Naira 12
Tun missed calls in da Alhaji Usman ya min, ban neme sa ba shima bai k'ara k'ira ba. To daman ni bata shi nake ba. Jabir ne dai, na k'ira sa yafi sau talatin, amma sam bai d'aga ba. Daga karshe ma kashe wayan sa yayi.
Baba tun ranar ya bar garin. Dama mota yake ja, gari zuwa gari. Shiyasa ba a ganin sa ma balle a tambaye sa kudi sau da dama. Wani lokaci ma sai ya shigo garin washegari ya k'ara kama hanya bai dawo gidan ba. Ni Allah na tuba ma, ba son zuwan nasa nake ba ma. Banda masifa to ba abinda yake. Mama kuwa Allah ya d'ora mata tsoron sa. Kullum kaji tana fada damu, tunanin ta kar muyi abu azo a gaya masa ya hau mata fad'a.
Wannan kadai in aka barni, ina ganin darasi ne da ya kamata in gujewa talauci. Domin da a ce yana bayarwan, ko bai zama ban ganin abun zai wani dame mu sosai kaman yanzun. Tunda na taso nake ganin mahaifiyata a wahala, bazan so ta dawwama a haka ba.
Wannan na daya daga cikin dalilin da na sare bayan na cigaba da k'iran Jabir da tura masa sako bai d'auka ba. Buri na daman ya fahimce ni, tun da abu yaci tura zan bari ya huce sai in tura masa da sa'kon hakuri ko ta takarda ne. In da rabon ni matar sane, sai yaga ko daga baya munyi aure.
Washegari da sassafe Alhaji Usman ya k'ira ni. Zai aiko driver yazo ya d'auke ni, akwai abubuwan da yake son yaji ra'ayina. Ban ma kowa magana ba a gidan na shirya, sai da na gama na gaya wa Mama. Allah ya tsare, kawai tace.
Gidan sa na garin, da yace zai ajiye ni muka je. A falon farko, na iske wata mata. Bayan mun gama gaisawa ta hau tambayana choices ina na kaya, da abubuwan da nake bukata da sizes.
Ban wani gaya mata abu dayawa ba. Da alamun dai sana'an tane had'a lefe. Da note inta, da komai a tsare. "Zan tafi Jibi, so kawai sai mu dinga magana ta WhatsApp ina tura miki kina gani right?"
Yarda nayi da shawaran ta. Duk da haka ta cigaba da tambayana abubuwa, tana min bayanin wasu. "Kina da wani specific cream da kike using, powders, spray, perfume."
"Kowanne ma zai yi." Cikin fahimta ta jinjina kai. "za dai mu dinga magana kawai" daga haka muka yi sharing contacts, ta min sallama ta wuce. Da alamun sun gama ganawa da Alhaji Usman in tuntuni.
K'iran sa nayi a waya, ganin ni kadai na rage a falon. Nan yasa aka kaini, wani hut dake ta wajen dinning area in ranar.
"Pretty har kun gama duk kyale kyalen ku na Mata?" Bayanin yanda muka yi da ita na mai.
Nan yasa aka kawo min breakfast daman ban ci komai a gida ba. Kallon sa kawai nake, yanda yake abubuwan a cikin natsuwa. A raina, ina hango wai wannan ne zai zama mijina. Sam, ban taba hango hakan ba.
Gadan gadan na lura shirin bikin ne a gaban sa. Sai a bakin sa nake jin cewa wai ashe wata biyu aka sa bikin. A raina na hau tunanin yanda y'an gidanmu zasu iya aurar dani cikin wannan lokacin, lafiyan Baba kuwa?
Kaman ya shiga zuciyana, sai naji yana maganan furnitures. "Yan kamfanin na kan hanya, in da wani abinda kike so sai ki musu bayani." Ni kam, idanu kawai na zuba masa. Ni inka barni furnitures da a yanzu suke gidan ma, sunyi. Ko da suka zo ma, sai dai suka yi ta nuna min furnitures in da ya gama tafiya da imani na. Da k'yar na rufe idanu na zab'a. Ji nake da za a barni ma, ni din mai daukan duka ne.
Ko dan abubuwan dana gani ne, ke kara tabbatar min da rayuwa na ya fara chanzawa tun daga yanzu. Sai naji abubuwan da ke damuna a jiya sun fara wartsakewa. Kawai nima na maida shirin auren nawa shine a gabana.
"Sai batun shirye shirye, ki gaya min abinda kike buk'ata kawai, sauran ma k'arasa maganan ta waya."
Kwalalo idanu nayi "Tafiya zaka yine?"
"Ehmm akwai Taron da zamuyi a Italy. Gobe zan wuce Lagos. Daga can jirgin mu zai d'aga."
"Sai yaushe?"
Murmushi yayi, yana shafa kasa gemun sa yace "Amarya na bata so tayi nesa dani ko?"
Marairai ce fuska nayi, da shagwaba nace "Eh mana ni kadai zaka bari da shirye shiryen kenan."
"Ba zaki wani wahala ba ai. Zan dawo satin bikin In Sha Allah."
Har ga raina, naji banji dadin tafiyan nasa ba. Amma to yana iya? Ashe shi har da gidan ya ke da niyyan k'ara gyarawa, Kuma wai duk a sati shiddan. Ina zaune yana min bayani, tsarin da yake so a maida gidan. Nikam dai ba wani ganewa nake ba. A raina dai ina ta ayyana in kudi ya ma mutum yawa, to fa ba abinda ba zai ba.
Bayan ya gama ne, yasa aka m'iko masa keyn mota. Kallona yayi yana murmushi "Pretty muje ki raka ni Unguwa ko?"
Tuno abinda ya min ranan nayi, don haka nace masa "Ba dai gaisuwa zaka k'ara kaini hannu rabbana ba."
Sai da ya d'an dara yace min "Hajiya zan Kai ki, ki gaida. Shekaran jiya ta dawo, an mata aiki a k'afa." Hararan gefe ido na masa. Sai naga ya wani zuba min idanuwa. Na dai lura sau da dama baya gajiya da kallo na.
"Da yanzu haka kake so inje, inji kunya ko?"
Murmushi kawai yayi "Sha'anin ku mata sai ku."
Haka dai ya tsaya, muka siyan mata fruits, drinks da gasashen kaza.
A falo muka tadda su suna hira. Ita da yaranta mata, da alamun dai duk sunyi aure don naga k'anana Yara. Ko dayake daman Zainab ta gaya min k'annen sa mata duk sunyi aure. Kana ganin su kaga wayayyu. Don faran faran muka gaisa dasu har suna tsokana na.
"Ba shakka, wannan ruwan kyau haka? Dole a tafi da Yaya Babba ai."
Dayan ta cab'e da cewa "Da kuwa yace shi baida ra'ayin k'ara aure ba." D'an darawa suka yi. Ta ukun su, Wanda da alama ita ce k'arama tace "Anty Amarya, events nawa za a mana ne?"
Ni dai murmushi kawai nayi. Ko dan ganin mahaifiyar su a wurin yasa ni kame baki. Kafin a mak'ala min rashin kunya tun yanzu.
Haka suka yi ta nan nan dani. K'aramar da naji suna kira Ameera ce tayi ta insisting maganan events. To ni daman banda wani shiri. Niyya ta, yau in na koma gida in kira Zainab. Tun da Itace tayi aure kwanan nan zata samu ideas.
"Anty Amarya, akwai fa event planner da nake son hada ki da ita ne. Sun iya tsara biki sosai wlh."
"To ke Amira ki amshi numbana ta mana ba sai ku karasa zancen a waya ba." Hajiyan ce da kanta tayi magana wannan karon. Nan take muka yi exchanging contacts da dukkan su. A raina na k'udiri aniyan zan tmby Amira numban Hajiyan in dinga k'ira ina gaishe ta. Sosai na k'ara yadda da maganan Zainab da tace dukkansu murna suke da bikin. Don ma dai duk sun girme ni, hatta Amiran kuwa.
"Y'an gidan ku nada kirki." Na sanar masa bayan mun bar gida. Murmushi kawai na ga yayi yana girgiza kai.
Ba jimawa ya sauke ni a k'ofan gidanmu. Kallon gidan namu nayi da nazo shiga. Nan take naji wani abu ya darsan min a rai. Ba abinda ya fad'o min sai k'ayataccen gidan da muka fito a yanzu da irin mutanen da suka fito daga cikin sa. Ba sai na hau zulumi ba, yanzu a haka zasu zo su ga gidanmu? Kar fa su raina ni. Tsoro ne ya fara mamaye ni. A haka na kwana ranar. Sai dai duk wani hanyan manufa bansan ta yanda zan bullo mai ba.
A bakin Yusuf nake jin an sallami Jabir jiya da dare. Yau kuma ya koma Lagos. Gabadaya kuma sai naji jikina yayi sanyi. Amma to ya zanyi? Mai afkuwa ya riga da ya fara. Tsakani ga Allah ina son Jabir. Kawai dai ina tsoron gobena a gidan sane.
Haka na daure nake kauda tunani sa. Har yau wani lokaci na kan kira amma bai dauka. Haka nake zama in ci kuka in gode Allah sannan in fuskanci abinda ke gabana.
Musamman Amira ta je ta dauke ni daga gidan Zainab. Ita ma maganan bikin naje muyi da ita. Wurin event planner in muka tafi. Wani tsari da aka fara min bayani, ban wani gane ba. Na dai fahimce gagarumin bikine suke son su shirya ma. Dinner da bud'an kai da kuma Walima Amiran tace za suyi. Nima daman biyu nake da niyya. Kamu sai friend's eve.
Irin kudin da matan tayi charging sai da ya girgiza ni. Ko d'ar Amiran ta ciro wayan ta tayi transfer. A gidan Zainab in ta k'ara sauke ni. Na bata labarin abinda ya auku "Wai Zainab daman akwai irin wannan kud'in banzan a k'asar nan?"
Dariya tayi tace "Kika sani ko angon naki ne zai biya ta." Nan dai muka bar maganan, muka gangara fannin anko. Guda uku, akan 38k ya kama. Zainab ince zata yi order insu. Don haka na barta tayi handling sha'anin ankon duka. Tunda dai nikam banda wanda zai iya ankon ko dubu goma ma a tsofin kawaye na. Shiyasa ma bazan wahalan da kaina ba in nuna musu. Rahma dai ce, nan take ma na bawa Zainab in kudin nata. Don Alhaji Usman bai bar k'asar ba, sai da naji alert in kudade da dama. Wanda na mai magana na fara abubuwan bikin.
Kwana ki naja, bikin na ta k'aratowa. Nice kawai nake shirye shiryena. Sai Rahma da take sa min hannu wani lokaci. Banda haka, y'an gidanmu ba abinda suke yi. Hatta Mama tunda nace mata yace ba sai an siya komai ba. Hankalin ta ya kwanta. Wacce zata had'o lefen aka bawa hadda ordern kayan kitchen. Y'an gidan namu ma, da zasu yi wani abun gidan nake so su gyara. Mama dai nasan gwagwarmaya take da abincin da za aci ma. Yanzu ko da muna da komai, sai dai kayan miya. Shima yawanci kafin ta ankara na bayar an siyo. Sai ya zamto a gidan, nike sawa ayi, ni kuma ke sawa a bari. Ba k'annena ba kawai, hatta Mama wani irin girma na, na fahimci tana gani.
A/N: Hajiya Siyama fa na dau hanya hutu tun yanzu. Amma hakan zai haifar da d'a mai Ido kuwa? Ku muje dai zuwa.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top