2
"Siyamaa Siyama wai ba zaki tashi hakanan ba?" A tsakiyan kaina naji sauk'an k'iran da Mama ke ta faman kw'ala min. Tilas na mik'e ba don baccin ya saki idanuna ba. Gabadaya baccin bai isheni ba, haka dai na daure na fito sanin ko na koma ba kyale ni za ayi ba.
"Mama gani" turo baki nayi gaba, idanuwa na kuwa har lokacin basu washe ba.
Mama bata kula da mitana ba ta hau fad'a "Amma dai kinsan yau kece da wanke wanke zaki zauna kina sharan bacci ko?"
Wai! Nan take wani k'ululu ya min tsaye a wuya. "Mama yanzu wai saboda wanke wanke ne aka tashe ni?" Ji nake kaman in rusa ihu. Ga mafarkin Dubai da aka katse min.
"Kinga ban son rashin mutunci. Ga yar uwarki nan har ta gama aikin ta. Ince tare kuka shigo gidan nan da dare.
Wuri na samu na zauna akan carpet in dake shimfid'e a tsakiyan falon "To Mama abun karyawa na fa? Me aka dafa?"
"Abinda muke dashi mana"Jina yi raina ya kara b'aci. Kai dole ma na nemi mafita a wannan rayuwan wahalan. "Badai yau ma Taliyan akan dafa ba?"
Mikewa nayi ina nufan hanyan kitchen ganin Mama ba tanka ni zata yi ba. Ni ban san me ya bata mata rai ba. Ko da yake ba wani abu farin ciki a rayuwa irin namu, da kullum sai ka nema zaka samu kasa a bakin salati.
Kallo daya na ma abincin dake dankare a kulan nasan ba zan iya cin sa ba. Don haka na juya falon ina k'unani
"Mama dan ban aron dari biyu mana"
"Banda ita" cigaba da tsintan shinkafan dake tray tayi gaban ta. Narai narai nayi da fuska, amma ganin yanda Maman tayi da nata fuskan yasa nasan yau dai ba zan samu abinda nake so ba.
"Mama ni zan wuce, sai na dawo." Rahma ce ta fito cikin shirin fita.
"Rahman dan ban dari biyu Dan Allah mana." Yunwa nake jin ya fara kw'akulata.
Murmushi Rahman tayi "Dama kin ajiye makaman yak'in ki, mu dinga zuwa Restaurant in nan tare. Bada abinci ne fa kawai, kuma zaki samu canji."
Ai bansan sanda na saki tsaki ba. Banda Rahma da wani irin tunani, ina ni Ina aikin bada abinci a restaurant? Ai sai in kori mutanen arziki. "Kudi na tambaye ki, in kina dashi ki miko kawai. Haka kurum a yanda nake, da darajata a ganni Ina bada abinci a restaurant. In jawa kaina raini a banza."
Tab'e baki Rahman tayi "Ni da nake son rainin ba gashi Ina zuwa ba? Ko bakomai ai yafi zaman banza. Zaman jiran a dawo yajin aiki."
"Ni kike gaya ma magana don na tambaye ki kudi?" Cikin masifan na rashin wadattacen bacci da yunwa da ya fara kwakulan ta nayi maganan.
"Hmmm" Rahma ta furta tayi saurin yin hanyan waje. Kw'afa nayi hade da cije leb'e. Takaici naji yana mamaye ni, a kowani sashe na jikina nake jin na gaji. An kai gab'an da bazan iya ba kuma.
A yanzu dai yunwa dake damun nane babban matsala ta. Gashi Jabeer na fushi da ni balle ko indomie nasa ya aiko min. Zama nayi jigum, ina zubawa uban wanke wanke dake jiran na ido. Ganin su kadai suna sani jin kaman nayi ta kurma ihu.
Mama na lura dani, ba ta k'ara tanka ni ba ta cigaba da abun gaban ta.
Ganin ba sarki sai Allah ne yasa ni mikewa na nufi wanke wanken gadan gadan. Ko bakomai Mama ta sauko in taga nayi. Nasan daga cikin dalilin da yasa Maman ke fushi hadda wanke wanken da kuma abincin da na k'i ci. Daman in mutum yana fama da rayuwa, abu kalilan ke tunzura shi, ya rasa me ke Mai dadi.
Ni kam har ga Allah ba zan iya cin wannan abincin ba. Don haka kawai na hau fama da wanke wanken. Ina yi ina jin wani kuka kuka na taruwan min a idanu. A gefe daya ina tuna Zainab da muka je dinner inta a daren jiya.
A jami'a muka had'u da ita. Dukanmu shekaran farko muke. A farkon second semester aka tafi yajin aiki. Yau kusan wata biyar kenan ba wani labari mai dadi kan batun komawan. A hiran da muka yi da Zainab in kafin mu tafi wurin event take sanar dani ba zata koma Makarantan ba. Mijin da zata aura zai maida ta private university ta k'arasa. Wani tukikin bakin ciki naji ya tsaya min Kai tsaye nace mata "Ke kam kinyi dace abin ki, kin samu wanda zai rufa miki asiri." Duk da ma su Zainab inma na da iya kudin su daidai gwargwado.
Haka na cigaba da wanke wanken ina tunanin rayuwa irin wannan. Ina ganin Mama na kokarin hada kayan cincin da donut wanda ya kasance sana'ar ta. Duk haka muka taso muka ga tana yi. Nikam da na gwada na fahimci kawai aikin wahala ne shiyasa na guje masa. Kafad'a da baya sun yi ta faman ciwo kenan, duk ranar da nayi dole sai na gasa jiki da ruwan zafi nake iya bacci.
Lokacin da na gama wanke wanken har idanuwa na sun fara dishi dishi saboda wahalan da ga yunwa. Tunawan da nayi jiya naga tuwo ne yasa ni nufan gun Maman ina mata sannu da aiki. "Mama nikam tuwon jiya bai rage bane?"
"Akwai kadan a Kitchen, Wanda na ajiye ma yayan ku to ina ga ya riga ya fita Kasuwa, tunda bai shigo ba. Naga ai dumamen ma ba ci kike ba."
"Ai yafi Taliyan" hanyan kitchen in na nufi. Allah ya taimake ni gawayin bai mutu ba, don haka na kara hada mukubur in na daura. Ni da kaina nasan yunwa ce tasa naci dumamen, don sam bana shiri da abinda ya dangance sa ma.
Wanka na shiga bayan na gama, don bakidaya kyankyami jikina nake saboda wanke wanken da na jibga. Ance dai wai ana sabo da abu, amma wanke wanke kam sam na kasa sabawa dashi. Har gwara su shara duk da su inma ma kayan wahala ne da k'ura. Don ma wai raba mana aiki ake da Rahma da sauran kannen mu mata, da ban san yanda zan yi ba.
Bayan na gama shiryawa na nufi wurin Mama "Mama bara na taya ki aikin nan, naga dayawa."
Ba tare da ta kalle ni ba tace "Wani abu kike so ne?"
"Kai Mama" na fada ina murmushi, Sarai daman nasan zata d'ago ni.
"Kawai dai albarka nake nema"
"Ehmm" Kawai Maman ta amsa ta cigaba da aikin.
Samosa ne, sai donut da meat pie zata yi. Duk cikin su ba wanda ban kware akai ba. Kusan komai ma na iya yanda zan fidda shi sai dai juriyan yi dinne sam ba zan iya ba. Amma ko abun siyarwa na gwada yi, nan da nan yake karewa. Ita kanta Mama tana jinjina min.
Tsaf na dage na hada Samosan. Naman cikin sa, da na meat pie na fara hadawa, Maman kuwa na kokarin buga kwabin donut.
Duk da gawayi ne, sai da idanuwa na suka yi ja. Na dade da sanin bamu biyo hanya daya da aikin wahala ba. Shiyasa ma dole na tsere masa. Da yake nasa kaina dai, hakanan na cigaba da yunkurin yi.
Wuraren la'asar muka gama aikin. Dake hannu biyu ne munyi sauri.
"Mama Ina son Samosan nan in ya hau kai. Da sauran ma duka."
"Ahaf!" Mama ta fada, tare muka sa dariya, zuwa lokacin ta riga ta sauk'o.
"Ni nasan ruwa baya tsami banza."
"Kai Mama, bafa haka bane. Zan d'eba ma Ya Jabir ne daman, yana so sosai."
Tab'e baki Maman tayi "Ai shikam ya gamu da mata, ko yana so bashi zai sa a masa ba. Halan wani abun kika masa kike son lallashi."
Dariya kawai nayi jin yanda Maman ta gama dago ni bakid'aya.
...
Yau ma dai aikin ya gajiyar dani. Da kyar na lallaba nayi Sallah, kan abun Sallan na kwanta, don wannan katifar namu sai dai ya kara min ciwon jikin.
Wannan karon ma muryan Maman ne ya sake tada ni. Inda sabo kam na saba ai.
"Ki tashi ki daura mana sanwan dare ko."
Nan take na hade fuska, sai kuma ga idanu na sun ciko da hawaye. "Mama fa ko ina a jikina ciwo yake Allah. Ni ina zan iya wani girki kasusuwana duk sunyi tsami."
Rike baki Mama tayi "Oh ni Allah, Wani ma yazo gidan nan ai ni zai zaga yace ban saki aiki Siyama. Mutum yace yana son hutu bayan ba a gidan hutun yake ba?"
Share hawaye da ya fara zubo min nayi "Mama kinga fa su Hauwa sun kusa tashi daga Islamiyya, ba sai su yi girkin ba."
"Ke da kike zaune a gida baki yi sai wadanda suka dawo daga makaranta? Tashi ni ki kai min kayan nan gidan bikin, zan daura girkin."
Sai a lokacin na saki zazzafan ajiyan zuciya. Ni daman fita ba wani matsala yake bani ba. Aikin gida ne dai sam bamu k'awance.
Shiri na nayi mai kyau, na shirya snacks in. Sannan na debi wanda zan sa ma Jabir na b'oye. A Napep na kai sakon na juyo.
Can na hango shi a bakin shagon da abokanan sa suna magana. Muna had'a idanu ko ya dauke kansa. Duk da naji wani iri har raina, basarwa nayi saboda nasan har yanzu fushin yake. Nasan sarai yanda zan bullo mishi, shiyasa banma wani damu ba na wuce gida.
Ina shiga na kira shi a waya. Duk rintsi bama kin daukan wayan juna ni dashi. Ko da kuwa za a daukan ne ana magana kowa rai a bace. To fa mun zabi hakan akan rashin ji daga juna.
"Ya bir" Sunan da na kan kira shi kenan in ina son tsokanan shi.
"Ya akayi?" Ya fadi cikin basar da tsokanan.
"Haba Boo har yanzu fushi kake dani? Shine tun safe baka kirani ba?"
"Ke meya hanaki kira na?"
Matse dariyan da yazo min nayi, don na fahimci abun ya dame sa. Da gangan nayi don nasan hakanne zai sa ya sauko, ya kuma saurare ni da kyau. Don da munyi magana a daren jiya kam, abun ba zai yi kyau ba.
"Tunda na tashi na ke aiki Allah. Na taya Mama aikin snacks. Jiki na duk ciwo yake, baka ji yanda nake ji ba." Cikin marairaicewa nayi maganan.
"Eyyah Sannu" a takaice yayi maganan, bai dai sauko ba din kenan.
"To zaka zooo yau? Kazo please kajiii?" Lankwasa murya nayi, ta yadda na tabbatar zai ratsa shi.
"Aina dauka ba a bukatan ganina kuma."
"Har abada duk wani wanda zanso gani a bayan ka yake. Dan Allah kazo muyi magana kaji?"
"In nayi Sallan Isha'i" ya amsa a takaice.
A/N: Wai Siyama ke so? Me kuma take nema a wurin mazan nan guda biyu?
Ka/kin gaji da jiran Update? Kuma kina da Instagram account? Ruga kan manhajar yanzun ki karanta har zuwa babi na takwas @aysher.bee
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top