1
Siyama
Na sha jin ana cewa matsatsun kaya sunfi dadin juyi da kyau wurin rawa. Ban tabbatar da hakan ba sai a yau, da na zage damtse ina ta kwasan rawan da yaja hankula da dama. Biki ne na gani na fada, shiyasa na dage na shirya mishi da kyau.
Sautin kidan da ya tsaya ne ya sani dakatawa da rawan ba don naso hakan ba. Yanda abun nan ke tafiya, banki ayi tayi har a tashi ba.
"Jama'a wa yaci wannan gasan?" Mc ya tambaya.
"Siyamaa siyamaa" Ihun suna na ya karade wurin bakidaya, sai naji ana wani fasa min kai. Hakika, ba abinda ya kai ka burge mutane dadi, domin a yanzu haka ji nake kaman inta tsalle.
"Kinyi kokari fa Yan mata, wannan shine zakaran mu a ko wani fanni na rawa." Daya daga cikin abokan angon ya fada yana dafa kafadan wanda muka yi rawan dashi.
Murmushi na musu, ganin yanda suke kallona da yabawa, ba ma su kadai ba kusan duk wani dake wurin. Jiki na, na kare ma kallo. Asoebin da ke jikina fa dubu Ashirin na siye shi, ga kudin dinki goma, yanda naci kwakwa na hado kudin nan ai dole ma na dauke hankalin wurin nan, in ba haka ba ai buri bai kai ba.
Hanyan seat in kawayen Amarya dake a gaba na nufa, Ina jin wani farin ciki na daban na kutsa cikin jiki na.
Jin da nayi an jawo hannu na yasa ni juyawa. Rahma ne tsaye tana turo baki.
"Haba ke kuwa an kusa tashi fa."
Kaman zata yi kuka tace "Anty Siyama goma fa ya wuce, har sha daya saura. Tun dazu Mama ke kira wallahi." Nuna min wayan tayi, sai ga kiran ya kara shigowa. Kafin in ankara har ta dau wayan ta sa min a kunne. Muryan mama ne ya karade kunne na duk da hayaniyan dake wurin "Ku baku da hankali ko? Sha daya kuna waje ko Siyama? So kuke munafukan Unguwan nan su hadani da Baban ku ko?"
"Kiyi hakuri, gamu nan." Na fada a sanyaye. Takaici ne ya yayime ni gabadaya, daukan clutch bag in da na aro wurin matan Yayanmu nayi.
"Ai sai kizo mu tafi." Ko tsayawa sallama ban wa Amaryan ba da sauran kawayen na nufi waje. A raina ina bakin cikin asaran kudin ankon da zanyi duk da nayi hotuna da kuma rabin event in a wurin.
Dare ya riga ya fara tsalawa, sai ya zamto ababen hawa duk sun yanke. Kalilan da muke gani kuma duk da mutane a cikin sa, a cike suke zuwa.
Bansan sanda naja wani irin tsakin takaici ba, ga wayan Rahma sai faman ruri yake taki dagawa. Daman ni ban fito da nawa ba.
"Dakin bari an tashi har kofan gida za a sauke mu."
Rahma bata tanka ba. Wayan ta, ta miko min tana fadin "Anty Siyama ki kira mana Ya Jabir kawai ya zo ya dauke mu."
Daga Rahman har wayan nata na hada na watsa ma kallon banza. "Miye maraba to, ba gwara kawai mu nemi Napep in da kanmu ba."
Bude baki Rahma tayi, tana shirin magana, karan tsayuwan mota a gaban mu yasa ta yin shiru. Dukkan mu biyu muka zubawa motan idanu, irin motocin nan ne da ke nishi da kyar. Tinted glass in jiki bai bamu daman ganin waye a ciki ba. Nan take gabana ya hau dukkan uku uku, waye wannan ya tsaya a gaban mu? Ba dai tunanin wucewa yasa bai bude glass in ba har yanzu.
Numfashi na da glass in windown a tare suka sauka. Gudun kar ya gane hankalina na kanshi yasa nayi saurin sadda kai kasa.
Sautin muryan shi ne ya ratsa kunnuwan mu. Tsaban yanda zuciyana ya hau lugudi, ban iya amsawa ba sai Rahma ce ta amsa mai.
"A shigo mana in rage hanya, dream girl." Jin idanun sa a kaina ne ya sa na gane ni yake ma magana.
Dago idanu nayi, na sauke a kansa.
"Ma Sha Allah" na furta a raina. Irin mutanen ne da kallo daya kasan Naira ta samu wurin zama agun. Ban san kayan maza ba, amma na shaida na jikinsa ba na banza bane.
"Friend in Zainab Amarya ce ke ko?" Ya kara tambaya, ganin ba wanda yayi alaman shigo motan daga cikin mu.
Da kai na amsa. Sai gani nayi ya matso da hannu ya bude kofan kujeran gaba.
"Bismillah mana, nima daga bikin nake." Yana fadin haka nama Rahma alaman ta shigawa kawai mu tafi. Ba musu ta bude ta shiga, da alamun dai ta gaji da tsayuwan.
"Allah ya so ni da rahma." Yana kokarin tada motan yayi maganan.
Kallon shi nayi, muka hada idanu, wani irin murmushi ya sakan min.
Gudun kar yayi tunanin ina basar da shi yasa nace "Wani gata Ubangijin mu ya maka a daren nan?"
Sai da ya kara fadada murmushin sa yace "Gatan samun matar aure, har rokon Allah na dinga yi, kar na fito ban same ki ba. Motoci ne su kayi blocking ina sai da na kira su daga cikin hall in. Na kasa tantance irin yanayin da zan shiga in ban same ki a hanya ba."
"Ba sai ka tambayi Zainab ba."
Girgiza kansa yayi "Hakan ma mafita ne. Kawai dai ban jin zan iya jure har gobe ban kara saki a idanuwa na bane. Amarya kuwa kinga ban zan samu kanta yau ba."
Jinjina kai kawai nayi, domin har ga Allah banjin maganganun shi na ratsa ni. Tun a farkon ya tafi da hankalina, kalaman sa basa daga cikin dalilin hakan.
"Ya sunan matan nawa?"
Bude idanu nayi "Dama miji yana rasa sanin sunan matar sa ne?" A tare muka saki siririn dariya.
"To wannan mijin dai a mai afuwa a sanar dashi."
Fada mishi sunan nayi. "To kanwar tamu fa?"
Tab! Har ga Allah na manta Rahma na cikin motan.
Juyawa nayi ina kallon ta, daidai sanda take fada mishi sunan ta. Tabe baki nayi na juya, ganin irin kallon da take aika min. Na kuma san dalilin ta.
Kwatancen na dinga mai har muka isa gidan mu. Motan na tsayawa Rahma ta bude tana mai godiya ta fice.
"To mungode sosai" Na fada a sakawanne, har kasan rai na nake rokan Allah yasa ba dadin baki kawai ya min ba. Ganin ina shirin fita bai amshi numbana ba.
"To yaushe zan zo in gaida Mama?"
Kallon shi nayi, a raina Ina kiyasta Maman mu ba za ta haifi kaman sa ba. Babban yayanmu ko talatin bai cika ba.
"To sai ince mata wa?" Na fada Ina zare idanu.
"Sirikin ta, mijin Siyama." Tsaye naji maganan ya min a kirji. Na lura da gaske yake niyyan kiran kanshi da mijin nan nawa.
"Kyawun ki yaja ra'ayina dayawa Siyama. Da ban ganki a yau ba, bansan yanda zanyi ba." Yayi maganan yana dan lumshe idanuwan sa.
"Bara na shiga dare na kara yi."
"Ko sunana ba za a tambaya ba pretty?"
Bude baki nayi zanyi magana ya riga ni.
"Shikenan ni zan fada miki. Am Usman Nadabo"
Nadabo? Nadabo fa? Wannan sunan ai sananne ne.
Card ya ciro ya mika min
"Alkawari, ki kira ni please kafin kiyi bacci."
Gyade kai nayi, na bude motan na fita.
Turus! Nayi ina kallon wanda ya zuba min idanu. Ya makale hannayen sa kan kirji, giran sama da kasa a hade ba alamun annuri a fuskan.
Idanu na fara zarewa, kana gani na kaga mara gaskiya. Sai ga hawaye na kokarin cika min idanu. Cikin sanyin jiki na fara daga kafafuwana ina nufan inda yake.
Sai dai tun kafin na karasa ya dauke kai, ya bar wurin da sauri, a hasale. Citse yatsa nayi ina kallon sa har ya bace.
Cikin sanyin jiki na shiga gidan.
Raurau nayi da idanu ganin Mama a tsaye tana jiran shigowan mu "Mama Allah abun hawa ne bamu samu ba tun dazu. Sai daga baya muka samu wani a wurin ya maido mu."
Tsaki Maman taja "Yanzu da kun ja min Baban ku ya san ba kwa nan fa? Nifa banson haka gaskiya. Na gaya miki duk inda zaki ki dawo kafin Baban ku ya shigo gidan nan ko."
"Yi Hakuri Mamana" na fada ina dan kwanciya jikin Maman. Sai lokacin Rahma ta shigo. Ashe bayi ta shiga ta boye. Gudun fada ne da ita kaman me. Niko nasan yanda nake bi da Mama a wuce wurin.
Daren gabadaya sai naji ni wani irin. Saboda na saba duk dare sai nayi bacci Jabir ke kashe wayan sa. Amma yanda na ga idanuwan sa sunyi ja da muka hada idanu bayan na sauka a motan mutumin nan, ba shakka nasan ko na kira sa ma ba lallai ya dauka ba. Amman ba komai, zuwa gobe zai huce. Nasan yanda zan bullo mai.
A gefe daya kuma tunanin kamun da nayi yau nake. Nan take kuwa na tuno da card in da ya bani, ga alkawarin da yasa na mai.
Usman Nadabo
CEO Nadabo group of companies
Bansan lokacin da na mike daga kwance ba bayan na karanta abinda ke jikin katin. Tsammani na ma ai bai kai hakan ba. Anya Jabeer ba zai jira ba?
Cikin rawan jiki, na dauki waya ta na danna numban MTN in shi.
"Siyama ce" Na ambata bayan an dauka.
"Amma ko pretty kin kyauta min. Ina nan tunanin ki ya addabe ni ya koran min bacci." Murmushi nayi kasa kasa.
"To tun da na sama ma zuciyan ka natsuwa, bara nima nayi baccin." Murya kasa kasa nayi maganan. Ban jira cewan sa ba nace
"Na gaji sosai, sai da safe." Kitt! Na kashe wayan.
Ni a dole jan aji. Dole ne in iya taku na.
Wani kallo Rahma ta watsa min. Ba takan ta nake ba, hannu nasa na kashe wutan dakin. Na juya mata baya. Ina kara shigewa cikin katifan da gabadaya ta gama lumtsewa.
"Na kusa hutawa da ciwon baya da jiki kullum." Na ayyana a raina. Haka nayi ta sake sake na, a raina Ina hango irin rayuwan farin cikin da yake jira na. A haka bacci ya tafi dani cike da mafarkin rayuwan walwala da jin dadi.
A/N: Su Siyama daga ganin sarkin fawa sai miya tayi zak'i. Ya kuke tunanin yanda abun zai kasance?
For a fast update, ku duba shafi na akan Instagram @aysher.bee Acan zan gama littafin In Sha Allah, kafin na maido shi nan.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top