Naira 10
Da fara'a tsohuwan ta amshe ni. Don dana durk"usa gaishe ta ma, hannu ta miko min alamun in taso. Kusa da ita tasa na zauna tana fad'in "Ni ai ban kishin dake. Yanzu bani aka ma kishiyar ba, waccan dai mai k'afan karen naka ita za a ma."
Murmusawa kawai yayi. Ya mike yayi wani wuri. Ba tarkacen da bata sa akawo min ba. Sai dai na taba na barshi.
Da yazo zamu wuce kuwa Atamfa da turare tasa aka dauko min. Sai na ji kunyan da ban zo mata da komai ba. Duk da ma bansan da zuwan ba.
"Gobe zan koma. Yanzun haka daga wurin Baffanmu nake, za suyi magana da Alhaji na dai ce mishi ban so a wuce satin gaba gaskiya."
Nikam dai ba son maganan nake ba sam. Amma ba daman dakatarwa. Ga Jabir next week zai dawo, shi ma Alhajin yace next week zai turo ko yaya zai kasance kenan?
A ranar muka rabu da Alhaji Usman. Kaman yanda muka saba, bai k'ira ba nima kuma ban k'irashi. Don haka a kwana biyun gabadaya hankalina ya gama karkata kan Jabir.
Rahma dai idanu ta zuba min. Kwatsam! Ranar naji shiru Jabir bai neme ni ba. Don haka ni na k'ira sa, wayar bata shiga ba. Kaman wasa wuni ranar gabadaya duk naci na, na gaza samun sa a waya. Haka na zauna nayi ta tsaki ni kadai. Rahma sai ce min tayi "Ke Anty Siyama ji yanda kika rikice kaman kin dauke sa da mahimmanci." Ai ji nayi kaman in kwad'a mata mari.
"Ki fita harka na Rahma ban son rashin kunya."
Ina ji k'asa k'asa tana k'iran "Nikam bani na kar zomon ba." Tayi saurin barin dakin.
Kw'afa nayi kawai na cigaba da juyi akan katifa. Don sai nake jin kaman an mun mutuwa. Tafiyan nan nasa sosai ya k'ara shak'uwa a tsakanin mu. Haka nayi jigum ina jiran tsammani.
Gaf da Magriba, sai ga muryan Yusuf k'anina ya karad'e falon yana k'iran "Anty Siyama ki fito, numban ki ta fito." Haka kurum! Sai naji gaba na ya fad'i. To wai meke shirin faruwa ne?
"Baba na k'iran ki. Yana shagon k'ofan gida."
Mik'ewa nayi cikin sanyi jiki na sa hijab na fita. Ina tunanin lafiya Baba ke k'irana? Me kuma ya faru haka?
"Baba gani." Na fad'i ina durk'usawa. Gani nayi ranshi a b'ace. Duk kusan kullum haka fuskan yake, na yau Sai naga har yafi wanda muka sani.
Kai tsaye yace "Ke kika turo min mutane?"
Sakan baki nayi ina kallon sa, don ban gane kan zancen ba.
Cikin fad'a ya cigaba da fad'in "Yayan wannan yaron, abokin yayanku ne yazo yau, wai har shine ma zai sanar min zasu zo gobe da mutanen su."
Ai ji nayi kaman an zare min lakka, jikina ya k'ara wani irin sanyi kaman mai shirin narkewa.
"Tambayan ki nake ke kika turo su?"
Cikin rawan muryan na fara had'a magana da k'yar "Baba daman daman dai muna tare har yanzu. Amma amma bai gaya min zasu zo goben ba."
Kallo sama da k'asa ya min "Kar ki maida ni mutum banza mana. Shi kuma Alhajin da kika turo fa?"
"Shima ma muna tare."
Girgiza kai yayi, fuskan yana bayyana irin wautana da ya gani. "Tashi ki bani wuri. Allah ya kaimu goben." Cikin rawan jiki na mik'e nayi cikin gida.
Daganan kuma labari ya canja. Gabadaya hankalina ya karkata daga tunanin rashin k'iran Jabir. Me zai faru da rayuwa ta? A cikin Jabir da Alhaji Usman wa zan aura?
"Anty Siyama lafiya?" Duk da a k'ule nake da Rahma, sai na kasa boye mata damuwa na. Na saba daman itace abokiyar shawarata. Duk wata k'awa a makaranta ko a chatting nake yin ta. Na Unguwa kuwa tunda aka yi saukan Islamiyya kowa ya kama gaban sa. To ma dai yawanci duk sunyi aure.
"Anty Siyama, kefa kika rikita kanki tun farko. In kin tambaye ni zance Ya Jabir shi yafi cancanta da ke, saboda shiya san darajan ki kuma yana miki so tsakani da Allah. Amma waccan inma ni dai bansan halin sa ba. Don haka in zan baki shawara ce miki zanyi ki nemi zab'in Ubangiji kawai."
"Rahma gobe fa zasu zo, shima Alhajin ba zai wuce goben ko Jibi tunda weekend yayi. Jabir inma daman gobe zai dawo."
Jinjina kai tayi tace "Ko yau, ki hana idon ki bacci. Ki duk'ufa rokon zab'in alkhairi. Sai kiga Allah ya amsa miki."
Shawaran nata nabi. Baiwar Allah, kunsan tare mu kayi sallolin da ita. Sai hud'u na kwanta, ba d'ad'ewa kuma ta tashe ni Asuba.
Ina idar da Sallah. Ba sai ga k'iran Jabir ba.
"Afuwan Noorie, kin jini shiru ko."
Ajiyan zuciya naja. Ina jin wani tuk'ik'i a raina.
"Yi Hakuri mana wife. Tafiya ce tazo min ba tsammani. Yanzu haka Ina fitowa daga Katsina. Oganmu ya turo ni can daga Lagos in."
"Ka Sha tafiya." Abinda baki na ya iya furtawa kenan.
"Sai wuraren Ukun dare na samu nayi caji. Shiyasa ban samu k'iran ki ba. Yaya Sabo yace min ya sanar da Baba yau zasu zo ko?"
Dum! Gaba na ya buga. Zancen dai yana nan kenan.
"Nan da wata uku zuwa hudu dai k'ark'ari zaki zama mata ta Noorie."
Yak'e nayi, da k'yar na ce masa "Kai dai kawai sai ka iso."
"Za a ajiye min abinci Mai d'ad'i to? Nayi kewan girkin ki Noorie."
Zancen shine ya sani murmushi sosai "Baka da damuwa. Bara nayi bacci na tashi."
Nishad'in Sallan dare ya wuce misali. Wani irin bacci nayi cikin annashuwa duk da zulumin da nake ciki. Bacci ne mai nauyi da ban ma san meya ke gudana a gidan ba. Ko da na tashi, na ga gidan ko ta ina aiki ake, ana gyara wasu na girki wasu na wanke wanke. Muna had'uwa da Mama tace min "Shirya ki tafi gidan Maman Ameer, nan za ayi bak'i."
Ban mata musu ba na fita daga gidan. Don kam nasan kan zancen. Kenan yan'uwan Jabir in Baba ya amincewa da suzo? Sune dai nasan sunyi maganan zuwa ranar.
Bayan na shiga gidan Maman Ameer in ne naji na gaza komawa baccin. Don haka nayi tunanin d'aurawa Jabir abincin kawai. Wa ya sani? Watakila shine abincina na k'arshe da zai ci ko kuma shine mafari.
Maman Ameer in kanta tana gidanmu, suna aiki. Raham ce ma ta d'an leko. Na kasa shiru nace mata "Rahma wai suwa zasu zo?"
"Anty Siyama ke kam ba kin nemi zab'in Ubangiji ba?" Da kai na amsa mata.
Tace "to nima bansani ba. Mama tace Baban bai gaya mata ba. Kawai siyayya yayi yace a shirya ma bak'i abubuwa za azo tambayan auren ki. Amma ki kwantar da hankalin ki, ko wanene In Sha Allah shine alkhairin ki."
Na ko d'auki shawaran ta. Cikin natsuwa na hau had'awa Jabir abinci kala kala, bayan nasa Khalipha ya min cefane. Ni kaina nasan nayi k'ok'ari, sai sam barka.
Daman tun tuni ya turo min message sun shigo gari. Nasan yana gida kenan.
Ana idar da Azahar yazo gidan Maman Ameer in. Dake daga gidan nata ba a wani iya hango gidanmu. Shiyasa bansan ko mutane sun iso ko basu iso ba.
Dan zakwadi har Kitchen in ya biyo ni. Ina k'ok'arin had'a kulolin abincin. Ko zulumin da na b'oye a raina ne? Muna had'a Ido nayi sautin dauke idanuna. Gani nake kaman inda muka had'a idanu zai iya gano abinda na boyewa.
"Ba zaka ki juyo na kalli fuskan mata na ba." K'ak'alo murmushi nayi nace masa "To fita falo mana."
Daukan tray in da na gama had'awa yayi "Bara nayi aikin lada."
Ko da muka zauna, kaina na kasa amma Ina jin idanun sa k'yar a kaina. Gajiya nayi da sunne kai ma dago, muna had'a idanu ya sakan min murmushi. Farin ciki ne k'arara akan fuskan nasa. Murmushi kam ya gaza daukewa. Ji nayi gaba na ya buga da karfi. Wai mena sa kaina a ciki ne.
"Serve tunda kunya na aka koma ji." Kaman jira nake yayi magana na fara zuba abincin. Ko bakomai zan so ace abincin ya ratsa jikin sa kafin isowan labarin, da ka iya kasance mai na farin ciki ko akasin sa. Ni dai ban iya tantance ya abun zai iya zuwa min ba har yanzu.
Yana cin abincin yana bani labarin Ikko da irin rayuwan da yayi a can in. Nikam rabi rabi na ke sauraren zancen nasa. Don hankali na, yafi karkata gun me ke faruwa a gidanmu.
"Ga tsaraban ki, duk da baki tambaye ni ba."
Amsan leda nayi, kai tsaye na hau bud'ewa. Turare na a ciki da handbag. Idanu na zuba musu, yayin da murmushi ke taruwa akan fuskana. Hakika da, ada ne da Alhaji Usman bai shigo rayuwa ta ba, Jabir ya kawo min wadannan abubuwan, to fa da ba Wanda zai kaini murna a ranar. Amma yanzu, murmushin dai kawai na tsinci kaina ina yi. Domin nasan kudin su, gabadaya ba zasu wuce 20k ba, su ma saboda abubuwa sun k'ara kudi ne na kiyasta a hakan. Nasan, a matsayin Jabir dai da yake gwagwarmaya da rayuwa ya kawo min irin wannan ba k'aramin k'ok'ari yayi ba. Shi mai yan'uwa dayawa amma ni ya zabi ya girmama.
Kallon sa na k'ara yi, sai naga kaman zai b'ace min. Kaman ina shirin rasa wani babban jigo na farin ciki na. Bansan sanda na kamo hannun sa daya nasa a nawa ba. Sai da yayi wani turus! Yana kallo na.
Lumshe idanu yayi sannan ya sauke su a kaina "Noorie, ba abinda bazan iya miki ba. Ban taba hango rayuwa da wata ba ke ba. K'ara tamke rik'on da nayi ma hannun nayi. Ina jin kewan rashin ganin sa a kwanakin nan na ratsa, Ina jin yanda kewan ya ke ninkuwa. A lokacin zuciya ta, ta fara wani irin harbawa, ba abinda nake ji sai rashin adalcin da na masa da nake jin yana ratsa gabbana jiki na. Nan take na fara jin, ba zan iya ba. Zuciya ta bata da karfin iya rasa abu mai mahimmanci sosai a gare ta. Wani irin kwalla mai zafi naji sun cika min idanu. Bansan sun fara zubowa, sai da naji muryan Jabir in yana fad'in.
"Subhannallahi Noorie, kuka kuma?" Nan take ya rude, ya fara lallashina, yana kokarin ganin kukan nawa ya tsaya.
A wannan yanayi, Maman Ameer tayi sallama a falon. "Au ango da Amarya ne. To me kake ci na baka na zuba? Ai sai ka bari a kai maka ita ko." Dake sun saba wasa da Jabir in. Yau dai bai biyewa tsokanan ba, kokarin ganin na daina kuka ne a gaban sa.
Ni kam, maganan nata ya kara sani kukan. Ango fa tace? Kenan Baba Jabir ya bawa aure na?
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top