Naira 11
Bansan wani irin zuciya gare ni ba. Da ta gaza tantance abinda yafi mahimmanci a gare ta. Zuwa yanzu kuka nake sosai, har sautin muryana na fitowa. Tunda Maman Amir ta furta kalman ango wa Jabir, sauran sukuni na ya kau. Ba abinda na fara hangowa sai irin rayuwan walwala da nake hangowa kaina a gidan Alhaji Usman. Yanzu duk babu shi? Burin da na dinga yi na ganin na fidda yan gidanmu daga k'angin talauci duk ya kau kenan. To yanzu ya kawaye na zasu kalle ni. Shikenan naga samu naga rashi?
"Siyama lafiyan ki kuwa?" Maman Ameer ke maganan cikin kula. Ba k'aramin godiya na mata ba a raina da ta dauke ni daga wurin Jabir. Bayi ta kaini na wanke idanu na, tana ta bani baki akan aure fa ba wani tashin hankali bane. In kwantar da hankalina.
Kwanciya nayi a dakin ta, ina sakin ajiyan zuciya. Jabir dai ya kasa tafiya, duk da irin tsokanan da Maman Amir ke masa yau ya gaza ramawa. Can dai naji yana tambayan ta "Ke wai Ina mijin ki, tun dazu nake bid'an ganin sa."
"Ban son sharri, taka ta kawo ka." Suka cigaba da rahan su.
Can dai naji tana ce masa "Bayan da y'an gidan ku suka tafi, yace min zasu tafi can gidan Baba Aminu da Baba." Wani abu ne ya darsun min a rai. Sauri mik'ewa nayi na zauna. Me Baba ke shirin aikatawa?
Jin Jabir na ma Maman Ameer sallama ne yasa ni saurin mik:ewa nayi falon.
To daman shi dinma dubawa yake ko zan fito "Noorie ya dai?" Murmushi na mai. "Shine zaka tafi ba sallama?"
"Ban son in k'ara sa Amarya ta kuka ne."
Hade leb'e na nayi wuri d'aya. Zai yi magana wayan sa tayi k'ara. Cikin ladabi naji yana maganan. Bayan ya gama yace min "Bara naje Noorie Ya Sabo na nema na."
"Nagode." Da mamaki ya zuba min idanu. Sai Kuma ya min alamu da godiyan na mene.
"Na komai. Duk abinda ka tab'a min a rayuwa." Ni kaina zantukan sun min kama da na sallama.
"Wannan wayan fa?" Daga sama naji tambayan saboda tunanin da na fad'a.
Kallon wayan nayi. "Jeka, anjima in min had'u zan gaya maka." Idanu ya zuba min, kaman me neman yadda dani. Murmushi kawai na masa. Yana kallo na, ni kaina nasa karfin hali kawai yayi ya fita, saboda sanin girman da yake bawa wanda ya kirasan.
...
Ina shirin fita gidan, Baban Ameer ya shigo. Sai naga idanun sa sunyi ja, yana bina da wani irin kallo.
"Yaya lafiy..." Saurin dakatar dani yayi da hannun sa. Yana watsa min wani irin kallo. Bansan sanda jiki na ya d'au rawa ba. A iya sanina dashi, nikam ban taba ganin sa yana jefa min irin kallon nan ba.
"Dan iskanci mu zaki rainawa hankali Siyama?"
Shiru kawai nayi ina kallon sa. Na riga da na gaano me ke faruwa, ko kuma ma ince me ya faru kawai.
"Kinsan yaudaran sa zaki yi kika sa shi turo mutanen sa?"
Jiki na har yanzu rawa yake, girgiza kai na hau yi. Kawai sai ya ja tsaki, ya wuce ya barni a wurin. Da gudu na fita daga gidan. Ko ganin hanya ban yi da kyau a haka na isa gidanmu. Ina shiga, naci karo da Mama. Bansan sanda na fad'a jikin ta ba, na rushe da wani irin kuka mai k'ara. Tuni mutanen da basu gama tafiya a gidanmu ba suka taru a kaina.
Kowa tambayana yake me ke faruwa. Amma na kasa magana. "Ki daga ni in baza ki gaya min abinda ke faruwa ba." Mama tayi maganan cikin zuciya. Ganin haka, yasa Anty Aisha ta ja hannuna zuwa dakinmu.
Muna shiga, na iske Rahma a zaune ta sha tagumi. Sai naga itan ma idanuwan ta sunyi jajawur. Da sauri na k'arasa gare ta, Ina kamo hannuwan ta duka biyu "Shikenan Rahma an raba ni da Jabir, shi kenan na rasa masoyi na hak'ik'a da gaskiya."
Wani irin murmushi naga tayi mai ciwo. "Kin dai raba kanki dashi." Tana fad'in haka ta fara kokarin mikewa. Sakin ta nayi, na fad'a katifa ina cigaba da kuka na. Har mutane duk suka gama watsewa a gidan.
Anty Aisha ce kadai ta rage. Sallah la'asar tayi a dakinmu. Har lokacin kuma kukan nake. "Siyama tashi Dan Allah miye haka? Shi Alhaji Usman in wani ya kawo miki shi?"
Dago ni ta fara k'ok'arin yi. Ni ma na bita na tashi. Ina ganin yanda idanuwan ta duk suka gama fad'awa.
"Anty Aisha ni na kawo sa. Amma wlh zuciya na Jabir take so. Ku yadda dani mana."
"Ko na yadda dake in ba zai canja komai ba fa. An riga angama magana." Girgiza kai tayi tace "Wlh Siyama Kukan dad'i kike. Da wata soyayyan ma ba gwara ba ayi taba." Tsakin takaici ta k'ara yi "Wlh ki natsu, ki godewa Allah ya miki gata. Tunda bayan kudin mutumin ma naji ance yana da kyauta. Dube ni mana, dubi irin rayuwan da nake ciki. Kinga wani riba a cikin ta?" Huci tayi wannan karon sannan ta dan mik'e. "Gwara ki rungumi mijin da Allah ya baki." Sautin muryan ta kadai ya isa tabbatar da zafin da take ciki.
Ikon Allah tun daga lokacin kuma na d'an ware. Bayan nayi Sallah, na duba waya ta naga missed calls dayawa. Gabadaya na Alhaji Usman ne, sai Uban gayya Jabir. Kawai, sai na kafawa sunan sa idanu, ina jin tuk'ik'in bakin ciki na zagaye ni.
Sak'on sa na ga ya shigo.
Noorie d'aga waya please. Wani irin mugun labari nake ji haka? Wai meke faruwa ne? Don Allah kizo ki bayyana min gaskiya. Tun dazu nake aikowa, Rahma tace min baki jin dadi.
Da sauri na tura masa
"Kana ina ne?"
Gidan Yayan ku
Ina ganin message in, na ziri Hijabi nayi waje. Tun a kofan gidan muka had'u dashi. Jikin sa duk rawa yake, ya kasa tsayawa wuri d'aya.
Bansan sanda na saki wani kuka ba, mai cin Rai. Sautin ne ya fiddo da Baban Amir. Yana ganin mu yaja dogon tsaki. Sai yaja hannuna zuwa cikin gida, Jabir ya biyo bayanmu.
"Kimin shiru ban son iskanci banza." Wani irin tsawa Baban Amir ya daka min a ka. Tilas, na natsu ina zuba musu idanu.
"Waya turo wancan mutumin wurin Baba?"
"Ni ni nine, matsa min yayy yi." Wani kallon kar ki raina mana hankali ya min. Ya juya yana kallon Jabir. Shi dai ya kasa zama ma, sai gaba da baya yake a falon, idanun sa na kai na.
"Da ya matsa miki, dukan ki zai yi?" Girgiza kai nayi.
"To waya ce masa ya tura magabatan sa fa?" Ina ganin yanda ya hade giran sama da k'asa.
Cikin rawan muryan na bude baki "Wlh Yaya Baba ne."
"Baki san zai ba? Bai sanar miki ba?" Jiki na bari na ce masa "Ya gaya min, amma ni fa Allah ban amince ba. Ban ce masa eh yazo ba. Kawai ya gaya min ne. Baba ne yace s..."
"Ya Isa!" Har tsakiyan kaina naji sauk'an tsawan wannan karon. Daman tuni hawaye na sun k'afe.
"Ina taya ki murna, burin ki ya cika zaki zama matan Billionaire." Juyawa yayi yana kallon Jabir, da idanun sa suka kad'a, ko wani jijiya na jikin sa ya kad'a.
"Daman na gaya maka, munafunci ne kawai irin na mata. Tana sane da komai."
Da k'yar ya iya jinjina kan sa. Sannan ya maida idanun sa a kaina. Akayi nasara nima shi nake kallo, Ido cikin Ido muke kallon juna. Har sai da na ji zuciya ta ya gaza daukan irin kallon da Jabir ke watsa min. Kallo ne mai nuna sarewa, kallon wanda aka cuta zuwa ga wanda cuce sa. Kallo ne dana san zan cigaba da rayuwa da tunanin sa, don ba alamun zai barni inyi numfashi.
Da k'yar ya iya furta "Nagode." Daga haka ya juya idanu a runtse ya fita daga gidan. Wani irin kukan bak'in ciki na k'ara rushewa dashi, kukan ta faru ta k'are.
Duk k'ok'arin Maman Ameer ta kasa rarrashina. Sai Rahma ta k'ira, aka ci sa ta fara bani baki. A kunne ta rad'a min "Kar ki damu Anty Siyama, k'ilan Alhajin shine alkhairin ki." Ni nakan rasa gane kan Rahma. Kaman ba Itace dazu hadda gaya min magana ba.
Da k'yar na natsa, amma hawayen basu daina zuba ba. Suna fitowa ina bata labarin kallon da Jabir ya min.
"Rahma wallahi bai ce komai ba. Kawai ce min yayi ya gode ya wuce."
"Karki damu, yana cikin zafi ne. Zai huce."
A haka ta lallabani muka tafi gida. A bakin ta nake jin, Gidan Baba Aminu ya sauke mutanen Alhaji Usman in. Su Yaya Sabo kuma a nan. Halin Baba sai shi, wato kar a gano yana shirin yin wani abu kenan. In ba haka miye na zuwa gidan Baba Aminu, mutumin da ko kad'an bai damu dashi da iyalin sa ba dum da kasancewan mahaifin su d'aya. Ina ganin Baban, ranar yana ta washe baki, hak'an sa ya cimma ruwa kenan. Mama kam harkan ta, ta cigaba dayi. Kaman ba abinda ke damun ta. Sai ta dan kalle ni, ta kauda kai. Shima sai na wuce ta inda take.
Haka na kwana na tashi da radadin rashin ji daga Jabir. Sai da rana nake ji daga bakin Yusuf, wai yana asibiti an kwantar dashi.
Lallaba Rahma nayi muka saci jiki muka nufi asibitin. Na kuwa ci sa'a namiji ne kadai a kansa bare na sha tsegumi. Yana ganinmu, ya runtse idanun sa. Rahma ta gaishe shi, ya amsa k'asa k'asa. Nikam kaman ma da bango nake.
"Jabir Dan Allah mana" da kukan da ya tarun min a wuya nayi magana. Juya mana baya yayi. Nayi saurin zagayawa, ya k'ara juyawa daya gefe. A lokacin kuwa na saki kukan da kyau. Sai ma yasa pillow ya danne kunnen sa.
Zan k'ara magana sai ga Baban Ameer ya shigo. Yana ganina ya hau ihu "Ke wannan wani irin munafurci ne wai." Shiru nayi ina d'ar d'ar.
"In baki bar nan ba sai na taka wuyan ki wallahi." Da sauri na fita daga dakin. Ina ji ya kwala ma Rahma kira. Bata dade ba tazo ta ja hannu na.
Ranar dai har kumbura sai da idanuna yayi. Sai da Mama ta gashi da abun tazo tace min "Siyama kika k'ara wani kuka wallahi dukan tsiya zan miki, kiyi mai dalili da kyau." Haka nayi shiru ina bin kowa da idanu kawai a gidan. Nan da k'ofa ban fita. Daman Yaya ashe cema Rahma yayi ko k'ofan gida naje ta kira ta sanar mai.
A/N: Hmmm! A ganin ku Siyama ta kyauta da ta bari soyayyan Naira tafi karfi da tasiri a rayuwan ta? Akwai ranar nadama ko ranar farin ciki zab'in da ta ma kanta?
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top