CHAPTER 14

Ganin babu sarki sai Allah yasa ta yanke shawarar zata kwana a bandaki kawai in ta tsula ma kawai sai ta kunna wa kanta shower ta nuna kamar jikewa tayi. Mikewa take kokarin yi lud ya kara gyara kwanciya ya dauke Mata nauyi baki daya hakan yasa ta fara tunanin toh bari ta kwana ido biyu amma matsalar bazata iya kwana da nauyin katon nan ba kar da safe a kwashi gawa ta.

Ajiyan zuciya tayi fara burbuwa ko Allah zaisa ya daga ta amma shiru. Turo baki tayi tace umma na za'ayi kisa za'a kashe miki diyar ki. Sautin Hhhha lud ya furta cikin buguwa yace ke... daina mutsu mutsu kin hanani bacci.. mtsw mutum sai kace tsutsa.

Numfashi ya sauke yaci gaba da baccin sa yayinda taci gaba da kallon ceiling. Dariya dariya ta soma jin yadda numfashin sa ke dukan wuyanta kamar cakulkuli. Gyatsa yayi ta dauke kai saboda warin giyan da ya daki hancin ta. Tace eww yayinda take tunanin in ba tsautsayi da asara ba menene abin dadi a cikin giya?

A haka har bacci ya dauketa. Kiraye Kirsten assalatu yasa ta bude idonta tana shirin mikewa da gudu Dan haka take yi a cewar ta inka bude ido ka Mike a take kamin ma kayi addu'an tashi daga bacci in ba haka ba toh saide kaga rana a tsakiyar kanka. (This is literally me😂)

Jin nauyi da kuma dakin da taga tsarinsa, fasalinsa, kalarsa hatta kamshin sa yasha banban da nata yasa ta tuna da abin da ya faru. Ba sai ta tambayi kanta ba domin kuwa tabbas tasan cewa ta tsula. Dan haka ta fara bubbuga bayan lud Wanda yanzu Rabin jikinsa na kan hannun ta yayin da yayi matashin kai da kirjinta ya sakala hannu ya rike ta, ya danne kafarta na hagu yayinda ta lubga masa na dama.

Hakan yasa ya zamto hannunta na dama is free. Turo baki tayi tana kunkuni tace nasan maganinka. Dakarkarewa tayi ta hankade sa sanda ya fado daga gadon Tim. Da ashar ya bude bakinsa yace bakida hankali ne Dan......ki me ma kike yi a dakin nan? Shegiya munafuka? Haka kawai ta abinci bakinta da cewa da uban wa yace ka dauko ni ?  Kazo kasha giyar ka sannan ka tsula min fitsari kuma Dan wulakanci kake tambaya ta me Nike a dakin ka? Yanzu dubi yadda hannuna na hagu ya sha jini.

Hankade ta yayi karyar banza da wif nasan na kawoki daki na amma kawai gyara min na kawoki yi ya akayi kika hau gado na?

Kamo hannunsa tayi fuska a turbune ta sakashi a inda take jiya ta daukwalbar giyan nasa ta fara tangal tangal yadda yayi jiya ta fada jikinsa amma ko gezau baiyi ba sai ma hade gira da yayi. Ido cikin ido suke kallon juna ganin zata zame gashi bayida niyan rike ta yasa ta mike da kyau ta tsaya ta saka yatsa tana dangwalar kirjinsa da babu Riga yayinda dayan hannunta ke kwankwason ta tace haka kayi min jiya ka danne ni da kyar nake numfashi yin duniya nayi ka barni na tafi sai ce min kayi na daina mutsu mutsu kamar tsutsa.

Tabe baki yayi yace karyar banza ya cacumo hannun ta ya finciko ta zuwa jikinsa sai ta dawo kamar wata yarinya dukda tsayin sa take da shi yace Dan uwaki kinga alamun inason in kalli wannan kananun lemon tsamin naki  bare in taba. Tace hhhhh tana bude baki kamin tayi magana taga yayi yatsine, kawai ya wanke ta da amai tun daga tsakiyar kanta Wanda ta tufke har zuwa kafarta.

Da gudu ya shiga ban daki ya karashe yayinda ta raho a zafafe ta fara bubbuga kofar tace wallahi ka bude mugu kawai ga Mari ga tsinka jaka ya zakayi kayi min fitsari ka ci min fiska sannan kayi min amai yanzu sai na sake wanke kaina.

Kurkure bakin sa yayi ya bude kofar ya cafko wuyan riganta ya hankada ta bayin ya bude Mata shower ya samu guri ya tsaya ya fara latsa wayar sa. Ganin bayi da niyan tafiya yasa tace um..ah zanyi wanka.

Ba tare da ya kalle ta ba yace da na bude miki shower wanki nace kiyi? Tace AI..  naga..ka..ka tsaya ne. Yace toh duk daya ai tsolon rake wai me zan gani a jikin ki ne? Ke banda abinki ya kamata ki gane cewa tsabar bakiyi ba dukda kudin da daddy yake dashi da komai har yau bakida saurayi amma ni dubeni.

Yan Mata ta ko ina ni suke mafarkin samu,har fans ma akwai masu crushing in karya nake ki tambayi miss untichlobanty. Abinda yasa daddy bai miki aure ba kenan yanaso atleast in zakije gidan Wanda kaddara ta kaddaro masa ki Dan kai koda certificate ne na kwakwalwa tunda ba a haifo ki da na jiki ba. Nide nasan mom Dina akwai shape kamar ita tayi kanta.

Haushi zancen ya bawa marakisiyya ta ja tsaki tace shiyasa naga an makalkale ni jiya da daddare kuma aka tsaye min a ban daki. Bige Mata baki yayi sanda ya fashe yace AI ni ban taba bacci mara dadi irin na jiya ba. Shiyasa na dinga mafarkin ana jifana da dutse ashe kashinki ne ke tokare ni.

Kasa kasa tace banza makaryaci in ma kaga an jefe ka da dutse ai hukuncin zina ce akayi maka. Murmushi yayi Dan sarai ya jita kuma maganar ta sokeshi kawai ya fice Dan yasan in yasa ta a hannunsa balla ta zaiyi babu musu.

Parlour ya fita ya kunna TV abinshi club ne ma ake dauka ya soma shan coffee ya barbaje yana kallo.
Marakis kuwa wanka tayi ta fito amma ya zatayi tayi sallah ba kaya?

Wajen kayansa ta nufa ta dauko wani farin riga tasa tare da saka hijab dinta tunda har kasa ne tayi sallah. Sum sum ta fito zata gudu yace zo nan. Tsayawa yayi yace da izinin wa kika taba min kaya? Zare ido tayi... ya akayi ya ganta?

Yace ba leka ki nayi ba ko me kika taba a area na waya na zai turo min alert, hakuri kawai ta bashi ta fice bayan ta furta ka tashi kayi sallah sannan ta fice kallonsa ya ci gaba da yi bai ma bi ta kanta ko maganar ta ba.

Tana shigowa parlour tayi mika tace ahh kai gaskiya na gaji sosai mugu kawai gashi da shegen nauyi juyowa da zatayi suka hada ido sanda numfashinta ya tsaya Dan tabbas sunji zancenta kuma duba da idon su to tabbas sun dauki zancen a baibai.

NO CAPTION 😉

TAKUCE KARAMARSU BABBARSU WATO

Miss untichlobanty 💕

10th August,2020.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top