15:accidentally on purpose

15...Accidently on purpose!

VOTES..

Asad tun yana yi yana kaucarwa wani bin aran shi sai ya fara jin kamar Hes becaming obsessive abt her condition secretly sai ya shiga bibiyan duk wani halin datake ciki da noah...

A Dayan bangaren kuwa shi baima sani ba amma dama burin su kenan,duk dama da kyar harsashen su ya bayyana musu cewa lallai asad zai ji tausayi ya kula,dan Fita daga shirgin su da Asad din yayi kwana biu carmila bata taba tsammani ba kuma hakan bakaramin taba zuciyar ta yayi ba'..tambayar kanta take meyasa take jin tsananin kaunar sa amma sai batagane komi a idanun shi face zallan tausayawa halin data ke ciki?,a makrta zaka ganta normal karyan ka ma kace Asad ya sha mata gaba,sau dayawa zata wuce ya wuce ko kallon inda yabi bata iyayi bare ta nuna ta ma san da shi,amma babu wanda ya sani sai inta koma gida ta kulle kanta a daki takan shiga wani hali,gaba daya ta rasa nitsuwa bare ta kula da kanta haka ma da dare bata iya runtsawa bata ji kewar sa na yawo a jinin ta ba..sosai take son shi sai dai bata san ko hakan aikin banza bane ko zai iya amfanar da su nan gaba ba..

Shikuwa asad ya dauka duk akan burin ta take haka,kwana biu dayake observing he has neva seen her so focused nd dertemined shiyasa ya dada kama kansa ya ki yace mata ko da sannu

While ita da kawayen babu wani motsawar sa da idon su bai kai his slightest smile or gesture in yayi sai sun dau lokaci suna fassarawa,actualy ita carmilla bata jin ta tsane kowa a aranta kamar ni,she feels natural hatred dan ji take ko shedan zata iya yafe masa laifukan sa amma banda ni..but over what?Akan Asad..?cike da taurin kai sai taja tsaki cikin rashin son ta yarda da cewa kishin yadda Asad yake mun biyayya a fili kawai take ji aranta

"...Haka rayuwar mu ta cigaba har muka kusa kaiwa lokacin rubuta jarawabawa na shiga shekaran mu na na karshe a schl of law, by now na gama fahimtar wani abu gameda carmilla,sai inga duk randa Asad yayi wani abu mai kyau na musamman sabida ni to sai wani abu marar dadi ya kaure a competition din carmilla da noah.

Asad kuwa yanajin labarin zai daga hankalin sa,tun yana boye min dan baisan bacin raina har ya gaji ya fara bayyanawa

"Nace da shi babu ruwan sa ya kyale su,sai yacemin tausayi carmillar nan take bashi ba

Nace asad tausayin yarinyar da ko kallon arziki bata yi maka?sai yace min karya ne wallhy ta damu da shi dan  yana lura da ita sosai akan haka

Har nagaji na kyale sa,in wani abu mai muni ya same ta a ranar zai yi ta mita wani bin in kula shi,wani bin shiru nake masa shida kansa zai saduda yyi shiru.

Yau Ana saura kwana sha hudu ayi exams,waje ya kacamme da surutayya dan yau aka manna mana wata shiryayyen time table me abun ban mamaki wanda ya nuna cewa rana na farko zamuyi muhimman courses uku a paper guda each section carries 45 minutes kuma da safe ne karfe 7.30am..Ko ina maganan exams din akeyi amma sai asad bai damu ba

To aranar Bayan mun raka fatima ta tafi gida Asad ya riko ni da hannun sa daya jakata na dayan hannun sa a nitse muke takawa za muje inda yayi parking motar sa mu tafi gida..

A Daidai zamu sha kwana daf da student exit hall sai mukayi gaba da gaba da su camilla da molly da rico nasty,dukan su wando suka sa ita kadaice ta saka dan guntun skirt abin cinyar ta tana faman taku cikin yanayin nuna haduwar fatar jikin ta..take ta kankance ido tayi tsinin baki da wutsiyar gefen idanun nata ta jefo kallo daya me zafi wa hannun sa dake rike dani,nikuwa naji wani iri araina da Asad ya kalle surar jikin su,duk dama basu ko kula mu amma sai da naji kishi sosai harda satan kallon kaina...mama ce ta hana ni saka kaya kamar yadda da nake sawa farkon zuwa na,most time yanzu da atamfa nake zuwa da hijabi ko abaya,da kyar ma ta ban dama na ke iya sa kimono sai na tuna da chan har wandon jeans da falazo nakan sa muddin jiki na dai baxai nuna ba.

Har muka isa Dai dai zai bude min mota idon sa ya sauka akan wani abun wuya akasa,yyi sauri ya daga yana kallo"nima na kalla sai..nace abun waye?ya dada kalla da kyau can ya tuno ashe akan abun carmilla ta fara sauke masa mari...bai amsa ni yyi maza ya juya yabi bayansu ya barni na tsaya kallon sa chan dai danaga wajen sun ya nufa dagske sai na shiga biyo bayan sa a nitse.

Sanda ya kawo daf da su ya dafa kafadun ta kadan
Yace"Excuse me...a nitse kuma cikin aji ya fada bai sake fuskn sa ba.

Sosai carmilla taji dadi daya biyo din Wani kyabe fuska tayi,Dukan su uku
Suka juyo cikin wata kaskataciyar yanayi suka tsura masa ido,"he has the habit of hiding it in his palms duk dama dagangan suka shirya hakan,da bata gani a hannun sa ba sai ta shagala da kallon dayake mata mai narka mata zuciya..,chan cikin rigima ta gwalo ido ta hade rai tace what?..sai ya dan kau da kansa..rico nasty tace ure wasting our time mister...tsaban ta cika dede face dinshi tayi twirling yatsun ta...,"hello...nace babu kyaywan mata masu diri agarin ku ne?Molly ta bishi da dan karamar dariyar rainin wayo tace,"i gues so.. cikin wuya ta karashe wanda yyi dede da isowa ta.

Na kalle su sama da kasa,aran carmilla ji take kamar ta waye gari ace mata na mutu bana nan a duniya.. .bance uffan ba na ware hannun shi nace Asad bata abun ta mu tafi...nan ne taga yadda ya dunkula abun,cike da borin kishi ta wani kawo hannu zata fauce daga hannun san sai nayi saurin bankade hannun ta na kwace abun amya dawo hannu na...A hatsale tayi rolling idanun ta irin ita tafi tama karfin ta bude baki tayi magana da ni bare ta karbi abu a hannu na,nikuwa na dada gyara tsayuwata gaban sa,na musu kallon raini isar raina,kamar karnuka haka nake kallon su..nayi tsaki boldy and confidently na shiga mita ina cewa wato idan mace bata da aji ta shiga uku,comon sense of courtesy ace mutum bai da shi?nace wai meyasa baxa ku nitsu ku daraja mutum ba?..to in ma kina tunanin kina da wani abun da maxa zasu gani su biki ne this time arnd kin danna wrong button,nace taje dai ta sake lalumawa
..nayi ta mita ina surutu cikin manyance kamar ni na haife su abun kuwa na cin musu rai amma ban fasa ba sanda nayi facali da tattalin feeling din jin kansu da sukeyi anan

Dake basu da gaskiya Tsit sukayi basu ce dani komai ba sai harara sai uban gyara tsayuwa

A idanuna Babu alaman da ya nuna ina shakkar su ko ina jin tsoron su bare aje ga zan ragar musu dan suna da all that.
Dan haka na fito fili na nuna mata nagane nufin ta akan duk abunda take yi dan ta jawo attention din asad zuwa kanta

A lokacin Ninkin baninki carmilla ta dada jin ta tsane ni aduniyar ta

Nikuwa A bazata Na jawo hannun ta da karfi ta shiga fixgewa tana jan tsaki tana faucewa tana komi amma haka na damke ta  ban kuma sake ta ba sanda na dangwala mata abun wuyan ta a hannun ta a walakance...ranta ya mugun baci har bata iya dena bin hannun nata da kallo ba

"Nace u drop it on our way...nasan bakida manners din yin godiya..Anyways ure welcome..

Tana dagowa Naja shi nace mutafi.
...carmilla taji kishi matuka tuni idanun ta suka tattaro hawaye sukayi jazir kawayen ta kuwa haushi na sukaji har wani huci suke kamar zasu kashe ni

Asad ya lura da hakan sosai sai ta bashi tausayi aransa he tot duk rashin samun yancin kan kenan,gashi tana so ta masa magana suyi mua'mala normally amma shi kadai yasan tanabin ta wani hanyar ne da tana basarwa gashi tana yarfa kanta duk dan kar ta shagala da karatu.

Aikuwa kamar ta karance shi sai taki motsawa anan ta tsaya lumui abar tausayi uwa an hana marainiya abinci

tsaki nayi mai sauti na ja hannun shi cikin harara naga shima yanayin ta yake kallo"it feels like she is emotionally blackmailing him..a mugun hatsale na juyo kansu duka nace can you guys pls move on? Sai na kalli camilar na daka mata tsawan da sanda ta dago ta dube ni a firgit..what r u looking at?Nace miki Asad babu ruwan sa da kungiyar ki wai ana dole ne?he is not intrested in anything with u..pls face ur front mayya kawai.

A razane Camilla ta dauke idanun ta anawa batace uffan ba dan Sosai taji haushi wannan tsawar da na mata...gashi ji take kamar zuciyar ta zaiyi amon wuta ya fashe da nace Asad is no more intrested in her.

Bayan ganin yadda tayi reacting Asad sai ya jawo ni dadan karfi,yace nady ya isa haka,naki in kulashi, ranshi adan bace yace pls stop it...lets go sai ya jawo hannu na..

dai daikun student da suka fito wanda dama sun dade suna wandering meya ke hana asad sake dawowa brain box,toh Ganin mu tare mu uku anan sai yaja hankalin student magulmata dayawa suna so suji kanun labarai,altho bawai an taru ana kallon mu directly bane,amma 40% anan sun kasa kunne ne kuma babu abunda basu ji ba

A mugun hatsale carmilla ta fisge jiki ta shiga gaba tana tafiya kawayen ta nabin ta a baya.

Shi hawayen da tataro lokacin danake magana ne ya dame shi,baisan meyasa ba amma harr yau Allah be nufesa ya fahinci cewa son shi ne a idanun camilla ba...a tunanin sa daban nata ma daban, har muka shiga mota zamu bar schl baice dani uffan ba.

Nikuwa na bata raina,wayar sa daya jefa a back sit ya hau ringing,dana yunkura zan miko wayar sai ya ture min hannu na a fusace

Nace asad meye haka?...yace baby i hate wht u doing...raina abace nace menayi?yamin shiru...nace dan na ce mata ta rabu dakai?abun tane fa ya fadi kasa ka dauka shine taje zata walakanta ka,that girl is insane bukatar ta baifi ta walakan ta abainar jama'a dan suyi dariya da kawayen ta,wato kafi son haka ko?..why r u angry at me now,da ihu na mayar masa Tsaban bacin da raina yayi muryan na har rawa yake.

Tsimewa yyi dan ya danne masifar sa shima..Controling himself sai Yaki ya amsa ni,dauke kai nayi sai nayi shiru na maida kallo na window har muka isa gida tun kan ya gama parking nasa hannu zan bude car da sauri ya jawo ni ya maido ni kan seat

"Fuskan sa adaure yace nadra Bana so..Bana son kina nuna kin tsane yarinyar nan a fili...i hate that..babu ruwan ki da yadda take treating dina ok?..mugun hade rai nayi,yace
im serious,sosai muryansa ya nuna alaman ranshi ya baci ..A zuciye Na fauce jiki na dan wasu xafafan hawaye naji suna shirin sauko min cikin dauriya sai ban sake na barsu ba Iya dauriya sai na daure,nace asad Kace Babu ruwana da yadda take treating dinka?are serious?yamin shiru..araunane nace..to meye nayi na abun jin haushi anan..ko bacin ran carmilan yafika maka mutuncin ka
Ne?..sam shi baison jin murya na ahaka sai ya dauke kansa
Ya lumshe idanun sa chan ya bude su akaina yana ciza labba Yace nadra yess ni banaso
...take na dakatar shi ban barshi yay dogon sharhi ba, Murya na a rarrrabe Nace dashi its ok.. fine..Kayi duk abunda kaga yafi maka in kaga dama ka tube tsirara ka bata bayanka tayi ta doka i .... dont.... care.. nayi saurin boye hawaye na cikin sauri na bude motar a fusace na sauka,bai biyo ni komawa yy yana mai maida kansa kan seat din motar ko kulani bai yi ba.

Wasa wasa mukayi kwana hudu muna daure fuska ma juna,da kyar shi ya sauko ya fara min magana sama sama ina basarwa yana basarwa alaman dai baxai ban hakuri ba nima banga dalili guda da zaisa in ba shi ba..

Haka muka cigaba har exams ya rage ana washe gari za afara,Makaranta ya nitsu kowa yay exusting kansa da karatu.

Muna fitowa nida asad zamu gida,charaf sai naji an wani cahfko ni an damke hannu na wani gaf kirji na ya buga,tun kan nafarga naga waye sai naga Asad ya hatsala da mugun hanxari ya juyo ya kwace hannu na yana mai tura ni bayan sa a  kamar wanda akace zuciyar sa ne ni kuma aka taba..,ganin yadda Asad yy reacting azafafe yasa noah yay wata shegiyar dariya yace woah bro calm down,just tryna catch ur attention..nasan in ba ita na taba ba bazaka saurare ni ba,sai ya dan leko cike da wasa in a simple wavy pose yace min hy preety?naja tsaki na hade rai..

"What do u want?asad ya masa tambayar batare da ya sake fuska ba.

Noah Ya sake yin dariya mai kulawar ganin asad yaja tsuka ya kamo ni zamu bar wajen sai yayi motsi  da sauri ya sha gaban mu

babu wani bata lokaci ya fidda wani special yellow and black card katin ya hadu dan ko jikin sa ma da logo mai dauke da kan kwanrangwal,bones da adda guda biyu akayi masa kwalliya..

Mannawa yyi akan kirjin Asad yace
Pls be my quest...
Daga nan bai sake tankawa ba yyi hanyar sa,.

.Asad kuwa tunda ya bude katin ya karanta sai ya finciko hannu na muka shiga mota munyi rabin hanya amma baice min komai ba..

Nikuwa nayi tunani kala kala danaga hnklin sa ya koma kan driving sai na shammace shi na dauka na bude card din na shiga karantawa"..katin gayyata ne bucanners night party ashe agoben bayan first exams din mu wai shugaban makaranta yace xai yanta club dinsa abasu cikakken licence kamar na carmila...

Its a hallowen party da horror mask ma za'aje kuma da dare ne karfe 10.30pm za'a fara..sai nayi shiru araina nace tabb,wani jifa nayi da katin naja karamin tsuka da kamar Asad baxaiyi reacting ba sai naga ya dage abun sa ya adana..na kasa daurewa nace me kake nufi ne?xai yi magana na dakatar da shi a dame nace Asad bazaka je wannan wajen ba
Is late,and is a party

Ransa adan abace Yace yess nadra its a party shiyasa dole naje..

Wani Horn ya danna mai karfi da cika kunne dan ya dada kular dani da wani irin fichaka ya murxa striing ya shigo haraban gidan yyi parking,ko in kalle sa na sa hannu na bude kofar ina fita ya biyo baya na da sauri ban hankara ba naji an wani cahkumo arms dina anyi dani gefe tare da manne ni jikin bango...wani zazzafan nunfashin bacin raine ya kufce min Asad yaso mu hade ido amma na kau da kaina naki sam kuma babu alaman fara'a a tattare da ni

Araunane..."Yace nadra zan je partyn nan i swear to u zanje.

Toh Bahalin in daure abunda nake ji araina kuma Nasan in nafitarr da abunda ke rainan mama dake cikin gida ma zata iya jiyo hayaniyar mu,wani irin shakurarren kuka na fashe masa da shi mai karamin sauti mai kuna..sai naga ya bata ransa sosai bai iya daurewa ya jawo ni muka koma ta bayan gida can tawajen gidan engine din generator

Anan ya manne ni ajikin sa yana mai sauke nunfashi yana kuma sauraran kukan danakeyi..

Sanda nayi me isata na shiga bori,"na ce ni kasake ni,ya kura min idanun sa na tura hannun sa ajiki na amma baiji da ya kyale ni ba.

Yace ndy Wai meye damuwar ki ne in naje din?Nace dashi babu,sai kaje ni babu ruwana wallhy,hawayen daya sauko min sai nayi saurin sharewa kallo ya dada bina dashi kamar wanda nake kashe shi duk nasan baison yaga ina kukan ne

Ya matso zai kama hannu na na fauce a zafafe,jikin sa a muce yace nadra kiyi hakuri mana
Wallhy zanje partyn nan..u need to calm down i need u to..pls

Idanuna kamar zasu fado kasa  wajen harara cikin shessheka nace baxan taimaka makan ba,ina ruwan ka dani?..ina dama cewa kayi na fita a damuwar ka?cike da bacin rai nace tokaje kayi partyn Asad,kayi duk yadda kaso i...dont... care anymore

"Zaka yi saurin fahmtar cewa Baiji dadin cewa hakan danayi ba dan Idanun shi take sukayi ja sai yji yarasa me ke masa dadi a hankli ya dube ni yace "nadra U dont care?..nace eh...yace toh why r u crying meyasa hakan yake ci miki rai nadra... A hatsale nace ina ruwan ka? nima bansani ba,kai da kasani mekayi?..
look ni daki fa zanje kuma kana bata min lokaci 

Ya tattaro nunfashin sa da kyar yace wait.. Naki na kulasa,da karfin sa ya tarkato ni jikin sa ya matse ni,hawaye na sauke a raunane ina jan nishi tun kafin na tsaida numfashi naji sautin muryansa cikin yanayin karkarwar da karayar zuciya yace"...nadrah,pls am sorry..ban barshi ya idar ba na fashe da wata misiliyar kuka mai taba imani, cikin kukan nace mishi nifa babu ruwa na kaje inda zakaje kawai..ina ruwa na da rayuwar ka?"besides who am i to u?just let me go ..i dont wanna fight u anymore.. im tired..

Langwamewa yyi Kamr xaimin kuka..duk jikin sa sai yyi sanyi,sai Ya juyo dani da sauri ya maida bayana jikin bango yana duban cikin idanuna.."my answers are right there in his eyes,yau Asad ya soma amincewa da cewa so na yakeyi kamar ya mutu..har kokari yake ya hada goshin sa danawa dan naga hakan a idanun shi amma sai naki sam na sauke kaina kasa na kau da kai..

da kyar da fitina na bashi hadin kai sai dai  ban barshi ya kalla cikin idanuna ba dan sosai na runtse su kuma naki na kalle shi sam sam...wani xaxxafan nishi yake saukewa a hankli,saukar dumin nunfashin sa akan fuskata na dada zautar da ni,nd with each strike sai nakejin ina dada samun bugun zuciya akan sa....amma da na tuna carmila wani shaukin kuka keci araina wanda ni kaina bansan dalilin sa ba

Kamar da gaske Asad ya maraice ya susuce ajikina muryan sa kalan tausayi cikin lallami yace..."Nace kiyi hakuri ko?..nifa ba fushi nake da ke ba ranar da wasa nake miki masifan duk dama ke kika bata min rai, nadra meyasa zaki tsane ta?,..bby..nadra meyasa bazaki fahimce ni bane akan wannan maganan?a hnkli Nace nidai ban tsane ta amma inde akan wancan yarinyar ne bazan fahimci komi ba Asad,she is ruining ur tots...u look like a coward in front of her.. kaga yadda ka dawo baka da tunani kuwa?...nasan ko partyn nan zakaje ne sabida ita ne..bai kula da yadda nayi maganan ba...wani rungumo ni jikin shi kawai yay dan ya dakatar da kukan dake so ya kufce min mai cike da damuwar sa

muryan sa a sarkfe har yana karyewa yace..baby shuuu, shuusshhhhhh,banfasa ba ya dada matso ni har kunne na yabi da lips dinsa ta inda vibe din sexy tone din nunfashin sa zai kashe min jiki na sosai...cike da tausayi sa lallami yace nadra idan dan carmilla ne xan je wajen xan gaya maki wallhy ban taba boye miki komi ba,amma am sure ba dan ita bane,im going there bcos its a party kuma na miki alkwari i wll do just as u say muddin kika bani goyon baya...i cant do this if ure sad..baxan iya ba..i hate when u act like this with me...kuma gaskiya ina so inje...so wll u me help me pls?

Kallo daya na masa na dauke ido,na maida kaina akasa na shiga goge sauran hawaye na...Shirun danayi masa tsawon minti 10 ina sauke ajiyayyun numfashi yasa ya fahinci amsar sa,is true nd clear to him that am weak,and very much in love with him..wani tausayi na ne ya mamaye ransa...ya dau lokaci yana sakawa yana warewa a kwalwalr shi game dani.

Shidai baya gane komai but He wished ba haka yake treating dina ba,dadin karawa da yau yaji aransa kamar he feel the same for me,yasan im going tru alot akan sa,tun da muka mallakin hankalin kanmu ya fahimci ko mama bata shan wahalan da nake sha akan sa..that makes him so emotional  matsayi na a kullum karuwa yake a zuciyar sa amma bai sanda haka ba tukuna,ya lura bani da tacewa"is like i want to say no and yes at same time..da kyar ya danne abunda yakeji aransa ya shiga min wasan dole tun ina yi a fushi da kuka har sanda yasa na murmusa.

Daya ga hakan wani ajiyan zuciya ya sauke kamar an yaye mashi nauyi azuciyan sa gashi sam Yaki ya sake ni wai sai na amsa shi inba haka ba bai damu kowa yazo ya ganmu hakan ba..

Ganin zai bata min lokaci cikin harara nace mishi na amince din amma in ya yarda cewa ko minti 15  baxai dauka awajen patyn ba,ya karaiyaye min wuya a shagwabe cikin magiya yace 30min pls ...nace nooo..ya rusuna har kasa kamar maraya yace 45minuts to..

nayi tsuka nace i said 15 kana kaiwa 45?yace in kara ne?to 1hr..na share shi..karar bude horn yasa muka farga its obvious kawu ne ya dawo so da sauri yaja ni muka wuce muka shiga gida inda muka ci karo da Mama a falour ita kadai hanunta dauke da remote tana sauya channel

Duka muka rusuna mu kayi gaisuwa ta amsa da fara'a ta,inata faman kare fuska ta dan karma taga alaman nayi kuka ko wani abu,asad daya lura da hakan sai ya kau da hanklin ta akan surutun banza har na sabule na haura sama na barsu batace min komi ba.

Ta waya muka karashe maganan na bashi damar zuwa akan 45min
Yamin alkwari Yana gida

Karfe 10 dai dai na daren ranar sai juyi nake ni kadai akan gado duk abun duniya ya dameni
Jim kadan naji saukar faint knck abakin kofa ta.

A firgit Na taso babua bata lokaci mentally thinking of who cud that be?ina budewa kuwa ya turo ni ciki muka mannu da wall alaman baison kowa ya ji motsin mu

Idanun mu muka xuba akan ma juna
Na dade da sumewa ina kallon dressing dinsa,shikuwa da alamn duk hankiln sa akan zaro idon dana keyi yake  sai ya shiga sakar min murmushi mai taushi

"Bakin wandon jeans ne wanda ya dan zazzago ta kasa kadan tayi masa cas cas ya rike face cap fari kat to match da pure white naked cashmir shirt daya kama structun sa shi wanda ya dada bashi irrestible look

Na daga ido sai naga bakin leather jackect a kafadun sa ya rataye...wani kishin sa ya sa na sauke ido na dan dole nayi murmushin yake..,ajiyan zuciya shima yyi yana kallo na a hankli ya dago haba na ya kure min idanun sa,".. Ganin shirun baxai kare ba gashi ni bana son kallon daya kemin din dan bakaramin kishin sa ne yake hauhawa na ba," cikin dauriya na ce har xaka tafi?ya gyada kai cikin sanyin jiki zai shafa gefen fuskata na slowly na kau da kai ina tura sa gefe,"..nace Asad dan Allah kar ka dade..dan ya kaucar da yanayin yadda nayi maganan,a wasa ya dafe kirjin sa yace ok wify...

  Na juyo cikin hararar wasa a baxata ya taho ya dora min kiss mai tsayi a goshi na har sanda na riko arms dinsa batare da na sani ba,ya dago ni queit seriously hey that...pulchtride.. will u take care?sai naji wani kunya da sanyi araina na dago a slow ina kallansa cikin sanyin jiki na gyada mashi kai..wani kiss din ya taho zai sake min na tura sa na ce Asad bana so...dariya yayi mai sauti yace ok 45min i promise...tun kafin nace bye ya juya ya fita da sauri abunsa..

Na dade a tsaye ina bin kofar da kallo cahn Cikin wani irin karayayyn yanayi mai mugun saka tsumayi da tsoro na koma bakin gadona,a sadade na sulale ina me jefa kaina tunani sai na lumshe ido na sosai ina sauke ajiyan zuciya da wasu irin dogayen numfashi...

Only Allah knows why,bana iya bacci in Asad yana waje yau cikin ikon Allah sai gashi wani irin bacci mai nauyi ya sure ni ban san ma inda nake ba.
HABA MUTANEN ARXIKI WALLAH THE VOTES R TOO LOW,500 reads sai 100vote?im seriously baby crying myself is nat fair amma bakomi zan fara tsallaken rana toh tunda dadin yyi yawa
#hmmmmmmm Today kam am queit,banda tacewa but im sure ma fans will say alot..Am All earrs....whats gonna happen in the party?

TALLAH!

_"uhm uhm ina yan mata da uwaye  masu bukatar karanta littafi domin samun karin ilimin sanin  istimna'i wato(masturbation )?nau'oinsa,illarsa na fili dana boye?...labarin kudi kumbar susa ya kafa jigo ne da hikiman Allah,zamantakewar Aure,yarda da qaddara da abunda ya shafi sihiri da son duniya'kks littafi ne mai tsada badon kudin da za'a saka mashi sai dan darasun da zaizo da shi wanda suka fiye faruwa agaske shin ko kina so ayi budirin nan dake?TOH👇🏿.._

_MAZA GARZAYA KI NEMI KUJERAN ZAMAN KI A KKS PAID GRP,domin kuwa labarin Kudi... kumbar susa zai fara zuwa ne a ranar Ashirin da shida ga watan mayu 26/5/2020 AMMA Kofa a bude take ga duk mai bukatar biyan kudin labarin iyanzu".FARASHIN SA #300ne kacal,zaka iya biya direct ta ACCT  0152983148  @surayyah muhammad suleh GTB ko VTU transfer ko mtn digits ta wannan number 08060712446 sai ka tura shaidar biyar ta 08036651119 domin Asanya ka a grop din!..hey masoya  abun alfahari inbada kaina a sare domin ku inje gida ince ya fadi😁kuyi kokri ku shigo adama daku don tsabar kauna da nake muku yasa bazan so ace wannan labari ya wuce masoyi na ko daya ba😆ITS GONNA be WORTH..insha Allah!_

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top