14:mindset

_14...mindset._

Dear nusaiba kabeer,thanks for trusting nd being the first person to download complete qur'an from ma said favourite sheik abdlrasheed alfasy minshary"she said its wow..i was so happy for her..pls remain blessed..nd jaxakallhu khaairan

...blushing shyly na matso kadan na sauke masa peg a gefen kuncin sa shima juyawa yyi tare da sauke min numfashin sa akan fuskata yana gogawa kadan kamar wanda xai cinye ni,karin bugun zuciya yasa na dan dafe kirjin sa zan matsa sai naji ya riko waist dina da dayn hannun shi.

Wani heavy knock daga bakin kofa shi ya fargan damu muka juyo shikam ko damuwa baiyi ba sai nayi saurin ture sa zan sauka agadon bai sake ni ba a firgice kuma a hankli nace,"asad pls let go..bakajin knock?..yay min shiru ya matse ni jim kadan mukaji sallaman mutum akan mu.

Hannun sa cikijn nawa yana mrzawa Muka waiwayo a tare,Hade ido da mama da mukayi yasa Asad yyi sauri A dan dolen sa ya sake ni,nima na mike na tsaya a tsakure inajin kirjina na mugun bugawa,in shock mama ta zuba mana idanun ta,wani shirun minti 3 tayi tana kan kallon mu tana kuma kare ma yanayin dakin kallo,evrything looks suspicious ga gadon abarbaje gashi babu wani kayan arziki na cahn chan ajikin mu,yadda tayi da fuska zaka san sam bata ji dadi ba yanayin fushi ya bayyana sosai...

Asad ne ya motsa zaiyi magana ta tsare shi a hatsale tace wai meke faruwa anan?sai yyi shiru bai amsa ba mama ta juyo ta dube ni tana maida min muguwar kallon tuhuma, saurin maida kaina kasa nayi dan ko kayan dake jiki na ya isa yasamin fargaba da bugun zuciya,tace nadra mekike anan da sassafe?meye ya faru?da kyar na dago cikin sanyin murya nace mama dama dama na kawo ma Asad abu ne,da sauri ya cabe maganan yace mama nine dama na kirawota,a tsawace mama ta juya tace mashi "shut up nacr kamin shiru...yanayin ta yasa Sai da duka muka hadiye yawu,"..

Tace baku da hankali ne? since when has this been happening,Asad ya mike daga zaunen dayake yace mum pls dont over react ba wani abu takeyi anan ba,"..da wani irin harara mama ta tsare shi sanda yay shiru ya kasa cigaba,tace so what? ya dace na ganku tare a wannan lokacin kuma acikin dakin baccin ka?wani wasan banxa kukeyi da zaka rike mata hannu in bani na shigo bafa me zakuce da abban ku?to yanzu ka dube ka dube nadra,ko wani kayan arziki babu ajikin ku kun kyauta kenan,murya na na tsananin rawa nace mama dan Allah kiyi hkri,
Ranta a bace matuka ta dube ni,hanya kawai tayi min muni da shi,a sadade na taho na fice da sauri na barta da shi a dakin,fitan da nayi ahakan yasa Asad ya hade ranshi sosai mama bata fasa ba ta cigaba da yi masa masifa,
"nagaji da irin maganganun da kake jawo min agidanan,in auren kuke so ba sai ayi muku ba?wannan dabiar ai abun tsoro ne,Asad da hanklin ka zaka kebe da mace a daki har kana riko ta jikin ka?nadra muharramar kace?ko ka manta shedan ne,wato so kuke ku jawo mana abun kunya ko?..im higly dispappointed in all of u.,.yy tsam baice uffan ba har tagama ta rufe bakin ta tana kallon sa shikam ma gyara tsayuwar sa yyi kamar me shirin barin wajen in few moments,yin hakan dayayi yasa mama ta dada jin zafi sosai aranta a zafafe tace".. im talking to u ya bazaka ansani ba,ya ce mama bawai bazan
Amsa ki bane ai naga har kinyi concluding ne bayan ke kinsan babu abunda zanyi ma nadra,mama nifa bana hakan kuma ai na gane kuskure na nadra baxata sake ba,mama kiyi hakuri pls,tunda haka ne baxamu sake ba, nide gaskiya bana son ke dakan ki kirika min wani iri kallo kamar bani da tarbiya,..for sure i wll neva do that ai kema kinsani ko?tsaban takaici hmm kawai mama tace alaman bata qamsu ba,tace nidai bana son wannan salon naka,baiyi kama da na me tarbiya ko addina ba yau yaxama rana na karshe da zan ga haka atsakinin ku...asad kaine babba so am i clear?yace yes,tace ka shirya ka fito yanzu bari inje in same abban naku,har ta juya
Sai ya dan lumshe ido yace zaki je ki gaya masa ne?ta juyo cikin banka masa harara tce tsoron me zakaji ai in nafada ma rufin asirin mune,kaga sai asan nayi daku..bai sake tankawa ba yay shiru abunsa har ta fice..

Nikuwa ina daki na babu abunda na iya
Yi sai jeka ka dawo duk fargaba ya cika min xuciya da nacin ran da mama ta nuna,tsoro na inta kai maganan wajen kawu fa?..qani girrrr naji kamar an cure min hanjin ciki na a tsorace nace na shiga uku..kawu zaiyi fushi dani..me zance na wanke kaina?

A haka har na bata lokaci Banfito ba sai ana daf zamu wuce makaranta,nasan kawu ya wuce offis dan haka na taro karfin gwiwa slowly nake takawa kamar wanda kwai ya fashe mata har na isa kfar babban falo wani ajiyan zuciya na sauke nayi sallama a sadade,muryan mama naji sai na shigo wani muskiliyar kallo ta bini dashi kafin ta hade fuskan ta,da kyar nattaro nitsuwa ta na sadda kai a kasa zauna a kusa amma bata sake kallo na ba

Wani shiru ne ya ratsa wajen kafin can nacem."Mama dan Allah kiyi hkuri,nasan nayi laifi insha Allah bazan sake ba

Tayi shiru abun ta kamar bata ji menace ba Can  kasan makoshi tace
"Tashi kije ki sauya wannan kayan baxaki je ko ina da shi ba,kuma ki rage pawder dake fuskan ki wai meye haka ne nadra?..nayu sauri na mike tsaye gwanar tausayi nace to kiy hkri zanje..a sace na dan dube jiki na dama english wears ne riga da skirt sai nayi rolling

Ba musu na haura na koma daki after 10min na fito da abaya baki da dan guntun hijabi ajiki na..tun kan na karaso gare ta mukaji sallama daga ido nayi sai ga asad shima ya shigo cikin kammala shirin sa daf a baya na ya nemi waje ya zauna"...nikam cike da rakubewa na zauna kasa kusa da mama tunowa da ko ina kwana bance mata ba sai nayi gyran murya cike da fargaba na gaishe tan ba laifi ta amsamin amma ciki ciki,chan ta daure dai tace har zaku wuce?nace eh,tace toh...daga nan batasake cewa uffan ba Asad yana ta kallon ta ya tabe bakin sa,"kamar bani na furta ba a hnkli na juya kalar tausai nace mama?kallo na kawai tayi nace mama kinyi hakurin na miki magana baiki ce min komi?da ajiyan zuciya mama ta tare ni,"to ni me zan ce daku nadrah,ai kun girma ne shiyasa kuke abunda kukaga dama..quiet unserious Asad yy kwafa cikin rolling idanun sa yace haba mama nafa baki hkri nima,.bata bari ya karasa ba ta wani banka masa harara

'Tace Nidai na gaya muku kar ku kuma,ke kuma bawai bakiji ba?toh ni nasan matakin dazan dauka akanki,ku wuce ku ban wuri bana son wani magana

Yddda ta bata ranta sosai yasa duka muka kama kanmu muka wuce sallamar mu ma bata amsa ba

Araina Naji tsoro sosai,Asad kam ko ajikin sa har muka isa schl.

Normally muka cinye ranar muka dawo gida Asad bai je brain box ba sannan bai kula da inda carmilla campbells take ba.

Hakan da yyi ya dada sauke min tension,amma da muka dawo sai na lura babu abunda ya sauya ta fannin mama.

Sosai ta dauke mana wuta,ko ince ma ni don Asad kam shashantar da maganan yakeyi ko tana maganan sai ya nuna awajen sa baiyi tsauri haka ba

Haka mukaci kusan sati biyu a wannan yanayin na dawo sam bana jin dadi agida,in munje schl ne nake samun sukuni sabida kaurace wa damuwar su carmilla dana saka Asad yyi ya mugun sawa bama shiga wani hayaniya.

Da kyar mama ta yafe min,bisa hawayen danayi ina rantse mata bazan sake shiga dakin Asad ba.

Mama ta tausaya min data ga ina kuka kuma na nuna ma damu da bacin rantan,araina nasan taki ta fada ma kawu ne sabida tana matukar kaunar mu duka,maybe da ta fada ko schl din bazai yarda mu karasa ba hala sai dai yau yace zai mana aure..this is the first time mama ta boye ma kawu abu hakan kuma bakaramin damun zuciyarta  yayi ba sabida mama bata iya boye ma kawu wani sirri sam sam hakan yasa na dau abun da gaske nima da kaina na kaurace ma Asad har sanda na shawo kan mama ranar ma da kanta ta kirawo ni kitchen babu kowa sai no da ita a lokacin zulai taje kasuwa shoping cikin nitsuwa da hikima ta min nasiha Tace nadrah,bawai zan rabaki da dan uwanki bane,ina guje muku sharrin shaidan ne.

Ki duba kiga yadda kawun ki yake,yau in wani abu ya faru tsakanin ki da asad me zan ce masa?,da wani ido zan kalle shi nace yar da ya bani amana ce na tarbiyan tar haka..kema kinsan ai bakuyi min adalci ba.

Shi namiji babu ruwan sa,kece zaki duba ki kiyaye martaban ki...mace an santa da tsada ba wai zaki sake ma namiji ba..yau ko aure na muku i still expect u kija mai aji da kanki wajen nuna masa ke mace ce zinariya mai wuyan samu..mama ta kawo ayoyi da hadisai tamin ftawa akan su sosai jiki na yayi sanyi"na saka hannu na share hawayen dake biyo kunci na Hakuri na dada bata na kuma Jaddada mata cewa bazan sake ba.

Abu ne mai wuya in rabu da Asad amma da shike naga gaskiya karara cikin maganan mama dan dolw na na dena bin hanyar dayabi dakin sa.

Zamuyi magana normal ayi hira amma duk wayon sa bana yarda naje dakin sa"sumtimes dan ya kular dani sai yace min nazo na kirga kwalayen taban daya sha dan na ji haushi sai nace zan je amma duk da haka sai na daure na kama kaina

Sumtimes Nakan ce da shi babu kyau mukebe..amma daga nace hakan zai bata ransa.

Har nagaji na dena fada dashi na soma masa magiyar cewa to ko dan mama yayi respecting haka...Da shike shi kansa yasan abu mai wuya ne wajen mama ta rufa mana asiri sai kawai ya share maganan bai sake cewa komai ba

Wasa wasa har Nayi wata guda bana samun shakuwa da Asad kamar yadda muka saba ada chan

Shikuwa kamar an bude masa hanya daga mun dawo,zai sabule ya fita yawon sa cikin dare wani bin sai dai naga tex din shi inzai fita da in zai dawo

Thinking of how he is behaving at parties,da kuma yadda yake hndling cigarettes a dakin sa ya kusa galabaita mun zuciya..haka dai na daure

A schl bani da wata matsala sabida ta yadda banyi tsammani ba Asad ya cika min alkwari na na fita a harkan brain box da ita kanta carmila campbells,samsam ya dena shiga harkan ta da  damuwar ta kamar wani me aljanu,..a fannin brain box kuwa Har aci a kare wani bin bama sanin me akeyi dama fatima ce take kawo mana labarin abunda ya wakana toh Tun abun bai dame ni ba har ya zo ya fara damu na,sabida da abun yayi tsamari sai na lura a ko yaushe fatima ta fadi magana me ban tausayi game da carmilla sai Asad yayi ta mata tambayoyi..

Fatima tace mana Yanzu gaban tsakanin ta da noah ne...

A zahiri competion din ya dawo tsakanin club biu,
Brain box da kuma buccanners altho wai shugaban makarnta bai bada bucanners cikakken licence kamar brain box ba.

A yadda fatima take bayyana mana,tace tsakanin carmilla da Noah babu sauki kuma noah ba karamin bada carmilla ciwon kai yake ba.

Abubuwan da ta zargi asad da cahn akan yanayi dan yaci mata mutunci sai gashi kaarara shi noah yake mata kusan kowa a schl din yanzu ya fahimce haka

Asad yakan dade yana jimamin yadda carmilla zata na coping da abun aranta amma sabida ni sai ya kaucar da tunanin sa akai ko acikin wasa bai taba cewa xaije ba.

But deep within him yana jin tausayi sosai musamman in muka ci karo ko yagan ta da kawayen ta suna karatun fanfalaki,duk da bata kula shi itama amma yakan dau lokaci yana tuna ranar datayi masa kuka tana fada masa damuwar ta...
#wow..Allah sarki surayhms yau da xanyi editing shafin nan sanda nayi murmushi sai na tuno da lokacin ina posting page 4 wata tace min relship din nadra da asad bakomai bane illa ina amfani da dama na ina bata tarbiyan yara,wai mace ta xauna akan cinyar namiji al'adar hausa fulani bla bla bla,i tried my best dan in fahimtar da ita na riga na rubuta littafin nan na tsara farkon sa da karshen sa, but she judge me horribly nd unfairly irin lallai tana so ni na amince cewa ni din mai batawa ne babu wani gyara a rubutu na abun mamaki har tace dama haka nake hmm..thats life..ko ita bata sani ba shafin nan na ajiye ina kuma kallon sa a time din dtake korafin, ni bance yanayin shakuwar su yana da kyau ba,but abunda ke faruwa ne azamnin nan nd i knw i will address this issure definately..so pls my ppl kuyi hakuri kudinga yi mana uzuri in muna rubutu,wallhy nidai ba kara zube nake shirya littafi ba and most writers sai sunkai page 10,20 har fiye kafin suke fara muku posting..so just follow inkaga abunda beyi maka ba ka aje korafin ka in kaga an kai karshen book ba a kawo gyara ba sai ka fadi duk abunda xakace ma writer..but is not fair to judge us like taht..gaggawa fa aikin shaidan ne..Allah dai ya sa mu dace Ameeen.

Tallah💃
_"uhm uhm ina yan mata da uwaye  masu bukatar karanta littafi domin samun karin ilimin sanin  istimna'i wato(masturbation )?nau'oinsa,illarsa na fili dana boye?...labarin kudi kumbar susa ya kafa jigo ne da hikiman Allah,zamantakewar Aure,yarda da qaddara da abunda ya shafi sihiri da son duniya'kks littafi ne mai tsada badon kudin da za'a saka mashi sai dan darasun da zaizo da shi wanda suka fiye faruwa agaske shin ko kina so ayi budirin nan dake?TOH👇🏿.._

_MAZA GARZAYA KI NEMI KUJERAN ZAMAN KI A KKS PAID GRP,domin kuwa labarin Kudi... kumbar susa zai fara zuwa ne a ranar Ashirin da shida ga watan mayu 26/5/2020 AMMA Kofa a bude take ga duk mai bukatar biyan kudin labarin iyanzu".FARASHIN SA #300ne kacal,zaka iya biya direct ta ACCT  0152983148  @surayyah muhammad suleh GTB ko VTU transfer ko mtn digits ta wannan number 08060712446 sai ka tura shaidar biyar ta 08036651119 domin Asanya ka a grop din!..hey masoya  abun alfahari inbada kaina a sare domin ku inje gida ince ya fadi😁kuyi kokri ku shigo adama daku don tsabar kauna da nake muku yasa bazan so ace wannan labari ya wuce masoyi na ko daya ba😆ITS GONNA be WORTH..insha Allah!_

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top