Naira 4

Har na fara shirin tafiya saloon in ban san ta ina kudin zasu fito ba. Ni dai sisi bana maganin sa. Mama ma fama take da kanta, kudin aikin da tayi jiya ma ba a biya ta ba. Wannan na daga cikin dalilin da yasa ban son yin aikin. A yanda nake ganin inda aka cigaba, sai an biya kudin ma mutum ke aikin. Shiyasa dole mutum ya nemi canji a rayuwa. Cike da takaici na ja tsakin da bansan ma ya fito ba.

"Lafiya?" Rahma ta ambata sanda take kutso kai cikin dakin. Dawowan ta daga wurin aiki kenan. K'are mata kallo nayi ina jinjina yanda take iya fita cikin wannan ranar da ake kwalawa. Akan kudin da bai taka kara ya karye ba.

"Ke kam duk rana ya miki tabo a fuska."

Cire Hijab in jikin ta tayi tana mai zama kan lumtsatsiyar katifanmu "Anty Siyama kenan, halal ai da wuya."

Tab'e baki nayi "Wani halal in ba. Amma wannan kam ai wahala ne kawai. Kud'in da a Saloon kadai ma sai a kashe su."

Zaro idanuwa Rahma tayi "Kai Anty Siyama, dubu ashirin a Saloon? Wannan ai almubazarranci nema."

Kaji irin ta ba? Na ayyana a raina. In ba haka ba nawa dubu 20 yake da za a kira sa almubazarranci? Inaaa dole na nema mana mafita. Na lura burin y'an gidanmu sam ba iri d'aya bane da nawa. Su na rufin asiri suke nema, nikam wanda zai canja mana rayuwa ne a gabana.

K'in tanka Rahma nayi da ke cewa "Kedai Anty Siyama wannan burin Allah ya wadata Ya Jabir kawai."

Jabir in na kira. Bayan mun gama musayan kalmomin soyayya nace masa "Jay, Saloon fa zani." Shiru ya d'anyi, kafin yace "To nawa zai isheki?"

Tsayawa kiyasta adadin da ya kamata in fada mai nayi. Na dai san da wuya zan same su.

"Shikenan zan aiko miki da 1500 kiyi hakuri kinji, ina had'a kud'in da zanyi tafiya ne." Yayi maganan cikin sigan lallashi. Sai na ma rasa abinda zan ce. Nasan in ba Saloon in cikin Unguwa da basu iya komai ba, ba inda 1500 zai ishe ni gyaran gashi, kitso da lalle. Ba haka ba ma, ba abinda suka iya, duk kame kame ne kawai, ga uban kazantan da wurin ke min.

"Ina zaka je ba labari?" So nake na kauda zancen. Don in zanyi magana ma, ce mai zanyi ya bar kudin sa. A hakan ma nasan gani yake k'ok'ari yayi.

"Kedai bari, anjima in na dawo zamu yi maganan."

Yana kashe wayan nayi dialling numban mutumina.

"Pretty girl"

Murmushi nayi, ina jinjina yanda a ko yaushe yake kokarin jaddada min nid'in mai kyau ce. Na d'ad'e da sanin hakan, saboda yanda mutane da dama ke fad'a. Amma nashin yana sanin jin kaina na k'ara fashewa, yana sani jin cewa tabbas ni din wata ce, na kuma kai a goga dani.

"Daman na kira ne in tambaya ka sauka lafiya?" Cikin dabara nayi maganan.

Murnar da naji dauke a muryan sa ya tabbatar min da yaji d'ad'in hakan. "lafiya k'alau na iso ba d'ad'ewa. Har kin dawo daga saloon in?"

"Ina fa, yanzu dai nake shirin tafiya. Ina son rana ya d'anyin sanyi."

"Ahh gaskiya fa ana rana. Amma ai naga ana d'ad'ewa, ai gwara kije da wuri saboda in samu in ganki ko?"

"Ehmm, nima na so hakan amma bara na fita yanzun." A raina, Ina addu'an ya dago zance na,  sai naji nauyin tambayan sa nake. Ba kaman sauran samarin da na kanyi ba."

"Gashi zan d'an fita yanzu, dana zo na sauke ki. Amma dai ba Napep zaki hau ba ko?" Zuciya ta naji ya tsinke, nasan dai yaga gidanmu balle yayi tunanin mota gare mu ma.

"To ya zanyi." Cikin shagwaba nayi maganan.

"No Pretty gaskiya bai kamata ba. Banyi supporting fita a public transport in nan ba. Ina zuwa." Kit! Ya kashe wayan.

Ba d'ad'ewa sai ga k'iran shi ya kara shigowa "Ki shirya Pretty, zan aiko driver ya kai ki. Zai kira sai ki mai kwatance ko?"

Habaa, bansan sanda na saki wani irin ajiyan zuciya ba.

Amma da yake nima yar duniya ce sai na gyara murya "Kai haba kuma harda wahala?"

"No no no, zafin nan da ake I won't tolerate ki hau Napep, wahala zaki Sha."

A haka muka yi sallama dashi, ba jimawa sai ga drivern ya kira ni.

Rahma da taga ina ta faman shiri ne tace "To wai Anty Siyama kuma ko tsoro ba kya ji? In yana da wata manufa fa?"

"Allah zai tsare." Handbag na dauka nayi waje.

Ina tsaya a kofar gida, saboda drivern kar ya kasa gane wurin sai ga Isiya mai shagon kusan da gidanmu.

"Ah afuwan Hajiya Siyama. Ko lokacin da Jabir in ya kirani bana kusa ne. Allah yasa ban b'ata miki lokaci ba."

Har ga Allah, sai da na d'au mintuna sannan na tuno yawanci shi Jabir ke ba kudi ko wani abu in bayanan ya bani.

Kafin ya bud'e shagon drivern ya iso. Ban tsaya bata lokaci ba nace mishi "Isiya bari sai na dawo in amsa." A raina ko, fadin nake na bar maka kudin kai ma ka huta. Don dai a yanzu nida 1500 ba dai a bani ba, sai dai nayi kyautan sa. Haka na dinga rayawa a raina. Ko da sisi bai shigo hannuna ba, ina da tabbacin samun abinda ya ninnika haka.

Ina k'ok'arin ma driver kwatancen Saloon in yace min ai oganshi ya bashi umurnin ya kaini wani wuri. Amma bari ya kira shi in ina da wanda nake so.

Hana shi k'iran nayi, kawai na rungume hanaye Ina jiran ganin inda zamu. Mun d'an yi tafi ba laifi, sannan yayi parking wurin da naga an rubuta Saloon and Spa.

"One minute Hajiya" Fita yayi, can sai gashi ya dawo da wata mace a bayan shi.

"Hajiya Barka da rana." Dan risinawa tayi alamun girmamawa. Kallo na k'are mata, ina ayyana matan zata bani kusan shekaru bakwai. Bansan sanda murmushi ya sauk'a a fuskana ba. Shakka babu, ina shirin shiga rayuwa ta daban, wanda ko a hange na ban yi tsammani ba.

"Hajiya, muna iya shiga daga ciki in ba matsala." Kallon ta na k'ara yi, ni din dai take jira. Cikin isa da takama na sauka daga motan nabi bayan ta ina taku da d'aid'aya. Tun daga haraban wurin na fahimci wuri ne na daban.

Saloon in da nayi niyyan zuwa dama inda Zainab tayi gyaran jiki da gyaran gashi lokacin bikin tane. Sosai ya tafi dani, amma yanzu na fahimci k'aramin alhaki ne.

Wani magazine suka bani, in zabi abinda nake bukata. Wasu abubuwan ma ni bansan su ba. Gudun, kar inyi k'auyanci yasa ni pointing steaming in gashi da kitso, sai pedicure, manicure da Jan lalle.

Nan take kuwa naga aiki da cikawa. Ana wanke min kai, wata na wanke min k'afa, daya kuma farcen hannuna ta ke gyarawa.

Sai gashi ba a ida awa biyu ba, angama min komai sai lallen da nake jira yayi. Shi dinma sunce awa daya ne kawai, an mai had'in mai karfi da zai yi saurin kamawa.

Ana cire lallen kiran shi ya shigo.

"Pretty an gama ko?"

"Eh yanzu zan bar wurin."

"To nace wa drivern zai taho dake inda nake."

Shiru nayi, ina jin wani d'ar ya diran min a zuciya.

"Ko da wani matsala ne?"

Da sauri nace "Aa daman dai ina son sake shiryawa ne. Duk na gama zufa a saloon."

"Ba matsala, zaki iya shiryawa a nan. Kinga dare yayi, ina bukatan lokaci dayawa a tare da ke."

Ji nayi zuciya na ya tsinke. Amma a k'asan raina kuwa sai na ayyana ai koma miye dai da wayau na.

"Kaya fa?"

"Karki damu, za a kula dashi."

"Anya kuwa?" Na ambata a raina. Sai kuma wani sashe na zuciyana yace haba Siyama, ya kike tunani kaman baki waye ba? Ke fa yanzu Babban yarinya ce. Murmushi na saki, ji ma nake kaman in tashi sama.

"Shikenan, sai na iso."

Bakin wani rantsatsen gida drivern yayi horn. Maigadi ya bude. Kai tun daga yanayin unguwan kasan ba gidan banza za a shuga ba. Yana parking wani ya k'araso bakin motan ya bud'e min kofa. "Welcome ma." Turus nayi ina kallon sa. Kafin tunani na ya sanar min bai kamata ina haka ba gudun raini. Kafafuwana na ziro kasa, kafin na mike a hankali na bi bayan sa. Sai a lokacin na lura daga drivern, mai gadin da wannan da bansan waye ba duk kaya iri daya ke jikin su.

"You can enter please ma." Bude k'ofan yayi ya ja ya tsaya.

Cigaba da takun da sai yau nima nasan na iya shi nayi na shiga cikin gidan. Hankalina ya kusa dauke wa sanda na dira a falon. Nima duk iya rayuwata inba a film ba ban taba ganin wuri mai kyau haka ba. Bansan sanda na fara kalle kalle ba, cike da kauyanci.

"Barka da zuwa Hajiya." Muryan ne ya katse ni. Da sauri na dawo cikin hayyacina. Dattijuwar mata ce tsaye a gabana, tana dan murmusawa. Ina ga tarbiyyan gida, unguwan da Islamiyya ne ya sani dan rusunawa, sai gashi ina gaishe ta. Da sauri ta d'ago ni "Aa Hajiya." Tana dai fara'a a fuskan ta ba.

"Bismillah mu shiga ciki ko?" Bin bayan ta nayi. Idanu na kuwa, sun kasa daina k'arewa ko ina muka wuce kallo. Sai nama rasa tunanin da zanyi.

Rawa jiki na ya kama sanda muka shiga wani daki. Daki ne da girman shi zai yi falo da dakunan gidanmu baki d'aya. Ga wani rantsatsen gado da aka shimfida da wani irin bargo. Ta gefe daya kuma ga wasu hadaddun kujeru da yawan kallon indian film yasa nasan na daki ne. Ba dai tarkace dayawa amma gabadaya nikam ya tafi da Imani na.

"Hajiya ya zan had'a miki ruwan wanka." Tofaaa, daman ruwan wanka ma da yanayin da ake hada shi? Ni banma san ana hadawa mutum ruwan wanka ba.

"Ina nufin kina son shi da zafi sosai ko da d:imi." Kaman ince mata koya ma tayi ba laifi amma sai zuciya na ya gargad'e ni. "Ina ga mai d'imin zai fi."

Juyawa tayi ta nufi wani kofa. Ni kuwa na cigaba da karewa dakin kallo. Ko bangon ba wani hayaniya, agogo ne kawai a mak'ale.

Hmmm! Bansan ana wankan dadi ba sai yau. Dama ashe har wurin wanka sai da muka bambanta da masu kudi? Ji turare fa, su ashe tun daga ruwan wanka suke zubawa. Shiyasa suyi ta kamshi, ashe sirrin kenan? Haka na fito wankan nan, Ina wani irin kamshi mai sanyaya jikin D'an Adam. Ni fa ko da tawul in da na daura aka barni, ai nagode. Gaskiya kudi duniya ne, ko mutum bai so dole ya so shi.

A/N: Naira ba a ganin ki a yaga, in ba mhaukaci ba 😚

Sorry for not updating, am quite busy ne shiyasa. But you can check my Instagram page @aysher.bee nayi nisa a can.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top