Naira 8
To ni inma dai bansan ko yana da wata manufar ba bayan na aure da ya min magana. Koma dai menene ai gani gashi, zan gani. Ban k'ira sa ba, nasan tunda hannun sa ya iso shi dinma yana kan hanya.
Ilai kuwa haka aka yi. Muna cikin waya da Jabir call in shi ya shigo. Ban katse ba, muka cigaba da hiran mu. Zuwa can muka yi sallama saboda zai fita da wuri ne washegari.
Da kanshi ya k'ara k'ira, Ina dauka yace "Ran Gimbiya ya dad'e."
"Tare da naka" K'asa na d'an yi da murya na gaishe shi. Ko bakomai ina matukar ganin girman sa.
"Allah ya sa Pretty, yau hira yayi d'ad'i kenan?"
Ban d'ago zancen nasa ba, don haka nace masa "Hira kuma dawa?"
"Da saurayin ki mana." A tare muka sa dariya.
Can yace "Gashi kuma ina shirin mishi kwace. Ya za ayi kenan?"
Cikin raha yayi maganan amma ni sai ni ji wani irin abu ya ratsa jikina.
Ganin ban amsa ba yasa shi canja zancen "Kina lafiya dai ko? Ya gida ya Mamanmu?"
"Kowa na lafiya, sai kewa da aka barni dashi."
Wani d'an siririn dariya yayi "Ayi min afuwa pretty, kinsan sha'ani da d'an kasuwa ana neman na abinci. Gobe dai zan zo gidan ai In Sha Allah."
Daga haka muka yi sallama dashi.
Washegari, har na fara cire rai da zuwan sa sai ga k'iran sa ana idar da Sallan Magreeba.
"Na iso" shine abinda ya fad'a ya katse kiran.
Tun kafin in isa motan driver ya fito ya bude min baya, hakan yasa na gane yana baya kenan. Waya yake, ina shiga ya ma drivern alama ya tada motan. Ba sai na tsaya shiru ina shirin ganin ikon Allah ba.
Har muka isa wurin waya yake yi, ba dai wani tafiya mai nisa bane. Ina gaba yana biye dani a baya muka shiga classic restaurant in da motan yayi parking.
"Pretty me za a kawo miki?" Bayan ya gama wayan ya buk'ata, yana duba menu book.
Tabe baki nayi, na juyar da kaina. Ba k'arya ji nayi zuciya na ya sosu da sha'anin sa.
"Nayi laifi ne?" Dad'a turo baki nayi, fuska na dauke da shagwaban da bansan a ina na samo ba.
K'asa k'asa naga yayi da ido kaman mai shirin lumshe su. "Kina da kyau." Ya furta, idanun sa kyar a kaina.
Bansan sanda fuska na ya dau murmushi ba. "Ba ku dayawa a cikin mata Pretty, ko mai kika yi kyaun ki fitowa yake." Habaa, ji nayi kaina na wani irin fashewa. Musamman in na k'ara duban mutumin dake gabana, yana furta min irin wannan kalaman.
Ni sai na manta fushi ya kamata inyi, yanayin sa ya gusar min da komai. Har muka gama cin abincin, idanun sa na kaina, yana jefa na da wani irin kallon samun ki dace ne.
"Muje na bad'a hakuri da kyau ko?" Bangane mai maganan da yayi ya ke nufi ba. Amma dai naga drivern yayi parking gaban wani mall. Wannan karon, a jere muka shiga wurin.
Muna shiga ya d'an kalle ni "Feel free, ki dauki dukkan abinda kike buk'ata."
Kallo na bi wurin dashi, ina tunanin ta ina ma zan fara. Shi dai bina kawai yake a baya. Da k'yar, na kauda ruwan ido na fara daukan kayan ciye ciye da abubuwan sha.
Sai wurin kayan shafa, nan kam zagewa nayi na dau duk wani abu da nasan muna buk'ata ni da Rahma. Wasu ma ni bansan su, akwai dai wadanda nake ganin tallan su a TV ko IG. Duk yanda nake ganin na debi abubuwa da dama, mutumin nan ko d'ar ya mika cards aka yi debiting kudin ba tare da ya damu yaji ko nawa bane. Nice ma na zuba idanu, naga kudin da matan ta cira. Ai sai da jiki na ya dau kyarma. Fuske nayi, yayin da nake jin wani irin abu na ratsa zuciya na. Hatta tafiya na canjawa yayi lokacin da muke komawa mota.
"Ammaaa dai ba gobe za ka koma ba koo?" Turo baki gaba nayi, cikin shawagaba ina wani narai narai da ido. Na gane hak'a na ya cimma ruwa ne sanda ya juyo gabadaya yana kallo na ko kiftawan kirki ya gaza.
Ji nayi ya kamo hannuna, ya rik'e yana zuba wa yatsuna idanu "Komai naki mai kyau ne pretty, ba ki so na tafi ne?"
Da kai na bashi amsa. Sai dai maganan sa na gaba ya sani jin kaman in yanke jiki in fad'i "To gobe kawai ba sai nazo naga Baba ba? Kinga ai shikenan, zamu kasance a tare har abada."
Wani irin bugawa zuciya na, yayi. Wai meke damu na ne? Jabir kadai ya kamata ace yana da wannan tasirin akaina.
"Kina da account no?" Idanun sa ya maida kan fuska na. Don haka na bashi amsa da idanu kawai.
"Yi min dropping insu a SMS yanzun nan."
Ba tare da wani tunani ba, na ciro wayan ina k'ok'arin tura mai. "Ba ki had'a waccan wayan bane." Ai sai naji kunya ya rufe ni. Gabadaya na manta na mai godiya.
"Yau zan had'a. Nagode, Allah ya k'ara..."
Hannu yayi saurin daga min "Ba abinda ba zan iya kashe miki ba pretty, ba godiya tsakanin mu. Burina kawai, ki zama mallakina." Ya k'arasa zancen yana hade yatsuna da nashi.
Kafa mishi idanu nayi, naga sahihin abinda ke cikin su. Sai naji jiki na yayi sanyi. Nan take na fara zufa duk da sanyin AC da ke ratsa ko ina a motan.
"Zan k'iraki, in kin sanar da Baban sai nazo goben ko?" Da kai na amsa masa. Sannan na bude k'ofan zan shiga gida. Jin idanun sa a kaina ne ya sani juyawa, hada idanu muka yi. Naga wani irin kallo da yake ji fana dashi. Ba sai guiwowina suka kara sagewa ba. Da k'yar na iya takawa zuwa cikin gidan, rike da ledojin siyayyan da nayi. Yayin da zuciyana ke hango Jabir da irin tarin kaunar sa. Wani sashi na zuciyan kuwa, yana hango min walwala da farin ciki, cikin rayuwa da ba wahala ko kad'an.
Dabas, na zauna a falo. Bamu wani dade ba, shiyasa daren bai wani ja sosai ba. Amma dake Yan gidanmu, sun iya bacci da wuri ba kowa a falon. Haka na zauna, ina k'arewa duhun da ya mamaye fallon idanu. Ba abinda na ke tunanin, sai irin hasken da ya mamaye restaurant da mall in da mu kaje, kace yanzu ne rana a wurin. Amma muna shigowa Unguwan mu wuri yayi dimkim.
Motsin tafiya naji, ina daga kai mu kayi idanu hudu da Mama. "Kin dawo?" Da kai na amsa mata. Na mike mata ledan naman da musamman nasa aka min packaging a restaurant.
Sai da ta ajiye, sannan ta zauna a gabana, tana fuskantana da kyau. "Siyama, me ke tsakanin ku da wannan mutumin?'
"Yace aure na yake son yi."
Jinjina kai tayi, can tace "Jabir in kuma fa?"
Rasa amsan da zan bata nayi.
"Kinsan dai bansan k'ananan maganganun ko? Mutum yanzu shi ake kiwo ba dabba ba. Don haka bansan ruwan ido, yanzu haka an fara wa Babanku k'ananan maganganun."
Murmushi na k'ak'alo. Ina ganin ta tashi na mike nayi daki. Rahma na kwance, tana kallo a waya. Gefen ta na zauna ina fad'in "Tashi kiga na samo miki sunscreen. Yanda rana ya bata miki fuskan nan."
Ajiye wayan tayi, tana kallon ledojin. Daya bayan daya ta fiddo abubuwan da ke ciki. "Lallai Anty Siyama" tabe baki tayi, ta koma ta kwanta.
K'ara dagowa tayi "Wai ina kika sa wayan ki? Sau biyu Ya Jabir na k'ira na yana neman ki?"
Sai lokacin na tuna wayan a silent take. Cirewa nayi, na k'ira sa. Yanda jiki na yayi sanyi ne yasa ban wani saki jiki munyi hira mai kyau dashi ba.
"Noorie, albishirin ki."
"Goro" k'asa k'asa na amsa. Na lura sabanin ni da na shiga rudani, yau Jabir cikin wani irin farin ciki yake. Haka yasa bai d'ago ni sosai ba.
"Na gaya ma Yaya Sabo maganan zuwa tambaya in na dawo. Yaji dadin abun sosai, kinsan daman na gaya miki ya na ta min maganan aure. Shine fa yace zai bani daki daga cikin gidan hayan sa na sabon Unguwan nan in zauna."
"Ma Sha Allah, gaskiya abu yayi kyau." Har cikin raina na fad'i maganan. Don nasan gidan, akwai k'awata da aka taba kaiwa nan farkon auren ta ya kaini. Shine yake gaya min gidan Yayan sa ne. Daki biyu ne da falo, hadda dinning area, kitchen da store hatta toilet guda biyu ne. Ga wadataccen filin tsakan gida. Duk da flat hudu ne a gidan. Tabbas, samun kaman wannan a matsayin Jabir ba k'aramin cigaba bane. Sannan ko bakomai, in har na auri Jabir ba zan so mu zauna a unguwanmu ko kusa da damu in ba ma.
"Daman ance min ba a neman kudin aure, ban yadda ba sai da abun ya zo kaina. Kinga fa har lefe, in zaka yi auren farko a gidanmu yi maka ake." Ya K'ara fad'i. Da ke Unguwa daya aka taso nasan abubuwan gidan nasu sosai. Don akwai k'annen sa da suke cousins ma k'awayena da suka yi auri. Suna dayawa sosai, hakan yasa duk wani sha'ani ake taruwa a rufawa juna asiri a tsakanin su.
"Ai ina dawowa yau, to fa washegari za azo."
"To miye na azarbabin kuma?" Da tsokana nayi maganan, don zuwa lokacin na fara sakewa.
"Hmmm!" Dariya ya danyi "Noorie kina wasa da soyayyan da nake miki ko? Ke nifa da zai yiwu ma, sai ince ayi komai kafin na dawo."
"Bafa guduwa zanyi." A tare muka dan d'ara. Yace "Allah ya bar min ke Noorie na."
Cikin kwarin guiwa na amsa masa da "Ameen Nurul qalb."
"Me zan kawo miki in zan dawo?"
Dan jim nayi ina tunani, can nace mai "Abinda kasan zai dace dani, I trust you love."
Wani murmushin nishadi, mai dan k'ara yayi "Shikenan, nasan abinda zai faranta ruhin ki, My Noorie."
Duk sanda na ke magana da Jabir, sai in dinga ganin kaman rabuwa dashi wani ganganci ne da zan ma kaina. Yanzun ma hakan na dinga ji. Don haka muna gama wayan, na kwanta kawai jiki na a sanyaye.
Ina cikin juye juye na, Ina tunanin wani hanya zanbi don samo mafitan ga abinda ke shirin kunno kai a rayuwata. Naga tsohuwan wayan da har yanzu sim ina ke ciki yayi haske. Jawo sa nayi, ai bansan lokacin da na mik'e tsaye kan kafafuna Ina k'are ma wayan kallo ba.
Kafin can na silale k'asa. Rudewa iya rudewa, ciki na har wani k'ara naji ya fara. Ya zanyi? Ina son Jabir, Ina son kudi.
A/N: Shin wa zai ci gasar? Wa zai saki nasaran d'aukan Siyama? Jabir ko Naira?
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top