Naira 14
Daya daga cikin ma'aikatan dake cike a gidan ne ta min jagora har zuwa falon. Yanayin da na gansu sai da gaba na ya tsinke nan take.
Dukkansu suna zaune a kasa ne, yayin da k'afafun nashi ke kan tumtum, da wani tray a kasa tana gyara masa farce. Tashin muryoyin su ne ya cika falon. Cikin nishadi harda darawa suke magana. Hiran da yayi matukar tafiya dasu kuwa saboda ko sallaman da nayi Ina da tabbacin ba wanda yaji a cikin su.
Sallaman na k'ara cikin hade zuciya. Ai ma sai ana son mutum ake kishin sa. Bansan tsakanin Alhaji Usman da matan sa ba. Amma a yau kallo daya na musu na fahimci alaqa ce mai karfi.
"Ah Amarya har kin shigo kenan, Bismillah zo ki zauna mana." Alhajin ne yayi maganan bayan sun amsa sallaman. Sai nayi zuru ina kallon sa, domin nikam tunda muke dashi ban taba jin ya kira ni hakan ba. A raina nace, yau ba pretty kenan? Ko da yake ga pretty nan a gaban sa.
Dagowa tayi fuskan ta ba yabo ba fallasa ta zuba a kaina. Wlh bansan sanda na bude baki ina gaishe ta ba. K'ak'alo murmushi tayi ta amsa, sannan ta mike.
Wani irin kululu naji ciki na ya bada bayan mikewan ta. Sai na tsinci kaina da ambaton miye dalilin Alhaji Usman da ya aure ni? Meyesa yake k'ira na da pretty bayan yana da wannan matan a cikin gidan sa? Abu d'aya nake ganin zan nuna mata, shine kuma haske. Baya ga nan sam banga makusa a jikin ta ba. Baka ce kam, amma bakin ya matukar mata kyau. Sannan ko ni da nake kishiyan ta na shaida kyakyawace ajin farko.
Mai aiki ta kira ta tattare wurin da suka yi gyaran farcen. Ba dar ko wani shakka ta zo inda yake zaune ta zauna cikin wani salo da alamun jikin ta yabi. Hannun ta naga ya kamo yana ambaton mata "Sannu My queen na baki aiki ko? Nifa ko ina nake nafi son in bari sai mun hadu ki min gyara farcen nan, banga wanda ya kai ki iyawa ba kaf yawo na a duniya."
Kanne ido tayi, tana mai magana a hankali. Sai naga sun sa dariya. Kaman inyi tsuntsuwa in bar wurin haka naji. Sai nake ganin kaman ana yi ne don a muzanta ni. Na sha ganin Alhaji yana zuba min idanu in muna tare dashi, amma irin kallon da naga yana ma matar nan daban ne. Kallo ne na natsuwa da nishadi, kallon soyayya tsantsan da na haddace daga idanun Jabir.
"Afuwan Amarya, ya bakun ta da gajiyan Hanya?" Cikin murmushi da sakin fuska sosai tayi magana. Tabbas wayewa ya samu wurin zama.
Amsa nata nayi ina ambaton "Mun same ku lafiya? Ya yaran?"
"Muhibba ce kawai a gida ai. Gobe zata shigo ku gaisa. Yayyinta na boarding school." Murmushi nayi, yayin da a raina na hau ayyana ko meyesa ake cewa tana yawo tana barin yara? Tunda naga duk suna boarding.
Daga nan falon ya dau shiru. Sai kayan motsa baki da ta sa aka kawo min. A takaice dai ita ta tarbe ni a falon mijin mu. Zuwa can suka hau hiran su, su biyu. Sai nake jina kaman wata jemage a cikin su. A tunanina, ya kira ni ne ya mana nasiha da na sha jin miji nayi a tsakanin matan sa sannan a raba kwana. Ko dan mu bama a wuri d'aya zamu zauna bane? Tun ina sauraran su sama sama suna hira, har na fara jin baccin yana diba na. Don haka na mike domin in musu sallama. Tun da dai naga zaman ba nawa bane.
Cikin kasalalliyar murya na furta "Zan koma, sai da safen ku."
"Da wuri haka?" Ta furta tana murmushi, Wanda na kasa gane na mugunta ne ko kirki. "Gashi dai kin kasa sakin jikin ki Amarya."
Sai cewa yayi "Ai sai a hankali queen."
"Toh shikenan sai da safe mun gode."
Cikin sanyi jiki na koma sashe na. Raina ya gaza tsaida mai ma ya kamata inji ne. Ban son wahalar da kaina, don da alamun matar nan nashi ta kere min da komai. Ilimi, wayewa, kudi to shi meya ja hankalin sa a kaina? Abinda ya min tsaye har washegari kenan domin Nadabo ko kara leko ni bai yi ba.
Ina k'ok'arin yin breakfast in da aka shirya kace wata Gimbiya sai ga k'iran Amira ya shigo wayana.
"Anty Amarya, Kun iso lafiya?" Amsa mata nayi. Tace "Yaushe zaku wuce to?"
"Gaskiya bai fada min ba."
"To shikenan zan shigo anjima." Daga haka muka yi sallama. Na cigaba da rayuwata ni kadai a sashe na. Mutumin nan ko waya, hakan yana karasa ni jin wani irin sanyi na ratsa ko wani sassa na jiki na.
Ban damu da cewa a shirya abincin rana na mutum biyu ba saboda zuwan Amira. Naga abinda sai ke shirya wa mutum biyar zasu ci su koshi tsaf abin su.
Bayan Azahar Amira da Maijidda, sakon Amira suka iso gida. Na tarbe su ina dar dar domin dai har yanzu ban wani gama sakin jiki dasu ba. Har gwara ma Amiran.
"Na ji ance a Singapore za a ajiye ki?"
"Eh zan shiga School ne." Na amsa ma Anty Maijiddan. Wani girgiza kai naga tayi cikin takaici "Kash! Naso ai duk inda zai je ki bishi ne, muga ta tsiya."
Amira tace "Kedai bari Sister. Amma kun hadu da sarauniyar tunda kuka iso? Ko mulkin nata bai bari ya hada ku ba.
Ganin sun tabo inda ke min kaikayi ya sani fadin "Jiya mun gaisa a side insu." Shiru nayi, Ina tunanin me zan ce.
Sai Majiddan ta cab'e "Ya muku fad'a tsakanin ku?"
Girgiza kai nayi "Kila sai gaba, gaisawa kawai mu kayi na dawo."
"Ai ba zata bari ba" suka fad'a a tare.
Kaman wacce aka matsewa baki sai gani ina fad'in "Ni rabo na dashi ma tun jiyan."
"Ah ah ah ah" Amira tayi maganan tana cije leb'e "Haba Anty Amarya, kaman ba Yan matan zamani ba? Mikewa zaki yi ai, zama bai ganki ba fa. Matar nan da kike ganin ba Allah a ranta. Yanzu sai tayi Kane Kane ta nuna ita kadai ke da mijin ai."
"Ina bai raba muku kwana ba kika ce?" Maijidda ta tambaya, na girgiza Kai.
To tashi maza muna jiran ki, kije kice kin Zo gaishe shi ne.
Mikewa nayi cikin dar dar na nufin sashen nashi. Falon tsit ba kowa don haka na juya, cikin sanyi jiki na koma sashe na.
"Yaya dai?"
"Ba kowa a falon" na basu amsa.
Maijidda tayi saurin shan mur "Haba Dan Allah, Banda abin ki ai dakin zaki shiga." Zaro idanu nayi. Tace "Tabdijam akwai aiki kice."
"Kinsan Allah in baki yi wasa ba Yar kallo za a maida ki keda mijin ki. Matsayin ku daya fa. Kar ki wani ji tsoron ta. Matan nan makira ce ta karshe..." Maijiddan ne tayi saurin dakatar da Amira.
"Siyama ina miki kallon wayyaya kar ki bada ni mana. Ba fa abinda take dashi da zata nuna miki. Kuma abun nan da zaki yi bauta ne. Kije maza ki gaida mijin ki, lada ma za a rubuta miki."
Cikin karfin guiwa na koma side in. Kai tsaye na nufi hanyan bedroom in bayan na tambayi masu aikin sun nuna min, ganin akwai kofofi dayawa a side in.
Da Sallama a baki na, na murd'a handle in. Bansan ya aka yi ba, muna had'a idanu da ita naji duk wani kwarin guiwa da na taho dashi ya kau. Wani irin kallo ta bini dashi, ba shiri naji jikina ya dau kyarma.
"In Ina kwana?" Girgiza kai tayi, kai tsaye ta furta "Lafiya kalau?" Ta amsa da alaman tambaya. Ga dukkan alamu so ta ke taji dalilin tsayuwana a nan.
Bata sauke idanun ta, tuno maganganun su Amira ya sani hade rai nima. "Nazo gaishe shine." Kokarin shigowa dakin nayi, maganan ta ya dakatar dani.
"Ki jira shi a falo, ya shiga wanka." Daga haka ta juya, ta cigaba da danna wayan ta.
Jiki a sakwanne na fita, a raina ina ayyana ba shakka da gaskiyan su Amira. Sai kuma naji kunya komawa in sanar dasu abinda ya faru. Sai nayi zaune a falon kawai ina zulumi, duk da har k'asan raina ba son zaman nake ba.
A k'alla sai da nayi minti fiye da ashirin duk na gama kosawa. Can naji tashin muryoyin su cikin raha. A tare suka fito, sunan darawa. Sai da suka fito falon ta k'are min kallo. "Ah Habibi na manta fa Amaryan ka na jiranka ashe."
Kallo ya zuba min ba tare da ya amsa gaisuwan da nake shirin yi mai ba. Irin kallon da ma kina nan. Ba sai naji gaba na ya bada wani fat! Ba.
"Kije part inki ina zuwa." Wurin irin tuk'ik'in bakin ciki naji ya tsaya min a wuya. A raina ko na hau ambaton "Ya ilahi! Mena ja ma kaina? Ko kuwa ince mai su Amira suka jama min?" Tilas na k'ak'alo murmushin dole saboda su Amira, ban son suga gazawa na su raina min. Hakika sun min adalci ma da suka share nasu suka karbe ni, bai kuma kyautu ace na watsa musu k'asa a idanu ba.
Ba jimawa sai gashi ya shigo, Su Amira na gaishe sa ko amsawa bai yi ba. Kallon su kawai yayi sai gashi sun mike sunyi daki.
"Sannu da bakun ta pretty." Ban amsa shi ba. Fuskan sa ba yabo ba fallasa ya sake fad'in "Koda yake ma na gama ai har kin zama yar gida. Kina da buk'atan wani abu ne?"
Sai na ma rasa me zance mishi. Ba kuwa tare da ya jira nayi maganan ba yace "Na miki transfer in kud'i. Next time duk abinda kike da buk'atan ki tura min message kawai. Ko ki jira in na gama zan zo nan ba sai kinje part in can ba." Tsakanin shi da Allah yayi maganan. Takaici yasa na kasa amsa mishi ma.
"Da wani abu kuma?" Banza naso inyi dashi, sai dai kwarjinin shi da girman sa da kan cika min idanu ya sani girgiza kai a hankali.
"Shikenan zamu fita da Maman Muhibba. Ki zauna cikin shiri dai ko yaushe zamu iya tafiya."
Wannan karon kam ko amsa bai jira na bad'a ba ya mike yayi waje. Ba sai na tsinci kaina da tambayan da ya min tsaye a rai ba. Shin wa nake aure?
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top