Naira 13

Duk iya tunanina da hange na ban tab'a kawo cewa bikina zai iya kai haka ba. Tun daga ranar da na fara bridal shower nake ganin abun kaman a mafarki. Barin ma in na duba naga irin kud'ad'en dake shak'e da account ina. Kusan duk bayan kwana biyu sai Alhaji Usman ya turo min. Abu k'arami in ina bukata Amira zata ce min "K'ira shi ki fad'a mishi zai baki." Ko na gaya mata akwai kud'i a hannuna zata ce "Wannan ai na daban ne." Ganin ina samu in, har na saba da tambayan.

Hatta da gidanmu sai da nasa aka gyara ko ina. Abu d'aya na arziki da zan ce gashi mahaifin mu ya mana a rayuwa kenan. Shine na wadata mu da muhalli. A gine ya siye shi, kusan dukanmu a nan aka haife mu. Yaya ne kawai kafin su dawo. Da naga kud'in kullum shigowa suke, har siminti nasa aka yi a tsakan gidan, dake akwai wadataccen fili. Zulumi na, daya kar wani daga cikin dangin Alhaji Usman ya ga gidanmu ya raina mana. Ballantana kuma yan'uwa ne da uwar gidan. Don haka dole sai da taka tsan tsan. Musamman na ware kud'i na ma Mama set in gado madaidaici, da kujerun hana gori a falo. Sai dakinmu da Rahma na canja katifan.

Biki na yayi suna. Musamman saboda yanda aka tsara sa. Hatta da photographer, na manyan mutane aka d'auka. Kan kace mai, sai ga pictures ina na Bridal shower da Kamu na trending a social media. Wedding blogs sai faman d'aurawa suke tayi. Kaman in ta kurma ihu dan murna, kaina kaman zai fashe. Duk yanda nake hango bikin Zainab, ya gama birge ni. Har nake tunanin ba mamaki bazan k'ara zuwa bikin irin shi ba. Sai ga shi, wai yau nawan ne ya zama abun kwatance a ko ina. Hadda wadanda ban sani ba d'aura ni suke. Barin yadda make up artist in ta dage ta fito dani, duk da nasan kud'ina yayi aiki ne. Kamu na ya had'u matakin karshe ma kuwa. Tun daga kan yanda aka k'awata wurin zuwa shiga kala ukun da nayi duk abun kallo ne. Mama da na ganta a ranar, sai da naji wani kwallan murna ya cika min idanu. Daman musamman na shirya mata shiga ta alfarma yanda za a san ita din ta musamman ce a ranar. Duk dai yaran gidan mu ba wanda yayi shigan banza.

Ana washegari d'aurin aure Alhaji Usman ya k'ira ni yana sanar dani ya shigo gari. Sai naji abun wani irin, sam ban wani dokin zuwan nasa kaman yanda nake dokin bikin. Damuwa na d'aya yanda aka fara comments "Wai ina angon?" ta ko Ina. Sai kuma nayi hamdallah. Alhajin bai da muni ko kad'an balle ayi ta tsegumi.

Tsakani na da Alhaji Usman kuwa sai a wurin picture in ranar biki. Muna had'uwa ya bini da wani irin kallo, sai naga ya saki k'ayataccen murmushi.

Hannuna ya koma duka biyu yana kare musu kallo. Zuwa yanzu na fahimci yanda yake son lalle. "Wannan kyau haka pretty? Ni da nake angon ma ba za a ragan min ba?" Cikin nishad'i yake magana. Jikin sa har wani irin rawa naga yanayi, yana cigaba da kallo na. Da k'yar ya saita kansa aka fara daukan mu hotuna. Tun Ina marmarin abun har na gaji.

Photographer na kokarin creating mana wani style in, naji raina duk ya jagule. "Wai bai isa ba?" Wani irin harara Amira ta sakan min. A kunne ta rad'a min "Baki son yau mu tada hawan jini ne? Duk munafuncin rashin zuwa dai duk inda hotuna suke sai an ganshi." A fili kuma tace "Gyara kinji, a samu na sawa a social media. Let show them abinda basu dashi. Duk Wanda ya shiga Social media bai da wani sukuni, ya dinga cin karo da hotunan kenan." Wani irin kallo naga Yayan nata ya jefa mata. Ta dauke idanun ta.

Maganan ta ne ya k'ara fad'ad'a min kai har yasa naji gajiyan ma na neman washewa.

Bayan angama picture in ne yaja hannuna zuwa daya daga cikin dakin da aka kama a hotel in. Cikin natsuwa, ya jawo ni jikin sa. Kamshin jikin sa bakidaya ya gauraye da nawa. Natsuwa na tsammaci inji, sai gashi na tsinci kaina da hawaye. Wannan abun da ke faruwa ban taba hango shi da wani bayan Jabir ba. Shi naci alwashi, shi na dauka zai fara samun hakkin mallakata.

A kunne ya rad'a "Pretty hakika na kasance mai sa'a a rayuwata. Samun ki alkhairi ne. Allah ya bani ikon rike ki iya karshen rayuwata." Wani kwallan na k'ara jin ya cika min idanu. Ni banyi niyya zama dashi da nisa ba ma balle wani har abada. D'ago ni yayi, yana ganin hawayen ya rikice ya hau k'ok'arin goge min.

Ranar da daddare aka dauko Amarya. Kai tsaye gidan kakarsu da ya fara kaini aka wuce dani. Washegari aka yi bud'an kai da dinner. Ko ana surutai ma, ni dai da kunnena ban ji ba. Banda su Amira dake ta faman mitan k'in zuwan matar Alhaji Usman. Nidai ko nice ba zuwan zan ba. Anan nake jin ba ta ma k'asan baki daya. Ni dadi ne ya mamaye ni, don nima ana daura auren ba yarda zanyi ba. Sai ya kaini yawon shak'atawa.

Daga wurin dinner aka wuce dani gida na. Da naga irin tsarin da aka zubawa gidan. Sai da na raina kaina. Har ina tunanin me za a gyara? Naga gyara kuwa na aji. Kawayena sai santin gidan suke, kaman suyi ya. Girma na ya k'ara kankaruwa da kyau a wurin su. Haka da aka zo siyan baki, dubu d'ari uku aka basu. Kaman in rungume Alhaji Usman a wurin don murna.

Allah da ikon sa, sai gashi angama biki an watse. Banda wani tunani sai na Jabir. Shima a hankali ya fara washewa, to wani Jabir irin wannan Aljannar duniyan da na tsinci kaina a ciki? Ban aikin komai, sai bacci da cin abinci. Ba irin abun da babu a fridge da store ina. Ga kudi shak'e a account ina. Wannan kad'ai na samun farin ciki da alfahari da mijina. Shi dinma haka yake rawan jiki akaina. Tun kafin In furta abu ya min shi. Satin mu uku da aure yace zai tafi Abuja. Tab'ara ta samu wuri nan na hau mishi sakalci, akan nikam ba zai tafi ya barni ba. Da k'yar da siddin goshi ya lallabe ni, bayan naji alert in dumin kudi.

Yana tafiya na kira Rahma ina tambayan ta ko akwai abinda suke bukatan "Anty Siyama, wancan satin fa, Alhaji ya aiko mana da kayan abinci ba abinda babu. Kuma ya ba Mama da Baba kud'i. Da kudin Maman take amfani tana mana cefane, komai muna dashi."

Ajiyan zuciya na saki, ina jin murna na ratsa ko ina na jikina "To Rahma kaya fa"

Murmushi tayi k'asa k'asa. Sai kuma na tambaye ta ko har yanzun tana zuwa wurin aikin. "To Anty Siyama sai in ta zaman gida? Kud'in ma ai zai mana amfani."

"In dai dubu ashirin ne. Ki daina zuwa zan baki abinda ya fishi a wata ma."

"Hajiya ta" ta fad'a tana dariya.

Nan dai na takura mata sai dai tazo mu zauna. Haka na dauke ta muka je muka siyo ma kowa kayayyaki, hadda Anty Aisha da yaran ta da kuma Ameer da Maman sa. Duk da dai Yayan har yanzu fushi yake dani. Gaisuwana ma sai da Mama ta mai fad'a sannan ya fara amsawa.

Kafin Alhaji Usman ya dawo yasa aka min Visa. Don haka yana dawowa ya dauke ni muka luluk'a duniya. Saudia muka fara zuwa, daganan likafa ta cigaba. Naga duniya ta ganni. Wani lokacin jina nake kaman wata mai tashi a sararin samaniya. K'asa da ta kai k'asa haka muka dinga ratsawa. Gashi lallaba ni yake kaman ya cinye. Da abinda nake so, da wanda bansan shi ba ma duk Alhaji Usman ya min. Duniya ta min dadi, ta kuma zo min fiye ma da yanda nake tsammani. Tuni na manta da wani batun soyayya, na kama masoyin ainihi, wato Naira. Mafitan dukkan wani bawa. Nan na hau tunanin irin wautan da mutane suke kudi na bibiyan su su bi wani soyayya. Ni dai kam Allah ya tsamo ni. Kare na kawai nake ci babu babbaka.

Muna can nake jin labarin anyi calling up strike. Da na gaya masa sai cemin yayi "Ai ke kin gama makarantan nan Pretty. Wani zan sama miki." Nima daman ba son komawa in nake ba. Don haka ma na share maganan. Muka cigaba da watayawan mu.

K'asar Singapore ne muka fi d'ad'ewa, saboda  yawan hidiman da yake yi anan in. Na gane akwai abinda yake a garin. Inda muka yi masauki. Na kara tabbaatarwa da yace min zai sama min gida da makaranta a nan, in dai zan zauna, sai nayi karatun a nan. Har wani bukatan amincewa na yake. A sittin na yarda. Cikin kwana uku yazo yace min duka an samu.

Gida na, na Nigeria yafi na nan in girma sosai. Sai dai tsarin da wannan in ya tafi da mai irin gigitar da d'an Adam ne. Wani abun duk yanda za a gaya maka ba zaka fahimta ba sai ka ganshi. Kasa natsuwa nayi, duk na susuce hadda dan tsalle tsalle. Yayi ta min dariya.

Bayan Sati biyu muka dawo Nigeria akan  zanma mutane sallama. Sai in koma. Abuja muka farawa tsinke. Ban taba ganin gidan sa na Abujan bama sai dawowan mun nan. Ashe da yace yana gini bani kadai ya mawa ba. Sabon gida yayi hadda na matan sa. Ni gidan ma sai ya min kaman har yanzu a turan muke. Nifa duk tunani na bai bani Alhaji Usman na da irin wannan kud'in ba. A haka kuma har ya iya zuwa k'ofan gidanmu? Dole ya dinga gaya min kai tsaye zai turo magabatan sa a cikin umurni. Ai kuwa dai ya taimake ni. Side ina yasa aka min jagora. Ni wani abun ma sai ina ganin sa kaman a mafarki. Sai na duba naga gashinan dai zahiri ne ke faruwa.

Ranar bayan Magriba, ya kira ni a waya akan in same shi a side in farko. Wanda na fahimci shine nashi. "Pretty kizo ku gaisa da My queen ko?" Nan take gabana ya bada wani irin fat! Nagane ita yake k'ira hakan ne saboda wayan da suke yi.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top