri abinda nayi maka dazu ban dauka kai bane karka bani carry over na dauka assistant class rep din mu Dan nasan shine yake bangajar mace da gangan.
Murmushi yayi yace babu komai AI ya wuce kuma bazan taba baki carry over ba saide in ke kika bawa kanki ranta hanyar yin karatu amma kuma ke ba haka kike ba kece ta uku a masu gp sosai a ajinku UNTU/17/PHY/1184. (ÙNTU=Untichlobanty University)
Zaro ido tayi tace malam kasan MATRIC number na? Yace I am your level coordinator kin tuna? Tayi murmushi yace muje na daukeki a gida ko? Tace m. Ahmad ka barshi na gode zan hau mota ta yace karki damu muje ki bawa mansura kawarki ko beeba ganinsu yakai miki kinga ke bakida lafiya kuma akwai Dan shawarwari dazan baki ko.
Tace toh malam na gode sosai Allah ya saka da ALKHAIRI. A bakin SLT (Science lecture theater) kuwa suka samesu bai ma bari ta fito a motar tasa ba ya karbi key din yace ko jakar ma a su kawo miki ne tace ah ah. Fitowa yayi fuskarsa babu murmushi kuma ba a daure ba. Cikin sanyin murya yace sannunku sukace yauwa sannu malam yace ga key din motan kawar ku sai ku kai Mata gida kunji batada lafiya.
Yana kaiwa nan bai kara ce musu wani Abu ba ya shige motarsa sai gidan su marakisiyya a hanya ne yake cewa rakisiyya kisa Allah a lamuranki kinji karki damu komai mai wucewa ne ki yawaita azumi sannan ki dinga shan maganinki on time Allah ya baki lafiya.
Abu daya da nakeso ki rike shine komin rintsi kimin wuya karki bawa Allah kunya ki kare kanki daga dukkan wani Abu da zai tada miki hankali. Baisan zamansu wake daya ma jagwal bane ga yadda yake magana irin kasa kasa bawai irin na aji ba kawai sai ta soma karkarwa hannunta kamar an jona inji.
Yace subhanallah menene kode ciwon ne? Kankame jikinta tayi, tayi shiru ganin ya rikice yana Mata tambayoyi yasa race malam na gode da shawara amma ka dena magana yana daga min hankali.
Shiru yayi abinsa Dan yasan me take fada saide nashi ba irin nata bane. A ransa yace Allah sarki rakisiyya da inada iko da na aure ki saide kash hakan ba mai yuwuwa bane.
Bazan taba yafe wa mahaifina ba azzalumi mugu ya cuceni ya cuci mahaifiya ta ya tagaiyyara rayuwata. Ya mayar dani dabba karfi da yaji tun kamin a haifo ni ya Allah da na Saba maka na gwammaci na zauna babu aure na gwammaci sha'awa ta kashe ni.
Suna isowa lokacin ta dawo saiti tace malam na gode Allah ya saka da ALKHAIRI tana kaiwa nan ta fice abinta daga motar. Shigarta keda wuya tayi kicibus da ludu yana busa sigari sandarsa ta mulki dogare a kasa sai hura hanci yake.
Tsaki tayi tace malam Dan Allah matsa min a hanya mutun ba kayan gani wani gaka ga kamarka kamin kerere a hanya AI sai ka bani tsoro in dare ne ka wani kafa hana sallah aka.
Wuceshi tayi ya finciko ta har sanda tayi Tuntube yace zo nan Dan...... KE DAGA MOTAR UBAN WA KIKA SAUKO?
LUD
MARAKISIYYA
TOH NIDE NAYI NAN DAN NAGA FADAN NA MANYA NE.
WAI INA FANS DIN M. AHMAD NE? ME YAKE NUFI DA KALAMANSA NE?
TOH SU MARAKISIYYA ALLAH YA KAWO SAUKI .
TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO
Miss untichlobanty 💕
22nd July,2020.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top