CHAPTER 2
Zaro ido tayi kamar mujiya ganin Wanda tayi wa aika aikar ba kowa bane sai crush dinta kuma malaminta Wanda take matukar kauna saide ta lura kamar ma bai taba lura da ita ba.
Mikewa tayi sum sum ta shige aji abinka da masu waya har an dauka an fara yadawa. Shi kuwa gida ya nufa ya Kira class rep yace yayi shifting lectures din zuwa 3:45pm dama 3:00pm za'ayi yace suje suyi sallah sai a dawo sannan ace ma marakisiyya musbah Aminu taje office dinsa ta jira sa.
Haka ko akayi class rep yace "class, good day to you all! I just spoke to our lecturer and he said the lecture has been shifted to 3:45 I think that must be due to the accident of collision theory we just witnessed.😂😉 Thank you!" Wato
"Yan aji barka da yau! Yanzun nan mukayi magana da malamin mu kuma yace an matsar da lecture din zuwa karfe uku da arba'in da biyar Wanda nake tunanin saboda abinda ya faru ne Wanda muka kalla yanzu.😂😉" Ya fada cike da miskilanci
Kunsan yan jami'a ba'a rasa zogaye nan de suka hau ife ife su. Marakisiyya tazo zata fita wani yasha gabanta ya fadi a kasa tace baby ni bazaki fado jikina bane ? Abokansa suka kyalkyale da dariya. Da ta daga kafanta bata sauke ko ina ba akan .......
Ta take ta mutsittsike yana ihun yana kururuwa ganin zatayi kisa ne yasa Beeba janye ta itako fadi take barni inci..... sa,sh*ge Mara mutunci ana kokuwa da ita sanda mansura tasa hannu tukunna ta bari. Class rep ne yace Ayya kekam marakisiyya sunanki sorry a makarantar nan toh kije office din malam Ahmad level coordinator dinmu yace ki jirasa sannan kuma bayan kun gama mu hadu a office din HOD.
Yana kaiwa nan yan ajin suka sa ihu ana shewa ana saikayi our one and only class rep. Hatta saurayin da ya tsokaneta aikin class rep din ne Dan haushin clique dinsu suke ji badan komai ba kawai sai Dan sun kare mutuncinsu basu shiga hayaniya.
Gumi ne ya tsattsafo Mata sanda suka nufi office din malam Ahmad tunda take ko kallonta a aji bai taba yi ba. Ko tambaya yayi ta daga hannu baya zabarta kai koda ita daya ta daga hannun ya gwammaci ya fadi amsan da ya zabeta.
Hanky mansura ta ciro tana goge Mata gumi tace haba marakis ya kike Abu kamar ba big girl ? ba ji yadda kike gumi sai kace kin kashe mutum yo ko filin alkiyama albarka. Beeba tace banda filin alkiyaman de. Hawaye ne ya silalo wa marakisiyya tace waiyo Allah ya zanyi beeba? Mansura ku bani shawara kunsan ko magana bana iyayi a inda yake jikina sai yayi rawa ko tunaninsa nayi tsikar jikina tashi yake. Gashi gani nake kamar ya tsaneni. Kuma ni kaunarsa nake wallahi kunsan banida wani Wanda nake crushing akai irinsa.
Wani numfashi taja Wanda ya bawa su beeba tsoro Dan sun dauka suma ma tayi. Jin tace "na shiga uku tana dafe kirji ta daura hannu aka idan ya bani carry over fa kinsan phy 304 prerequisite ne😭" yasa hankalinsu kwanciya.
Da fari mansura ta dauka drama ce irin ta marakisiyya amma ganin da gaske take yasa tace kiyi hakuri mana kinsan bazai baki carry over ba kodan mahaifinki saide idan da gaske faduwa kikayi kuma AI kinada kokari sosai ba saide hassada kece fa me highest Gp na 3 a ajin mu shiga ki jirashi mu zamuje mu warware matsalan d'an tashan can a office din HOD.
Godiya tayi musu ta shiga tana addua duk wacce tazo mata yayinda kirjinta ke dukan tara tara. Gashi gaba daya abinda ya faru dazu ya daga Mata hankali saboda Abu kankani ke motsa ta. Zugi maranta ya soma Mata ganin babu sarki sai Allah kawai sai ta fashe da kuka.
Malam Ahmad kuwa yana gama fadawa class rep sakon sa ya kunna motarsa yabar makaranta ya nufi gidansa domin ya canja kaya. Tuki yake ya Dan kanne ido daya yana nazari sosai wannan yarinyar is different from others... baya kyankyamin ta kamar yadda yake kyankyamin sauran Mata. 😳(kyankyami kuma?)
Hasali ma burgesa take yi, bata kula maza batada hayaniya kamar shi. Shima haka yake ko magana bayason yayi idan ba formal ba kamar lecturing ko meeting haka. Toh ai ga irinta nan dalilin da yasa baya ko San shiga harkarta kenan saboda yadda take like ma tunaninsa. Bawai he is attracted to her ba amma kawai burgesa takeyi ko kuma yace hanasa sukuni take toh yau dole ayita ta kare dole ya titsiyeta.
Farar shadda kamar wacce ya cire ya sake sawa Dan shi kullum bakin kaya yake sawa acewar shi tafi fito da haskensa. Tunowa yayi da dalilin da yasa ya sanya farren kaya. Jiya ya shiga school market zai karbi typing da ya bayar ayi masa na test din dalibai amma a shagon photocopy din makaranta saboda kar question yayi leaking sai ya hangosu su uku tsaye a bakin wani shago.
Da alama ruwa zasu siya fasa shiga motarsa yayi yaje shagon dake gefen inda suke ya tsaya yana kallonta cikin abayanta kamar kullum tana kyalkyala dariya tare da kawayenta.
Beeba yaji tace amma yanzu let's be serious marakis idan yanzu m. Ahmad dinki yace yanason a daura muku aure in 2 weeks zaki yarda? Marakisiyya tace two weeks? Mansura tace eh marakis tace da alamu kun karya kumallo da piya piya AI cewa zanyi da weekend ma an gama komai sake kyalkyale wa da dariya sukayi mansura tace kaji maiya.
Beeba tace nikam wai shi kullum bashida kayan sawa ne sai baki? Mansura tace toh ai yana yi masa kyau shiyasa kuma kinga ni favourite color na kenan. Marakisiyya tace nikam ko na arana daya ne in yasa favorite color na fari toh sai nayi wata ina farin ciki.
Bai tsaya jin sauran zancensu ba kamar Wanda akayi masa tsafi haka ya shige mota ya koma office take ya Kira umminsa yace a siyo masa ready made na kaftans farare guda 30 dan na wata daya cir zai saka.
Murmushi yayi bayan ya dawo daga tunanin da ya fada ya nufi gaban madubi yana girgiza kai yace marakisiyya kenan gashi nasa miki farin kaya kuma sai Kika bata min.
Fesa turare yayi ya fice tare da komawa makaranta ya nufi office dinsa. Tun daga office din take jiyo takunsa lokacin ta nannade a dungu a office din tana ta zubda hawaye.
Da sallama ya shigo bakiga kowa ba yace lallai yarinyar nan tana neman maga..... kasa karashe maganar yayi jin shesshekarta ya juya da sauri ya ganta a bayan kofa.
Yace rakisiyya dago jajayen idanunta tayi jin sunan da ya kirata dashi. Dama yasan sunanta harda yi masa wani salo kusa da ita ya karaso yama rasa abun yi yace me.. me ya sameki? Goge hawayenta tayi tace ba komai tana shirin mikewa a take ta koma saboda yadda taji kamar an zaro hanjin ta yayinda taji wani Abu nabin kafarta wadda ta tabbata ba jinin al'ada bane Dan baifi sati da gamawarta ba.
Yace ya zakice min babu komai bayan gashi kina kuka kuma da alamu baki iya tsayuwa? Kode .... sai kuma yayi shiru Dan tunowa da yayi cewa zaiyi banbarama. Dan shi ya dauka al'adanta ne ma yazo yace Bari na Kira class rep dinku ya turo min kawayenki su dauke ki su saka min ke a mota bakinsa kawai take kalla tana nazari iri iri jin wani Abu na sake fita a jikinta yasa ta kankame jikinta ta rufe ido.
Wata lecturer wacce ke mutuwar son (malam ) m. Ahmad sai bibiyarsa take tayi knocking daga marakisiyya yayi daga bayan kofar har zai ajiyeta akan kujera sai ya fasa saboda gudun zargi balle a yanayin da take sai yazaunarta gefe tare da bude kofan.
Dalilin da yasa dukda akwai larura amma bayason ya dauketa ya fitar da ita saboda halin dalibai babu Wanda zai duba larura tasa ya dauketa yanzu sai ayi gaba daku balle ga abinda ya faru. Abinda bai sani ba kuwa shine zama daki d'aya da yayi da marakisiyya ya daga Mata hankali ba kadan ba balle kuma ya dauketa kawai sai ta sume Dan ita dai taci alwashi bazata taba yin zina ba saide ta mutu.
Saboda zina guba ce.... zina masifa ce kuma bomb ce ko da mai yinta ya tuba sai ta cutar da ita musamman ma diya mace karancin abinda zai faru shine babu zumunci ko kadan da zai yanzu a cikin iyalinki Lamar yan tasha haka zasu zama danki baya daraja baya kaunar yan uwanta, baisan mutuncin danginki ko na mahaifina ba.
Kai mazinaci! Dakai nake, wallahi ka sani in ka samu yar mutane kayi zina da ita toh yarka ce zata biya ma. Ku duba mana a shekarun baya muyum bai isa yayi zina da karuwa ba sai yana da kudi. Amma yanzu fa? Ba tare da ko Kabo ba. A baya ka bata 10k kayi zina da yar mutane wallahi ko naira 10 gate bazai bawa yarka ba zaiyi zina da ita. Zakin bakin minti Goma zai Mata ya gama da ita.
Mazinata in Baku sani ba toh bari na fada muku da dumi dumin sa. A yayinda zakuyi zina komai na Allah sai ya barka, ko ka haddace kur'ani sai ya barka. Duk wani Abu dake da hadi da Allah ko manzonsa sai kun taba hanya. Akan jin dadin awa daya kun tarko wa kanku masifa ba na kwana daya ba.
Ba na sati daya ba, wata daya ba. Ba shekara daya ba wallahi har ku mutu bazai barku ba...shiyasa Allah yace kar ma mutum ya kusanci zinan balle ya aikata.
Kallon ms madeena dake tsaye tana kallonsa yayi yace thank God ms madeena kinzo please wannan dalibai zaki kama min mukaita sick bay I think anxiety attack ta samu saboda tsoro. Murmushi ta sake masa yau wace rana bai ja tsaki ya dauke kai ba... kuma har sunanta ya Kira harda neman alfarma a wajenta.
Tace with greet pleasure malam Ahmad rike min jakana karba yayi yana tabe baki ganin shigar da tayi daga ita sai Riga da siket. 'Daga marakisiyya tayi ta nufi waje da ita idonsa ne ya fada a jurwayen dake bayan marakisiyya ya kalli wajaje biyu da ta zauna duka biyu a jike.
Zaro ido yayi kamin ya hau kiftasu da sauri ya.......
😳😳KAI JAMA'A 😂😂 NI DARIYA MA ABIN YA BANI SU MALAM AHMAD ANGA TA MATA.. NAMU BA IRIN NASU BANE IKO JALLA JALALU SAI KALLO.
WAI SHIN YAYA ZAI KAWANCE DA MARAKISIYYA NE? SHIN MALAM AHMAD KO DE YA FADA NE HAI GANE BA? INA LABARIN OGA LUDU UBAN JARUMTA😂
KU BIYONI DON JIN YADDA LAMARIN ZAI KAYA ANYA KUWA KUNA JIN DADIN WANNAN LABARI ? YANZU DE MUKA FARA KUMA KUNSAN ME NAKE CEWA KULLUM ANA KARA ZURFI LABARI YANA KARA CITTA😉
DAN ALLAH KARKU MANTA DA FOLLOWING DINA SECOND BIYAR KACAL ZAI DAUKA.
TAKUCE KARAMARSU BABBARSU KU TABBATA KUN ANTAYO MIN COMMENT TARE DA VOTES FA. A NA GOBE AKWAI WANI JAWABI DA ZAN ANTAYO MUKU
Miss untichlobanty 💕
21st July,2020.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top