33:goodbye
*♡TUNTUBEN HARSHE🌺*
_Voyage within the hearts!_
*WATTPAD*
*@SURAYYAHMS*
_Brilliant writers Association_
_Any resemblence of story or lifestyle shud be considered as a coincedence!_
_33..Goodbye._
_cambordia 9:45am_
Tunda Asad ya isa yake ta ziriya shikadai wajen neman hanyar da zaiga carmilla ashe anan ma case babba akeyi akan mijin twin sis dinta wato megahn,sun shiga kotu anan sabida mijin ta ray white ya mutu kuma bincike ya nuna boro boro cewa meghan ce ta kashe shi gashi anan nigeria ma an turo jamiai ana jira ne atafi da carmilla
Domin case din karyan da akayi na fake death dinta
Kuma Already babban kotun tarayya daga can sama ta yanke zunrutun kudi da zasu ban na lefin bata min suna da akayi,molly da masu temakn ta r already behind bars..
Har washe gari ba aga asad ba kawu sai ya damu sosai sanda azad ya gaya masa yadda sukayi da shi jiyan akan inbasu gansa yau ba zasu neme sa,har kotun da ake case din anan carmbodia asad yaje dan yaga carmila da idanun sa,itakan ma bata lura ba Asad yana ji aka yanke ma megahn hukuncin daurin rai da rai sunata kuka su biun har suka rabu..
To jami'an da zasu tafi da ita ne suka zo,she is already traumatised to say no Daga idanun ta ta da zatayi sai ga asad agaban ta A Tsaye kamar statue ya zuba mata qarwashin wutar dake idanusan da duka hannayen sa cikin aljihun sa,daga ganin sa kasan ba lapya ba
Cikin matukar kaduwa da raxana Bakin ta na rawa tace ASAD?Tashin hnklin data ji ya taso mata be kai wanda yanzu takeji ba,dakan ta nemi alfarman yin masa magana na minti 30...cikin saurii da rudewa ta nufo gaban sa..Asad yana tsaye be motsa ba,hawayen ta ta share sannan ta dago ta kalle idanun sa da sukayi rammm tsaban fushi da damuwa wani sabuwar karayar zucia da kuncewar kai shike neman mamayar ta sede ta riga ta san rayuwar tane ya kare,soyyr dake zuciarta game da ASAD beda amfanin komi,Duk tanbayar dake rubuce a idanun sa ta fahinta,ta dada matsowa gwanin tausayi ta kalle sa cikin sarkewar murya tace IM SORRY ASAD..pls i am sr..wani sautin tass me gigitarwa taci karo da shi a fuskan ta tun bata karasa kalaman ba..."araunane yace sorry for what carmilla?ni bawai nazo bane dan na saurare ki,nazo ne in tambaye ki menene nadra tayi miki?why did u choose to blackmail her nd send her to prison?sabida nine,ko saboda karatun ki?..dafe da kuncin ta tayi masa shuru,wani tsawan ya dakata mata sanda ta razana yace answer me carmilla,kinsan gaskiya mesa baki fada min ba?why did you make me believe that nadra is wrong nd ure right,why?anan seya fara hawaye..is this another betrayal?another game?kamar xai mata kuka yace carmilla..pls tell me
Why did u make me hurt the woman i love so much why
..kuka carmilla ta dada fashewa dashi tanaji sa yana turasasa ta akan ta amsa,sanda tayi me isar ta sannan ta kalle sa cikin yanayin rudafden masifa da azaban kaunar sa dake damun ta tace pls
Stop...Asad.. A was only apologising for what my dad did to ur nadra,nide baxan baka hakuri akan kome ba ni babu abunda na maka.."duk abunda ya faru kai ka zabar makan ka,da ina iya zabar maka rayuwa ko sauya maka ra'ayi da na sa ka so ni ka rabu da soyayar nadra aranka cos u actually derseve me not nadra..nadra bata dace da kai ba.
Bakin sa har na bari Yace what?
Kukan ta cigaba dayi tace
"ni da kai duk muna iya cutar da abunda
Muke matukar so akan wasu dalilan mu....but her love for you was limitless...it has no right or wrong
Ko da shike Ka kasa fahimtar soyayyar mahaifin ka ta yaya zaka fahinci na nadra?
Nikuma na dade da gane mugun hali da son kai irin na baba ba" i know he nava loved us"...Asad baban ka ya taba saka abu dole ne ko yataba cewa in baka masa abu dede ba zai kashe ka?but i still obey my dad...not bcos he is right..but bcos he is my FATHER kuma Bambanci na dakai kenan
Nafika fushi da damuwa akan mahaifina da shi nake kwana intashi arayuwata,amma ni ina iya ganin abunda yake da muhimmanci arayuwata kai kuma zuciar ka kawai kake yi wa biyayya.
Lokacin dana zo maka da soyayya ta
Baka karbe sa dan nasan baka so na ne,amma nadra fa?
Asad ni ne nayi matukar tsanan nadra,araina ji nake kamar in kashe ta, amma baka gani ba sabida ra'ayin ka akan biyayya"ita biyayyan ta dan ta kare ka ne ba zuciar ta ba..kaine kake fama da cutar biyayyar wa zucian ka.
Ni ban yaudare ka ba kaine kayi wauta daka manta wani abu game da yaudara
"...betrayl dosnt depend on how deeply or truly u love someone,Betrayal is an inherant part of love..yes har yau ina matukar kaunar ka"
Amma nafi fahimtar cewa hakan bazai taba samowa ba,so i choose to obey my dad sabida shima ya nada muhimmaci arayuwata,na yarda ne akan game din dan inyi maka gata,ai in aka saka ka jefa nadra a prison sanadiyar ra'ayin ka wata rana dole zaka gane cewa kaine baka da gaskiya akan kome ko?.
Nd Shamelessly u testify againts her character"ka amince nadra zata iya aikata komai..ku maza kuna da wani irin rainin wayo..ka dauka duka rayuwan ta ta aje ne sabida kaiko?a tunanin ka zata mutu in babu soyayyar ka?shiyasa kake ganin zata iya aikata komi akanka?
Now that u know that ba itan bace ta dauki video me xaka ce mata?...barin fada maka molly tayi min hakan ne a matsayin fansar soyayyar datake yi maka wanda ta san har abada bazata samu ba To meye ne in nima nayi maka haka?ai kowa fansar soyayyar sa yake dauka right?
Amma kai ka samu soyayyar nadra se ka kasa sanin yadda zakayi da shi sabida baka san meke maka ciwo ba u cant love anyone asad,bcos u fail to lov ur self.
Duk wanda be san darajar iyayen sa ba bai san darajar kansa ba.
Ina fada maka haka ne sabida yaune rana na karshe da zamu gana daga yau har abada,..Kayi hakuri...in abunda baba na yayi muku ya muku zafi,u see my dad neva loved us,dama nine da mahaifin kan nan da ko kashin sa yace ina lashewa zan rike sa kuma in masa biyayya
Look at me ina raye yace ince na mutu..my sis is now imprison for life shiya jefa ta acikin wannn rayuwar..
Is This ur defination of freedom Asad?go home nd apreciate ur dad..in ka samu uba irin nawa nan ne zaka san biyayya ba abu bane me saukin kin yi ma mutumin da be taba sonka ba.
its time..ni zantafi..
I hope zaka mance da ni..in sory but i wll neva ask u for forgiveness..soyyarka da baxan taba samu ba shine azaba ta kuma shine ya bude min ido na gane ni wacece'so thank you..i did a favour to ur life by showing u things that matters too..Kayi anfani da da darusann shi ko ka zubar,is upto u..GOODBYE ASAD ZAIN ABDUSHAKUR.
Until now I am still
CARMILLA CAMPBELLS OBASI.
Kaiwa NAN ta juya tabi jamian tsaro suka barshi tsaye kamar gunki yana ta kallon ta har suka bace ma ganin sa be iya cewa komai ba se kuka
Asad har ya iso nigeria be dana maimata ma zuciyar sa maganganun carmilla ba dan ko kalma daya nata data furta be bace a a zuciyan sa ba.
Kamar kurma hakanan zaka gansa,daga carmbodia zuwa nigeria bazai iya cewa yayi maganan da yakai na sentece uku ba
he felt lost and stupid at the same time. An dade ana ce da shi wawa sai yau yagane ashe gaskiya ne
Carmilla is really a god sent karma,not only to his life but to his heart.
A Washe garin ranar Yana sauka a nigeria da ya shaki iskan kano sanda yaji kansa ya sara, Wani shegiyar tsoro ne ke nemen nakasa masa gabobin jikin sa,ta yaya ne ma ze fara gyara komai?..
Tin kan ya shiga jirgi yake duba maganganun har ya A jirgin tunani yake
He realized that he has been the most foolish fella in the century...gashi nan de namiji har namiji me ji da wayewa,kyau da ilimin amma ba abakin komi ba..
Kuskuren dayayi akan kawu ne ko wanda ya tafka akan nadra?ya rasa da wanne zai faraji aransa..kansa tuni ya dau caji jjkin sa ya dau dumi sosai,daga nan prison ya nufa ko zaiji labarin yadda ake ciki da case din nadra,gaba daya ba a hayyacin sa yake ba bare ya kawo cewa an riga an wanke ta she is free now...
Anan bangaren kuwa tunda azaad ya bincika ya fada ma kawu cewa asad yaje cambodia ne tuni kawu ya fara harsashen Shiriya ce ta zo ma dansa Asad,shiyasa yy shiru be damu da cewa a neme sa ba..zazzafan arrangement ya shigayi na exams shifts,daga school zuwa yola garin mama na,ina zaune a gidan baristr ranar fatima ta kawo min ziyara kawu yake ce dani,zefi dacewa na tattara na tafi na kammala karatu na a gida chan ba'a schl ba,aganin sa sabida abunda ya afko students da malamai duk zaa dinga distracting dina akan exams dina..yace gwara kije kiyi abunki online in yaso in Allah ya sa kika cimma burin ki,zasu ganki ranar karban sakamakon ki,babu tantama na amsa kawu dan nikaina nasan in na koma schl zan dawo topic of discusion,and ayanzu babu abunda nake so face naga na cimms buri na karatu,i want nothng but a peaceful life shiyasa bana jin soyayyar kowa araina,da muka koma gefe fatima ta dada zuga ni akan maganan,duk dama tayi bakin cikin yadda zamu rabu cikin giftawar lokaci
Nima na damu da rabuwar namu amma ba sosai ba dan na lura,fatima da Azaad kamar akwai boyayyen sirrin a zukatan su
Na lura kusan kullum suna haduwa,ga calls ga chats,saina rasa meke faruwa..lol
Yau 16days da zuwan azaad nigeria 14 days da haduwar sa da fatima amma in kagansu da kyar zaka ce basu san juna for long ba,yau da xata je gida ma shi ya rakata"abun de gashi nan a bayyane amma dukan su kowa na killacewa,kyabe baki nayi nace "tab di wannan shi ake kira so gamon jini,araina har na fara tausayin kawata in azaad ya tashi komawa egypts,thy seriously
Dersv each oda..kusan yanayin rayuwar su iri daya ne.
Duk wani kammale kanmale na shirin tafiya na angama har munyi sallama na karshe da fatima,azad yace min yana nan tukuna in komi ya dedeta a gidan zai zo har garin mu muyi sallama kafin ya koma egypts,naji dadi sosai,godia ta musamman nayi masa,wanda seda ya sa shi hawaye.
Shine muka raina masa wayo,the quiet nd shy version of asad,the good boy,bamu san duk gata Allah ya masa ba...he has a heart of gold..duk abunda ke faruwan nan shi har yau be dau gefen kowa ba kuma baya fushi da kowa...he just want peace...da wuya abu yake bata masa rai,sam be dauki dunia abakin kome ba,uwa uba ga alkunya sumtimes in yay wani abun kamar mace.
Toh Yau din da zan tafi yau asad ya dawo,dayaje prison sai akace da shi an riga an sake ni,case din carmilla ake yi da baban ta.
Nan ya juyo sai gida,duk a tunanin sa kowa na gidan wani tukin sauri yakeyi,amma besan ma in yaje gidan me zaice ba.
Horn ya danna a main gate aka bude masa a lalace ma yay parkin Ya nufi cikin gida.
Tun kan fuskan sa ya bayyana a sarari yace Salam alaikum sai kowa ya amsa da wassalam,a lokacin ni da mama da kawu da azad ne a falon,daya dube mu duka wani buff buff kirjin sa ya buga,kansa a sunkuye ya karaso ciki to tun kan ya budi baki yay gaisuwa kansa ya daure da kukan da mama takeyi tana dada neman gafara na,saima yanzu ya iya samun karfin zucia kallon inda nake a sace kamar munafuki ya dage idanun sa yayo kaina anan ne yaga akwatuna na a gefe gaba daya.
Kawu yace toh mu xamu tafi lokaci yy zamu kira ku in muka aisa
Slowly Na rusuna rungumo Mama ina hawaye,mama kan tsaban damuwan zamu rabun har muryan ta sanda ya dishe tana saka min albarka..tana min addua oi
Azad ji yay an rike hannun sa,ya juya suka hade ido da dan uwansa,be ce masa komai ba amma jajayen idanun sa sun bayyana tambayar da yake yi,so yake yasan ina zanje?
Murmushi kawai azad ya mayar masa,ya dada riko hannun sa sega kawu ya juyo ta kansu,"yace Asad kadawo?..da sauri ya dago kai ya dube kawun bema iya bashi amsa ba..kawu ya tabe baki yace to a kula..sai na dawo..nan ma azad ne ya amsa da toh,..
Mama ta mike ta haura sama tana boye nadaman ta,nikuma nayi karamin murmshi wa azad shima ya mayar min,kamar ban taba sanin asad arayuwata ba haka na saka kai nabi bayan Kawu na fita..farin ciki da kwanciar hankli na kawai nake bukata sai kwata kwata na cire Asad a duniar rayuwata
Muna fita A firgit ya zabura kamar xarrare,cikin tsananin rawan murya yace axad ina zata je?..ararrabe kalman suka sake fitowa abakin sa nunfashin sa na yankewa tun kan axad ya amsa yace in..a i..naa. z.at..ata tafi?azad ya dafa kafadun sa,yace she is leaving for good Asad..nadra bazata sake dawo ba araxane Asad yace mene?kamar an jona shi da electric haka ya shiga shock,be tsaya jiran wani amsa ba A haukace ya yunkura zai fice azad ya jawo shi da karfi ya riko sa,yace Asad pls let her go..ya isa hakan nan she made this decision...can you pls respect that?
A zuciye yace nadran ne tace zata tafi ta barni har abada?Azad yace yes..Asad kamar karamin yaro ya fashe masa da kuka hawaye na bin hawaye yace No..ya kuma cewa NO..ya kuma danna ihu yana cewa NO da dasasshiyar muryar sautin kukan sa
Gaba daya seya rasa yadda zaiyi yaje ne y dawo ne can sai ya sake jikin sa kamar nakasashe ya fado jikin azaad yana ne limshe idanun sa yana kuka sosai duk jikin sa rawa yake gwanin tausayi,a kafadun sa ya aje kansa,tare da sauke shessheka me zafi shikadai yake furta Am SOORRY...i made a mistake am sorry.. Axaad nayi kuskure!!...sai ya cigaba da kukan disheartedly
Wani turirin hawaye ne ya cike idanun azaad ayayin dayake jin kukan dan uwan sa har tsakar zuciyansa ta ko ina yana tsagawa,kukan takaici da azaba da na shiga uku asad yakeyi..har besan lokacin da Azaad ya ja sa ya kaisa dakin sa a cahn BQ ba..
Yana tare da shi yana lallashin sa har suka raba dare seda Yy da gaske sannan ya sha maganin zazzabi sannan bacci ya dan dauke sa
Washe gari da asubahin fari azad farkawa yyi yaga gogan na parking din kayan sa a jaka kamar mahaukaci shidaya yana ta bambami, saukowa azad yyi da sauri,yace meye hakan?Asad yana shiru Be amsa ba azad Ya fauce jakan yace nace ina zaka je?r u insane..yace yes im insane'bakka san ya nakejii bane'kowa ya share ni,mama bata ma duban inda nake..nide zanbi nadra..i said im sorry..wallhy i cant bear all this,azad kana gani fa nadra batace min komai ba,wai har ta tsane ni ne..nide ko ta tsane ni ina son ta...sai ya fara kuka yana nuna masa wayar sa..her phone is off now. I want to talk to her..Azad yamugun jin tausayin sa amma haka ya danne yaja tsaki,kaban jakata kanaji na ko?azad ya juyo yace kai ka nitsu mana babu fa inda zaka..nadra ta tafi ne dan bata san haukar nan naku pls let her rest mana yarinyar nan ta sha wahala sosai she just got out og prison,wai meyasa bazaka kyale ta ta huta ma ranta ba?
A zuciye asad yace bazan kyale ta ba,give me my bag now..Azad ma a zuciye ya juyo yace baxa a baka ba,kai kafi kowa rashn nitsuwa ko?sai ya juyo ya kuma wurga masa jakar yana me nuna tsadadden fushin sa..yace
Go...ka dau jakar ka bita din,who i am to stop u..dama ai akan ra'ayin ka kake zantar da rayuwan ka...baka taba daraja uzirin wani ba..follow her now who cares..its ur call after all..nadauka by now kaga rayuwa amma ashe har yanzu a wawan kake...if u cant even respect her decison
Yaushe zaka gane matsalar ka asad?..
Bacin duk abunda kayi ma zuciarta, and u still think she wll listen to u now?
Kasan me?Matsalar ka ba nadra bane kawai,right now u need to calm down nd think abt ur life first,ure confused... in kaje ma me zakace mata?
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top