20 who do u love most

This page is All for ma wonderful ppl  who wishes me happy birthday!nagode, nagode, nagode.Allah ya bar kauna ehrrr🙏🏻

_20 who did u love most?..._

Da kyar carmilla ta iya tattara sauran karfin ta ta shige gidan wani gulluton rudani shiya ke so ya shake mata wuya,tafiya take a sanyaye idanun ta gaba daya sunyi jajir sai taga gidan ya kara mata fadi,a sadede kamar barauniya haka take haurawa matakalan harta shige dakin ta

Akan gadon ta zube ta sake wani irin ajiyan zuciya from no wher sai ta tsinci kanta da fashewa da marayan kukan da baya saka zuciya samun sauki bare ya hana rudani

Asad has done hiis worst today,kenan duk abunda ta fada mashi game da famlyn ta ya watsar kenan?ya ze mata haka..har gida har gaban baban ta?..yanzu tayaya xata ma fara lallaban iyayen tan?
Tasan yau kam Babban zunubi ta aikata wanda bata ma tunanin kalar purnishment din dan tasan wuya xataci sosai

daga sama kuwa babu abunda ke tashi sai sautin yaren igbo cikin azalzalan masifa..

"Ai Dama nafada maki yarinyar nan tun haihuwar ta ta tsane ni...batajin tsoro na..her sis meghan wil neva try to insult ma dignity this way,..kai a kasa mr michelle ta dada matsowaa amma takasa taba shi tsaban yadda jikin sa yake shaking har yana gurnani," "obasi..pls calmdown err...carmila has done her worst amma ai yarinyace ko,wani watsa mata harara yyi ji yake bazai taba yafe mata ba har abadan abada"mrs michell ta rusuna kan gwiwar ta da tattausan murya me ban tausayi tace forgive her nnai,she is still a child...i beg u.biko nu nnai..
purnish her,but i beg u do not hate her..nima na maka alkawri zan dau nawa matakin musamman akan wancan marar kunyar yaron..sai ta mike tsaye tana huci

Hakan sukayi ta tattaunawa,sun dau lokaci suna jani in ja ka da kyar ma sannan mr campbells ya sauko  ya bar maganan ya fice

Ranar Har yanma Carmilla bata fito ba,ko abinci bata sauko ci ba tsawon kwana biu bata je ko ina ba..tunani takeyi cikin nitsuwa dan tana sane da cewa da zarar fushin mahaifin ta ya sauka akan ta this time around to fa ta bangaren ta za'ayi mumumnan al'amari.

Duk da abunda ya faru jiyan sai taji son asad be gushe aranta ko da dan kadan ba,yanzu kam tasan in har aka ma asad wani abu akan ta bazata iya daukawa ba,gashi tana matukar tsoron fushin mahaifin ta,"ziriya take yi ita kadai,tama kasa kiran kowa bare ta nemi shawara..can in tagaji takanyi kuka mai rauni koda abunda ya cinkushe zuciar tan ya dan ragu,"but she knew she had to think fast too ,dan hakka ta harhade plan cewa itama wanann karon
Zatayi wasa da kwakwalar baban ta akan asad..

Tana so tace mishi ai duk wannan salo ne na cimma burin su,ita babu ruwan ta da Asad,kawai yardan asad din kawai take nema again dan ta sake danne shi,karma  yace zai dau fansa akan su.

The plan seems perfect,anma tsoro ya dame zuciarta akan ko zataci nasara mr camp bells ya yarda ko sabanin haka
Sosai ta tsara karyan cikin makirci da maganganu masu kama hankali
Kanta ne kamar zai fashe tsaban tuno da abubuwan da tayi ma asad dib abaya,cin amanan wanda ya nuna maka matukar yarda mummunan abune,shin in har asad zai iya daurewa da iyayen sa lokcin da baiyi exams ba ita meyasa bazata iya ba?

"she betrayed him,insult him,tasa shi ya tsallake dokar gidan su ya kwana awaje nd he missed his exams for nothing..to kenan shi ya iyayen sa sukaji dashi a lokacin?...gama wannan tunanin aranta yasa taji sabon karfin gwiwa dan haka ta shirya tsaf,tana jiran lokacin da iyayen ta zasu je dakin bauta

Sai can Da misalin bayan ishai tafito hakan tayi ta rakube daga zuwan su har shigan su tana kallo,basu rufe kofar ba dan haka sanda ta bari sun nitsu suna addua sannan a hankli ta rakube ta shigo ta tsaya abayan su

Lokacin Duk hanklin su bainan,cikin dauriya da rawan murya ta soma bayanin ta tsaf batare da ta fara bada hakuri,..

Jin muryan tan  abayan su yayi matukar shockin dinsu bare aje ga abubuwan datake furtawa,Sun sha mamaki kwarai yadda carmilla ta fi su dogon tunani,.

Mrs michele ce ta juyo tana kallon yadda take maganan..

I will neva betray u father..."despite the fact that we breed lions,that dosnt mean that lions arent scary

Baba,ka fahimce shiri na,wani lokaci makiyin bayyane yafi makiyin dake boye,we made a mistake by showing Asad what we want.." Yau bakuga behavioura dinsa ba?da ai ba haka yake ba..na lura a yanzu tako wani hanya yana so ya rama ya kuma wulakan tani, then i tot abt my studies,i tot abt u father.. Inajin tsoron irin shirin da asad zai mana nex semester...i have to think fast,i must come up with a plan wani wasar da zan sakeyi da kwakwakwsr sa,..."
Dan Allah ku fahince ni ta dada marairacewa tana me zuba gwiwan ta akasa

cike da mamaki da farinciki mr campbells yy kwafa can shima sai ya juyo ya kalle ta,dada sauya muryan ta tayi,just to show how serious she is dede nan gabar ta
Rusuna har gaban sa ta fara bada hakuri,"tace na tsorata ne da abun da nake harsahsje shiyasa na fara game din ban sanar da ku ba...father I must gain his trust again, kayi hakuri in hakan baiyi dede ba,zan karbi duk wani hukunci..

Mr nd mrs campbellss ji sukayi kamar an yaye musu duhun bakin cikin da suka shige ciki akan maganan nan....

"Feeling so proud yace Thats my doter,yarinya me nazari da hangen nesa..Babu bata lokaci ya sauko,ya dada jin bayanan ta
Suka sa mata albarka sosai,suka kuma bata daman yin abunda taga ya dace akan Asad.

Sude campbells in har abu dan ci gaban su ne basu damu da munin sa ba,wani bin zumudin cimma burin sa yakan hana sa nazari me zurfi.

Yaune rana da carmilla ta ji sanyi da farinciki wanda ta dade tana begen sa aranta..

Betrating her parent isbt easy amma sabida son datakeyi ma Asad tana kallon abun ba komai ba...gashi tayi karyan har anbata full permissoin na fita waje da zuwa wajen Asad duk lokacin datake so

Sede plan din sun shine,iyayen sun sha alwashin zasu cigaba da nuna cewa bada sannun su bane,har se ta durmuya Asad again

Haka nan aka bar maganan,carmilla ta koma daki dauke sa wani sabon nishadi a zuciar ta

Dadare ma Bacci me ni'ima tayi bayan ta kamalla tunanin yadda xata fara baza game din ta dan ta samo zuciyar Asad..Tunda hakan ya faru take da yaqinin inta sake komawa gidan ta jadadda masa shi ta za ba iyayen ta ba to tabbas Asad zai sauko

Babban burin ta ayanzu Asad yace mata."i love you too"

Alkwari tayi daga ranan ko musulunci akace ta karba ta aure shi she wont waste any time. She dont care if she wll loose her family  .

Washe gari da nazarin abun ta farka Dan haka ta shirya tsaf,dresses shoes,da duk wani charm da mace ta san inta sanya wa jikin ta zai dauke hankalin namiji shi take matsowa dasu,duk ta maida kayan ta ta sauya da wasu masu shegen kyau,babban shiri takeyi dan yakin samo kalma ukun nan daga bakin Asad.

Bayan kwana biu,blessing ita kan ta bata san meke faruwa dan carmilla bata gaya ma kowa plan din nan ba,shiyasa asad ma beji komi game da  shirin ta ba..

Ita de blessing ta fada masa cewa Iyayen suna fushi da carmillan har kwan biu tayi bata fito ba,so anan hankalin sa ya kwanta atleast koba komi shima ya rama raba shi da albarkan uwar sa datayi na kwana biu.

Shide har yau fargaban sa nadran sa ce,yau saura sati uku a koma schl gashi basu yin waya shide adduar sa baifi yaji ance sun dawo ba cos duk sanda zai kwanta bacci baya iya dena tuno fuskan ta.

Wani bin se ya sha tabar sa akai,wani min in shaukin ta ya kama sa bai iya ma shan tabar..tsananin son ta yakan taba zuciar sa har da kwakwalr sa,sai ya fara tunanin ko ya sa serious akan abunda yakeji dinne?,amma kuma baya so yayi da garaje,but he needs nadra...yana so ya fahimce wani abu guda atattare da feelings din ta akan sa..zumudin hakan ya hana sa sakat,kullum yakan duba calender dubar ranar da zasu dawo kano su same shi.

To Yana cikin wannan yanayi ranar ya fito falo kenan yaci karo da budewar kofar carmilla,tasha kyau,fari kat din riga da wandon jean wanda ya mata jahilin kyau tasa ta tsaya tana kallon sa.

Shima kallon nata yayi sede fuskn sa tamau babu alaman dariya ko wasa har ya taho y zauna uffan be ce mata ba'aransa je wonder wannan wata irin mayyar yarinya ce.'shi seda yagan ta ya tuna ashe ma wai tace tana son shi..."cikin wannan tunanin ta katse shi da cewa Asad?sai ya juyo ya kalle ta..hakuri tafara bashi,tana gaya masa yadda ta juya zancen ma iyayen ta har kansa ya so ya daure da maganganun nata

Kenan tana nufin ta bijere ma iyayen nata duk akan sa?..
He cnt just believ that,dan abinciken sa ya san tana matukar daraja ra'ayin iyayen ta,what a shock sosai ya juya yake kallon bakin ta

Yau itama daurewa tayi bata kawo maganan soyayyar ba,ita de damuwar ta su shirya,su dawo kamar da chan.

Wani yanayin Asad ya shiga na tausaya ma halin da ta tsinci kanta aciki duk dama yasan bazai taba iya taimaka mata ba ayanzu ba.

Da dukkan zuciar ta take rokon sa,da dukkan imanin ta da nuna gaskiyar ta.

Give me a chance Just one chance

Rasa kalmomin bakin sa yasa ya ki cewa komi har tagama dramar nata tayi waje,shikuma dakin sa ya wuce carmilla har ta isa gida tana kan tunanin shi,shin tayi kuskure ne data yi hakan?ko de tagaya masa gaskiyar cewa itama wasa da kwakwakn iyayen tan takeyi ba kawai tayi hakan danta kubutar da shiba...to what if be fahimce ta ba?in ya sake tona mata asiri fa?tasan in campbelss yasan nufin ta awannan karon wallhyy kashe ta zaiyi..dan haka sai take samun rudani wajen sanar da Asad asalin shirin ta akan iyayen tan.

Kwana biu sai ta kyale sa bata zo masa ba.

Shikuma hakan yasa ya gamsu da cewa gaskiya take nunawa.,he tot over it,sai yace toh zai bartan suyi abota amma zai fito mata ne a asalin shi ba  kamar Asad na da chan ba...duk iya jajircewa data nuna masa,he still feel nd knws that babu macen da zata yi tolerating halayen sa kuma ta so shi face nadra

A kwana na uku Carmilla na kwance,sai ga sakon email ya shigo computer ta,

Its Asad zain Abdulshakur

Hannnun ta har n bari ta bude,tama kasa nitsuwa takarance
Dan haka saida ta karanta sau uku sannan ta fahince komi

Yace yafe mata'thy r friends again,amma bece komi akan soyayyar taba.

Wani irin tsalle tayi tana ihu tana murna kamar sakon shiga aljanna ta gani a rubuce,game da soyayyr aganin ta duk wannan me sauki ne tunda Asad din ta ya dawo mata.

Sai tanajin aranta bazata iya sake bata wani lokaci reply tayo masa da nuna matukar godian ta sharp sharp ta shiga shiryawa haduwar ta da shi a yammacin goben

Washe gari kusan awjen mama asad ya wuni,duk ya matsu yaji ance wani abu game da dawowar su amma sai shiru.

Perfect time mama ta samar makanta so idan taga yana zaune shirun sai ta shiga masa nasihan musamman akan yadda suka dauki rayuwar shida mahaifin sa.

Takance.."shi ya haifeka,yafi kowa jin zafin ka..menene ribarka a duniya in har bazakayi dabiar da zaisanya shi farinciki dakai ba?

Her points are all valids,shiyasa Asad baya mata musun abubuwa dayawa,shide damuwar sa abar sa yay rayuwar sa ba tare da an saka masa takunkumi,he hate to be told what to do,musamman in akan abunda yake da muhimmanci ne arayuwar sa"kamar choices din daya shafi karatu,saka kaya,abokai,inda zai je,me zaiyi?me bazaiyi ba,wa zai gaishar wa ze bari,he hates compulsion,duk wani abun da za'ace sai kayi baya so har cikin ransa.shiyasa har yau yake ganin
Baxai taba shiryawa da kawun ba.

Tun suna yara kawu baya sassautawa,
kusan komi nasu yana sa ido kuma yaga sunyi shi dede.

More reason da Asad yake ganin kamar Rayuwar Azaad da nadra babu yanci sabida basa son tsallake dokokin kawu da mama..

Amma be sani ba,Asali azaad da nadra suma suna rayuwan sun ne a yadda suke so bawai dan zallan biyayyar da suke ma iyaye ba,ya kasa gane cewa,kowannen su da ra'ayin sa amma sukan yi hakuri sosai idan ra'ayin yaci karo da na kawu ko mama,wanda Abu guda kenan da shi bai tabayi ba,Asad kullum akan ra'ayin sa yakanyi tunani."be taba sawa aransa akwai secrifice na Biyayya tsakanin sa da kawu ba bare mama.

So he tot evryone is imprisoned badan komi ba sai sabida rashin sanin ciwon kai irin nasu.

Shi aganin sa yana da yancin kansa kuma baya tsoron yayi irin rayuwar daya zabar makansa koda kuwa zaa cigaba da ware sa ne acikin su

Mama tayi bakin kokarin ta dan taga ta shigar masa nassoshin biyayya amma haka yaki fur karshe ma shiyasa taji wani iri aranta dayake yawan furta cewa"asali kawu be damu da shi bane..be san damuwar sa..yakan bada misalai dayawa in ta duba sai taga gaskyar sa

Jikin ta yy sanyin wajen yarda da laifin kawu akan relship dinsa da asad,duk dama tasan Asad din yafishi rashin gaskiya kuma akwai rashin fahimta tsakanin su sosai

She wished thy can talkd out,amma tasan abune mai wuya,dan haka ta sa aranta tunda kawu bazai nuna kulawar sa akan asad kamar sauran ba daga yau ita xata sa yaji aransa cewa ba a ware sa ba..

Har yamma suna tare,sannan ya fice inda yaci karo da motar carmilan parke har cikin gidan su.

As usual tasha gayu tayi kyau,so Tana ganin sa ta tashi daga xaunen data ke ta tsaya da dan zumudi a guskan ta ayayin ta ta iso gareshi zatayi magana,ya tsare ta yace pls do not come with u car inside my compnd

..bata damu ba tace ok sannan ta juya ta je xata shiga motar ta fitar waje,yana ta kallon ta har ta kunna tayi parking acan waje ta gefe da gate sannan ta dawo ta same shi aciki"..a hankli ya dube ta yace,i mean no harm,female visitors r nt allowd in here..ta gyada kai tace karka damu na fahimta..yace no baki fahimta ba,ur life nd mine r alot more dfernt so u cnt be seen hia alwys,...henceforth".

kamar wata mumu ta sake gyada kai tace ok,can kan wani plastic chair suka zauna,anan ne take sanin cewa dan ma baban sa baya gari ne take samun daman zuwa nan hr ake barin ta,dan hira sukayi kadan tana dada gode masa da amincewar sa akan ta,.

Takan tambaye shi abubuwa dayawa shima yakan mata tambaya jifa jifa,duk iya sauyawar Asad baya damun ta,itade she feel happy in tana kallon sa.

Bayan kwana sati guda Hakan nan ta nace da zuwa shi be taba zuwa ba,sabida cewa datayi iyayen ta basu san komi game da sirrin ta ba.ita de takan nuna masa cewa zata iya komi akansa ne.

Daga haka ta san Asad kwararre ne wajen iya zuwa night party,taji labarin yadda yake rayuwar sa complicated nd hard,duk hirar sun bataji ya kira sunan kowa nashi ba duk dama ita nadra kawai ta sani,tasha mamaki matuka data lura ashe sauke mata kai yayi a school sabida tausayin rayuwar ta"wanda ba lallai kowa ya fahimta ba "sumtimes sai ta tsura masa ido tayi shiru tana maganan zuci kash...,dana sani keya,she just wish da bata hakan ta fito masa tun farko...hala da yanzu sunyi nisa a soyayyar su.

Daga nan Kullum suka hadu tadin damuwar rayuwan su sukeyi,altho natan kawai ake maimaitawa,itama secretly yanzu ta fahimce cewa Asad yana fama da matsala da iyayen sa...sede ba kamar irin nata ba

A Ranar farko da suka fara hada dates" asad yace suje party ita kuma tace sam suje bakin ruwa at sunset suyi picnic'she wants more conversation with him koda ma zasu kai ga maganan soyayya tsakanunsu,tana son tasan ra'ayin sa akan ta har yanzu Aranta tanajin Hankalin asad baya wajen ta kwata kwata.

But where is his mind?Mesa baxai bude ido ya ga son datake masa ba,

Haka de ya amsa suka shirya zasu hadu a bakin ruwa fa ynma ne lis wajen karfe 5. 30 wani sky blue shirt ya saka akan farar skinny jeans da normal beach sleeper shima fari ya sa akafar sa sai yasa hoodie cap agaban an rubuta gifted ya fitoo so simple anma ji tayi kamar ta hadiye shi,ita kam tsinannen short barbie gown tasa wanda adede gwiwa kawai ya dakata ta barbaje gashin attach din ta,kalar rigar ta ja ne dan hakan kafarta dauke yake fa red sneakers mai kyau,ita ta kawo abubuwan sha a car din ta masu kyau masu tsada harda varieties na giya,.

Aganin ta tunda Asad yana shan taba hala ma yana shan giya,amma dataga be kula ba sai tasha mamaki.

Ita kam giyan ta dauko suka same waje bakin ruwa suna hira kadan kadan,
"Sai dura makan ta giyan take slowly tana kallon shi,gaba daya bata jin dede inta fahimci cewa ba ita bace agaban sa ba duk dama su biu ne anan.

Tashanye na farko ta dauke scnd botle stil be ce da ita komai akai ba,kurba daya biu sai ta ce masa "umm..ta mika masa kwalban da smilling face,a nitse ya kalle ta na 2 scnds shima smiles din yayi sannan ya girgiza kai alaman a'a,yakuma ce i dont drink...ta wara ido dan kyabe fuska tayi Tace why?.ya mata shiru..tace but u smoke..yace yeah,kema ai baki shan taba amma kina shan giyako?
Tace eh.juyowa yy shima yace why...?
tace i hate it..i cant smoke..bad for ma health nd ma personality,..karamar daria yayi yace ther u go..ashe abun ra'ayi ne..i smoke..amma bana shan giya bcos i hate it...againts ma stand againts ma religion...and all that u mentioned...
hmm kawai tace ta dada kurban giyan aranta she is wishing that yana sha shima tasan daya na sha hala zataji sirrin zuciar sa akan ta

Amma tun agida yau tasha alwashin se ta masa tambayr akan haka dan haka
Dan haka ta nitsu ta kira suna sa tace" asad"..sai ya juyo ya dube ta?

Tace menene yafi dauke maka hankali?..like what do u wanna talk about

Sautin Hmmm ya sake tare da ajiyan zuciya..yadann karkata kai kamar me tunani cahn yace yes.." Well,I hate small talks,i wanna talk abt atom,magic,the meaning of life, death,aliens،far away galaxies,
music dat makes u feel difernt,memories, the lies uve told  anan sai ya dan dakata ya kalle ta sannan ya cigaba"..ur flaws,ur insecurities ur childhood,ur fear,what keeps u awake all night?..i want ppl with depth those who speak with emotions from a twisted mind..anan sai yay shiru be sake ko kallon ta ba

Ita kuwa A daskare take kallon sa,she can feel the breeze so hard on her lips Tsaban burgewan da kalaman nasa yazo mata da shi duk dama bata sammace su ba.

Hot guy huhn...with twisted mind nd words.A duniya in aka ce akwai wanda  zata so kamar shi baxata iya yarda ba

Kamar ba itace a buge ba hakan tayi composing kanta  ta kyabe baki a nitse,tace "wow intersting...ok..zan gaya maka duka wayyannan wani lokaci..sai tay ajiyan numfashi.cike da gwarin giwa tace welll enough abt me,saura tanbaya daya zan maka ka shirya?sai ya dage mata gira,"tace mmmmm..shin wacece macen da kake matukar kauna arayuwan ka.

Babu tantama yace my mother..

Sai tyi murmushi tace and..sai yy shiru yana shan drink dinsa kamar be ji ta ba...."da fargaba aranta ta maimaita tambayar murmushi kawai yayi...sanda ya lura da cewa ta gama bada attention din ta sai ya juyo da murmushi mai sanyi ya kalle tsakar idanun ta a hankali ya furta NADRA.
🚶🏾‍♀️🚶🏾‍♀️In babu coments babu post akai akai,in akwai coments u wll see it everyday. .share  post to ur grps as well..😅😎

IG: SURAYYAHMS
WATPAD:SURAYYAHMS.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top