16:i love the hurt,i hurt the love
Toast:being happy and thinking the same for others is exceptional,being depressed nd thinking the same for others is a cursed,this is life.. what goes arnd must comeback arnd..ASTAGHFIRULLAH.
16...i love the hurt,i hurt the love.
wannan shafi na masoya na ne a duk inda kuke masu turo sakon kauna da masu kwana su tashi ana kan muhwara i can see ur love soooooo undiluted nd i feel the same❤👍🏻.
Da shike ma in har satan fitan zaiyi ba hali ya dau mota a gida machine ya hau ya sauke sa akan titi sai wajen karfe goma da rabi ya isa
Wajen da nisa ga wani uban shiru daya ke ratsa ko ina cikin duhun daren dan kuwa gidajen dake anguwan na Sabuwar estate ne project din gwamnatin tarayya hasalima yanzu ne ake neman haya anan so babu wani alaman wulgawar mutane.
Tafiya yake shikadai akan titi iskan rairayin dare na busawa sanda ya kusa cin rabin titin angwan sannan ya shako bugun sautin loud rap music na tashi to sautin yy ta bi har ya kaisa wata kafurar Luxurious Flat666,daga gate ya nuna invitation dinsa bouncers dake kofa suka bashi hanya ya shiga ciki
Katon flat ne mai dauke da 4 bedroom da fankacecen palour mai dauke da kala kalan yan mata da yan maza kowa da nauin abun da yake yi duka duka basu fi su arbain ba ,browsing wajen yyi da idanun sa baiga fuskkan sani ko daya ba,but da shike ya saba zwa nite parties sai hakan bai dame sa
Straight up yace wuce counter wajen da ake serving chilled drinks,dama shi in yazo party ya riga ya saba bawai rawa yake yi ko taba mata ba,chan dungu yakan nema waje yayi zaman sa yyi ta bushe bushe yana korawa da soft drinks yana jin loud music na cika masa kunne...dai daikun ranaku ne zaka ga ya bada idanun sa abinci wajen kallon yan mata masu rawa duk dam tunda yake bai taba takawa ba..
Bar attendant ya katse masa tunani da mai za'a bashi?,da har zaiyi magana sai charaf ya hango noah na tun karaso sa sai ya juya kansa kamar be gansa Yace ma attendant ya sa masa normal drink,he is ok with that. Ba bata lokaci aka shiga hada mashi parry special,noah ya ji matukar dadi daya gan sa,sun gaisa ba yabo ba fallasa,gayu suna ta kallon sa cos duk basu yi tsammanin sugan sa so free and confident a night parties ba gashi dan musulmi.
Sunyi Sunyi ya shiga cikin su,yace ah'a,..har ya musu karyan kanshi ne ke bugawa shiyasa ma baxai sha komai ba.
Ba laifi suka bashi waje ya zauna shi daya a hankli yake shan drink dinsa inda babu abunda yake fado masa aransa sai ni kadai!
Wani fargaba yakeji wanda besan da ita ba,ya fi minti 20 a haka daga bisani yaji abun kamar naso ya dame sa,yau ko tabar ma baiyi tunanin sha ba sai ya fita waje ta gefe yayi dialling number ta,"bacci nake kan kwasa,wayar tay ringing sau biu tex ya tura da kalman
"Baby,Im missing you"..tun kan ya yanke hukuncin zai jiran reply sai ga su molly da carmila da rico nasty,tare da sauren wasu yan mata da yan maxa a schl din mu
Da wani irin kallo ta bishi,duk yadda ta so ta boye sirrin zuciyarta akan sa bai boyu ba,"Asad is more than handsome he is a beautiful guy da komin jiji da kan mace zata so ace shi nata ne,sun gaisa da kowa amma su carmila ko kallansa basuyi ba suka shiga ciki. Shima daga nan ya biyo bayan su..
Drink ya sake karba mai sanyi ya xauna waje guda yana bin duk wani motsin ta da ido ya lura yarinyar kamar bata san kanta ba in tagan shi,yau wata sexy short gown tasa farare kal cinyoyin ta duk awaje suna kuma dauke idanu,ga rigar ya manne da jikin ta ya bi shape dinta ba wani kwalliya ta tula ba amma sosai tayi kyau,".. Partyn yayi dadi dan bakaramin rawa su molly da rico suke kwasa a dance floor suna tsalle kamar ba 5inches higheels ane akafar su,carmila ta kame agefe kusa da inda suke sunayi tana cherring dinsu amma ita bata motsa ba,ya dade yana satan kallon su duka har time ya tafi sosai baisani ba,anan kowa ya nemi waje yana hutawa ana playin cool background music a lokacin ne noah da yan kungiyar buccaners suka yi nasu show din, lips sinkers, comedians, akayi rawa,miming,ganstars clash..kamar wajen zai dage tsaban ihun dadi da dariya,da hakan ya faru sai noah ya fara bayanai akan abunda ya tara su cike da nuna farin cikin sa da schl ta bashi cikakken dama,toh tunda ya gama fadan hakan sai ya soma neman carmilla da magana cikin salo amma su biun sun san dawa sukeyi,da sunayi ana basarwa ana dariya ansan sun sha giya sosai ne,amma da abun yy tsamari sai carmila ta fara nuna bacin ranta,noah shima ya dau abun da zafi yace dama ba masoyan ka zalla zasu xo murnan cigaban ka ba,har da makiyan ka masu so suga abun da zai kashe su,ya nuna ta da yatsa yace basu gani ba?ai tsaban bakinciki da shi yasa carmilla ko rawa bata iyayi sai dai tasha drink dan kar ta shake ta mutu,carmila ta nuna taji haushi sosai,cikin bacin rai ta fara tuna masa rokon ta da yayi akan tazo partyn,noah ya cigaba da misbehaving yace ai shi ba dan Allah ya ce tazo ba,dama babu yadda xaici gaba bai kira makiyan sa sunyi witnessing ba,dama revenge is best served when chilled
a baxata ta watsa masa sauran drink din dake hannun ta a fuskan sa,tun kan ya dago wasu kattan gayu suka hyayako kanta kace wani abu waje ya rude da surutu,noah ya sa aka rufe door cike da barazana yana gwada musu asalin shi waye ne fiye da kowa awajen carmilla sai ta nuna ta tsorata sosai
"The buccaners confreternity dama kungiya ne na yan cult ko ince secret society da aka samo shi daga jikin national association of sea dogs wanda aka fi sani da suna the pyrates confranternity,in har kai dan kasar nigeria somhow one day dole zakaji ana cewa sune kungiyar secret cult na farko da aka kafa a nigeria tun 60s
2 crossed bones da anchor sune symbol din kungiyar,pyrates confratenity tana yaki ne akan nuna bambacin yare a tsakanin student (tribalism),sai bada karfi akan hadin kai ta hanyar patnership,Humanistic ideas,expiring convention da knigthood,Duk de da niyya mai kyau aka kafa secret societyn dan sosai suke taimaka ma dalibai
musamman a harkan karatun su,dan doka ne in kana cultism dn toh da grade mai kyau zaka na fitowa...
Daga nan Bayan wasu lokuta masu tsawo ne aka samu sirrai daga cikin kungiyar wanda suka baude suka ce grade din su baiyi musu yadda suke so ba,shine aka fara samun sabani inda masu kofarin suka rarrabu wasu suka bar pyrate sai suka kafa nasu Kungiyar mai suna the buccaners confreternity a shekaran 1972,wanda aynzu haka su aka fi sani da sunan national asociation of the sea lords,awasu wajejen kungiyar yawanci maza ne masu jini a jika suke tada shi..
Duk dama kusan abubuwa iri daya suke yi symbol ne kawai ya banbanta Buccaners dake sune kanana sai suka dauki skull da cutlass guda biyu da bones,dukan su biu suna amfani da kalar yellow,ja da baki,aynzu haka buccaners su suka dawo kishiya mafi girma ma uwar kijiyar su pyrates confraternity wani mutum mai suna babban bolaji carew shiya jagoran ce su a wancan lokacin.
Da noah ya gama fade faden sa by now yasan Abun fargaba ne wajen kowa ya san sh dan cult ne,duk dama is allowed to use the name in schl tunda ansan ba a akan zalunci da shan jini aka kafa ba sai akan karatu but hmmm na ciki na ciki.
Sai yau zaka gane cewa ba ilimmi ko baiwa ne yake sa wasu su ci exams ba,wani bin dalilin kenan daya sa noah yake fitowa da grade mai kyau a duk dama yakan shafi wata biu baizo aji ba.
On the other way round,acewar sa yau yaci nasara an basa daman kafa kungiyar a makarntn su wato exclusive law schl na marigold and azure"..yace burin shi ya gurfanan da duk wata wani mai ji dakan sa a makarntar har sai buccaners yayi karfi ya mamaye ko ina
a ynzun Wani kungiya ce tafi karfi in ba brain box club na carmilla ba?yace shiyasa dole yau zai fara da ita..kuma acikin daren nan zai nuna mata iyawar sa.
Nan da nan Kowa ya tsorota fiye da tunanin mai tunani dan ko members ne na kungiyar sanye da bakaken kaya a zagaye da noah jikin su a murde sai wani bari suke
To add to thy misery sai aka kashe wuta," tuni ihu da panicks ya cika wajen dai daikun maxan da aka gayyato suna ta kokari wajen ceton ran yan mata ta hanyar fitar da su waje
Sosai hanklin asad ya tashi,kirjin sa na bugawa yasan dole carmilla ta shiga hannun su nd only god knws me xaayi mata anan,aikuwa ya kwala mata kira cikin ribibi ya yunkura zaije nemo ta,wani ne wanda bai sani ba ya finciko sa y ce dashi a'a kar yaje ya gudu kawai ya tafi gida abunsa...
Asad yaji tsoro sai kawai ya hakran ya fito yana isa waje sai ga rico da molly sun nufosa suna kuka sai ya tambaye su ina carmilla?"..arikice rico tace dashi basu ganta ba kuma tana ciki Dan Allah ya taimaka musu .. tun kan ya sake magana ya ga sunbarshi sun bar wajen.,baiyi tunanin komi ba sai ya koma ciki,wajen yyi fayau kamar ba anan ake holewa ba,yyi tsam kirjin sa na bugu,kamar an tsakure sa yajiyo sautin ihun ta cikin raxana tana cewa some one help,..daga nan bai sake ji ba sai kakarin kuka alaman an toshe ma mutum baki,sautin yabi a slow daf wani corridor yaga wani na jan ta akasa tana fincikewa kamar yar tsana tana kukan fitan rai,tausayi sosai ya kama shi a take yaji wani azama ta zo mai..labewa yy dan yaga ina sauran suka shiga,har ya gane cewa shiri fa suke awani dakin alaman ko su kashe ta ko su tsafe ta..
Ko tunanin kansa baiyi ba ya soma sakawa da warwarewan yadda xai ja hankalin wanda aka bashi gadin ta ya ceto ta,aikuwa da sauri ya hada idea inda ya shiga zirya dan ya ja hanklin sa,..
Dayayi hakan kuwa a saukake ya samu ya barta anan ya shiga farautar sa.
Wasan boya suka shiga yi da shi,gashi wasu mayukan adduna ne a hannun sa sai huci yake,da kyr ya masa wayo ya zaga ya taho inda take "carmilla ta zube a dukunne tana ta kuka har ya iso wajen ta bata dago ba".. Daya taba kafadun ta a firgice ta tashi,ganin Asad ne yasa ta kara fashewa da kuka cikin yanayin kaduwa da raxana ta fado jikin sa ta wani kankame sa.
Hannun sa Bai iya taba ta ba"..Sorrry..kawai yace shima duk tsoro ya cika masa zuciya...zatayi magana yace mata shuhhhshh,hannun ta ya riko acikin sanda suna tafiya amma da kyar suka fice a gidan a guje ana binsu
Gudu sosai sukayi tana ta kuka basu tsaya ba amma tsaban dan ta nuna ta razana takanyi amai jifa jifa
Sun dau lokaci a haka inda Sukan su basu san ina suke shiga ba,jin kadan wani bakar honda ce kawarbbiya ta shiga gaban su a mugun firgice carmilla ta bankade shi ta shiga gaban car din tana roko agigice akan ya taimaker su,dattijo ne ya sha giyar sa sosai har kaman bai gane me suke cewa sai ya dauke sun dai suka bar wajen,duk yadda suka roke sa ya kaisu gida haka yaki fir ya kuma bisu da maganan banza..da kyar carmilla ta roke sa akan yakai su makaranta..bata dena hawaye ba duk jikin ta sai rawa yake,shikm yana shiru
Chan Asad ya dubi agogon sa its 2.45am na dare runtse ido kawai yay a nitse kamar bashi yaci gudu yanxun ba,fuskn su ta nuna ma watch men tare da masa karyan libry xasu je,wacht man bai wani bada ciwon kai ba dan yasan gobe da safe ranar exams ne maimuhmacci nan aka bude musu gate din libryn suka nifa ciki su biyun su..
Batare da sun ce ma juna komai ba suka samu waje suka zauna kowa na sauke ajiyan numfashi,"...minti talatin suka dauka ahaka,kafin ya dago ya kare mata kallo har yanxu hawaye ne ke bin kuncin ta,scnd biyu ya dauka yana karantar yanayin ta,kafin ya taro karfin hali ya dora hannun sa akan nata gently yace soryy..cikin wani yanayin weakness mai sa aji tausayi ta bude idon ta kalle shi sai ya dada cewa are u ok?..ta kau da kai ta gyada mishi kan a hankli,wani kukan ne ya kufce mata wanda ya bashi damar dawo wa kusa da ita cikin yanayin rarrshi
Yace,"its ok,..pls stop cryng..lumui tayi a hankli har ta fada jikin sa batace komi ba sai kukan takeyi tana sauke ajiya zucya
'Pls calm down pls sai ya dago fuskan ta,bata iya hade ido da shi ba,ran shi ya kai makura wajen tausayin halin data ke ciki ayanzu
"Shi Tunani ma yake aganin sa inda ba dan iyaye sun tursasa tayi karatun dole ba da baxata shiga wannan halin ba..aynzu bai ganin laifin kowa sai na iyayen carmilla.
Yana kuwa sake ta ta sulale kasa zata fado so helpless yace carmilla its ok,cikin sauri ta girgiza mai kai cikin kuka tace is not ok,im scared,ni ba haka nake so nayi rayuwata ba,this isnt my life .
Ya taho xai dago ta ta mike zaune ta kife kanta akan gwiwon ta slowly tafara blaming mahaifin ta,tana cewa ta shiga uku ya zatayi ta iya shan gaban yan cult?...shidai asad shiru yyi yana jin ta tana ta maganganu anan har yakejin ashe asali carmilla medicine take so ta karanta ba law ba. .baice komi ba kuma bai taba ta ba dakan ta tayi shiru ta nitsu sosai,sai sannan ya xare Handwipe ya mika mata dan ta goge fuskan ta,tana karban kuwa ta goge tasss har da ce masa ta gode,ya sake tambayarta if she is ok,ta gyada kai,bata barshi ya bude baki ba ta riko hannun sa tana kallon cikin idanun sa,"tace thank u Asad,..ya dan gyada kai,first time dayaji ta kira sunan sa in a normal way cike da saukar da kai,"..tace ure a nice guy,thanks for helping me nd hearing me out,kasa aranka na yarda da kai kuma nasan baxaka fada ma kowa sirri na ba...sai ta dan yi shiru,chan ta dago ta kalle sa..."tace in fada maka wani abu?Asad yace hmm sai gyada kai..tana so tace i knw u love me to amma bataga alaman hakan a idanun sa ba sai ta saje tace i know u care about me,..kuma nima i feel the same..shi kam bai wani ji mamaki sosai ba da ta furta hakan,ganin yy still baice uffan ba sai ta matsa daga kusa da shi tace,na fahimce ka in baka yarda da hakan ba but i really do care, infact i like u ...sai ta juyo ba kunya kadan ta shafo kirjin sa, erotically,,wani kallon daya watsa ma hannun nata yasa ta dauke da sauri sai ta fuske..."tace nasan kasan dalilin daya sa nake maka haka ko?yace ehm...tace ok im sorry again pls forgive me,kasan ba haka nake ba. .i admit ure doing so much for me,nasan badan ka damu dani ba yanzu hala da kana gida preparing for ur exams ko?....but i have to do what i have to do.. bansan cewa abun zai dawo hakan ba da banzo ba pls am sorry asad
"..Yace its ok ..kar ki damu..im here..ya dan dafa hannun ta cikin yanayin kallon juna she xpect long essay sai taji yace,".. Im glad u care too,.bai sake cewa uffan ba Tayi murmushi mai ciwo mai kuma sace zuciya,a sace ya maido mata irin sa..
"Yace kisa aranki babu wani abun da zai same ki..naji wai ba akai karan su noah ko?but with me i assure u ure safe...hannun shi ta dada rikowa cikin shauki tana ta kallon yadda yake maganan a nitse,a slow ya fincike hannun sa yace,...so lets forget abt it and think abt tomorw..tace ok,'..gyara zama tayi kamar bata damu ba,can kuma kamar wanda ta saba da shi ta shiga gaya masa abubuwan data keyi arayuwan ta, tace ita baxata kwanta ba cos karfe hudu ne dai dai lokacin karatun ta
Asad yace shi baxai iya ba bacci yakeji,aikuwa kamar wacce take karantar zuciyar sa tace hanklin ka ya koma gida ko?yay shiru silenlty thinking of that
...murmushi tayi ta dafa kafadun sa tace sorry gashi zamu kwana anan,sai dai gobe after exams sai kaje gidan,u know u cant miss tmrw papers suna da muhimmanci sosai duk wanda bai rubuta ba zai iya samun prblem...eh kawai yace mata yayi shiru..yau sai gashi ita ta sake sosai tana masa hirraki most times yayi ta kallon ta yana tausaya mata aranshi,wani bangaren kuma mind dinsa yana gida,can dataga ba damuwar sa ita ba sai ta barshi anan taje ta hado coffe awani wajen cahn inda securityn su suke zama...
Daga wajen ta murza wani kwaya ahannun ta ta jefa aciki ta shigo tana murmushi babu bata lokaci ta mika masa,shima babu musun ya karba yace thanks a tare suka zauna suna sha har suka kammala sai ta shiga dube duben littafan da zata duba ta barsa a xaune,anan yana zaune bai sani ba jim kadan bacci yayi awon gaba da shi,koda ya so ya tashi sai yaji wani kasala ta mamaye shi chan a cikin magagin bacci yaji kanshi shi kamar akan cinyarta tana shafa mai kai ahnkli cikin dada zulma sa cikin bacci mai dadi mai nauyi..
Bangare na kuwa ban tashi farkawa ba sai 4am na duba waya ta naga miscall dinsa harda tex,sosai najidadi araina duk na dauka ko baima kai 45min din ma ne ya dawo ya samu ina ta bacci ba,i mentally scold myself akan haka,a duk tunani na asad yana dakin sa yana bacci.
Bayi na shiga na wanke fuska na fito littafai na na baxa na fara Karatun gobe da safe
Har nayi sallar asuba na kimtsa kaina tunda nasan ba zuwa dakin sa zanyi ba so arnd 5.50am na shiga kirar layin sa sai dai shiru ban ji an daga ba Nikadai ina ta masifan laziness dinsa,hankalina bai tashi tashi ba sanda naga karfe 6:47 yayi amma babu asad babu alaman sa a gidan
Hakali na a mugun tashe na fito inata tambayar zulai,wani bin gani nake kamar ba gaskiya take fada ba kawai bataje ta duba san bane
Gaba saya sai naji kaina na sarawa kirji na na bugu,a duk yadda ban son na karya alkwarin mama haka na daure na kama hanyar dakin sa..
Allah ya so ni na kiraa zulai tamin rakiya aikuwa muna karyo kwana naga kawu tsaye da mama duk sunyi cirko cirko a tsakar dakin sacWanda yake a gyare alaman ya nuna asad din bai nan
Tsoro ya kama ni sosai nace kar dai asad kwana yayi acan?hawayen bakin ciki da damuwa suka taso min amma haka na daure na sa fuska cike da ladabi na tsuguna na sake gaishe su,na lura ran kawu a matukar bace yake..'dan a masife ya ce min wai ina Asad yake?
A ina ya kwana,nazo nan neman sa
meyasa bai bude min kofar sa ba kuma meyasa bai sauko ya gaishe ni ba?
Cike da fargaba na fara i,i na murya na rawa kamar wanda zai tona min asirin tsananin tsoron dake tattare dani,na shiga magana kaina akasa,jiki na sai rawa yake slowly nace ma kawu,nima bansani ba amma inaga Hala Asad yayi fitar sauri ne,dan jarabwar mu karfe 7 ne.
Kawu yace in masa shiru,yasan karya nakeyi..ya juya kan mama yace ai dama ya fada asad yana fita agidan nan ta yadda yaso batare da izin kowa ba
Da alaman Mama ma ta rasa abun cewa ne, sai na daure na ce ma kawu lallai Asad yana schl na kakkaro karya masu kama hankli na masa
Kawu yana ta kallo na amma ko alaman yarda dani yau bai nuna a fuskan sa ba
Sai ma Ya rinka masifa kamar xai bugemu duka har da cewa in har shi ya haife asad to yau gaskiyar sa zai fito kuma sai ya gane kudan sa,yace min maza ki tashi akaiki makarnta shi asad kam ai da kafa ya yaje ko?jiki na a matukar muce na rusuna kai bance komai
Kawu ya barmu awajen ya fice a fusace,mama tana biye da shi a baya..a sanyaye nake saukowa step daga nan inaji kawu yana masifan cewa
"Har yar ni din nan zan kalle idanun sa ina masa karya?jikin shi ya bashi cewa Asad be kwana gida ba..he is pained really da ban fadi gaskiyar ba..masifa kawu yyi sosai dan ko mama bata samu damar cewa wani abu ba har ya fice..
Haka Naje schll inata dube dube kozan ganshi amma shiru,har na cire kunya na shiga tanbaye tambaye irin wasu masu yawan masa magana amma kowa sai yace bai gansa ba
Can Akayi anoucing exams starting Time kowa yazo ya xauna computer kowa na gaban sa,na juya yafi sau 110 ina kallon one empty seat na asad gashi babu mahalukin da baiya hall din..
Har lokaci yayi akace start kowa ya log in pasword aka dukufa
Amma Ni A adaddafe nake yin exams din sam bana cikin hayyaci na,ganin munci
Awa biu asad bai shigo ba ban iya daurewa ba na fara sauke hawaye a boye inayi ina gogewa dan kar na ja attention din kowa.
Su carmilla da kawayen ta ne a seat din gaba,ga fatima acan nesa kowa na abunda ya ke gaban nikuma ji nayi na kamar mutuwa zanyi yau inbanga asad ba..
..acan kuma Asad bai tashi farkawa ba
Sai washe gari karfe 9.57am,..tsintar kansa yyi awani dirty store room shikadai a kasan floor, dan karamin daki ne na tara tsofifin littafai duk rigar sa ya baci yayi dukun dukun da dattin korar dake wajen,a gigice ya duba agogon sa yaga time sai ya runtse ido"salati ya farayi tunowa da ko sallahn safiya baiyi ba,wani shegen nauyi da kansa yake masa yasa shi mikewa a daddafe,"..bude window yyi yagan sa schl atake sai ya tuno da exams"..ya sake kallon agogo 9.58am,cike da mamakiin abunda yake gani ayanzu ya dada runtse idanun sa
Tambayar kansa yake,ina ne nan? Shine yyi bacci haka Baiyi sallah ba,his examz 9.58 kenan saura minti 2 a fito? Har ya juyo zai bar wajen cikin sauri,sai kansa yayi hitting ya waigo a tsorace yace where is carmilla?....cud it yan cult din nan sun biyo su libryn jiya,shin ko sune suka aje shi anan?sai yace noo,ai doka bata basu da daman yin wani abu a schll ba,but wher is she?da kyr ya samo ma kansa nitsuwa ya warware kamar hanklin sa ba a tashe ba ya wuce massalaci ya wanke jikin sa yay sallah...
Banyi editing ba fatan kunyi hakri da errors
#it doesnt matter how deeply or truely u love someone,betrayal remain an inherant part of love.
#Arayuwa ga guji munafukin ka koda ciki daya kuka fito.
#hakama duk imanin ka da jin tausayin ka kaji tsoron me fuska biu
#tausayi imani ne amma at same time tausayi babban rauni ne da xai iya jefa ka yanayin dana sani a rayuwa..
#wani bin ba taurin zuciya ke sa mutum ya ke taurin kai ba,ah'a se dan mutum mugune,kuma sanin gaskiyar mutum sai Allahn daya halicce sa.
I urge my fans to be careful with life be selfish with urself abit,kar ki cika damuwa da damuwar wani,..we dont actually knw many things tat we seem to know.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top