39 our love
*♡TUNTUBEN HARSHE🌺*
_Voyage within the hearts!_
*WATTPAD*
*@SURAYYAHMS*
_Brilliant writers Association_
_Any resemblence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence!_
*For All my fans in whatsap grps and facebook pages*
_39...our dream_
Washe gari asabar shine ranar da zamu bar nigeria dukan mu Cikin bacci naji ana shafa lips dina a hankali na bude idona da suka yi min nauyi saboda kukan dana ci na missing din su mama da tuno da iyaye na
da fuskar Asad na ci kari dab da tawa yanata kallon fuskata A hankali tunani na ya fara dawowa yaushe ya shigo min daki?sai nayi sauri na mike zaune amma maimakon in ganni a kan gado dana kwanta sai na ganni a kasa a kan chinesse rug har nayi pillow da damtsen hannun sa
Na juya na kalle san naga ya wani cire rigarsa complete yayi pillow da ita sai singlet dinsa ne kawai ajikin sa na tabe baki,wai ashe shifa miji na ne yazu da sauri na kalli nawa jikin naga hijab dina yana nan amma duk da haka ban yarda ba sai da nayi ta taba jikina wai ko zanji wani chanji
Duk abinda nake Ssad kallona kawai yake yi yana dariya aransa sai da ya gama dariyar sa sannan yace "Don't worry hala gobe ne And when I touch you wally ko tashi zaune ba zaki iyawa na bata rai nace "wa yace Ka hana ni kwanciya akan gado itama sai da ka raba ni da ita" ba tare dana jira amsar saba na mike tsaye ina kallon waje, I don't know the time but nasan assuba ta wuce ya mike shima yana zuwa rigarsa ya karaso kusa dani yace zanje in shirya, karfe takwas zamu bar nan kasar saboda muje namu gidan akan lokaci" ban bashi amsa ba ya kara matsowa kusa dani yace "are you scared ne?da kamar bazan amsa ba anma sai a hankali nace "eh" quiet nervous yace "me too I am scared nadra,so scared that I might fail you as a husband Sai ya kamo ni jikin sa muna me locking idanuna yace nadra Na sani kamar yadda mutane suke ta fada min koda yaushe cewa I don't deserve you ban dace dake ba hakan ne..Ni kaina bansan dalilin da yasa Allah ya bani ke ba wallh kin fi karfi na nesa ba kusa ba Amma abinda na sani without doubt shine ke alkhairi ce a gare ni" ya riko fuskata da hannayensa yana kallon cikin idona da kyau yace "I promise you like I always did I will never let you down insha Allah Abinda nake bukata daga gareki shine ki kara hakuri dani I promise you you will never regret marrying me alkwari nayi maki atake sena lunshe idona ina jin dadin maganganunsa har zuciyata sannan a hankali na bude ina kallonsa nace "kar kake cewa bakayi deserving dina ba Asad you deserve more than me Dan haka ni ya kamata inji tsoron kar in gaza baka farin cikin da kayi deserving And I promis to suport u har karshen rayuwan mu,asad yanata kallo na Expression din fuskar sa is very clouded irin yanayin da bana iya karantar san nan ya jawo ni da sauri ya rungume a jikinsa ban hana shi ba ya jima dani ajikin sa sannan ya sake ni ya kamo hannuna ya saka min key din kofar sannan ya juyo yana kallona yace "see you on the other side wife" daga nan ya fice Ina kallonsa ya yi hanyar dakin su
Na jima a tsaye a gurin ina kallon hanyar da yabi sannan na juya na shiga daki Direct toilet na shiga nayo alwala nazo na fara sallali ina rokon Allah alkhairan da suke cikin auren nan da kuma tsari daga sharrukan da suke cikinsa ban jima ba aka fara sallamar baki sai na tashi na shirya Ina idar wa Mama ta shigo tace min "kizo inji babn ku na mike na bita a baya har part din kawu, ina shiga na tarar dashi a zaune yana shan coffee ya shirya tsaf daga dukkan alamu daga nan munyi sallama kenan
Jiki a muce Na zauna a kasa na gaishe shi ya amsa mun fuskar sa a sake Sai da ya gama shan coffee dinsa sannan ya fara min magana
'Nadra yau Allah yayi insha Allah nan xaku tafi kubarmu ke da mijinki wanda ke kika zabe shi da kanki mu kuma muka goya miki baya har Allah ya tabbatar mana da abin ni dai babu abinda zance sai Alhamdulillah. Na amince zan aura miki asad ne saboda abu biyu, na farko ina kwadayin ladan da zamu samu daga ni har ke in har burin mu ya cika na gyara rayuwarsa, abu na biyu kuma saboda tsananin sonki da naga yana yi, nasan wannan soyayyar zata iya saka shi yayi komai wanda nake saka ran soyayyar ki zata iya saka shi ya chanza sosai a rayuwarsa Auren Asad da zakiyi tamkar jahadi ne.
Duk abinda nayi a rayuwar asad tamkar sharar fage ne akan wanda ke zaki cigaba dayi bayan auren ku. Sai kin dage sosai yata. Nasan ke yarinya ce mai ibada amma ina so ki kara akan wacce kike yi da, ki dage da adduoi na neman tsari sannan ki tsarkake zuciyar ki daga dukkan sharri Allah yana tare da ke kuma bazai barki ki tabe ba Ina son ki sani cewa dani da mana n ki muna tare dake 100% amma hakan ba yana nufin muna so mu san duk wani sabani daya shiga tsakanin ki da mijinki bane duk abinda ya faru tsakanin ku mun fi son ya kasance ya tsaya a tsakanin ku, sai dai in har kinga yafi karfin ku sannan sai ki kawo mana shi mu kuma zamu yi iyakacin kokarin mu muga an samu maslaha a lamarin Allah yayi miki albarka Allah Allah ya baku zaman lafiya dake da mijinki"kuka na fashe da shi mama tace tace "Ameen" ya tashi yace "nina tafi"Allah ya kaiku lpya .sai da suka fita shida mama sannan na lura cewa kukan nake yi sosai n goge hawayen idona ina jin alamar jikina yana daukan zafi kamar mai shirin fara zazzabi Ina nan zaune har Mama ta dawo daga rakiyar kawu ta zauna kusa dani ta kamo hannayena tace "kuka kuma ndara? Wa yace miki yanzu 'yammata suna kukan aure?" Nayi mamakin yadda Mama take min magana a hankali cikin rarrashi duj dama har zazzabi tayi akan rabuwar namu..nan ta shiga yimin tata nasihar da kuma bani shawarwari akan harkar auratayya na koma na kwanta akan cinyarta ina sauraronta kuma ina daukan duk abinda take gaya fin na dan yi murmushi kadan Wayar tane yy kara tace to,sannan ta dube ni tace tashi ki kammala shiryawa duk sun fito to.
*♡TUNTUBEN HARSHE🌺*
_Voyage within the hearts!_
*WATTPAD*
*@SURAYYAHMS*
_Brilliant writers Association_
_Any resemblence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence!_
*Shafin mumyn yara💌*
_38...love is impatient_
haka rayuwa ta kasance mana a hankali munakan dawowa hayyacin mu su kawu kuma suna ta shirye shiryen auren namu duka batare da ansanya mu ciki ba
Kawu be barina na fulita ko ina so duk shaukin ganin fatima danayi duk awaya muka kare..sai Bayan sati guda Asad da azad xasuje hira wajen fatimar sai suka takura min wai sai na bisu
Hakan naje gaban mama da kamr nace zan raka azad gidan su fati mama tace "to ke sai driver ya kai ki ai.. na dan yi shiru nace "Mama da Asad ne fa shi yace zai kaimu ma..mama ta jima tana kallona ni kuma na sunkuyar da kai kasa sannan tace "toh shikenan a dawo lafiya" atake Na kira asad din nace masa mama ta bar mu gani nan fitowa A motar na same su already sai na shiga seat dib baya muka tafi
Murnan ganin juna da mukayi da fatima babu kamar sa muna cikin tadi sai Asad yace "fatima wai yaushe ne bikin ki,ta gwalo ido Tace "biki? Ai sai ka tambaye shi,ajiya cup asad yy ya tsura masa idanu can Yace "wacece ki ka fi damuwa da ita tayi aure?" Fati tace "ummmm se ta dibe ni,tayi murmushi..tace ok nagane asad to ga amsar ka zamu sa rana amma ai sai ranar da ka shirya to a ranar za'ayi" asad yace Allah? "to ai ni a shirye nake wallhy aure nake so"..nidai ina jinsu na rabu dasu nasan neman magana ta yake yi Dariya duka suke yi, ni kuma dramar asad ne yake ban takaici
Daga nan muka rabu muka koma gida azad yay gaba ya bar mu sai naga ya kama hanuna mun koma yin wata hanyar daban this time banyi magana ba Asad din yace nasan kin gaji but "pls I want to show you something" Bance komai ba har naga ya kaini cikin babban garden dake bayan gidan mu wani abu ya ciro acikin flowers kamar bulb ya kunna wutar ligher sa akai tayi dan kara kadan tuni wajen ya buyawae da wani irin haske da pink bubble suda kan su suke jeruwa a air suna rubuta "nadra...will please do me afvour of marryn me?
Sai na kalle shi da mamaki yace to ba kin ki gayamin kina so na ba?shi yasa na gaya maki kalaman da na fi so"pls marry me.. Finally yau daga ni sai shi nace masa ban fahimce sa ba"dada matso ni yy ajikin sa yace" pls marry me,nadra aure nake so muyi..sai nayi murmushi.
Yace "wai har yanzu Mama ba ta ce miki komai ba?" Nace "akan me fa?
Ya nuna kansa da yatsan sa sannan ya nuna ni yana sauke wata miskliya mischievious grins dinsa Na gane me yake nufi, na dan bata rai nace "ni ban san akan me kake magana ba" yace "habawa common how much longer do I have to wait ne wai Nide aure na ke so in baki gane ba ai na fada miki yanzu d wuri na rufe baki ina dariya nace baka jin kunyata kake cemin aure kake so? Ya gwalo ido Yace "nady ke din zanji kunya? Ke fa zan aura kuma sai inji kunyarki?
Nace tabbbbb hmm
To Please ki dan tambayi Mama mana kiji me ake ciki ne" nace what?ni me zan ce mata? Ince mama yaushe za'ayi min aure?"Yace yess yesss.."exactly"pls baby na..sai na girgiza kai nace "sai dai kai kaje ka tambayi kawu yace "OK, wato ke kina nufin ba kya son auren kenan?" Nace "wai me ke damunka ne yau?" yace "ai na riga na gaya miki me yake damuna nace aurenki nake so,l ai nayi kokari ko, ya kamata a bani abuna...Kinga yanxu abinda za'ayi irin in kuna magana da Mmaman nan sai kike gaya mata ga abinda kike so ayi da bikin ki tare da na kawarki fatima so mama zata dauki haske kinga sai tayi wa kawu magana" nace "wai ni na ce maka ina son aure? Kai da kake son auren ba sai ka fada ba?Ya juyo yana facing dina yace "look into my eyes kice ba kya son aure na"na ki kallonsa, yasa hannu zai juyo fuskata na kara matsawa yace "kin gani ko? You want it too na girgiza kaina nace "ni banson komi"cikin murya kasa kasa yce "then look into my eyes and tell me you don't want me" da sauri na kama hanyar zan tafi shima da saurin ya taho ya sha gabana "au guduwa zaki yi ko?" Nace "kafi karfina yau your mood is not for me" yana kallon cikin idona yace"I have always been in this mood for you nadd only you Kawai hakuri nake but please do something Ni fa idan ba'ayi mana aure kwanan nan ba to akwai rigima."
Dariya nake son yi amma shi fuskarsa dagaske ne can ya fara devilish smirks dinsa sannan na fara bayyana dariyar sa yana kada kansa yace "laugh all you want my time will come, then I will do the making noise and you will do the keeping quiet" bansan sanda na daina tosashen dariyar ba da sauri na nayi hanyar gida ina jinsa yana kira na amma ko waiwayowa banyi ba.
A cikin kwana biu gaba daya Asad ya rikice min wai shi lallai sai na fada a gida cewa aure nake so kuma shi in nace masa ya fada sai yaki a dan Dole yanzu na fara rage doguwar hira dashi tsaban sakin layin da yake Gaba daya ni yanzu lamarin sa tsoro yake ban kuma gashi kawu ko mentioning zancen mu baya yi duk sunyi shiru da magannan
Haka ya fara takura ma azd Rannan yace masa "to wai kai me yasa ba zaka je ka tambayi kawu ba? Ai kun fi kusa dashi naga,..shiru yy yana kallon sa sannan yace "kawu has done so much for me ne bana so inyi disappointing dinsa ne bana so yaga gazawa ta ko kuma yayi tunanin dama abinda nake after dawowar nady kenan Nafi so ace shi yayi min magana da kansa
Amma gaskiya na gaji da jira I don't know how long zai taking kafin yayi min maganar" ya dan bata fuska yana tunani yace gata itama ko ajikin ki ta wallahi hankalin ta kwance wai ita ko shekara nawa za'ayi ana magana haka babu ruwanta ko?" Axad yace "wa ya gaya maka haka?" Yace "to ai bata nuna wa At least itama ta dan ringa nuna min tana so mana,"ni wallhy tsoro take ban se inga kamar bata yafe ba azad yace komai fa da lokacin sa musamman aure in kaga anyi to lokaci ne yayi ba wai nuna ina so ko rashin nuna inaso bane zai sa ayi Kai dai kayi ta addu'ah sai kaga komai yazo da sauki"...Bayan kwana biu gidan mu ya fara cikawa da baki wannan na tafiya wannan zaizo tskanin yan uwan mama na da su kawu ibrahim
Its seems like Mune kawai aka barmu a duhu,ashe anata magana ana dinkewa zancen auren mu sossai yayi nisa harda shifts din aikin mu a inda zamu zauna dukan mu hudu
Nida Asad a us,su kuma fatima da azad a can cairo, egypts.
To aranar da aka kammala komai kawu ya tara mu yana me mana nasiha sannan ya sanar da mu ansa ranar auren mu ranar jumua bayan sallahn jumua 7,07...
Ata fannin iyaye har sun gama komai so yanzu turn din mu ne,We all have 12 days more mugama shirye shiryen mu..ai Asad tunda yaji haka be zauna ba don haka kawai yakanje ya gode mama kawu da mama,nikam ma gudun sa nakeyi dan a kullum baida aikinyi sai na firgita min ziciya Auren mu zai kasance geek nd simple liyafa kawai za'ayi na rana daya washe gari zamu kaura kowa yay tafiyar sa da matar sa,bayan gyara da kwalliyar da mama ta sa ana ta min haka nan ma hjy salma mahaifiyar fatima bata tsame ni anata fannin tattalin ba. .
Nide naji ddi da Ba a wani tula mana kayan mata ba amma ba laifi mun kintsu da asalin kimtsin tsoffin mata,munsha tsumin kayan itacuwa da wankan lalle da treatmennt domin dakile infection,acewarsu asali dama infection shine asalin matsalar matan aure bawai rashin ni'ima bane kadai.
#TUNTUBEN HARSHE BANA SIYARWA BANE.
Sabon littafi na wato
*#KUDI..kumbar susa*
shine na KUDI muna page 19 with vip ahead the drama has just begun,shin ya zakiji in mijin ki ya auro yar aminiyarki?hnmm dammuwa😃nemi naki kar abaki labarin...
_YADDA AKE BIYA,HOW TO SUBSCRIBE,plus payment details_
_FARASHIN SA👇🏿_
#300 naira ne
#450 naira for VIPs
*1- Biya Ta bank acct*
_Use👇🏿_
Account name:
Surayyah muhammad suleh
Acct number 0152983148
Bank: GTB
*Sai ki tura screen shot shedan ki wa 👉🏿08036651119*
*2.MTN RECHARGE CARD OR VTU TRANSFER👇🏿*
*08060712446*
*Sai ki tura screen shot shedan ki wa 👉🏿08036651119*
*3:yan kasashen da ba nigeria ba masu biya ta PAYPAL,OR*
Use👇🏿
Phone Number :07058797141
CITY:bauchi
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top