BABI NA TALATIN DA HUDU
Har wajen 10:30pm Sakinah tana waje tana soya awara, tun yan yara na zuwa har suka kare ya koma sai samari ne kawai wajen suke siya, dama mutum daya ce keyin awara a area dinsu kuma yarinyar ta dade da yin aure, it was a pleasure to see Sakinah has started it again.
Kowa yazo sai ya kalleta irin kallon nan na yan duniya amma kwata kwata babu fuskar ma dazai mata magana, ita kuma duk lissafinta ya jagule tunda tayi waya da Aunty Halima. A haka dai tana zaune tana ida soya kaskon karshe saiga Ya T yazo wajen hankalinshi a dan tashe. Kallonshi tayi da murmushi plastered on her lips, patting the stone beside her. He sat down.
"Sakinah me yasa baki tafi gida ba? 11 ta kusa fah. Dare yayi sosai kinji? Karki kara kaiwa har haka baki tafi ba." Da alamu bai dade da shan abun ba, dan kuwa ga idanuwan nan sunyi jajir dasu abun babu ko kyan kallo.
Gulping down tayi, dan tasan a single inappropriate word can trigger Ya T's anger ba kamar yanzu yadda yake jin kanshi dinnan. "Ya T Inna ce tace I should make sure I sell everything out kafin na koma mata, if not sai ta ci ubana." Itama tun tuni ta gaji da zaman wajen nan, banda sauro da zafin wutar dake dukanta ba abunda ke zuciyarta has surpassed everything.
"Ita Innar tace haka? Hada kayanki mu wuce gidan. Wannan matar tana neman wuce gona da iri!" Zumbur ya mike kamar wanda jefa da dutse ko wane abu. Sakinah sauri tayi ta kwashe awarar kafin ta tattara komai, babu gardama a haka shima ya tayata daukar kayan kafin suka kama hanya, dayake dama bakin titi ne.
Suna isa gidan suka iske Inna da Baba tsakar gida, da alama maganar rashin dawowar Sakinar yake mata dan kuwa tana ganinsu ta sauke wani numfashi. Wajen sanwarsu Sakinah ta nufa dropping all the things there and she proceeded to where Inna was and handed her the money. She held up the plate containing the last churns of awara a ciki tana nuna ma Inna.
"Na saida ta 1250, saura ta 150 ta rage Inna." She informed kafin ta nufi hanyr da tabarma take shimfide ko dan taci awarar, tunda she couldn't eat in public.
"Uban me kike tunanin yi? Sakinah badai sauran awarar har ta 150 zaki cinye ke kadai ba, wallahi kina da bukatar na saita ki cikin gidan nan yarinyar nan." Wuf ta isa wajen da Sakinah take zaune saman tabarma takai awara daya bakinta, duka da awarar da plate din ta hade ta karbe.
"Haba Inna banfa ci abincin dare ba, dan Allah ki bari inci," Sakinah ce ta dago da ido tana kallonta, trying to emote her plea with her eyes.
"Uban awara zakici ba awara ba, yanzu Sakinah tsabar rashin mutunci halan wani saurayin kika bi kukaje kukayi iskancin ku ko awarar baki saida ba shine zaki ragoman har ta 150 kuma kice zaki cinye? Na rantse da Allah saidai ki kwana da yunwarki dan ubanki!" Wani wawan duka ta kai mata a baya and Sakinah had to let out a yelp. It was too much.
"Innalillahi kai Inna, yanzu duk azabar danasha ta sauro da zafin wuta mugun abun da zaki fada kenan? Kuma wai ko shi jarin awarar ba kudin da nayi aiki bane aka biyani? Kawai dan zanci awarar 150 shine kike tada hankali? Kai Inna. Wai ni tsaya ma, tunda dai awarar 150 zaa hanani ci, ba kince muje aikatau ba saboda da kudin zamuyi ma kanmu kayan kitchen ba? To a bani kudin aikina tunda dai nasan koda bakar jaba nake tsafi baki taba bani ladar tuyar awarar nan, 150 ma an kasa balle." Ido runtse Sakinah take jero bayani, in ranta yakai dubu to ya baci, tunda dai Inna tace babu mutuncin, babu wannan compassion din, to aje a haka.
Koda Inna taji maganganunta saida gabanta ya dan fadi, tasan dama Sakinah was always like that, amma tunda ta dawo ta zama shiru, da da ne wannan abun data fadi saidai kawai ta fashe da kuka amma yanzu idanunta kem ta maida mata martani. Lallai kam Sakinah Abdullahi Bello is back!
"Ke dan ubanki ni zaki kalla kice in maido maki da kudinki? To wallahi uban kuturu yai kadan bare na makaho, kudi na cinye. In kin tashi auren a kaiki ba ko tsince that will be the least of my worries, daga Allah ya rabani da ala ka-kai? Awara ce dai baki cinta, kudi kuma ban badawa yar iskar yariny kawai." Kafin Inna ta bude baki Sakinah ta warci plate din awarar nan ta ruga daki tana furta.
"Wallahi ni kuma sai naci, kudi kuma na rantse da Allah Inna ko da sata ne sai na dauki abu na." Gam ta rufe dakin tasa sakata yadda ma Inna bazata biyota ta nada mata na jaki ba.
Wani irin wulakantaccen kallo Baba ya ma Inna flashing as he shook his head, "Ina fatan you've seen the hatred Sakinah has for you through her words and even her eyes? Allah ya tsayar kanki." Yana fadin haka ya raba ta gefenta ya wuce.
"Dama tsayuwar da nayi nan dan ku gama ne, karta kara kaiwa karfe 10:30pm waje, iyakarta karfe 9 inba haka ba zan hana uban kowa siyan awarar sai muga tayi." Yana fadin haka shima ya kama hanya ya fita gidan ba tare da ya kara koda kallon inda Innar take ba. Leaving her rooted to her spot.
•
Two Months Later.
Nothing has changed, not even an ounce. Sakinah ta share tsawon wata biyu a gida kuma kullum sai tayi aikin gidan nan kaf da safe, zuwa yanzu Inna ta daina bata abinci kwata kwata, dan yadda suke zaman kamar annabi da kafiri. Kullum Sakinah itace zuwa shago cin bashin garin kwaki, ko kuma in taje suyar awara ta diba taci in wani saurayin yazo yayi mata doubling kudin sai ta maida ma Inna. Tun Baba yana masu magana har ya gaji, dan Inna was presumptuous to the point he had gave up.
Kamar ko wane dare, tana zaune tana tuyar awarar ta ga kuma kanwar Maman binta nan da aka aiko ta siya tana jiranta ta kwashe ta zuba mata. Zuwa yanzu samarin bakin titin har ma wanda ba na cikin unguwar ba duk sun saba da Sakinah, dama can tana da rawar kanta masifar duniya ce ta saka ta shiru shiru. Yanzu kuwa kowa abokinta ne, wani abun ma tanayi ne dan aje a fada ma Inna ko tace ta daina tuyar awarar tunda iskanci take tana magana da maza amma duk a banza.
Ta fara kwashewar kenan sai ga wata mota tayi parking gabanta, tana dagowa ta washe baki, he was the guy that gave her 5k last week dayazo, yace daga abuja yake yazo yin serving ne a kaduna. He was such a nice guy.
"Su Sakinah yan mata," dama haka yakan ce mata duk ranar da yakejin yan fara'ar. Kallonshi tayi da murmushi.
"Yan samari, tunda har yau kaki barin na san sunan ka."
"Wannan ba damuwa bane. Gashi nazo yau na daukeki muje kisha ice cream din as I promised amma naga baki gama ba, ya zamuyi kenan?" He asked, looking between the unfried awara and Sakinah's face that has broken into a grin.
"That wouldn't be a problem, ke Lantana yi maza ki kai ma Maman binta awarar ta ki dawo ki ida soya man kinji? Zan baki naira hamsin idan na dawo." Tun kafin ta rufe baki Lantana ta zambada da gudu domin takai wannan awara.
Mikewa tsaye Sakinah tayi tana gyara zaman skirt dinta, "Bari a dawo sai muje, Allah yasa ba dadewa zamuyi ba. Ka saiman ice cream din kawai sai mu dawo nasha a gida." Wani kayataccen murmushi ya mata.
"Baki da damuwa, yauwa muje gata nan ta dawo."
Har ta fara tafiya sai kuma ta tsaya, "To ai kauri nake kuma, ko naje gida na chanja kaya?"
"Wannan duk bata lokaci ne Sakinah, muje ba wanda ya isa ya rainaki ai." A haka ta kara jaddada ma Lantana akan ta kula fah yanzu zata dawo kafin suka tsallaka titi har wajen da yayi parking.
Tazo zata shiga gaba kenan sai ta hangi abokinshi ciki, murmushi ta mishi kafin ta bude bayan ta shiga. In a swift, she was embraced, juyawan da zatayi taga maza biyu ne a bayan, sun maida ta tsakayin motar sun mata wani irin mugun dauri.
Shi mutumin nata ya shigo motan hade da danna mata lock yana kallonta da murmushi kan fuskarshi, "Menene haka? Me zaku man?" Yau babu sturdiness dinnan, ai tuni jikanta ya dauki rawa, bata tashi fashewa da kuka ba saida taga yaja motar in a very high speed gashi yanzu sun rufe mata baki da wani kyalle, hands inta kuma were in their grip.
Shure shure Sakinah ta fara amma tunda daya ya zabga mata mari taji tunaninta ya dauke saidai bude ido tayi ta ganta tsakar bayan gari sun kulle mata kafafu da hannaye suna kallonta with eyes full of lust, bata san lokacin data fashe da kuka ba.
Thank you.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top