3
Ance a way to a man heart is his stomach. Ba shakka na gamsu da hakan. Musamman da na fahimci yanayin hannu na. Share yabon kai, ko ruwan zafi na sarrafa d'and'anon sa daban ne. Don haka na rike baiwan da Ubangiji ya min a matsayin makami, musamman ta fannin maza.
Barin ma da na gane irin mahimmancin da Jabir ke ba ma cikin sa. Duk wani abu mai dadi, yana so. Wai ma don ban cika son aikin ba. Sau da dama yakan nemi abincin, na dinga mai hanya hanya. Sai daidaikun ranaku ne yake samu, musamman in mun samu sab'ani.
Duk da ina jin haushin Rahma, haka na saukar da kai na amshi d'ari biyu a wurin ta. Ginger hamsin na siyo, sai cucumber ma na hamsin da lemun tsamin ashirin, abarba da ake yankawa na hamsin sai ga sigan talatin na hada nayi ginger juice dashi. Daman musamman na shuka Lemon grass da Na'a Na'a a gidanmu. Saboda yanda na ke jin dadin amfani dasu. Suna tsinka na tafasa, nasa a ruwan Gingern bayan na tace. Sannan na lek'a wurin Maman Amir na amso k'ank'ara . Nan da nan kuwa juice in ya min yanda nake so. Daman bana sa wani artificial flavour in dai zan hada drink kowani kala ne kuwa.
Gab da sallan Magreeba na had'a komai a wuri d'aya. Nasan yana azumi, don haka na aika kanina Khalipha ya kaima sa har gida. Ta yanda tarko na zai yi kamu tun kafin mu had'u.
Ana idar da sallan Isha'i ba d'ad'ewa sai ga kiran shi ya shigo. Gidan Maman Ameer muka saba had'uwa, saboda rashin wadattacen wuri a gidan mu. Sannan kuma Yayan ma abokin sa ne.
Hijab na dauka kawai na fita, bayan na gaya ma Mama zani gidan Maman Ameer in duk da dai kowa a gidan yasan wurin Jabeer zanje. Ko hoda ban damu na shafa a fuskana ba in dai da shi zamu hadu. Sai dai in y'an kwalliyan na kaina. Shi dwman bai dame shi ba, don ya sha sanar dani na fi mishi kyau in banyi kwalliyan ba. Abu daya ne maganan shi, lip balm. Su kam ya sha siyo kala kala ya kawo min.
Sallama nayi a falon, su biyu ne a zaune a falon shi da Baban Amir suna hira.
"Simas" Baban Amir in ya fada cikin raha bayan shigowa na.
Gaishe shi nayi "Ke kam muna mak'ota amma in har aka ganki da dalili ko?" Murmushi nayi, don daman ya saba tsokanan ta. Cikin gidan na nufa don son in basar da maganan. Maman Amir na tattare tattare a kitchen, don haka na tsaya kawai muna hiran da ban fahimtan komai. Dan dai rabin hankali na, na falon.
"Ke banson gulma, ni bak'on kine da zaki shige ki bar mutum na jiran ki?" Muryan Baban Amir naji a bakin kitchen. Sai kuma yace ma Maman Ameer "Bara nayi aski na dawo"
Zama nayi a kujeran dake fuskantan sa. Fuska ba yabo ba fallasa yake kallon na. "Har yanzu fushin kake?"
"Meya had'a ki dashi?"
Sunkuyar da kai kasa nayi. Duk iya shirya zance na, sai aka samu akasi domin ban iyawa Jabir karya sam. Ni kaina na kan rasa dalilin hakan.
"Dare ne fa yayi ba abun hawa, shine ya sauke mu gida. Shima bikin yazo."
"Meyesa baku k'ira ni ba?"
K'asa na kara yi da kaina "Dare fa yayi, risky ne mu cigaba da tsayawa akan titi."
"Emhmm" kawai ya amsa. Daga Jin amsan nashi nasan bai gamsu ba.
"Ka fahimce ni mana."
"Siyamaa" yanda ya kira sunan ne yasa ni d'agawa na kalle sa.
"Ki fad'a min gaskiya, me kika tsaya yi a motan sa."
Dauke idanuna nayi, Jabir ya riga ya san lago na, ya gano abinda na kasa furta mai. Ina bud'e baki ya sa hannu ya dakatar dani.
Mik'ewa tsaye yayi, yana fitar da huci mai zafi ta bakin sa. Yanayin sa yasa nima na mik'e. Nan da nan sai ga hawaye sun cika min idanu.
"Jabir please, wlh duk wani Namiji a rayuwa na a bayanka yake. Ka sani banda kaman ka."
Hade yatsun sa yayi wurin daya "Kina so in yarda dake?" Ban amsa ba ya cigaba da cewa "Na riga na gabatar da kaina a wurin mahaifin ki. Ina so mu tafi mataki na gaba."
Ai bansan sanda na zaro idanuwa ba.
"Eh, Ina nufin zan turo a tambayan min auren ki Siyama. Na gajiya da wannan wulla wullan. Zuciya ta ba zata juri ganin ki da wani Namijin ba. Kinsan halin da na shiga jiya?" Yana maganan jikin sa na rawa, don haka ya silale ya zauna kasa.
Bin shi kasan nayi, muna fuskantan juna.
"Kwana nayi da wunin yau zuciya na, na min zafi. Ban ganshi ba balle ince yafi ni komai. Amma nasan yana da abinda za a k'ini a so shi. Siyama don Allah kar ki barni."
Nan take naji hawaye mai zafi na cika min idanu. Hakika, akan Jabir nasan menene soyayya, nayi mu'amala da ita. Sai dai a yanzu ra'ayina nake ji ya bambanta da abinda Jabeer in ke bukata.
"Kace kana neman aiki J, in ka samu zamu yi auren. Ni taka ce, gaggawan ba zai mana wani amfani ba J. Ina guje mana wahala."
Baki bude ya kafa min idanu. "Ba zaki iya zama dani a cikin kowani hali ba?"
Tambayan yafi kama da kanshi ya ma alamun mamakin ya bayyana kan fuskan sa.
"Kaine ka fad'a da kanka, na kuma gamsu da hujjojinka a wancan lokacin. Hakika ban shakkan Soyayya jigo ne, amma kuma ba zata wadata mu." Karfin guiwa na tattaro iya iyawa ta ina fad'in kalaman da nake jin amincewa su har cikin zuciya ta.
Shiru ne ya ratsa wurin, muna kallon juna cikin idanu. Ina kokarin bashi kwarin guiwan da duk nake ganin yana buk'ata.
"Siyama dole sai aiki?"
Girgiza kai nayi "Duk abinda zai ciyar damu, ya tufatar damu ya yanke mana wahala ya kawo arziki ina maraba dashi J."
Kai ya jinjina "Shikenan, zan samo mana mafita kwanan nan." Ya karasa magana yana ciro hanky a aljihun sa. Saitin idanuwa na ya kai ya goge min kwallan da ke d'iga.
"Ki daina kuka, komai zai daidai ta da izinin Allah."
Ya sake cewa "Kince kina Sona, na amince da hakan, naga alaman hakan. Amma meyesa kike kula wasu? Ko me kike bukata ki tambaye ni, zan nema na baki daidai karfi na."
Murmushin yak'e nayi "To in akayi auren ba shikenan ba banda abin ka." Girgiza kai kawai yayi, da alamun shi bai ga abun murmushin ba. Sai alamun tsoron da nake gani cike a fuskan sa.
Hannu yasa a aljihun sa, k'aramin leda ya fiddo na dankunne ya mika min. Hannu nasa na karba. Turus! Nayi bayan na fiddo dan kunnen da ke ciki. Silver ne, sai da na kara bude ido na tabbatar Zirconia in da na taba nuna mishi yana burge ni ne.
"Nawa ka siya?" Tambayan ta kubce min.
"Au abinda zaki fara tambaya kenan ko?"
Dariya na danyi, a raina ina k'imanta kwanakin da yayi yana tara kudin. Iya abubuwan gaban sa da ya danne ya hakura duk don ya siyan min wannan d'an kunne.
Nan take naji wani abu ya diran min a kirji. Gaskiya na fahimci naso nayi kuskure. Jabir yafi karfin ya jira.
"Nagode Miji na. Allah ya saka maka da alkhairi." Sunan da na kira shine yasa murmushi karuwa a fuskan sa. Nan take, tsoro ya koma mishi farin ciki.
"Muje na rakaki gida ko?" Mikewa nayi a hankali. Ni sam ma na manta ya kamata in ma Maman Ameer sallama, kodan ta kulle kofan ta. Gaskiya, soyayya rahma ce.
Tafiya muke ina jin wani farin ciki mara dalili na ratsa dukkan gab'b'ai na. Ba sai an gaya min ba, nasan haka take a wurin Jabir.
Sai da muka kai k'ofan gida yace "Naci abincin ki Nuri, hakiki ke d'in ta daban ce. Allah ya bar min ke."
Muna tsaye a wurin sai ga Baban Ameer ya fito daga cikin gidan. Da alama wurin Mama yaje hira bayan ya gama askin.
"Da kuka san baku gama hiran ba, ai da kunyi zaman ku a can. Za a dawo bakin titi." Hararan shi Jabeer yayi.
"Kaga dai kai siriki nane, kar kasa na fad'a maka abinda za aji kunya."
Tilas mukayi sallama saboda Baban Ameer ya mana tsaye yak'i tafiya. Na kuma san da gangan yayi hakan. Don muddin Baba ya ganmu a haka, to abin ba zai mana kyau ba.
Amma me? Jabir na shiga gida ya kira ni. Ranar ba abinda muka dinga jaddada ma juna sai irin soyayyan da muke ma junan mu. Sai wuraren sha dayan dare sannan mu kayi sallama.
"Naga ta kaina, tun dazu ashe Nadabo ke kira na, har sau biyu"
Tab'e baki Rahma tayi "Kai Anty Siyama, yanzu fa kika gama gayawa Ya Jabeer irin soyayyan da kike masa. Yaudaran sa zaki fara?"
"Yaudara kuma? Ke shaida ce ban iya ma Jabeer k'arya. Ina masa son da ko kaina ban yarda ina mawa ba. Kawai dai wannan inma da amfanin sa."
"Eh lallai ba shakka." Rahman ta amsa, tana mai cigaba da abinda ke gaban ta.
Ni kam danna mishi kira nayi. Ina ganin bai kyautu ba ace mutum mai girma irin wannan ya kira na share sa.
"Pretty da wanda ya tare min gaba ake waya hala?"
"Ehm ehm fa, ni da wata friend ita ce." Nayi saurin fada.
Sai cewa yayi "Ki dai fada min gaskiya kawai. Irin ku ba jerin samari ai dole da abun tambaya."
Banbarakwai naji maganan nashi. Dannewa nayi dai, muka cigaba da gaisawa.
"Kina da wani schedule ne gobe?"
"Zanje Salon dai da yamma. Banda haka Ina gida, ba abinda nake."
"Alright, gobe zan shigo garin sai na k'ira ki. Saboda Ina son ganin ki sosai da rana."
"Daman ba a nan kake zaune ba?"
"No, am always travelling ai. Uwargida dai tana Abuja da Yara, da suna nan saboda duk families inmu na nan. Da babbar daughternmu zata shiga secondary na maida su can. Cause Ina son ta samu school Mai kyau, sannan ban so tayi mingling da local children. Yanzu sai su bata maka tarbiyyan Yara."
"Ehmm" kawai nace, cikin rashin sanin yanda ya kamata na d'au maganan
"Yaran ka nawa?"
Kokarin kiyasta shekarun sa na fara yi a kaina.
A/N: Be nice to drop some comments if you are enjoying this story.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top