CHAPTER 18
Wani remote dake gefen sa ya janyo ya danna kawai sai kofar ta bude baice musu 'kala ba a ranshi kuwa fadi yake in ta gaji da tsayuwa ta shigo sannan ya gyara kwanciyar sa. Shiru shiru bai kara cewa ko.ai ba hakan yasa ran umma ya baci ta hankade kofar ta shiga.
Yana ji amma giyar dake kansa ya hanasa yin motsi ma balle ya kallesu. Umma ko ganin shi baje baje yana kwance ya barta tsaye a kofa yasa tace tashin hankali hannu tasa ta daka masa duka amma me makon ya tashi kawai sai ya janyo pillow ya rufe kansa Dan yasan bai wuce tazo tace masa ya koma gida bane.
Gyara liffayar dake jikin ta tayi tace wato yanzu lud so kake ka mayar dani mutuniyar banza ko? Nace ma ka koma gida wajen matarka shine kace babu uban da zai dawo dakai gidan ko?toh AI shikenan tunda ka nuna min ban isa dakai ba bazan mayar dakai gidan ba saide kamar kayi mantuwa. Ya dauka zata ce yabar giyarsa yaje ya dauka kawai yaji an hankado masa mutum.
Tace ga matar ka nan yanzu ba nauyin mu bace in kaga dama ka zauna da ita in kaga dama ka sake ta kai zaka mutu ba ni ba in kaga dama kuma ka kaita kwata a yanka kaji ko ? Tana kaiwa nan tayi ficewar ta tabar marakisiyya yaketa kuka me sautin da ba sauti.
Umma tana fita yace d.......uw*r nan wani kafa yayi wa marakisiyya sanda ta fado daga kan gadon yace shegiya kazamar banza har kika wani baje wa mutane a gado wallahi in kika yadda na shaki numfashin da kika sha ma sai naci.....
Tari ta fara saboda yadda numfashinta ya sarke tsabar yin kuka kwandon harara yake juye Mata kamin ya Mike daga gadon yace kai an gama rainani hankali fa. Ya za'ayi ace ni lud musbah na auri tsolon rake?
Ita de har yanzu tana cikin gyalen ta a dukunkune tana kuka. Dafe kai yayi yama rasa mai zaiyi ko yace kawai sai ya saka rigarsa ya kalleta yace ke idan ba so kike ki kalli yadda yayanki ke jarumta ba toh kar ki kuskura in dawo baki koma gidan uban ki ba.
Yana kaiwa nan ya buga kofa ya wuce abinsa. Kuka ta kara fashewa dashi yana fita kamar da ga gan aka samu matsalar wuta wani wire biyu suka hade hakan yasa aka kashe wutan hotel din gaba daya. Da gudu ta fito tana neman lud ta hango shi ya kusa fita. Da lalume da gwarewa ta karasa ta rungume sa ta baya tana gunjin kuka. Cikin muryar ta da baya fita tace ya lud Dan Allah kaeka barni wallahi tsoro nakeji bazan iya kwana ni daya a hotel ba idan wani ya... ya fada min fa?
Lud kuwa tunda ta kankame sa komai nasa ya tsaya baki daya. Zuciyar sa kawai ke bugawa yana tsittsilla ido sama da shekara ashirin kenan tunda marakisiyya tazo gidansu in ya kalle ta sai gabansa ya fadi. Ko su umma basusan yasan marakisiyya ba kanwar sa bace.
Haka ta dinga biniyar rayuwar sa a komai in yana game tazo ta takura mai, cin abinci, hatta bacci sai ya ganta a mafarki ya dauka da gangan takeyi toh amma yau ya gane inda matsalar take. Yanzu kam ya fahimci komai. Ya game dalilin da yasa take da naci gata da shegen taurin kai. Juyowa yayi ya kafeta da ido har sanda ta kusa zamewa ta fadi hannu yasa ya kamo fuskanta a hankali kamar me jin bacci yace tsolon rake DAMA KE MAYYA CE?
.......
M. Ahmad zaune a parlourn sa ya zuba uban tagumi kamar Wanda akayi wa mutuwa yana karanta wasikar jaki. Yanzu marakisiyya ko a wani hali take oho. Anya baiyi kuskure ba da yayi rejecting dinta ? Toh amm gara hakan in ya aure ta AI ya cuce ta gara da ya bari Dan uwan ta ya aure ta ko ba komai zai iya biya Mata bukatar ta.
Ji yayi an bude kofarsa yayinda ya kafe TV da ido dukda ko hankalinsa ba s kai yake ba yace ummi na me kike nema ne baki kirani ba kikazo da kanki ? Ji yayi an sakale hannu ta wuyansa an sumbaci kumatunsa yayi murmushi ya juyo yana fadin yau kumabkaunar ce ta mots....
Kasa karashe wa yayi ganin m.salis a Dan tsorace yace m. Salis lafiya dai ko me ya faru ba ganka da daddaren nan. Kewayo wa yayi ya kwanta a cinyar sa yace lafiya na kalau aboki na kawai kadai ci ke damuna kuma banda kai babu Wanda yasan matsala ta shiyasa nazo ni Dan nayi alkawari wa kaina bazan sake yi ba.
Shafa kanshi m. Ahmad yayi dukda yaji abun banbarakwai namiji da suna hajara amma sai yace karka damu m.salis komai zai ware zaka dena kaga ni dama can ban fara ba balle na tsoma kaina a ruwa. Zamu dinga zuwa asibiti ana maka therapy insha Allah zaka dena daga nan kuma sai musan yadda za'ayi mu fara sha'awan mace ko ya kace? Rike hannunshi m. Salis yayi yace wannan shawara ce mai kyau gaskiya nagode sosai fatan bazaka damu ba in na kwana anan? M. Ahmad yace ba damuwa zaka iya kwana.
Dariya m. Salis yayi yace nagode sosai aboki na. Daga nan suka ci gaba da hiran su yayin da suke shan shayi.
.....
Umma kuwa tana komawa gida ta samu yayar daddy wato atine ta saka shi a gaba tana kwashe masa albarka wai me yasa ya raini marakisiyya kuma har ya boye Mata Dan yaga ba mahaifiyar su. Wai in da mutunci AI ita uwa ce a garesa. Sauran kannen NASA sai hakuri suke bata suma ta samu take fada musu baka. Da abin ya bawa umma haushi ne tace atine ya isheki kuma enough is enough for a wise kina ji na ko ki fita sabga ta da na miji na.
Atine race dalla yi mana shiru asararriyar iwan kawai Wanda ta kasa tarbiyantar da danta sai shaye shaye yake yana yawo a gari. Cikin bacin rai umma tace jibi me magana sai kace ba kece kwanan nan aka tsamo ki daga harkar madigo ba kikayi wata sama da 10 a asubiti kamin kika fara dawowa saiti. Kodan banga laifinki ba da alama a garin harkar taku ce aka tsetse miki kwakwalwa.
Kukan borin kunya ta fashe dashi wai musbahu yanzu a gabanka wannan matar taka ke zagina kayi shiru kana ji. Bude baki yayi cikin in ina yace kiyi ha...hakuri.... ahhh innalillah wa inna ilaihi raji'un kawai ya dafe zuciya ya fadi kasa ashe basu sani ba hawan jinin sa ya tashi tazo ta kara masa zafi.
......
Marakisiyya kuwa dago kanta tayi da sauri ta zuba idonta cikin nasa yace damn it! Ga irinta nan kin gani ko? Dafa kafadar ta yayi cikin tsawa yace Dan..... ki ki sake min kurwa ta! Azabtarwan ya isa shekaru 20 kina bibiya ta me na miki? Nace me na miki? Ba rantse da Allah ko me suna irin naku na sake ki bare na gani saina karya miki kafafu balle kuma na ganki dama kisan inda dare ya miki yana kaiwa nan ya hankade ta ya fice.
Da sanda kamar barauniya haka ta fara haurawa sama Dan ma a floor na 2 suke. Da yake sanda aka kawota a cikin gyale take batasan room number din ba kuma sanda umma ke tambaya ita kukan ta take masga. Taimako daya Allah yayi Mata da take kallon kasa tana ganin kasan kofofin da suke wucewa kuma in batayi kuskure ba toh kofa na 5 ne nasu hakan yasa tayi shahadar kuda ta tura kofar ta shiga.
Har zata zauna a bakin gadon sai ta tuna da abinda yace Mata ta samu kujera ta Dan dosana mazaunan ta tana jiran tsamma a haka har bacci ya soma kwasarta. Kamar a mafarki taga Kato a kanta daga shi sai gajeran wando Wanda ta tabbata ba mijin ta bane.
GASKIYA INA JIN DADIN COMMENTS DINKU SISTERS WANDA BASAYIN COMMENT KUMA KUNAYI MIN DAN ALLAH.
NAGODE DA KAUNAR KU GARENI KARDE A MANTA DA YI VOTE
TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO
Miss untichlobanty 💕
14th August,2020.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top