CHAPTER 16
Karkarwa marakisiyya ta fara baki na rawa tace me? Me... me kake nufi m Ahmad? Cin kwalar rigar sa tayi tace Dan bakason la aureni shine sai ka miyar da kanka fasiki? Karya kake yi wallahi kai mutumin kirki ne Dan Allah ka taimaki rayuwa ta Dan Allah.
Zare hannun ta yayi a hankali yace marakisiyya karki manta ni ba muharramin ki bane ki daina rikeni ki sani komai yayi zafi baifi karfin Allah ba da ina da ikon aurenki da zan aurenku babu shakka akan hakan domin kina burgeni tsarin rayuwar ki gwanin sha'awa ce kiyi hakuri ki auri Dan uwanki kinji.
Fita kawai tayi da gudu ta koma daki tana shigowa mansura ta rafka salati Dan tasan an Sami matsala beeba tace yanzu dole sai ta auri mazina cin nan? Mun shiga ukun mu.
Marakisiyya tace beeba ku kalle ni menene AI bina da zan rasa miji ? Banida kyau ne ko Ilimi ne banida shi? Tarbiyya na rasa? Me yasa? Me yasa kaddara zatayi min haka ya zanyi na auri Dan iskan can waiyo Allah na! Waiyo zuciya na.
Umma be ta turo kafar tace kiyi hakuri marakisiyya na fahimci matsalar ki amma ki sani wannan aure contract ne tsakanin mu da ke a matsayin ki na yar mu kiyi mana biyaiya ki aure sa ki bashi tarbiyya daga ya shiru sai mu raba auren ki auri Wanda kike so.
Da sauri tace umma da gaske kike? Umma tayi murmushi tace kwarai kuwa diya ta diyar albarka da gaske nake ba sai kin yi rayuwar ki da lud ba. Ki yafe min da na biye wa duniya harma da ke cewa ke ba diya ta bace kaunarki ya mantani yin hakan kuma ki sani bamu taba shiryawa ko tsammanin akwai abin da zai kawo dole sai mun fada muku gaskiya ba.
Ki yafe min kinji ki yafe min. Goge hawayen ta tayi tace AI shikenan tunda ba sai na hada zuri'a ta da nashi ba zan aure shi umma kuma duk randa ya shiru zan barshi domin auren farin cikin rayuwa ta. Zanyi muku halacci kun rikeni amana bazan Baku kunya na ki taimakon jinin ku ba wannan hali sai butulu.
Fitowa umma tayi ta shiga da daddy daki ta sanar dashi cewa marakisiyya ta aminta da contract din ga paper din ma tayi signing karba yayi ya ajiye a killaceccen waje.
Dawowa parlour sukayi lud dake buga game din God of the war yace wai kuna bin garu kuna wani shawara ni ba'aji ta baki na ba. Allah sarki umma da shike ta dauka nutsuwa tazo mai tace babyn umman sa AI nasan bazaka ki farin ciki na ba ko ? Munsan zaka auri yar uwar ka kuma..... Daga hannu yayi yana wani bata rai yace look woman kina ji na ko? Dama fa bawai na aje makamai na bane boyewa nayi Dan na wallafa rai a wannan yarinyar amma yanzu da bazan same ta ba babu wani auren da zanyi.
Haba in ba an rena min wayo ba ya zaku aura min wannan kashin yarinya kirjinta kamar allo. Babu abin da zanyi da wannan halittar look malam musbah Aminu bazan auri muciya da zani, diyar kajinka ba.
Ya Kira sunan mahaifinsa yana nuna sa da yatsa yayin da ya fadi wannan maganar. Wani Mari umma ta sauke masa sanda zoben hannun ta ya yage masa kumatu. Tace kaicon ka lud, asara ta kare ma mai hali irin naka toh billahil azim ko kaki ko kaso sai ka auri yarinyar nan. Abin naka ya ishi mutane ka fita a kaina wallahi har na fara nadamar haihuwan ka.
Cikin bacin rai yace dakata dakata dakata malama nace ki dakata! Dan kin haife ni sai akayi kaka? Ni nace ki haifo ni? Ko na rike kafar ki daga shiga dakin zubda ciki? Ni duk surutun nan da kike ya daina tasiri a zuciya ta tsinewa ce karshe bismillah ga fili ga mai doki. Yarinya ce nace bazan aura ba ko ana dole? Yana kaiwa nan yayi cilli da babban rigan ya fice zuwa ban garen sa ya janyo akwati Dan guntun kayan NASA ma kwashedu yayi ya nufi hotel Dan yasha alwashi indai akayi auren bazai kara kwana cikin ba.
Kuka umma ta zube a kasa tanayi tace Alhaji na kar muyi kuskure fa Anya bazamu fasa auren nan ba? Dad yace kenan mubi umarninsa kike nufi? Ya zama dole mu nuna mai mu muka haifesa. Ba shi ya haifemu ba. Hakan da yayi ya kara tabbatar mon kansa ba daya yake ba. Aure ba fashi in an daura saide ya kashe ta.
Yana kaiwa nan ya fita da karfin guiwar sa. Har mamaki yadda ta fito jama'a suke zama yayi ya bawa al'umma hakurin bata musu lokaci nan liman ya karbawa lud auren marakisiyya a wajen daddy jama'a kowa ya rikice liman ma Kato bara yayi bayan an daura aure
Mai sanarwa ya bude makokoro yace ye kuwa jama'a dukda ni kaina ban gane me ke wakana a wajen nan ba, San dai fadi abinsa kunnena yaji ne. An daura auren lud musbah Aminu da kanwarsa Wanda a sunanta ni na sanar cewa sunanta marakisiyya musbah aminu amma dai yau ance ainihin sunanta marakisiyya lud Aminu. Baban amarya da ango ko zamu saaaamu Karin bayani?
A cikin gida Mata gaba daya aka Mike aka tsaye wa umma hajiya mu fa bamu gane ba wannan wani irin jahilci ne yaza'ayi wa ya auri kanwa? Umma tace da alamu bakiji sunan amaryar da kyau ba ko? Toh marakisiyya lud aliyu akace ba musbah ba. Marakisiyya yar kanwata ce kuma nice nan na raine ta.
Wata Mata Mata aikin banza yanzu ke da kikayi bayanin nan kin dauka an warware komai toh nonon da kika bata tasha fa ? Murmushi umma tayi tace tabbas babu shakka nice nan na shayar da marakisiyya tun daga ranan da tazo duniya kuma nice de na dauki cikin lud ba Dan wani ko wata bane.
Kowa ya tsaya kallonta wata Mata tace ke hajiya marakisiyya da alamu ke da mijin ki kunyi dimuwa ko ? Da alamu dai fasa auren danki ya taba muku kwakwalwa yasa kuke ta shige da fice.
Murmushi umma tayi domin zagin ya shigeta amma sai tayi shiru tana bin matar da ta fada Mata wannan maganar da kallo dan bata gane matar ba amma kamar ta Santa.
Ajiyar zuciya dadday yayi yace a takaice ba diya ta bace diyan kanina marigayi lud mai sunan Dana ce. Fatan Allah zai yafe ni kuskuren kauce batun manzonsa da nayi Wanda yace a Kira ko wani Dan Adam da sunan mahaifinsa koda kuwa Dan da aka samu babu aure ne.
Mai sanarwa ya hura speaker ta bada sauti yace toh kunji uban ango kuma marikin amarya yace amaryar diyar kanin sa ce Wanda akwai dogon jawabi dake boye amma dai da wannan kawai ya barmu saboda wani abun ba na tattaunawa a jama'a bane.
Umma ce ta Kira lud a waya yana kallo yaki dagawa kara rungume sailuba yayi wacce ke yi masa tausa yace my love nayi missing dinki fa. Tace Allah ko? Sako ne ya shigo wayar tasa dubawa yayi yaga umma ta rubuta lud idan kanason farin cikin rayuwar ka kazo ka gida Dan yau za'a kai maka matarka bangaren ka bayan matan ka sun gama idda a gyara gidan ka.
Emojin dariya ya tura Mata yace room number na is 156 sai kunzo. Kawai ya kashe wayarsa. Umma kuwa sake karantawa take tana hango diyata kwance a gadon hotel inda kazami karuwai suka kwanta. Wani zuciyan ne yace to sai me. Murmushi tayi tace wallahi ko ka dawo gida ko na kai maka ita har hotel din....
GENG ! GENG!! GENG!!! CABDI GASKIYA LUD RASHON MUTUNCIN SA YA WUCE TUNANI NA TOH FA WA YAGA AMARYA MARAKISIYYA A HOTEL? CABDI
KU BIYO NI DOMIN JIM YADDA ABIN ZAI WAKANA. TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO
Miss untichlobanty 💕
12th August,2020.
https://my.w.tt/
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top